Showing 78001 words to 81000 words out of 184937 words

Chapter 27 - KUDURAR ALLAH COMPLETE BY FATIMA Y ADAM

21 Jul 2024

16884

yayi dubu ya ɓaci da lamarin ɗan nata,ta rasa inda ya dosa cikin lamuran sa amma addu'a ita kaɗai ce zatayi maganin wannan matsala,cikin damuwa yace kiyi haƙuri Hajjah amma ina kan maganata bazaki gane abinda nake nufi ba yanzu sai nan gaba!'yana gama faɗa ya tashi ya barta,yayin da tabishi da wani irin kallo wanda yay kama da kallon tausayi, Ajiyar zuciya ta sauke tare da binsa da addu'o'in shiriya.


Cikin iya taku da ƙwarewa akan aikinta Samira tace"dear gaskiya idan muna so musamu abinda muke nema sai kayi tunani akan mutanen gidan nan sosai,dan ta hakane kawai zamu iya fuskantar inda za mu ɗora aikin mu idan kuma ba haka ba zamuyi ta bulayine,kuma ina ganin hakan kamar wata sabuwar hanya ce da zamu kuma samun bayanai akan kishiyoyin ku, tunda duk abu ɗaya kuke yaƙin nema!'Alhaji Sama'ila yace"gaskiya Samira kina da fikira da ace aikin jarida kikeyi ko aikin bincike baƙarmin alfahari ma aikatarku zatayi dake ba, wannan tunanin da kikayi tunanine me kyau dan duk cikin waɗan da suke neman duniyar nan babu wanda muka sani, saboda idan mu ya rufe batasu muke ba!'Samira ta ja wani dogon numfashi kana tace"amma kunyi sake ai sanin su shine zai baku damar mallakar abinda kuke nema,saboda dolene kudinga sanin shirin su idan ba haka ba ku kuna zaune sai dai kuji sunyi nasarar mallakar koma meyene kuke son mallakan sa!'tsaye ya tashi yana zaga gurin cike da tashin hankali yace" me yasa bamu taɓa yin wannan tunanin ba? gaskiya mun tafka babban kuskure!'Samira tace"ai gyara shi ba Abune da zaiyi wuya ba tun da har munyi nasarar gane hakan yanzu tunanin mu zai juya ne kan masu nema wato kishiyoyin ku!' tafa mata yayi tare da cewa gaskiya Samira kin burgeni dolene nayi miki babbar kyauta dan haka na baki motar can da nazo da ita!'ido ta zaro cike da mamaki tace"da gaske kake Alhaji!'murmushi yayi tare cewa kin fi ƙarfin haka duk abinda nayi miki ban faɗi ba saboda kin kawo babbar gudunmawa cikin tafiyar mu!'wani murmushi ta saki kana tace"tabbas bazaka manta dani ba wanda sai nan gaba zaka kuma tabbatar da haka!' batare da ya fuskanci inda maganar ta ya dosa ba ya miƙa mata mukulli motar tare da cewa ki tafi da ita yanzu zanyi waya za'a zo a ɗauke Ni!' karɓa tayi tana cewa kamar na san da wannan babbar kyauta shiyasa ban zo da motata ba!'koda kin zo da ita har gida zansa akai miki kyautarki,daga haka ya tashi ya rakata har bakin motar kana sukayi sallama tana tayi masa godiya.


Wata irin dariya ce ta ƙwace mata wato shi dai mutum duk girman sa da wayonsa bai isa ya kara da hukumar bincike ba,ga dai yadda tayiwa Alhaji Sama'ila wayo da ta shiga jikinsa,tabbas duk ranar da yagano ta zaiyi matukar mamaki saboda tanayin komai da lura bata zaƙewa yadda zai iya saka kokwanto akanta yanzu ta gama da wannan ɓangaren saura kuma jin sirrin abinda ya haɗa wannan rikitaccen al'amarin ita kanta tanason jin koda sunan abinda suke nemane, yanzun nan kuwa zata turawa Oga Abdallah recording ɗin da tayi saboda tana so yanzu yaji irin babbar nasarar da suka taka, lallai tana ji ajikinta baza su ɗauki dogon lokaci akan wannan case ɗin ba saboda duk wata hanya da ya kamata su kama dan samun nasara sun kama saura waccen tsohuwar Abigirl ɗin wadda tuni Oga Abdallah yasa ɗan leƙen asirin su yabi sahunta duk wani motsinta akan idonsa ne,gaskiya Oga Abdallah ɗan baiwa ne Allah ya hore masa basirar sanin makamar aikin sa shiyasa duk aikin da ya tunkara sai yaga bayan sa.


Tun daga ranar da ta kwana a ɗakinsa bata kuma bari sun haɗu ba yau kwana biyu kenan da faruwar al'amarin,ta ɓangaren sa kuwa yanzu so yake ya haɗu da ita saboda manyan tambayoyin da suke ƙunshe cikin zuciyarsa,wanda a yanzu ne yake ganin ya dace ya sakata cikin wannan al'amarin,amma taƙi bari su haɗu ko meye dalilin ta oho,


Yau rana ta uku kenan rabon da yasaka Bintu cikin ƙwayar idanunsa,haka nan yakejin son haɗuwa da ita saboda aikin ɓangaren ta da yake son fara gabatar da bincike akansa(hmmm su Abdallah manya daraktan wayo kayi sake dai fans ɗin ƙudurar Allah sun gano ka)

Yau ɗin dai kamar yadda tasaba haka taje ta jera masa dinnar ɗin sa kana ta wuce tayi wanka tayi sallar isha tare da shafa'i da wuturi,wata kyakykyawar riga ta zura iya cinya mai shegen kyau wadda ta karɓi jikinta tamkar kasace ta ka gudu, dogon gashinta irin na fulani da sirkin Larabawa ta haɗa ta tufkeshi ya sauka kan bayanta fuskarta ce ta fito tayi fayau da ita yayin da jikinta yake wani irin santsi da ƙamshi mai tafiya da imanin mutum,wanda sam tunda ta dawo inno da Hajiya Babba basu ƙyaleta da kaye kaye ba, wannan ta bata wannan wannan ta bata wannan wai maganin baki ne da tsari, duk da wani maganin ma da ƙyar take iya sha,har ta kwanta sai ga kiran inno wai ta manta bata kaiwa Abdallah copy ba,ɗan tura baki tayi kana tace"Allah yasa dai bai dawo ba kalan naje ya kuma kamani ya wani riƙe ya sani kwana aɗakinsa dan iskanci kawai!'cikin wannan gungunin ta gama haɗa copy ɗin ta nufi falon,bayan ta ɗora doguwar buɗaɗɗiyar Abaya akan kayan baccin ta,tana shiga sai da ya tabbatar ta kai tsakiyar falon kana yasawa ƙofar lock batare da tasan lokacin da ya motsa daga inda yake ba,ƙin bari tayi su haɗa ido har ta ajiye masa cikin miskilar muryar sa yace"bani nan a hannuna!' miƙa masa tayi tana kawar da kanta gefe wanda hakan ne yasa taci tuntuɓe da ƙafarsa kawai sai jinta tayi cikin jikin shi batare da sanin sa ko sanin ta ba,da sauri ta ɗago dan tashi amma sai caraf fuskarta kan tasa hancinta na gogar nasa laɓɓanta na kan tattausan lip ɗinsa.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 33 ```



Da sauri ta miƙe tana yi masa hararar gefan ido,bai nuna ya ganta ba sai ma cewa da yayi ki zauna inason magana dake!'zaro manyan idanunta tayi cike da tashin hankali itafa bata son zama kusa dashi saboda zazzaɓin da yake sata, dan ji take wani sanyi na ratsa ƙasusuwanta har cikin ɓargonta,ɗan zama tayi daga can nesa dashi,batare da ya kalleta ba ya kuma cewa,ina wasa dake ne?girgiza kanta tayi kana ta miƙe ta koma gefan sa a mai makon ta zauna kan kujerar sai ta zauna ƙasa kusa da ƙafafunsa tare da sun kunyar da kanta sai jajjan yatsun hannunta take zuciyarta kuwa cike take da fargabar abinda zai ce mata ga kuma zazzaɓin kusancin ta dashi,zuba mata ido yayi na ɗan wasu da ƙiƙai wanda bazaka taɓa fahimtar kallon nata yake ba sai dai ita kuma a jikin ta taji alamun idanun sa akanta dan haka ta fara ɗan motsa bakinta a hankali kuma cikin shagawaɓaɓɓiyar muryarta tace"Ni kam dai bacci nakeji!'yaji ta sarai amma sai ya basar tare da ci gaba da tafa wayar sa,sai da yagama ƙulal da Bintu, kana cikin wata irin murya mai cike da nutsuwa da san nuna mata mahimmancin maganar da zaiyi yace"

Duk abinda na tambayeki ina so ki nutsu ki bani amsa ta gaskiya idan kuma kika sake kika yimin ƙarya tabbas baza kiji daɗin hukuncin da zanyi miki ba!'ai tuni Bintu ta ruɗe iya ruɗewa dan bata shiryawa tutseyan Abdallah yanzu ba kuma bata gama shawara akan duk wani batu da zai tambayeta ba, cikin marairaice murya tace"dan Allah kayi haƙuri sai Allah ya kaimu gobe wallahi bacci nakeji sosai!'cike da alamun tashin hankali ta ƙara sa maganar,ba tare da ya dubeta ba yace"ki gaya min suwaye suka kawo ki cikin estate ɗin nan da kuma dalilin kawoki? duk da ya riga yasan wannan tun lokacin da yasa akabi masa ita tare da ɗauko masa tattaunawar su ita da Dije,amma yana buƙatar ƙarin bayani daga bakinta yana so ya tabbatar kuma yaji ko zata canja magana,ita kuwa Bintu tuni ta shiga wani hali na jin tsoran sanar da Abdallah wannan lamari duk da tanason sanar dashi amma idan ta tuna kashedin da suka yi mata duk sai taji tsoro ya kamata, fuskantar hakan da yayi ne yasa a matsayin sa na cikakken me binciken sirri kuma kwararre a wannan harkar yasa ya ɗan sassauta fuskar sa tare da muryarsa cikin tattausan harshe yace"Fatimah!'da sauri ta ɗago fuskar ta wadda take cike da fargaba ta dubeshi,saboda yanayin da kiran sunanta da yayi ya haifar mata ji tayi kamar shi ka ɗai iya kiran sunanta saboda salon da yayi amfani dashi gurin ambatar sunan,ganin tana kallon sa yasa ya kawar da fuskar sa saboda maganaɗisun da ke cikin idanunta wanda shine dalilin da yasa bai cika son kallon cikin ƙwayar idanun nataba,

Cikin basar da abinda yakeji yace"ki kwantar da hankalin ki ki nutsu ki amsa tambayoyi na ki cire tsoron da ke ranki babu abinda zai faru,ko bakyason taimakon bayin Allah n da suke cikin matsala?da sauri ta kaɗa kanta kana tace"inaso mana!'yauwa to kinga dole idan haka zata faru saikin cire wannan tsoron dake addabar zuciyarki!'cikin gamsuwa da kuma samun ƙwarin gwiwa tace"Anty Nafisa ce da mahaifiyarta Hajiya ladidi sune suka kawoni, shuru ta ɗan yi kana ta faɗa mishi komai kamar yadda ta faɗa wa Dije har daga inda tazo babu abinda ta ɓoye masa labarin dai sak iri ɗaya da na Dije,yace"ki gaya min dukkan abinda ya faru daga lokacin da kika zo zuwa yanzu ina nufin har labarin gubar da aka saka min!kuka ta saka masa cikin kukan tace"wallahi ban san yadda akayi ba ban san komai ba!yace"Ni ba cewa nayi kin san komai ba kawai abinda nakeso dake ki gayamin duk wani shirin su da kuma abinda suke shiryawa da kuma bayanin da kika sani akan saka min guba da akayi!'

Cikin nutsuwa ta bashi labarin ko mai hatta da haɗuwar su da sukayi da Dije da shirin da sukayi akan yaƙar magauta sai da takuma maimaita masa sai maganar guba wanda ta gaya masa gaskiyar abinda ta sani,abu ɗaya ne ta ɓoye masa aikin da Anty Nafisa takeso tayi mata, yace"ina wayarki take yanzu? shuru ta ɗan yi kana tace"Ni tun ranar ban sa ke ganin ta ba!'yace"a kwai ragowar abinda kika ɓoyen kuma idan baki gayamin ba na gaya miki zan yi matukar saɓa miki!'cikin lumshe idanu da tsananin baccin da ke cikinsu tare da fargabar da ta cikata,tace"Ni ka rabu dani bacci nakeji, Bintu tariga tayi alwashin baza ta gaya masa sirrin Anty Nafisa ba, saboda baza ta so Anty Nafisa ta kashe Oga Abdallah ba, lamarin cikin ahlin yana matuƙar bata tsoro tunda ta ga basu ɗauki cutar da mutum a komai ba,cikin wannan tunanin baccin da yake ta lallaɓowa idanunta ya samu nasarar surar ta, Abdallah cikin ƙosawa da yawan maganar yace"ke fa nake saurare!'shuru yaji daga ƙarshe ma sai ji yayi ta Kwaanto jikin ƙafafunsa,wanda shine da lilin da yasa ya ankara da abinda ke faruwa, ɗan tsaki ya saki kana ya shiga tashin ta dan ta koma ɗakinta.


A hankali take buɗe idanunta wanda suka cik a fal da bacci,alama yayi mata da ta tashi,a hankali ta miƙe batare da ta ce komaiba ta nufi ƙofar falon a hankali ta murɗa ta fita yana tsaye yana kallon ta har ta maida ƙofar ta rufe,numfashi ya ɗan sauke kana ya kuma zama tare da ci gaba da aikin da yake cikin computer sa.


Washe gari ta tashi cikin farin ciki saboda nauyin zuciyarta da ya ragu,sosai taji nishaɗi da nutsuwa, lokacin da ta kai masa break ɗin sa ya tafi motsa jiki dan haka cikin sauri ta haɗa masa komai tare da kimtsa masa sashen nasa,cikin sauri ta fito daga ɗakin ai yanzu kuma wasan ɓuya zata dingayi dashi dan ko mai zaiyi baza ta gaya masa ba,


Tana shiga ɗakin ta tarar da Anty Nafisa zaune a bakin gadon ta, tana ta faman jijjiga ƙafa kana ganinta kasan tana tafe da rashin mutunci dan sai wani hura hanci takeyi kamar zata fashe,cikin sanyin jiki Bintu ta ƙarasa kusa da ita ta zauna a ƙasa tare da sunkuyar da kanta ƙasa,Anty Nafisa ta ƙare mata kallo sama da ƙasa kana tace"kin kyauta min Bintu na gode da abinda kika yimin!' cikin zaro manyan idanunta tace"me nayi kuma?au tambaya ta ma kike yi? gaskiya Bintu wuyanki yayi kauri naga alamar kin zama ƴar gari,yanzu har kin manta da yadda mukayi da ke? tunda kin samu waɗan da sukafi mu sakin kuɗi,shikenan sai mu ki saki namu aikin wallahi Bintu kin bani mamaki saboda yadda kika iya juyamin baya amma kikaje kika yiwa wasu,to ko meye hujjar ki tayin hakan?cikin damuwa Bintu tace"wallahi wallahi wallahi kinji rantsuwa ta har so uku bani bace na aikata ba, kuma ban san waye ba kuma ban zargi kowa da aikatamin haka ba na barwa Allahu jalla wa'azza dan shine kaɗai yasan sirrin dake ɓoye amma ki yadda dani bani bace ban san komai ba!'zuba mata ido Anty Nafisa tayi na wasu ƴan daƙiƙa kana taja Ajiyar numfashi tare da cewa shike nan na yadda mu ajiye wannan batun mu dawo kan asalin labarin domin yanzu shi yafi ko mai muhimmanci a gurina,shin zaki yi min abinda nasaki ko bazakiyi ba? idan har yanzu kina kan bakanki to nima ina kan nawa bakan bazan taɓa ɗaga miki ƙafa ba Bintu, saboda kin riga kin san sirrina kuma nasan tun da kika sani sai wani ya sani,dan haka ina sauraren ki wanne kika zaɓa?

Wani irin gumi ne ya shiga ketowa Bintu ta ko ina bata da wata mafita a yanzu wanda ya wuce ta karɓi aikin nan inyaso daga baya sai ta nemi mafita,katse ta tayi da cewa kina ɓatan lokaci ki bani amsa!'a hankali Bintu ta ɗago kanta dake sunkuye tun ɗazu tace" na amince zanyi abinda kika sakani!'daga haka ta ƙunshe kanta cikin cinyoyin ta tana fitar da wasu zafafan ƙwalla masu tsananin raɗaɗi a zuciyarta, Anty Nafisa tayi wani shu'umin murmushi tare da cewa burina yana gab da cika, Bintu a hankali tace"nima nawa yana gab da cika insha Allah!'murmushi Anty Nafisa ta kumayi batare da tasan inda furucin Bintu ya dosaba,fita tayi da sauri ranta fari ƙal ji takeyi kamar burin nata ya gama cika,

Bintu ta bita da wani mugun kallo tare da cewa insha Allah Asirinki ya kusa tonuwa da ɗai ɗai zaku fara girbar abinda kuka shuka wannan alƙawarin da na ɗauka ne!' hannun ta ta ɗora kan ƙirjinta tare da cewa Bintu ki kwantar da hankalin ki ki cire tsoro wannan yaƙin ba zai yiwu da tsoroba dole ki zama jaruma a filin daga.


Taufiƙa ta kalli Farida tare da cewa idan kin san zaki lalata mana shiri ka wai ki bari tunda kina tsoron Abdallah, Ni dai nasan bazai kasheni ba kuma na gaya muku muna gamawa zamu gudu gidan Nana Babba!'Siddiƙa cikin yanayin tsoro tace"wallahi Ni dai babu Ni bazan dakar masa mata ba,saboda tun kafin ta zama matarsa idan mukayi mata abu rama mata yake ballantana kuma yanzu,dan haka Ni dai babu ruwana!'Taufiƙa ta kuma kallon Farida tare da cewa ke kuma fa meye ra'yinki? dake Farida kusan halin su ɗaya da Taufiƙa shi yasa batare da jin ko maiba ta amince da shirin da sukayi dan tarfa Bintu suyi mata shegen duka,daga nan su bar gidan sai komai ya lafa.


Kallon ta take cikin tsananin baƙin ciki da tsana mara misali, ji take da zata samu dama da itace mace ta farko da zata fara ganin bayan ta, to amma yanzun ma bata fidda ran watarana wannan matar da har yanzu bata san ko wacece ba, zata kwashi kashinta a hannun ta ba,matar da take sanye da niƙab ta duƙa gaban mahaifiyar Bintu tace"lallai idan na bari kika cigaba da rayuwa a haka baƙaramin adalci nayi miki ba saboda ko ba komai zaki dinga jin labarin ɗiyarki kafin kiji labarin mutuwar ta wanda Ni kuma dashi ne zan samu damar gamawa dake dan nasan yadda kike son ɗiyarki da mijin ki zaki iya haɗiyar zuciya duk ranar da kika samu labarin barin su duniya!'Allah ba zai nuna miki wannan ranar ba sai dai keda zuri'r ki ku wula ƙanta amma ba dai kiga bayana nida ahlina ba,kuma ki sani cewa zalunci baya ƙarko dolene kuga ƙarshenku,kuma yaran da kuka zalunta sune zasu ga bayanki ke da duk wani me irin halinki, insha Allah Bintu ta fi ƙarfin shu'mancin ki saboda tana tare da Allah kuma shine zai zama garkuwar ta ya kareta a duk inda take!'wani gigitaccen mari ta watsa mata tare da cewa, mu zuba Ni dake da duk wanda yake son kawo min cikas akan samuwar cikar burina,bazan ƙyale ko da ɗan cikina bane in dai har zai kawo min matsala cikin burina ballantana kuma ke bafulatanar jeji sakarya kawai!'laila ta kuma ɗaga muryar ta tare da cewa bazan daina faɗar abinda ke raina ba kuma idan kin san wuta to tabbas Bintu ita zata zamar miki wuta me azabtar da rayuwarki kafin kije ki tarar da ta gaske me azabtar dake a lahira,in dai har bakiyi gaggawar tuba daga munanan aiyukan da kike aikatawa ba!'kuma ina mai kuma sanar da ke ki ƙyale ɗan uwana domin babushi cikin al'amarinki!wata muguwar tsawa matar me niƙab ta daka mata tare da cewa to idan baki sani ba ki sani ɗan uwanki shine babban jigo shine mutum na farko da idan na sassauta wa zan yi babban kuskure a rayuwata, ko dan baki san yaƙin da nasha gurin ƙwato ku daga hannun waɗan can mutanen ba?Laila ya kamata ki saduda ki zubda makamanki, ko karɓarku da nayi a hannun waɗan nan matsafan iya haka ya kamata ki jinjinawa shu'mancina ki san cewa Ni ba abar sa in sanki bace!'Laila tace" Aikuwa tun da kika kasa gane mutanen da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login