Showing 63001 words to 66000 words out of 184937 words
uban gayyar, kansa A ƙasa yake bata fahimci ko mai a yanayin saba amma ta tabbatar a yanzu jiyake kamar yayi aman zuciyarsa, Alhaji Baba ne yaci gaba da cewa, wannan haɗin yayi min har cikin zuciya ta Abdallah kai kaɗai nake buƙatar jin ta bakin ka!'cikin nutsuwarsa da ba ta yadda za ai ka fuskanci halin da yake ciki,yace"Alhaji Baba ni bani da ja akan umarnin ka kai naka faɗa ne Ni kuma cikawa ce tawa,dan haka na amince da umarnin ka!'shiru falon ya ɗauka na wasu ƴan daƙiƙa kana Alhaji Baba yace"to masha Allah Allah yayi muku albarka baki ɗaya Batula ke kuma fa ko kina da abun cewa? da sauri ta gyaɗa kanta,yace to me kike buƙata?cikin tsan tsan biyayya da kawaici tace"Baba dama Anty Taufiƙa ce take son sa, Ni kuma na amince ka haɗani da Sayyid ɗin!'tunda aka fara maganar nan banga Abdallah ya kalli ɓangaren da Bintu take ba sai yanzu,amma cikin sakanni har ya janye fuskar sa ba tare da kowa ya ankara da hakan ba, Alhaji Baba yace"a'a Bintu ke Allah ya bawa itama ga wanda Allah ya bata nan!' ya nuna Sayyid da shi kam ko ajikin sa zan iya cewa laba asa a haka yanayin sa yake,cikin wani irin kuka na fitar hayyaci Taufiƙa ta shiga yiwa Alhaji Baba magiya da rokon ya warware haɗin ta da Sayyid amma ina ko saurarenta baiyi ba,inno ce ta daka mata tsawa tare da cewa ke kam wai Taufiƙa wace irin macece haka mara aji da kunya?to tashi maza kibawa mutane waje idan an kaiki gidan Sayyid ɗin kiyi duk abinda kika ga ya dace da rayuwarki shashashar banza da ta wofi!'Dady Mansur ne ya tashi fuu ya fita yayin da duk suka bishi da kallo,Dady Habib ne ya kalli Alhaji Baba tare da cewa Baba yaushe akasa ranar auren? kai tsaye Alhaji Baba yace"sati me zuwa in Allah ya kaimu!'daga nan su Hajiya Babba suka saka albarka sukayi addu'a kowa ya watse,
Tunda ta shiga ɗakinta take kuka wanda ita kanta tasan na tsorone yaza ayi ace wai Oga Abdallah shine wanda zata aura, har yanzu gani take kamar A cikin mafarki to ya zatayi da nauyin da yake kanta? tabbas tasan akwai ƙura ga Anty Hauwa'u ma da bata nan idan ta dawo tasan kashe ta zasu haɗu suyi kawai, wannan tunanin ne ya hana ta sakat duk tabi tayi sanyi,
Watsi take yi da duk abinda yazo hannun ta, Siddiqa sai haƙuri take bata amma tamkar tunzura ta takeyi cewa take wallahi sai naga bayan yarinyar nan sai dai duk kowa ya rasa,tsinanniyar yarinya ƴar mitsiyata almajira macijiyar sari ka noƙe wallahi bazan ƙyale ta ba kai kuma Sayyid ko dame kake taƙama bazan aureka ba,idan kuwa hakan ta faru sai na kasheshi na kashe kaina kowa ya huta!'Siddiqa ce ta kama ta da ƙyar tana cewa zama zakiyi munemi mafita ba wai kizo kinayi mana hauka ba, dan wannan abin da kike bashine zai rage miki raɗaɗin dake cikin zuciyar ki ba!'da wannan kalamin ta samu kan Taufiƙa ta nutsu tana maida ajiyar zuciya.
Cikin tashin hankali Hajiya ladidi ta tashi daga kashin geɗen da tayi tare da ƙara manna wayar akunnenta tace"aure kuma wani irin aure? Nafisa kina cikin hankalin ki kuwa yaza ayi maganar auren Zahra batare da sanin mu ba?ji tayi daga bayan ta Alhaji munir yace" Ni ai nasani kece dai baki sani ba!'kashe wayar tayi da sauri tare da juyawa tana fuskantar sa,tace"amma dai ko gayamin ayi ko ba dan neman amincewa ta ba tunda nasan ban isa ba!'Alhaji munir yayi dariya tare da cewa to yanzu baga shi kin sani ba,miƙewa tayi ta bar falon,
Tana shiga ɗakinta ta danna masa kira bugu ɗaya ana biyu ya ɗauka, dariya kawai taji yasa tare da cewa nasan komai akan zan cen auren, ina so ki cire hannun ki daga kan wannan yaƙin dan yanzu yaƙin ya dawo na cikin gida ki zuba ido kiyi kallo yanzu wasan zai fara!'ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa yauwa har naji sanyi da hankalina ya tashi saboda ban san yadda zaka ɗauki maganar ba!'yace"kar ki damu ai hakan shine dai dai agurin mu!'daga haka suka katse kiran,Hajiya ladidi tace"wayyo Zahra inaji ajikina kece zaki zama silar warwarewar matsalolin mu.
Ta mai maita saƙon Anty Nafisa ya kai sau goma,ta kuma karantawa A karo na sha ɗaya, Bintu har yanzu banji amsarki ba lokaci yana ƙurar mun kiyi gaggawar yiwa kanki da rayuwar ki sulhu bana son ki ƙara kwana uku ba tare da kin bani sakamakon buƙata ta ba!'share gumin da yake ta tsatstsafo mata tayi, kana ta samu guri ta zauna tare da zuba tagumi,matsalolin da suka sakata gaba sun fara neman zautar da ƙwaƙwalwar ta domin yanzu babu wani tunani dayake shiga yake fita A kan ta ko mai yatsaya mata cak,ji take kamar ta zauna tayi ta zunduma ihu,duk wata dabara ta ƙwace mata,
Rahima ta zubawa Hajiya Babba ido tana sauraran labarin da take bata wanda take jinsa kamar alamara, wai Bintu da Ya Abdallah aure, kai ita zata iya cewa ma ta daɗe bata ji zancen da yayi mata daɗi kamar wannan ba,tace"Hajiya Babba wai wane irin ƙauna kikewa Bintu ne?kai tsaye tace"mata irin wannan ƙaunar da nakewa jikokina mafi soyuwa A zuciyata!'dariya Rahima tayi tare da cewa, gaskiya keda Inno ban san wanda yafi wani ƙaunar Bintu ba,sai dai kuma dukkan ku Alhaji Baba yafiku san Bintu!'hararar wasa tayi mata, tare da cewa ai shi ta huɗu yake nema ba dole yafi mu santa ba,amma mu kuma kishiyoyine kar ki manta,Rahima tace"lallai kam Hajjah ce kawai take kishi da Bintu dan dama duk tafiku kishi!'Hajiya Babba ta riƙe baki tana kallon Rahima cike da mamaki na gaske wai har ta fahimci Hajjah ta fisu kishi kai yaran yanzu sai abarsu.
Ji tayi kawai an rufeta da duka ta ko'ina ta kasa kare kanta saboda shammatar da sukayi mata,Taufiƙa cewa take wallahi ko za'a kashe Ni sai na huce baƙin ciki na najiya akanki wannan somin taɓine na bijirewa magana ta da kikayi, sauran mataki yana gaba saikinyi namar zuwanki cikin ahlin mu saina gurgunta rayuwarki kin zama abin tausayi a idanun masu imani!'kuka take sosai Bintu dan wallahi tana buguwa,da gudu inno ta shiga kiching ɗin tare da salallami tace"amma wallahi yaran nan baku da imani uban me tayi muku zaku kashe ta?anya kuwa wannan mummunar ɗabi'ar da kuka ɗauka zata kaiku ga cin nasarar rayuwa? gaskiya ina tausaya muku nan gaba domin da hannun ku zaku shuke abinda kuka girba!'ta janyo hannun Bintu suka fita daga kiching ɗin,tana mai jaddada musu Allah saiya sakawa Bintun,ko ajikinsu dan wata uwar harara da suke ta bankawa Bintun kamar idanunsu zasu faɗo..
Bintu fa ta shiga cikin matsatsi da takurar Anty Nafisa,duk inda tayi motsi sai taji ƙarar saƙonta ya shigo mata har wata ƴar rama tayi, kana ganinta kasan tana cikin damuwa ga damuwar su Taufiƙa dan ma Rahima tana taka musu birki to yanzu Rahiman ma ba ƙyaleta sukai ba.
Sunkuye take tana saka zanin gado a danƙareren gadon Oga Abdallah,jitayi wayarta na zumm zumm da sauri ta ɗauko ta buɗe saƙon Anty Nafisa ne kamar yadda ta canja salo har da barazana yanzu take aikomata, zubawa wayar ido tayi tamkar A cikinsa zata samo mafita,ya jima tsaye A bayanta duk da bai samu ganin saƙon ba amma yaci nasarar ganin sunan Anty Nafisa saman saƙon,ji tayi kawai anzare wayar daga hannunta,wata irin zabura tayi ta juya,tuni idanunta suka shige cikin nasa take kuwa jikinta yashiga rawa tamkar wadda ake kaɗawa ganga, idanunta har sun kawo ruwan hawaye tunda dama A kusa take,cikin rawar murya tace"dan Allah kabani wayana!'ko kallon inda take baiyi ba yaci gaba da sabgar gaban sa takalmin sa na motsa jiki ya shiga kuncewa, Bintu kuwa magiya har da kuka amma yayi funfurus,ƙarshe ma banɗaki ya shiga ya barta da tashin hankalin ta,ƙarshen zance ma dai tana kallo yasa wayar gaban aljihunsa ya fita da ita batare da ya kula ta ba,zama tayi taci kukanta kana ta koma ɗakinta.
Dady jafar yace"Abdallah ya kamata mu fara zurfafa binciken mu akan Dadinku Mansur,dan gaskiya al'amarinsa akwai ayar tambaya,ko ya ka gani?ɗan kashin giɗa yayi jikin haɗaɗɗiyar kujerar sa kana cikin miskilar maganar sa yace"Dady ta manyan muke yanzu, ba tashi ba,nuna masa wayar da ya karɓa A hannun Bintu yayi tare da cewa wannan wayar zata temaka mana wajen samun abinda muke san sani, duk da ban binciki wayar ba me wayar nake san bincika domin iya waya baza ta gamsar damu komai ba!'Dady jafar yace"Abdallah dole kacire duk wani tunani A ranka game da yarinyar nan ka sako mana ita cikin al'amarin nan,kaga yanzu kana da iko A kan ta tunda ta kusa zama matarka nan da ƴan kwanaki!'ɗan lumshe idanunsa yayi kana ya fara da cewa, Dady nifa yarinyar nan zan aureta ne kawai saboda kariya ga haɗarin da nake san sakota aciki dan haka da komai ya dai-daita nan da wani ɗan lokaci zan rabu da ita ta samu mijin da yakeso ta aura idan ma Sayyid ɗin ne Ni zan tsaya mata ta aureshi tunda kaga saboda tana sonsa har Alhaji Baba takewa gaddama shine kuma zata haɗa shirinta dani ya ɗan ja tsuka tare da cewa dan haka ka daina yimin batun ta maras kunya kawai!'Dady jafar murmushi yayi tare da cewa to shike nan idan lokacin yayi ko Ni da kaina zan ne mawa Sayyid aurenta dan shine halaccin da zamu iya yimata bayan ta tai maka mana!'miƙewa yayi yana tattaro takardunsa ko yanzun ma zaka iya bashi ita!'daga haka ya fita ya bar Dadin A cikin office ɗin, murmushi Dady jafar yayi sosai tare da cewa Allah ya nunamin wannan rana.
Wasan ɓuya sukeyi domin ta riga tasan yagama bincika wayarta hankalin ta tashe yake tasan kashin ta ya bushe a wajen Oga Abdallah,shiyasa duk hanyar da tasan zasu haɗu taƙi bi acikin kwana guda,shi kansa ya fahimci haka amma ya riga ya gama shirin sa na kamata A hannu duk wannan gudun da takeyi sai dai idan bai shirya kamata ba.
Bintuna ki kwantar da hankalin ki ki natare da mai taimakon tsanin ki kuma mai tallafar rayuwarki,kuma muna nan araye Ni da mamanki gaskiya ce kawai zata baiyana mu ki dage da addu'a al'amarin gidan nan bai fi ƙarfin ƙudurar Allah ba,dan haka ina mai sanar dake ki cire tsoro ki tunkari matsalar ki,babu wanda ya isa yaga bayan rayuwarki sai lokacin ki yayi, wannan dai dayake taimaka miki cikin dukkanin matsalar da kika shiga shi zai cigaba da taimakon ki tare da taimakon Allah buwayi gagara misali,akwai ƙalubale a gaban ki Bintu karki wasa da addu'a Allah ya cigaba da taimakonki ya kuma kareki daga sharrin su!'zufa ce ta shiga keto mata buɗe idanunta tayi daga mafarkin da tayi da fafin ta tare da ambatan sunan Allah,a hankali maganganun da fafin yayi mata suka dunga dawowa cikin kunnuwanta,to me fafi yake nufi shine wa?waye wanda yake taimakonta?miƙewa tayi daga saman gadon cikin zurfafa tunani, Oga Abdallah kenan fafi yake nufi shine wanda yake yawan gaya mata zai zo dan tallafa mata?to ya akayi suka kasan ce guri ɗaya? Ƙudurar Allah kenan,duk abinda nake nema sai ya kasan ce yana tare dani kai masha Allah da ƘUDURARSA da kuma dogara dashi tabbas wanda ya maida lamuransa ga Allah zai ta ganin dai dai arayuwarsa, Allah kaine abin godiya,sai dai kuma tunani da ya sare mata gwiwa bai wuce wayar ta dake hannun sa ba,idan yaga saƙonnin dake ciki zai ɗora mata mummunan zargi,ko dai gaya masa zatayi?to kuma idan yaƙi yadda fa?tashi tayi kawai ta ɗauro alwala dan miƙa kukanta ga jallah wa'azza.
Jinta tayi sawai saboda kusan kwana da tayi tana miƙa kukanta gurin Allah assamadu,shi yasa taji ƙuncin dake ranta duk babu ta tattara komai ta barwa Allah tasan zai kawo mata mafita mai kyau arayuwarta,cikin ƙanƙanin lokaci ta gama shiryawa ogan nata kayan karin kumallo wainar masa tayi masa wadda tayi matuƙar kyau da laushi sai kunun tsamiya da suyar chips da ƙwai ta haɗa masa ruwan liptom,kana taje ta shirya komai cikin nutsuwa, cikin ɗakin ta shiga ta fara da wanke toilet,sannan ta gyara ɗakin kan kace meye ya ɗauki ƙamshi da haske tsaftar Bintu ta musamman ce saboda bata da ƙwuya ko mai a nutse take yinsa shi yasa zaka ga komai tsaf bata barin datti ko ta allura ce,
shiyasa duk ƙaƙalen Abdallah bai taɓa ganin kuskure a tsaftar Bintu ba,ya riga ya yadda da ita ta wannan ɓangaren ya bata maki ɗari bisa ɗari,ɗan dube dube ta fara so take ta gani ko zata ga inda ya ajiye wayar ta, har su ƙarƙashin gado sai da ta duba duk da gyaran ta har nan bata bari ba,me kike nema? taji muryarsa daga bayanta da sauri ta ɗago tana rarraba manyan idanuwan ta masu tamkar zaiba, tashi tayi tana son barin ɗakin,jingina yayi da ƙofar alamun dai ba zai bata hanya ba,tura ɗan ƙaramin bakinta tayi tare da cewa sharewa nayi!'ɗan ƙara girman idanunsa yayi akan ta batare da yace mata komai ba sannan kuma bai bata hanya ba,ɗan matsawa tayi daf dashi tace" zan tafi inno tana jirana!'saurin sunkuyar da kanta tayi saboda kaifin idanunsa,gaba ɗaya jikinta ya fara rawa saboda kusancin su yanayin da take shiga da zarar sun fara musayar numfashi shi yake ƙara yawa har wani sanyi takeji can cikin ƙashi da ɓargonta, da ta rasa mafitar ta tatserewa shu'uman idanunsa kawai sai ta fara sana ar tata,ɗan ɗage gira yayi yana ƙara zurfafa duban sa akanta,kana kuma ya taɓe bakinsa tare da cewa ke gyare sarkin kuka,tambayar ki nayi fa,cikin sangar tacciyar murya tace"to wuce wa zanyi!'bata hanya yayi batare da ya kuma tanka mata ba,da gudu ta fita,batare da ko waiwaye ba,jinjina kansa yayi tare da cewa lokacin kamaki ne baiyi ba.
Sai da taga fitar sa kana ta koma ɗakin cikin sauri ta shiga dubawa, cikin Sa'a kuwa tayi karo da wayar ga alamu ma manta ta yayi,ɗauka tayi ta koma ɗakinta,lambar Dije ta fara gwadawa cikin sa ar datake da ita yau, wayar ta shiga,haba mama Dije hankalina ya tashi da rashin jinki gashi bani da wata hanyar da zan ganki!' cikin nutsuwa Dije tace"Bintu muna cikin masifa matar nan ta fara ganewa muna ƙulla wani abu Ni dake, Bintu rayuwar ƴaƴana nakeji shiyasa kika ga na ƙulle hanyar haɗuwa dake!'cikin tashin hankali Bintu tace"yanzu kina nufin kin karya alƙawarin da kikayi min? Dije taja wani sheshsheƙa tare da goge zufar dake sauko mata kana tace"Bintu ban karya ba kuma bazan karya ba,ina daiyin ta katsantsan ne saboda rayuwar marayun Allah, wannan matar shu'uma ce Bintu ta iya takunta, yanzu abinda nakeso na gano shine wai shin acikin gidan nan take zaune ko kuma daga cikin ahlinsa ne wanda basa zaune a gidan nan? daga nan zamu san yadda zamuyi mugano abinda suke wannan san zuciyar akansa dan tabbas a kwai wani abu daya dan ganci dukiya me razana zuciyar mutum a cikin estate ɗin nan!'jin kamar za a shigo ɗakin dan ta manta ba tasa key ba yasa tace"to shike nan mama duk abinda ake ciki ki kirani!'tayi saurin kashe wayar tare da cusa ta cikin zanin ta.
Da wuri ta gama girkinta ta kai ta jera saboda bata san su haɗu da Oga dan tasan ita mai laifice A gurinsa,haka kawai take jin faɗuwar gaba jikinta duk a san yaye yake,shiyasa ko da Rahima tazo suka zauna A falon inno kasa gane mata tayi,tace"Bintu wai ko baki da lafiya ne duk na ganki wani iri? cikin faɗuwar gaban dake ƙara kusan tarta tace"wallahi Rahima kaina ne tun ɗazu yake sarawa kamar zai rabe biyu!'ayya sorry bari na kama maki sai kije kisha magani!'kama mata kan tayi kana ta miƙe tare da cewa bari na wuce sai Allah ya kaimu gobe!'Bintu tace"ki gaida min da Ammi na gode,daga haka sukayi sallama,zama tayi A falon ta kasa tashi har su Taufiƙa suka sameta,basu ce mata komai ba suka wuce ɗakin su, Sayyid ne ya shigo yana ganin Bintu ya fara washe mata baki zama yayi kujerar dake fuskantar ta ya shiga yi mata surutai bata tanka masa ba dan ita kaɗai tasan halin da take ciki,a haka Oga Abdallah ya shigo ya same su bai kalli inda suke ba ya wuce part ɗinsa,yana shiga ko ɗakin bai ƙara sa ba ya wuce dining dan wata muguwar yunwa ya dawo da ita,savin kansa yayi ya fara cin haɗaɗɗen tuwan farar shinkafa da miyar ɗanyen kubewa wanda taji ragargajejjen naman kaza sai ƙamshin daɗi takeyi.
Acan falo kuma Bintu ta gaji da surutun Sayyid tashi tayi ta barshi ba tare da ta tanka masa ba tun zamansa,sai da ta shige kana ya ankara da wayar ta ɗauka yayi da niyar miƙa mata saƙon dayaga ya shigo wayar ne ya saka shi da katawa tare da zaro idanu cikin tashin hankali da firgici...
Bintu kuwa tana shiga ta wuce wajen taga ta ɗaga labulen,dan samun iska ko zataji sanyi,takarda ta gani saƙale ajikin tagar da sauri ta ɗaga tare da warwareta,innalillahi'wa'inna ialaihi raji'un da gudu ta fito daga ɗakin cikin tsananin tashin hankali...
Turƙashi wani kaya sai amale,wane saƙo Sayyid ya gani A wayar Bintu?me saƙon wasiƙar Bintu ya ƙunsa da ya tayar mata da hankali haka?wane tashin hankali ne yake shirin faruwa da Bintu da har take jin faɗuwar gaba? amsar na cikin nest page insha Allah
Alƙalamin✍🏽
Fatima y Adam
More comment.....
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 29 ```
Karo sukayi da Sayyid sauri tayi ta ɓoye takarda hannun ta tare da yagata ƙananu, bin yagaggiyar wasikar yayi da kallo,kana cikin sanyin jiki ya miƙa mata wayar tare da wani irin kallo na tsantsan tuhuma,karɓar wayar tayi hannun ta na rawa,da sauri ta wuce shi bata re da ta tsaya duba wayar ba.
Paper da ta zubar ya tsaya ya tattara