Showing 111001 words to 114000 words out of 184937 words

Chapter 38 - KUDURAR ALLAH COMPLETE BY FATIMA Y ADAM

21 Jul 2024

16888

san ya yadda dake ya kuma yadda bazaki taɓa cutar dashi ba,kuma da akwai amana da gaskiya a tsakanin ku to kawai ki tunkare shi kai tsaye ki tambaye shi,ina mai tabbatar miki da cewa indai yayi miki waɗan nan abubuwan dana lissafa to wallahi zai gaya miki batare da ya ɓoye miki komai ba!'shuru tayi ganin yadda Nafisan take mata wani irin kallo wanda kamar ma bata san tanayi mata shiba,can dai da ƙyar tace"Bintu kina da hankali kuwa ta yaya zan san duka waɗan nan abubu wan alhalin ban shiga zuciyar sa na gani ba,ban san meye a zuciyar sa game dani ba, ban kuma san wani irin kallo yake min ba, ban san wane irin zargi yake min ba? gaskiya Bintu ki sake tunani!'tsura mata ido Bintu tayi kana tace"Anty Nafisa ya akayi KIKASAN yana zarginki?bayan kuma kin ce baki san ta yadda za ayi kisan wane irin kallo yake miki a cikin idanuwan sa ba?tuni Anty Nafisa ta diririce gaba ɗaya Bintu yariyar cikin ta ta saka ta a kwana tamkar wadda take tuhumar ta da laifin kisa,ganin irin rikicewar da tayi ne yasa Bintu ta kuma tabbatar da zarginta tabbas a kwai Babban abinda Nafisa take ɓoyewa wanda kuma zai iya taimaka musu sosai cikin tafiyar su,kuma tayi alƙawarin sai ta faɗa mata kome taƙe ɓoyewa,yanzu zata bar ta da wannan sai kuma zama na biyu,miƙewa tayi tare da cewa,Anty Nafisa Ni zanje kiching ke kuma kije kiyi tunani akan shawarar da nabaki idan ta karɓu sai ki aikata ta,idan baki gamsu da ita ba,sai mu canja wata Kinga Nima sai na samu damar ƙara yin nazari,kinga dole sai kin yi haƙuri akan wannan aikin saboda ya ban banta da sauran ayyuka,su waɗan can na san komai shi kuma wannan sai dai nayi lalube,daga haka ta fita daga ɗakin batare da ta jira abinda Nafisan zata iya faɗa ba,ita ma tashi tayi jiki a saluɓe ta koma ɓangaren ta cike da tunanika iri-iri.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 43 ```


Tana shiga kiching ɗin ta fara ƙoƙarin ɗaurawa ogan nata sanwa, sai dai gaba ɗayan ta bata jin ta dai dai saboda tunanin da ya cika mata ƙwaƙwalwalwa, ƙoƙarin ta kawai a yanzu gano me wannan muryar,duk da cewa yanzu duk wanda yayi magana ji take kamar waccan Muryar to amma da izinin Allah hakan ba zai sa ta kasa gano me ai nahin Muryar ba.


Wata tsawa shugaba azukyi ya dakawa Nanu, me kake yi haka ne?kasan wannan hanyar da ka biyo ba hanya bace me ɓullewa,me yasa baka tsaya akan wan can shirin namu ba, tabbas kayi gangan cin fallasa Muryar ka ga yarinyar nan,domin tabbas yanzu da abinda zata samu dama akanka ke nan!'ya ajiye maganar cikin wani irin huci na tsananin ɓaci rai da abin da nanun yayi,wanda aka kira da nanu yayi ƙasa da kan sa tare da cewa afuwa nake nema shugaba yanzu meye abinyi?babu wani abin yi nanu saboda ka nuna mana bamu da wani amfani a cikin wannan tafiyar dan haka sai kaje ka ƙara sa aikin ka kai ɗaya!'cikin tashin hankali nanu ya kwanta a ƙasa yana mai neman afuwar shugaba,nasan nayi kuskure amma ayi min afuwa!' shugaba yace"tabbas yanzu yarinyar nan zata dinga bibiyar ka ta muryar ka, don kuwa ka riga ka buɗe mata hanya da ace kayi haƙuri ka barta a iya tsoron da muka dasa mata da yanzu bamu da wata matsala yanzu ka riga ka rusa komai!'yanzu lalata wannan shirin yana da matukar wuya, saboda muryar ka ta riga ta zauna a cikin ƙwaƙwalwar ta,cikin ƙara yin ƙan da kai yace"yanzu meye abinyi shugaba?yace"dole sai mun nemi taimakon dodo jack dan haka yanzu kaje za muyi magana bayan na gana dashi!'nanu dai ya haƙora ne amma ba dan ransa yaso ba dan sai yanzu ya ankara da babban kuskuren da yayi baya son wannan abin da yayi ya zama shine sanadin tonuwar asirin sa, duk yadda zaiyi da yarinyar nan sai yayi dan samun cikar burin sa da kuma rufuwar asirin sa,


Nafisa dai tana cikin tsaka mai wuya ta rasa inda tunanin ta zai tsaya maganganun Bintu ne suke ta kaiwa da kawowa cikin ƙwaƙwalwar ta,anya kuwa tana da wannan ƙwarin gwiwar a wajen Umar?duk da tana da tabbacin bai san komai akan abinda ta aikata ba,amma bata tunanin akwai wannan yardar da Bintu take faɗa a tsakaninsu,haka kawai take jin bata yadda da kanta a wajen Umar ɗin ba,to ko gwadawa zatayi ta gani ko zata dace?goge zufar dake ta tsatstsafo mata tayi,a fili ta furta,zan gwada Bintu zan ga yadda Umar ya ɗauke Ni da kuma kallon da yake min zan tambaye shi abinda yake damun sa zan gani ko zai gaya min indai kuwa ya faɗa min to tabbas zan ƙara kwantar da hankali na saboda na yadda ya amince dani ba kuma ya zargi na da aikata masa babban laifi.


Abdallah ya samu duk wasu bayanai daya buƙata a kan Alhaji Rufa'i kuma ya gamsu da gaskiyar sa,yanzu yana tunanin kiran sa dan su tattauna akan batun Alhaji Shamsi tunda har yana tunanin shi Alhaji Shasin zai iya sanin kome ne ake rigima da neman sa ta kowace hanya,yinin ranar bai samu sukuni ba saboda yawan aiyukan da ya aiwatar a ranar duk wasu baya nai da yake bukata na mutanen da yake da alama akansu ya samu,dan haka ba tare da wani ɓata lokaci ba ya fara baza ma aikatan sa dan soma bincike akan su,


Bai samu shigowa gidan ba sai misalin goma na dare,a gajiye ya shiga ɓangaren sa,kai tsaye ya faɗa toilet ya sakarwa kansa shaya,sai da ya shirya tsaf kana ya nufi dinnin dan samawa cikin sa wani abun,

Tun ƙarfe takwas take duba agogo da leƙen window ko zataga dawowar sa amma shuru bai dawo ba ga yanayin garin da hadari alamu ya nuna dai yau zasu iya samun ruwa,dan ma dai damunar batayi nisa ba,
hakan ne yasa taji duk ta damu da rashin dawowar tasa ko lafiya yake?ta riga ta daɗe da sanin baya wuce wannan lokacin,shi yasa duk tabi ta damu,dan hararar hanyar tayi tare da cewa ko me yasa ma na damu bayan ko ya dawo ba lallai ne yayi min magana ba!'ta faɗa tamkar yana kusa da ita har da dan murguɗa baki,sai dai kuma duk da hakan ta kasa haƙurin shi yasa tana jin karar mota tayi saurin bude labilan tana leƙawa,wata sassanyan Ajiyar zuciya ta saki lokacin da ta tabbatar da cewa shine ya shigo, komawa tayi ta zauna abakin gadon tana tunanin ta yadda za ayi taje ɓangaren nasa tunda bata da sauran wani abu da zatayi acan ɗin,ta gumi ta zuba,can kuma sai ta miƙe, toilet ta shiga tayi brosh tana fitowa ta saka wata rigar bacci wadda ta tsaya iya cinyoyin ta daga nan tayi kwanciyar ta dan ta rasa hanyar da zatabi dan zuwa ɓangaren nasa,kalan ma inje ya koroni ta faɗa tana tura baki tare da shigewa cikin ɓargonta saboda yanayin iskar da ake ga dukka nin alamu dai ruwa zai iya zuba ako wane lokaci.


Abdallah ma dai a gurin sa kusan hakane,aiki yake amma hankalin sa yana kan duban hanya,tunanin zuwan ta yake akoda yaushe,sai dai har zuwa wannan lokacin baiji motsinta ba,ɗan tsaki yayi tare da janye laptop ɗin dake gaban sa,tashi yayi ya shiga toilet Jim kaɗan ya fito,ya ɗanyi abinda ya zama al dar sa,kana ya kwanta bayan yayi addu'oin sa,so yake ya kwanta ya ɗan rage bacci kafin ajima ya tashi yayi nafilfilu,sai dai kuma hakan ya gagara a wajen sa,mamakin yadda akayi ya kasa samun sukuni saboda yarinyar yake,ta wani bangaren kuma yana mamakin yadda ta iya kwanciya ita ɗaya,ya santa da tsoro gashi kuma yana gani kamar a kwai abinda yake damunta a kwanakin nan,lumshe idanun yayi yana jin wani irin yanayi a can cikin jikin sa,iska ce ta fara kaɗawa mai ƙarfi wadda take tasowa da ƙura,da sauri ya tashi ya kuma gyara windows ɗin ɗakin,duk abinda yakeyi zuciyar shi na wajen ta, gani yakeyi tausayin Bintu zai iya saka shi a wani hali,duba da yadda ya kasa sukuni ganin yau gaba ɗaya bai ganta ba,ga yanayin tsoronta dayake taɓa masa zuciya, ji yake tamkar yaje ya dubata,kasa zama yayi a ɗakin ya fito falo saboda yana ganin kamar zaifi samun kusanci da ita.


"Can cikin baccin ta ta dinga jin kamar ana ta shinta a matukar firgice ta farka tana son yin addu'a amma hakan ya gagara saboda yadda taji tamkar an rufe mata baki, cikin zuciyarta ta ta dinga ƙoƙarin yin addu'ar yayin da duk jikin ta rawa yake,ga wata irin walƙiya da ake yi da tsawa saboda ruwan da akafara tamkar da bakin ƙwarya,kuka ta saka tana laluben hanyar da zata sauka daga gadon dan ta kunna hasken ɗakin,da ƙyar ta samu ta lalubo wayar ta ta kunna tare da saukowa daga kan gadon hasken ɗakin ta fara kunnawa,raɓewa tayi a can lokon ɗakin babu abinda jikin ta yake sai rawa saboda tsananin tsoro,ji take kamar ba ita kaɗai ce acikin ɗakin ba, zuciyarta kamar zata faso kirjin ta haka take ji,

Gaba daya ya kasa samun sukunin zuciya ba ma kamar yadda yaga an tsuge da ruwa wanda yake tafe da tsawa da walƙiya,baya jin zuciyar shi zata barshi ya nutsu ya aiwatar da wani abu ba tare da yaje yagano amanar da Alhaji Baba ya bashi ba,cikin wani irin zafin nama ya miƙe tare da fita daga ɓangaren nasa,kai tsaye ya nufi ɗakinta yana kusanta ɗakin yanajin bugun zuciyar shi na ƙaruwa,a can lokon ɗakin ya hango ta a rakuɓe kamar wata ƙadangaruwa,tanajin buɗe ƙofar tasa ta ƙara ƙarfin kukan ta,tare da runtse idanun ta,cikin ta kun shi na zaratan maza ya nufo inda take,yayin da zuciyarta take ci gaba da wani irin bugu jira kawai take taji yadda Ubangiji zai yi ikon sa akanta,lokacin da ya ƙaraso kusa da ita sai taji yanayin bugun zuciyar ta ya sauya wani irin sanyi taji yana shigarta haka kuma hankalin ta yana kwanciya zuciyar ta na fita daga cikin mugun firgicin da ta shiga,zuba mata ido yayi batare da yayi mata magana ba,A hankali ta shiga buɗe idanunta saboda sassan yan ƙamshinsa da ƙofofin hancinta suka fara shaƙa wanda ya riga ya zama hadda a cikin hancinta,idanun ta ne suka sauka akan kyawawan ƙafafunsa da suke kwance luf cikin tattausan carpet ɗin dake shimfiɗe a ɗakin,cikin wani irin sauri wanda yake gauraye da wani irin shauƙi ta faɗa jikin sa tare da ƙankameshi tana kuma sakin wani marayan kuka mai cike da ban tausayi,riketa yayi sosai tare da ƙara gyara mata kwanciya,yana ɗan shafa bayanta wanda hakan yake nuni da calmin ɗin ta da yake son yi, bai ce mata ko mai ba sai ɗan sunkuyawa da yayi ya ɗauki wayar ta datake yashe a ƙasa,kana ya jawo hannun ta suka fita daga ɗakin,suna gaba da shiga falon sa,suka juyo muryar inno,ɗan tsayawa yayi saboda ƙarasowar innon gaban su,cikin yanayin damuwa tace"me yake faruwa ne Abdallah,me yasa mu Batular?ta jero masa tambayoyin tana riƙon Bintun da har yanzu hawaye basu daina saraftu akan kyakykyawar fuskarta ba,

Cikin yanayin sa na ƙoƙarin ɓoye damuwar dake cikin zuciyar sa ya ɗan karyar da kan sa tare da cewa"inno tsoro ne kawai da ita san nan kuma,,sai ya ɗan yi shuru kamar yana lalubo abinda zai cewa innon,kana ya cigaba da cewa, sannan tana yawan tsorata ko mai tsoro ne yake bata,kamar dai bata jin daɗi!'ya ƙarasa maganar da ɗan kallon Bintun,inno cikin damuwa da tashin hankali tace"subhanallah me yake tsorata ki Bintu?ta juya tambayar ta kan Bintu, Bintu dai ta kasa magana sai hawaye,dan bata san mai zatace da inno ba,inno tace"anya ba makaraine suke san shafar ta ba?tayi maganar tana duban Abdallah,yayin da shi kuma ya zubawa Bintu idanu wanda maganar inno tayi saurin hasko masa wani abu makamancin abinda ta faɗa,(idan baku manta ba Abdallah yayi ilmin addini mai matukar zurfi,so dan haka yana da ilmin sanin sihiri ko jinnu saɓanin wasu ƴan bokon da zaku ga sam basu yadda da irin wannan abun ba, Abdallah yasan cewa sihiri gaskiya ne haka jinnu ma gaskiya ne,dan haka bai jahilci maganar inno ba)tsai yayi da ransa yana mai hasaso al al'amarin Bintu tabbas tana buƙatar addu'a,amma dai bai kawowa ranshi ga wanda yayiwa Bintu wani abu ba kawai dai yasan Bintu al'amarin ta yana buƙatar addu'a duba da yadda gaba ɗaya ta birkice ko addu'a bata son yi wanda shi kansa shaida ne akan Bintu ba haka take ba tun kafin suyi kusan ci da juna yasan tana da matukar riƙoda ibada,shi yasa yanzu bai sha wahalar gano yadda take sakaci da addu'a ba.

A hankali ya ɗauke idon sa daga kallon da ya ƙure Bintu da shi,ya maida kan inno tayi zukuɗi tana jiran amsar sa,sai da ya ɗan huro iska daga bakin sa kana yace"hakane inno addu'a ya kamata ayi mata,insha Allah gobe zamu fita akwai wani malamina zamuje gurin sa!'murmushi inno tayi dan da tayi tunanin Abdallah ba zai yadda da abinda tace"ba,yauwa hakan yayi Allah Ubangiji ya kareku daga sharrin mutum da aljan ya tsare bayanku da gaban ku yasa kusa zama abin kallo da tsoro a idon maƙiayan ku,Amin Abdallah ya amsa yana mai juyawa dan shiga falon sa,yayin da inno ta bar zuciyar Bintu cikin wani irin hali na tunani da,tsoro mai tsanani,a hankali ta ta taka tabi bayan sa,tana waiwayen inno da take ta Binta da wani irin murmushi mai cike da ma anoni masu tarin yawa,a haka ta shige falon wanda shine sanadin rabata da kallon inno,tana rufe ƙofar ta zame ajikinta tare da saka wani irin kuka mai taɓa zuciya wai ya zatayi idan akace yau binciken ta ya gano mata inno cikin mugayen da take zargi,ya zatayi da rayuwar ta idan akace yau macen da take ƙauna,takewa kallon tafi kowa ƙaunar ta,a cikin gidan nan, tabbas wannan fargabar ita zata jefata cikin wani mugun hali na damuwa,jin an kamota yasa ta ɗaga jiƙaƙƙun idanun ta tana kallon sa wanda shima ɗin kallon idanun take bayan ya samu nasarar ɗagota daga zaunewar da tayi,cikin neman agajin makusancin ta ta faɗa jikinsa tare da fashewa da kukan da take jin ta fara shi kenan har sai zuwa ranar da gaskiya ta baiyana,idan kuma gaskiyar ta baiyana a gaɓar da bazataso ba tabbas hawayenta bazasu taɓa daina zuba ba,tana ƙaunar inno har cikin ƙashi da jinin ta,kamata yayi suka fara tafiya har zuwa ɗakinsa zama yayi da ita ajikin sa,yayin da zuciyar sa take san gagarar ɓoye damuwar sa a wannan karon,wanda yake tunanin girman damuwar wannan lokacin ne yayi mata yawa,jingina yayi ya ɗan kashin giɗa ya kasa ce mata komai har yanzu dan bai san ta ina zai fara ba,

Cikin tausayawa kanta da rayuwar da zata fuskanta nan gaba ta fara bashi labarin yadda sukayi da Dije,ba tare da ta ɓoye masa ko alif ba,ta gama maganar tana mai cusa kanta cikin jikinsa tana murzawa wanda hakan ne yake nuni da tsananin damuwar da take ciki,cikin muryar ta da ta dashe tace"Yahh Abdallah,yaya zanyi da wannan aiki da ya ɓullo min?kagayan ta ina zan fara bincikar matan da suka fi nunamin ƙauna ta gaskiya a cikin wannan duniyar,su kaɗai ne matan danasan sun fara ƙaunata bayan ƙaunar mahaifiyata,su kaɗai ne matan da suka karɓeni batare da ƙyama ba su kaɗai ne matan da suka fifita ƙaunata akan ƙaunar jikokin su batare da sun san Ni ɗin jinin su bane,su kaɗai ne matan da suka fara yarda dani alokacin da narasa yadda da amincin kowa a cikin gidan nan,sun maida Ni mutum sun maida Ni jikar su sun yi faɗa da jikokin su akaina,to kagayamin me yasa ba zan shiga wani hali ba duk ranar da akace wannan ƙauna ta munafunci ce ta yaudara ce ta ha inci ce,me kake tunanin zanyi a ranar, wallahi ba zan iya ɗauka ba,Ni bazan iya ba!'ta faɗa tana bugun ƙirjin shi tare da ƙara sakin wani marayan kuka mai ƙun tata zuciyar maiyin sa da kuma mai sauraren sa,hannun ta ya kama duka ya riƙe kana cikin wata irin murya da ta saukarwa da Bintu nutsuwa da kasala yace"Bint!'shiru tayi tare da yin luf tamkar wadda bata numfashi,hannu yasa ya shiga gyara mata lallausar sumar kanta wadda duk ta bar baje,kana yaci gaba da cewa',Bint injin ke musulma ce?jin jina kan ta yi batare da ta ɗago ba,yace"yauwa to kinga kuwa dole ki amshi ƙaddararki duk yadda yazo miki domin wannan shine cikar imaninki da cikarki musulma,kuma bawa baya taɓa tsallake wa ƙaddarar sa to ki ƙaddara haka taki ƙaddarar tazo kuma bazaki taɓa iya sauya ta ba,ko baki ga yadda Ni nake rayuwata ba?Bint kin san rayuwar da nayi kuwa kin san rayuwar ƙuncin da danayi kin san yadda aka ƙuntatawa rayuwata,kin san yadda nayi rayuwa a hannun kafurai alhalin Ni ina cikakken musulmi?kin san yadda zuciyata takeyi aduk lokacin da aka ƙuntatawa rayuwata da yin ibadar da batawa ba kuma addinin da ban yadda dashi ba, Bint amsar itace duk baki san wan nan ba baki san meye abinda na fuskanta a cikin rayuwata ba, taki kawai kika sani,dan haka ina so kiyi haƙuri,mu fuskanci abinda ke gaban mu abinda Dije ta gaya miki gaskiya ne,baka taɓa gane munafukin ka sai da dabaru,kuma baka taɓa gane masoyin ka na gaskiya sai kashi ga halin rayuwa,ɗago kanta yayi,yana kallon fuskar ta sauri tayi ta rufe idon ta saboda wani kallo da taga yana mata mai shiga cikin jiki da jini,ɗaga mata gira yayi cikin wani irin salo da shi kansa bai san ya iya shi ba, hakan ne ya bata kunya har ta maida kanta ta sunne ajikin sa,

Ɗaga ta yayi tare da cewa bamu ga ta bacci Bint muna da babban yaƙi agabanmu muna da buƙatun da muke nema Allah ya biya mana,dan haka dole

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login