Showing 141001 words to 144000 words out of 184937 words

Chapter 48 - KUDURAR ALLAH COMPLETE BY FATIMA Y ADAM

21 Jul 2024

16879

bai tankawa Dady jafar ba har yayi ya gama ya barshi awajen,

Dady Mansur yayi mamaki lokacin da ya koma gida ya samu Sayyid tsaf dashi duk gida ya ɗauka da barkar dawowar sa, sai zuwa sashen Dady mansur akeyi barka kamar wanda akayi wata haihuwa,cike da farin ciki ya rungume ɗan nasa duk da halin da zuciyar sa take ciki a yanzu na rashin walwala da tsananin damuwa amma hakan bai hana shi jin dadin ganin ɗan nasa ba,duk wanda yayiwa Sayyid tambayar waye suka sace shi,to amsar dai ɗaya ce,shima bai sani ba,dole kowa ya haƙora da tambayar ya kama sabgogin sa.

Kamar daga sama ta samu wayar uwar gidan ta, Cikin rawar jiki Dije ta ɗaga, daga can ɓangaren matar tace"Dije ya batun alƙawarin mu?ina fata dai zan samu kyakkyawan labari?cikin farin ciki Dije tace",tabbas kin kira lokacin da ya dace dan kuwa cike nake da ɗokin haduwa dake dan sanar miki abinda zai matuƙar faranta zuciyar ki!'wata dariya ta saka daga can kana tace"shi yasa nake matuƙar ji dake Dije, kuma na koma inuwa nayi zamana hankalina kwance saboda nasan ina dake,yanzu yamma tayi kuma kinga akwai al'amuran da ake dan gabatar wa a cikin gidan dan haka gobe kiyi sammakon fita zan tura miki da wajen da zamu haɗu bayan fitarki!'Dije tace"to ranki shi daɗe,Allah ya nuna mana goben da rai da lafiya,tana kashe wayar tayi wani murmushi wanda yake baiyana ƙwarin gwiwar ta tare da cewa ko ke wacece taki ta kusa ƙarewa gobe i War haka kina nan kina zaman makokin kanki da kanki.


Tun daga farkon shigowar sa gidan yasan cewa komai yana tafiya yadda suka barshi,ga wan can al amarin ga kuma dawowar Sayyid,kai tsaye ya wuce part ɗinsa dan komai dake faruwa ba baƙon sa bane,yana shiga duk sai yaji falon yayi masa faɗi har cikin jinin sa yake jin damuwar ta da kuma kewar ta,ga kuma uwa uba tausayin ta dake neman zauta zuciyar sa,cikin sanyin jiki ya gabatar da al'amuran sa na yau da kullum,wayar sa ce tayi ringin, har zai basar da kiran sai kuma yaga Dady jafar dan haka ya daga tare da yin sallama,ba tare da ya saurari gaisuwar da Abdallah yake masa ba, yace"Abdallah tun tuni na gaya maka ka saka idanu akan Mansur amma ka banzar da maganata,to yanzu umarni nake baka kasa ka ido sosai akan sa dan ina matukar zargin sa,nan ya bashi labarin yadda sukayi ɗazu da yadda ya damu sai yasan inda suka je shida Bintu,numfashi Abdallah ya fesar kana yace"Dady karka damu zan kula da komai!'kafin ya sauke wayar daga kunnen sa wani kiran ya shigo ba tare da ya duba ba ya ɗaga, dan azaton sa ko Dady jafar ɗin ne ya sake kira.


Sannu ɗan zaki to idan kana buƙatar zakanyar ka,ka taho da zakin ubanka ka fanshi zakanyar matarka,idan kuma baka buƙatar ta yanzu saina fasa kanta da bakin bindiga, zanga irin naka halaccin idan ka gama tunani zan kuma kira dan yi maka sauran bayani inda zaka same mu kuma muddin kasarwa na jami an tsaro to wallahi ina tabbatar maka da cewa sai na kashe matar ka koda za akamani, na barka lafiya kayi tunani mai kyau matar ka ko mahaifinka?daga haka ƙit aka datse kiran.

Fatimah Y Adam✍🏽
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 52 ```


Wani irin rawa jikin Abdallah ya shiga yi,ɓacin rai da tashin hankali shi kawai zaka iya hanga akan kyakykyawar fuskarsa,wani irin miyau yake haɗiyewa mai tsananin ɗaci da kauri,gaba ɗaya kansa ya kulle ya rasa ina zai nufa,da abinda ya kamata ya farayi yanzu,kiran Dady jafar yayi wanda tuni shi har yayi bacci,cikin yanayin bacci ya daga wayar tare da cewa lafiya dai ko Abdallah?kasa magana Abdallah yayi saboda abinda ya tokare masa aƙirji da ƙyar ya iya cewa Dady sun ɗauke Bint!'Dady jafar dake kwance bai san sanda ya miƙe tsaye ba cikin tashin hankali da kiɗima yace"kagani ko Abin da nake gaya maka,Mansur ya sace yarinyar nan,shine dama dalilin da yasa yazo yana min tambayar inda kuke? Abdallah yace"Dady yanzu ya zamuyi ban karbi lambar su Hajjo ba bare na tambaye su naji gaskiyar maganar!'Dady jafar yace"kaga Abdallah fito yanzu mu haɗu ai bamu ga ta zama ba idan ma can sulejan zamuje sai muje mu duba!'

Abdallah yana fita motar sa ya faɗa yana shirin tayar da ita,aka dallare shi da futula,kare fuskar shi ya shiga yi,ba kuma tare da ya saurari me haske shin ba ya fixgi motar da wani irin mugun guda, Dady Habib dake tsaye hannun sa riƙe da fitila ya zubawa hanyar da Abdallah yabi ido cikin tunanin inda zashi da wannan daren, sai kuma yayi tunanin ko wani aikine ya taso masa,dan haka ya juya ya koma ɓangaren sa.


Gudu yake tamkar zai tashi sama bayan ya dauki Dady jafar,magana wannan ta gagara a tsakanin su kowa da abinda yake tunani acikin ransa, zuciyar Abdallah kuwa ko shiga kayi to tabbas sai ka ƙone,saboda tsananin zafin da take masa ƙirjin sa har wani sama da ƙasa yake yi,a cikin wannan halin suka ƙara sa gidan Hajjo,ko kashe motar baiyi ba,ya fita da wani irin saurin gudu,Dady jafar ma binsa yayi dan bayajin zai iya tsayawa jiran iso,buga gidan ya shiga yi cikin wani irin sauke numfashin fargabar abinda zai tarar,daga ciki kuwa atsorace, Asma'u ta kalli Hajjo tace"Hajjo yau mun shiga uku, wannan wace irin rayuwa ce,wai yanzu idan kana da arziƙi ashe baka huta ba,idan baka dashi ma baka huta ba,ta faɗa tana fashewa da wani matsanan cin kuka,da ƙyar Hajjo tace"insha Allah babu abinda zai faru da Batula,ki duba wannan bugun ƙofar da akeyi ko da bamu buɗe ta ba za a iya ɓallata,aiko bata rufe bakinta ba, Abdallah ya saka mata karfi ya doke kofar sai ga ta aƙasa,shiga yayi ya tarar da su Hajjo atsaye cirko cirko cikin tashin hankali,zubewa yayi agaban Hajjon tare da sunkuyar da kansa ya kasa ce mata komai,Dady jafar ne ya iya cewa garin yaya haka ta faru?shin da gaske ne,an sace Bintu?ya jero musu tambayar cikin san amsar su da gaggawa,A hankali Asma'u tace"da gaske ne ku waye yasanar daku?miƙewa Abdallah yayi ya fita daga gidan ba tare da yace"kan zil ba,Dady jafar ne yayi ƙoƙarin yi musu tambayoyi ba tare da ya amsa mata tata tambayar ba,yace"ya akai haka ta faru?Hajjo da sai yanzu ta iya magana amma da tausayin kanta dana Abdallah ya hana ta cewa komai,ita kam anyi mata taleƙo ta koma,tace"bayan sallar isha babu jimawa suka zo, duk da gidan mu arufe yake amma bugun da sukayi mana cikin nutsuwa da jan hankali shine abinda ya kwashe mu har muka buɗe musu,abinda ya biyo baya ne baiyi mana daɗi ba dan kuwa ta ƙarfi suka ɗauke Bintu tare da saita ta da bindiga acewar su duk wanda ya motsa acikin mu sai sun fasa kan Bintu da bindiga!'ta faɗa tana mai ƙara fashewa da matsanancin kuka,Dady jafar yace"shike nan bari muje nasan zasu iya kara kiranmu zamu san me zamuyi ku kwantar da hankalin ku insha Allah babu abinda zai faru!'daga haka yabi bayan Abdallah,ya bar su Hajjo cikin rashin nutsuwar zuciya...

"Abdallah ya samu, ya kifa kansa da styarin motar har yanzu ko fitar numfashin sa baka jin sautin sa,Dady jafar yace"Abdallah dawo nan na tuka motar!',baiyi masa musu ba ya fito ya koma sit ɗin mai zaman banza.


Tafiya suke kawai ba tare da sun san inda zasu nufa ba gashi har yanzu sun rasa tunanin da zasuyi akan lamarin,kamar daga sama Dady jafar ya tsinkayo Muryar Abdallah yana cewa Dady na samo mafita!'Dady ya danyi slow da tuƙin,kana yace"da Abdallah mecece mafitar?lumshe idanun sa yayi tare da maida kansa ya kwantar yace"zamu kai Dady kamar yadda suka buƙata!'daga nan ban kuma jin abinda Abdallah yake cewa ba, ban ankara ba kawai sai gani nayi Dady jafar yayi ɗan murmushi tare da cewa wannan mafita ce mai kyau!'wayar Abdallah ce ta fara dan wani sauti mai daɗi, dagawa yayi tare da kaita kunnen sa,kamar yadda zuciyar sa ta raya masa wanda ya kira hakan ne ya tabbata, cikin shaƙewar muryar da kanaji kasan sauyata akayi,yace"ya dai ɗan zaki ka shirya?me kake da bukata matarka ko mahaifinka?zan kawo maka mahaifina idan shi kake buƙata,amma ina da sharaɗi!'wata dariya ya sheƙe da ita kana yace"ina jin ka ɗan zaki faɗi sharaɗinka!'Abdallah yace"karka kuskura ka taɓa Bint ko cizon sauro na samu ajikin ta baza kaji daɗin abinda zai biyo baya ba,kuma Ni zan baka lokacin da zan zo dan haka ka bani layin da kasan zan same ka!'nanu yace"lallai yau na kuma yarda ɗan zaki ya girma tunda gashi har kana shirin yi min wayo,to ban yarda da wannan sharaɗin naka na ƙarshe ba,zan kiyaye kiranka akai akai shine kawai abinda nasan zan iya yi maka!'daga haka ya kashe wayar,dan murmushi Abdallah yayi wanda yafi kuka ciwo,

Ƙara gudun motar Dady jafar yayi kana yace"tabbas Abdallah ina zargin Mansur sai dai kuma na rasa dalilin da yasa zuciyata take ƙin karɓar abun!'cikin wata irin murya wadda take cunkushe da ɓacin rai da baƙin cikin kasa kiyaye rayuwar Bintu,yace"Dady a yanzu ba mune abun tausayi ba sune abin tausayin tabbas rayuwar makafin zuciyoyin mutanen nan tana cikin hadari,nan gaba kaɗan zasu zama A baban tausayi a idanun waɗan da basu san abinda suka shuka ba!'daga nan gidan su na asali gidan Dady jafar nan suka wuce,


Washe gari da sassafe Dije ta fito daga cikin babban birnin estate,cike da ɗokin wannan rana, wadda take fatan tazo mata da nasara,wayar tace tayi haske alamar shigowar saƙo,dubawa tayi daga Hajiya ne tana sanar mata cewa taga fitowar ta ga kuma in da take so su haɗu,tana gama karanta wa ta fara kiran Bintu,sai dai kuma kash wayar akashe take,cikin cizon yatsa Dije ta juya akalar kiranta kan Abdallah,shi kam bata sha wata wuya ba ya ɗauki kiran, alokacin Dady ya tasa shi gaba da ƙyar sai ya sha koda ruwan shayi ne,da sallama ya fara,Dije ba tare da ta tsaya wata doguwar magana ba ta shiga zaiyano masa abinda ke faruwa da abinda take so su shirya ayanzu,da sauri Abdallah ya tashi tare da ce mata gashi nan zai zo yanzu,ta ce amma kayi hattara fa bana so ta ganka balle yaddar dake tsakanin mu ta rushe!'yace"insha Allah karki damu!'daga haka suka aje wayar,ɗan kallon Dady jafar yayi wanda tunda ya fara wayar yake kallon sa cike da san gano wanda yake wayar dashi,hanya ya kama zai fita yana cewa Dady yanzu sauri nake idan na dawo zanyi maka bayanin abinda ke faruwa!'jinjina kanshi Dady jafar yayi tare da cewa Abdallah fatan nasara!'yana zuwa ya shiga mota ya ja da mugun gudu,

A cikin kuma safiyar nan ne dai Anty Nafisa ta samu mugun saƙamakon da ya nemi zaucewar ta,wato yaran ta sun tabbatar mata da cewa mutanen nan daga Yola suka taso,kuma sunan Hajjo raɗau ya zauna mata da sunan Asma'u wanda bata manta su ba tun a wancan lokacin,tashin hankali wanda bazai misaltu ba agurin ta,da ta rasa yadda zatayi kawai sai ta ɗora hannun ta aka ta fasa wani gigitaccen ihu wanda yake haɗe da kukan tashin hankali,Abba Umar dake shirin fita dan tafiya gidan Hajjo,da sauri ya buɗe ƙofar dakin nata ya shigo yana cewa'lafiya dai Nafisa?meke damunki?bata iya bashi amsa ba sai wani irin mugun kallo da tabishi da shi a fakaice,tashi tayi ta wuce shi ta faɗa toilet tare da banko ƙofar,ɗage kafaɗunsa yayi tare da ficewa daga dakin,tana jin fitar sa tayi saurin fitowa tare da kiran yaran ta,yana daga wa tace"kawai kusa wa gidan wuta amma kutabbatar da cewa Umar yana gidan, ku saka masa ido dan yanzu ya fito kuma ina tunanin nan suleja zai nufo,kar ku sake kubar wata halitta da rai acikin gidan!'yaron yace"Hajiya Nafisa aikin nan ba zai yiwu da safe ba dole sai cikin dare, zamu saka wuta a gidan!'Anty Nafisa cikin tsawa tace"ni dai koma mai zakuyi ku tabbatar da cewa kun kashe mutanen nan ayau ba sai gobe ba,idan yaso shi ku kama shi a hanya ku fara kashe shi daga baya sai ku koma ku ƙona gidan!'tom ranki ya daɗe an gama in dai mu zaki bamu kuɗaɗe to baki da matsala da mu!'daga haka suka yanke wayar,

Abba Umar dake jikin ƙofar ɗakin Anty Nafisa,babu abinda yake sai zufa jikin shi kuwa wani irin kyarma yake saboda tsabar razana,wani irin tashin hankali ne ya rufe shi tare da mamaki tsanani,me hakan yake nufi?kashe su Nafisa tasa ayi shida su HAJJO?to akan me?me sukayi mata?a ina ta san su?ya akayi tasan inda suke?wai meke shirin faruwa ne?ko dai zarginsa akan Nafisa daidai ne?tabbas Nafisa itace ta salwan tar da rayuwar iyalan sa,ita ce Ummul aba'isin shigar sa wannan halin,cikin sauri ya sauka tare da wani irin gudu,motar sa ya faɗa tare da jan ta da wani irin mugun gudu.


Tunda aka dauko ta bata san inda kan ta yake ba,sai yanzu da ta farfaɗo daga suman da tayi,tun bayan shigowarta cikin ƙungurmin dajin,wanda komai akan idonta ya faru,ko rufe fuskar da ake yi wa wanda akasato basuyi mata ba,hakan ne ma ya bata damar gane cewa daji mai tsananin haɗari suka shigo,razar da tayi ne yasa ta suma,shine bata far faɗo ba sai yanzu wajen misalin ƙarfe tara na safiya, bin ɗan tsukakken dakin tayi da kallo kana ta tsaida idanun ta akan basamuden dake tsaye akanta da sunan gadi,kawar da fuskarta tayi,yayin da idanun ta suka ciko da ƙwalla,ko ya Yah Abdallah zaiyi da wannan sarƙaƙiya da aka saka shi dan komai da yafaru akunnen ta ya faru sai dai ba akan idanun ta ba tunda har yanzu batayi ido hudu da Oga kwatakwata ba,wanda ita kuma fatan ta kenan ganin wanene wannan baƙin azzzlumin,ko da daga haka ƙarshen numfashin ta yazo,yanzun ma bata karaya ba saboda tasan halin gwarzon mijin ta tasan bazai batta agurin nan ba,kuma bazai bari su kashe ta ba,indai har ba Allah ne yayi zata mutu ba,kuma tasan bazai kawo masa Dady Abubakar ba,kuma ko anan ba zata fasa ƙoƙarin ta na ganin bayan azzalumai ba,insha Allah alƙadarin su ya karye karshen zaluncin su yazo..


Ya dade da samun guri ya fake,tun daga zuwan ta har shigar ta ɗan tsukakken lungun da bai wuce kamu goma ba, duk akan idon sa,nutsuwa ya sake yi wajen miƙa hankalin sa kanta,sai da ya tabbatar ta shiga ciki kana shi kuma ya bi bayan ta cikin nutsuwa da sanɗa irin ta ɓarayi,Dije ta samu zaune akan ɗan kututturen dutsen dake girke a wajen tana saƙa da warwara,da sauri ta tashi tare da cewa ranki ya daɗe kin ƙara so?duk da bata ga fuskar matar ba ta tabbatar da cewa murmushi tayi,cikin ƙasai tacciyar Muryar ta ta isa da taƙama tace"Dije tawa Dije aikin ki na kyau yadda ya kamata,maza tashi ina saurarenki ki sanar dani inda Abubakar yake da wannan mutumin ko waye!'cikin yin ƙasa da kai Dije tace"ai ranki ya daɗe Abubakar yana hannun Mansur kuma man sur shine wannan mutumin dakike ta son sani tsawon shekaru amma hakan ya GAGARA,,daɓas taga ta zauna akan ƙasar gurin jikin ta yana wani irin kyarma kamar ana kaɗa mazari,shuru ne ya gifta ta ta wajen kamar babu wani halitta agurin,yayin da Abdallah ya kuma gyara tsayuwar sa yana mai kafe fuskar matar da ido zuciyar shi na dokin ganin fuskar ta ta ainahi.


Yana zuwa yasa su Hajjo suka fito da komai nasu ba tare da ya amsa musu tambayoyin da suke ta jera masa ba,sai da suka shiga mota kana yace"da Anty Asma'u ƴan biyu suna Yola ko? tace e suna can basu dawo ba!'daga haka bai kuma cewa komai ba yaja motar suka fara tafiya,tunda ya fara tafiya ya kula da motar dake binsa,kuma zuciyar shi ta aiyana mashi cewa mutanen Nafisa ne suke binsa,A hankali ya dinga rage gudun motar har ya tsaya agefan hanya,yana kallo suma sukayi fakin abayan motar tasa,Hajjo da ta kula da abinda ke faruwa tace"Umaru mai makon mu guje musu sai kuma kanemi guri ka tsaya!'yace"Hajjo da akwai abinda nake son aiwatarwa!'ƙwanƙwasa glace ɗin window sa da akayi shi ya maido da hankalin sa wajen,zuge glace ɗin yayi,yana kallon yaron da ya tsare shi da jajayen idanun sa da suka sha sukayi tatil,yaron ji yayi kawai ya kasa aiwatar da abinda yayi niya akan Abba Umar,wani irin kwarjini yayi masa,wanda har bai san sanda Abba Umar ɗin ya fito daga cikin motar ba,sai ji yayi yana cewa ɗan samari nasan abinda ya kawo ku gurina ko nace yasa kuke bina!'dafa kafaɗar sa yayi suka fara tafiya, ɗan nesa da su Hajjo suka tsaya,daga nan sukayi magana da Abba Umar wanda sam basu bari naji abinda suka ce ba,na dai ga kawai sunyi hannu da Abba Umar, da sauri, Abba Umar ya koma motar sa yaja ba tare da yayiwa su Hajjo bayanin komai ba..


Sai da taja mintuna a haka kana ta tashi ta kaɗe jikin ta,idanun ta sunyi jajur saboda yanayin firgicin da tashiga,kallon Dije tayi tare da cewa, Dije na gode da ƙoƙarin ki gareni kuma yanzu zan cika miki alƙawarin da nayi miki,daga nan ba zamu wuce ko ina ba sai inda na ajiye miki yaran ki,kuma suna nan babu abinda ya same su kamar yadda na alƙawarta miki!'Dije tace"naji wannan ranki ya daɗe saura ɗayan alƙawarin!'Hajiya tace"ina sane da wannan ma amma shi ina so kiyi min alfarmar bari muje inda yaranki suke sai na buɗe miki fuskata acan!'Dije ta jinjina kanta alamar gamsuwa,sai dai kuma Abdallah fa ya zatayi dashi?wata zuciyar tace"da ita, kema kin san kowaye Abdallah ba zai rabu da ku daga nan ba dole zai biku ko dan sanin manufar ki ta bin matar bayan ba haka kukayi ba,hakan yasa ta sauke guntuwar ajiyar zuciya,tare da bin bayan matar da ta ƙauta taga fuskar ta,


Sai dai kuma abinda Dije bata sani ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login