Showing 114001 words to 117000 words out of 184937 words
mutashi mu roƙe shi kiyi haƙuri ki Kore duk abinda ke kawo miki farmaki da wasu wasi cikin zuciyarki kinji ko!'ya faɗa cikin matuƙar nuna kulawar sa gareta,
Kallon sa kawai take cike da mamakin sa,dama haka yake da matukar tausayi, tabbas tayi mamakin yadda akayi ya tsaya yana nuna kulawar sa akan ta kamar haka,mutumin da tasan baya yin shiri da duk wani abu da zai saka shi yin surutu mai tsayi,ta shi tayi kamar yadda ya Umar ce dan yan zu ya riga ya karya mata zuciya da kalaman sa, sai taji tana matuƙar san jin labarin sa dan ga dukkanin alamu ya sha gwagwarmaya da ƙalubale a cikin rayuwar sa.
Sun daɗe suna salloli duk da dai Bintu dauriya kawai take yi, amma sam bata jin daɗin jikinta da dukkanin rayuwar ta,amma cikin taimakon jarumin mijinta mai tsananin riƙo da addinin sa mai kishin addinin sa ta samu ƙwarin gwiwar ganawa da ubangijin ta,cikin ƙarfin hali da miƙa lamuran su gare shi,basu suka kwanta ba sai misalin ƙarfe uku na dare,daga nan suka sami yin Bacci cikin salama da nutsuwar zuciya,
A cikin wannan safiyar kuma da ta waye Abba Umar ya dawo daga ƙasar Italiya,wanda hakan ba ƙaramin daɗi yayiwa Anty Nafisa ba, tunda ta riga ta sakawa ranta zata yi abinda Bintu ta shawar ta mata,hakan ne yasa tayi masa shirye-shiryen da ta daɗe bata yi masa irin sa ba,shi kansa sai da yayi mamakin hakan,amma dai bai kawo komai cikin zuciyar sa ba,lokacin da ya gama shirin sa ya fito tsaf dashi dan zuwa gaida mahaifinsa da iyayen sa mata har ta gama yi masa duk wani shiri,sai dai yace tayi haƙuri yaje ya gaida iyayen sa,dole tayi masa fatan dawowa lafiya duk da zaƙuwar da tayi suyi maganar datake cin ranta,
Sai da ya fara zuwa ɓangaren Hajjah kana ya fito ya shiga ɓangaren inno,wanda a daidai lokacin ne kuma Bintu da Abdallah suka fito dan zuwa gurin malamin sa malam Nuhu da yace zasu je,tunda ta doso falon ta dinga jin zuciyar ta na wani irin bugu wanda har saida ta dafe ƙirjinta, cikin kulawa Abdallah ya ruƙota ganin tana ƙoƙarin faɗuwa,kallon sa tayi idanun ta cike taf da ƙwalla, ɗan girgiza mata kai yayi kana yasa hannu ya goge mata wadda ta fara zubowa kan fuskarta,tare da jan hannun ta suka fito falon tare da ƴar guntuwar sallama saman leban sa,
A can ɓangaren Dije kuwa tun bayan rabuwar su da Bintu uwar ɗakinta tayi mata waya da ɓoyayyar nomba kamar yadda ta saba,ta sanar da ita a safiyar yau ɗin tana son su haɗu, sai dai bata gaya mata inda zasu haɗu ba, tasan dai sai tabar gidan zata faɗa mata kamar yadda ta saba yi,shi yasa tunda ta tashi take sauri dan tana son haɗuwa da Bintu,saboda tunanin da tayi,akan haɗuwar su da Hajiyar yau,zata gayawa Bintu ta yi ƙoƙarin biyota a baya,tunanin ta anan kuwa,tasan Bintu tana da tunani da wayo,idan taga koda bayan matar zata iya ƙoƙarin shaida ta aduk inda ta ganta, shi yasa take son lallai Bintu tabi ta ayau, tana ganin hakan ma kamar wata hanya ce zata sauƙaƙa musu aiki,cikin hanzari ta gama duk aiyukan ta,tare da kimtsawa ta fita dan zuwa sashen inno,
A can ɓangaren inno kuwa,cike take da farin cikin ganin Umar ɗin,sai da ta cika gaban sa da kayan taɓawa,kana ta samu guri ta zauna,tana cewa Umari na saukar sassafe kenan kayo mana?ya buɗe baki daniyar bata amsa wayar sa ta fara ringin,dan haka ya fasa faɗar abinda zai faɗa tare da zato wayar,ɗagawa yayi duk da cewa ɓoyayyar nomba ce aka kirashi da ita,karawa yayi akunnen sa tare da yin sallama cikin kamilalliyar muryar shi,daga can ɓangaren akace, ina fata dai da Umar Balarabe nake magana?Abba Umar yace"nine Ina sauraren ka!'daga can aka kuma cewa,yauwa to ba komai ne yasa nakiraka ba sai kawai ɗan na tambayeka shin ka shirya haɗuwa da iyalansa da karasa su tsawon shekaru....
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 44 ```
Wata irin zabura Abba Umar yayi tare da miƙewa tsaye,cikin tashin hankali da rawar baki yace"waye kai?sai dai ina kafin ya kuma cewa wani abu tuni ankashe wayar ɗif, Abba Umar gaba ɗaya ya ruɗe ya kasa yarda ma wayar ta mutu sai nanata hello yake, sai da inno ta tashi ta kama hannun sa tare da zaunar dashi cikin nuna kulawa tace"Umarina me yake faruwa ne?ka nutsu ai ina tunanin ankashe wayar,waye yakiraka a waya,yake son tada maka da hankali?hannu yasa ya goge zufar da take sauko masa kamar wanda aka sheƙawa ruwa,ya kasa amsawa inno tambayoyin ta,gaba ɗaya antayar masa da tsohon mikin dake dan ƙare cikin zuciyarsa,inno karki damu wata ƴar matsala ce daga wajen aikin mune!'to dan Allah ka kwantar da hankalin ka kar kace zaka saka yawan damuwa aranka kaji ko!'murmushi yayi wanda kana gani kasan na yaƙe ne,yace"shike nan inno,bari na wuce wajen Hajiya Babba,daga nan zan ɗan shiga na kwanta, sallamar Abdallah ce ta katse shi daga sallamar da sukeyi da inno, yana tafe hannun sa sarƙafe dana Bintu,inno tace"yauwa Abdallah zo ku gaisa da Abban ku Umar shine kuma ya baka auren Bintu!'ta faɗa tana kallon Bintu da ta rakuɓe a bayan Abdallah,tunda inno ta ambaci sunan Abba Umar ta shiga wani Irin yanayi na matuƙar shauƙi da ƙauna, A hankali ta fito daga bayan Abdallah tana takawa har zuwa gaban Abba Umar tare da durƙusawa kamar yadda taga Abdallah yayi,ƙasa tayi da kan ta tana sauraren bugun da zuciyarta keyi.
Abba Umar kuwa tunda ya zubawa Bintu da Abdallah ido ko ƙiftawa ya kasayi,kuma baya fatan abinda zai rabashi da kallon waɗan nan yara da yake kallon su tamkar wasu taurari acikin idaniyar sa,muryoyin su ne da suka gaida shi atare suka yanke masa tunani da ɗimuwar da ya shiga,cikin wani irin fillin da zuciyar shi ta shiga ya dora hannayen sa duka biyun a kawunan su,yana wani irin murmushi mai ɗauke da wani irin yanayi na tsananin tausayin kansa,yace"sannun ku ƴaƴana tunda kuke cikin gidan nan bamu taɓa haɗuwa ba sai yau,ko da yake Allah ne bai nufa tun can zamu gana ba sai yau ɗin,ina fata dai kuna lafiya? gaba ɗaya suka amsa atare har ɗan duban junan su sukayi saboda yadda suke yawan haɗa baki gurin faɗar abu alokaci guda, Abdallah ne ya fara tashi ganin Abba Umar ɗin yayi hanyar fita,itama tashi tayi tabi su A baya Abdallah yace"inno zamu tafi sai mun dawo!'tace"to Allah ya kiyaye ya bada sa'a ya amsa da Amin kana suka fita gaba ɗayansu.
Suna tafe da Abdallah da Abba Umar suna taɓa hira,tunda yake cikin gidan bai taɓa yin hira ko wata doguwar magana da ƴaƴan Alhaji Baba ba,Amma ƙaunar Baffan nasa da ban take azuciyar sa,ji yake tamkar da mahaifin sa yake magana,shi yasa yakejin wani irin nishadi da farin ciki mai yawa a zuciyar sa,Bintu ma dai tana cikin shauƙin ƙaunar mahaifin nata ji take tamkar taje ta rungume shi tace Abbana ina sonka,acikin wannan hali Dady Habib ya same su,shima cikin biyayya suka gaida shi,am sawa yayi fuska cike da fara'a yace"kai kam Umar kaci sa ar ƴaƴan naka har rakiya suke maka,mu da muke tare da su kullum har yanzu sun kasa sakin jiki damu kamar waɗan da zamu cinye su!'ya fadi maganar cikin yanayin zolaya,ɗan ƙasa da kai Abdallah yayi bai ce komai ba haka nan fuskar sa ba yabo ba fallasa,Abba Umar yace"kasan haɗuwar jini ya faɗa shima cikin zolayar yana miƙawa ɗan uwan nasa hannu dan su daɗa gaisawa,daga nan dai sukayi sallama ya wuce part ɗin Hajiya Babba Dady Habib ma ya shiga falon inno,
Abdallah ya kalli Bintu lokacin da yaga tabi bayan mahaifin nata da kallo,kamo hannun ta yayi cike da tausayi, suna ƙoƙarin shiga motar da Yahya tuni ya buɗe musu yana jira su shiga ya ja,sai ga Dije da sauri har da ɗan hakinta daga Ni dai tayi gudu kafin ta cimma su,tsayawa sukayi gaba ɗaya suna kallon ta sai da ta samu daidaituwar numfashin ta kana suka gaisa da Abdallah Bintu ma gaida ta tayi,Dije tace"ko zaku bani minti biyu zan ɗan yi magana da Bintu? Abdallah ya saki hannun Bintu tare da cewa babu damuwa!'motar ya shiga,ita kuma Bintu suka keɓe da Dije,duban Bintu tayi cikin nutsuwa tace"Bintu ko da hanyar da zaki bi dan bin sahu na A yau? Bintu tace"ban fahimta ba!' ɗan numfasawa Dije tayi tare da ɗan duba hagu da daman ta kana tawa bintu bayanin abinda take nufi da kuma manufar ta naso ta bi bayan nata a yau,sai a san nan Bintu ta fahimci Dije da manufar ta,cikin fargaba da sanyin jiki tace" anya kuwa Mama Dije babu matsala?Dije tace"Bintu wai me yasa kwana biyu naga gaba ɗaya baki da ƙwarin gwiwa ne? mai yake faruwa dake?ko tun maganar mu ta juya ne ya sauya ki haka?wato dai nasihuna basu shiga kunnan ki ba ko? Bintu ta goge hawayen da suke ƙoƙarin zubo mata tace"mama Dije kiyi haƙuri zanyi duk abinda kika Umar ce Ni,amma zan fara gaya masa sai musan shirin da zamuyi wajen bin naki,in yaso idan ta sanar dake inda zaku haɗu sai ki sanar dani ta hanyar kira ko text!'dije tace"insha Allah Bintu, kuma insha Allah mune da nasara lokacin mu ya fara, su sun gama nasu mu kuma yanzu muka fara namu,da haka suka rabu, tunda ta shiga motar tayi jugum ta kasa gaya masa komai,cikin taushin murya ya kira sunan ta tare da zuba mata narkakkun idanun sa, masu saka ta yin abu koda bata so ba,masu saka mata nutsuwa da saukar mata da kasala,hakan ne yasa ta shiga sanar dashi maganar dasu kayi da Dije,ba tare da yace"mata komai ba ya ɗauki waya ya kira, tare da cewa yauwa kazo min da mashin ɗin yanzu ina buƙatar sa cikin gaggawa!'daga haka ya kashe wayar, tafiya suka farayi domin fita daga cikin ESTATE ɗin.
Tunda ya shiga ɓangaren Hajiya Babba bai samu wata cikakkiyar nutsuwa ba saboda hankalin sa ya rabu kashi kashi,ga tunanin wan da yayi masa waya ga kuma tunanin hotan Bintu da ta kasa ɓacewa daga fuskar sa da zuciyar sa,ba tare da ya cika lokacin da Yakamata ya kai ba,ya miƙe yana cewa Hajiya Babba Ni zan je na ɗan kwanta ina so zan ɗan yi bacci!'hajiya bata takura masa da tambayar sa meke damun saba dan tasan tatsuniyar gizo bata wuce ƙoƙi, addu'a kawai tabishi da ita,
Wayar Bintu ce ta ɗau haske alamar shigowar saƙo, tare suka kai hannun su kan wayar ita da Abdallah,wani irin musayar kallo suka tsaya yi ga hannayen su a haɗe kan waya, Bintu ce ta fara janye idanun ta da hannunta,tana kuma jin wannan yanayin na shigar ta,ɗaukar wayar yayi ya buɗe sakon da ya shigo,sai yaga daga Anty Nafisa ne saƙon,ɗan satar kallon ta yayi sai yaga gaba ɗaya hankalin ta baya kan sa,hakan ne yasa ya buɗe saƙon tare da karantawa A hankali batare da Bintu taji ba,
Bintu na gamsu da shawarar ki zan tambayi Umar damuwar sa ko zai gaya min duk da cewa na aikata wani abu daban batare da sanin ki ba,ba dan komai kuma nayi haka ba sai dan inaso in zunguro damuwarsa tare da bugar cikin sa akan abinda nake tunani a game da shi,to bai shigo ba dai har yanzu ina jiran sa domin ganin ko aikina yayi kyau,ba lallai bane sai kinji komai amma dai nasa ankirashi awaya an bugi cikin sa tare da zunguro damuwar sa yadda idan ya shigo na tambaye shi ba zai taɓa iya ɓoye min ba,a wannan karon dai nayi abin kirki nayi abu da basirata ba basirar Bintu ba,daga haka ta saka alamar dariya,ɗagowa yayi daga kallon wayar sai karaf ya tsinci fararen idanunta akan sa,kawar da kan sa yayi tare da kashe wayar dan baiga amfanin wan nan saƙo ba kuma yana ganin kamar zai iya tada hankalin ruɗaɗɗiyar Bint ɗin tasa,kar bar wayar tayi daga hannun sa tana cewa waye ya turo saƙo?bai damu dan ta karɓi wayar ba kasan cewar ya riga ya goge saƙon,hakan ne yasa bata ga komai ba,sai dai kallon tuhuma da tabi kyakykyawar fuskar sa da shi,lumshe idanun sa yayi, yayi tamkar bai san me take nufi ba,ita kuma hakan ne yabata damar cigaba da kare wa fuskar sa kallo tare da kaifafa kallonta akan ɗan zagayayyen gemun sa da yake matuƙar burgeta, a rayuwar ta tana son wan nan Abu a fuskar Abdallah shi yasa take yawan satar kallon sa,dan sam bata gajiya da kallon fuskar tasa,jitayi yace"kallon fa?wani irin kunya ne ya rufeta wanda yasa tayi saurin rufe kanta cikin hijabin ta kuma shine dalilin da yasa bata kuma ɗagowa ba har suka je inda zasu,a nan ɗin ma daƙyar tafita daga motar sai faman sinƙe kai takeyi.
Suna shiga zauren malam bayan anyi musu iso,ji tayi kanta yana juyawa har tana ƙoƙarin faɗuwa da sauri Abdallah ya tarota jikin sa,suka zauna, cikin girmamawa Abdallah ya gaida Malam,daga nan basu sake cewa komai ba,bayaga tsurawa Bintu ido da malam yayi yana nazarin al amarin ta,can ya ja dogon numfashi kana yace"Abdallah kayi tunani mai kyau da ka kawo yarinyar nan,saboda akwai al amari mai girma wanda yake a lullɓe tare da baiwar ta,ɗan sihiri ne yayi tasiri ajikin ta amma da baka kawota da wuri ba abin zai iya girmama!'shiru yayi na ɗan wani lokaci kana yaci gaba da cewa,yarinyar nan sai da aka sha wahala kafin wannan sihirin yayi tasiri ajikinta,kuma damar da aka samu akanta shiyasa baza a zaunaba ake kuma binta da abun,amma dai har yanzu ba ayi nasara akanta ba,saboda jikin ta ya ginu kuma tana cikin kariyar ubangiji,dan haka yanzu baza musha wahala akanta ba!'wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya Abdallah ya sauke,yana kallon fuskar Bintu da bacci yayi awan gaba da ita,Tofi malam yayi mata tare da addu'oi sai magunguna da ya haɗa mata da yadda zata dinga amfani da su,ya miƙawa Abdallah tare da cewa gashi nan insha Allah kafin kazo karbar wasu ta samu lafiya, Allah Ubangiji ya daɗa karemu daga sharrin maƙiya, Abdallah ya amsa da Amin kana ya ajiye wa malam sadaka,ganin yawan kuɗin shi kuma yace"ba zai karɓa ba sadaka kawai yake buƙata,badan Abdallah yaso ba ya kwashe kuɗin sa kana sukayi sallama ya ɗauki Bintu kamar wata ƴar tsana ya nufi mota da ita,yana saka ta cikin motar ta buɗe idanun ta,gyara zaman ta tayi tare da kawar da fuskarta can gefe,suna fara tafiya wayar Bintu ta kuma yin alamar shigowar saƙo, wannan karon ma shine ya ɗauka,wan nan karon saƙon Dije ne,inda take sanar dasu ta fito ta kuma gaya musu inda Bintu zata zo ta same su,cikin sauri Abdallah yace"da Yahya maza faka motar nan kajira mu anan zamu dawo!'a kuma lokacin ne samuyal ya kawo masa a daidai ta,lokaci ɗaya naga Abdallah ya sauya kama wasu kaya ya saka baƙaƙe tare da wata hular gashi babu abin da zai sa ba zaka ce masa tsoho ba,dan sak ya juye wata suffar da ban,Bintu dai saboda tsabar mamakin sa tsayawa tayi tana kallon sa baki buɗe,ɗan ɗage mata gira yayi lokacin da suka haɗa ido da ita,tura baki tayi tare da cewa kai ka ɓoye kanka Ni kuma a ina zaka ɓoyeni?bata ankaraba taji ta cikin jikin sa yayi mata mayafi da rigar dake jikin nasa,cikin wata irin murya yace"anan zan ɓoyeki Bint duk San da kike buƙatar ɓuya kizo Ni zan ɓoyeki nayi miki rumfa yadda babu wanda zai ganki balle ya cutar dake!'wani irin rawa jikinta ya shigayi saboda wani shauƙi da ya lulluɓeta wanda ita karan kanta bata san komeye ba, ta dai samu kanta da matukar jin daɗin kalaman ogan nata wanda har saida ta kuma cusa fuskar ta tana shaƙar sassanyan ƙamshin sa me canja mata tunani,gaba ɗaya sun shiga cikin wani yanayi na matuƙar shauƙi,amma su duk basu san da haka ba, Bintu tana ganin kamar yadda yake matuƙar tausaya mata ne yasa takejin kanta a wannan yanayin,yayin da shi kuma yake ɗaukar haka amatsayin tausayi da kuma kasantuwar ta ƴar uwar sa ta jini wadda a yanzu ita kaɗai ke gare shi wadda zai kalla ya bigi ƙirji yace"ga ƴar uwar sa,ƙarar da wayar Bintu tayi ne ya dawo dasu cikin hayyacin su,cikin sauri ta ƙwace kanta daga riƙon da yayi mata tare da rarumar wayar tana karawa a kunnen ta, muryar Dije taji cikin faɗa faɗa tana cewa Bintu wai me kika tsaya yine?Ni fa har na kusa ƙara sawa wajen!'cikin rawar murya Bintu tace"ga,,, gamu nan mun taho!'kar ɓar wayar yayi daga hannunta bayan ya kashe,miƙa mata wata doguwar riga yayi baƙa me hula yace"maza saka kar mu ɓata lokaci!'karba tayi ta zura kana suka fito,a tunanin ta samuyal ne zai tuƙa nafef ɗin amma sai taga saɓanin haka,dan Abdallah wani mamakin ya kuma barinta dashi dan shine ya zauna a mazaunin draver ya kuma tada nafef ɗin,ganin ta tsaya taki shiga ya sashi cewa bazaki shiga ba kin san dai ba jiran mu zasuyi ba!shiga tayi batare da tace masa komai ba,sai dai zuciyarta cike take da mamakin sa da kuma tambayoyi.
Cikin gwaninta da ƙwarewa yake jan nafef ɗin har suka zo inda Dije ta kwatanta musu,sai dai daga can baya ya tsaya da nafef ɗin, juyowa yayi yana duban Bintu cikin bata ƙwarin gwiwa yace"ga ta inda suke can na sanki kina da dabara ba sai nayi miki bayanin yadda zaki ɓoye kanki ba!'jinjina kanta tayi tana ƙoƙarin fita,kama hannun ta yayi kana A hankali yace"Bint ki kula kinji,kiyi addu'a nima zanyi miki ki,ba tsayawa zakiyi sauraran wani abuba kawai ƙare mata kallo zakiyi,koda Allah zai sa ki ki iya gane ta a duk yanayin da kika ganta!'fita tayi da sauri ta nufi wajen da take da yaƙinin cewa su Dije suna gurin,guri ya samu ya ɓoye kan sa, sai dai ji yake kamar