Showing 183001 words to 184937 words out of 184937 words

Chapter 62 - KUDURAR ALLAH COMPLETE BY FATIMA Y ADAM

21 Jul 2024

16870

da Bintu taji labarin cikin da ummin ta take dashi sai da tayi kuka tayi suddar shukurr,sai kuma na ƴan uwanta wanda hakan yasa ta farinciki da kuma jin kwadayin samun ciki, ,fafy ne yake faɗa mata lokacin da suke waya,ya kuma sanar da ita an saka ranar usainar sa,daɗi kan daɗi ke nan,ganin tana ƙoƙarin fasa masa dodon kunne kawai sai ya kashe wayar yana dariya,wato dan bata san shima ya kusa zama Baba akaro na biyu bane, da ji zatayi kamar tayi tsuntsuwa, kawai ta taho naija, Abdallah yana dawowa da zan cen da ta fara tararshi ke nan,sai da ta gama faɗa mashi kuma wai sai ta saka masa kuka itama sai yayi mata ciki tunda su Taufiƙa ma suna dashi, bayan kuma ta riga su yin aure amma suka zo suka rigata,a kullum wautar Bintu mamaki da dariya take bashi amma kuma da yayi wani tunani sai yaga ai shi gaba ta kaishi,dan haka sai ya matseta cikin jikinshi yana cewa yi shuru my ukty ciki kike so ba?ta daga kanta kamar wata ƙaramar yarinya,yace"to maza share hawayenki insha Allah yau zan miki ciki,bazan ƙyaleki ba har sai na tabbatar da cewa na dasa ƙwaina a nan!'ya faɗa yana shafa kan mararta,dariya tayi cike da farin ciki tana da ɗa rungumo shi jikita tace"yauwa my zauji!'

Allah mai ƙudura da irada gagara iko gagara misali,sai ga shi maganar Abdallah ta tabbata dan kuwa tsakanin ranar da yau da ta zagayo wata ɗaya cif, Abdallah ya tabbatar da cewa ya dasa ɗan sa ko ƴarsa a marar Bintu,shuru yayi dan yana so sai ya tabbatar da hakan,yau tunda ta dawo daga makaranta take kwance ta kasa tashi ko da abinci taci,dan ma gurinta tsaf yake kamar babu halittar dake motsi acikin gidan,saboda tsananin tsaftarshi da ƙamshin da yake tashi,a gurin,a haka ya shigo ya same ta kamar ruwa,cikin sauri ya ɗauke ta yana dubata kamar wanda akace masa wani abu ya sameta,yace"my Bint meke damunki?langaɓar da kanta tayi akafadarshi tana cusa kanta a wuyanshi,ba tare da ta bashi amsar tambayara shi ba, tace"wayyo my zauji, inason wan nan ƙamshin naka dan Allah kabarni in kwana ina shakarshi!'ba tare da yace"mata komai ba ya ɗaga ta suka nufi bedroom kana yace"anya my zaujaty babu ajiyata acikin nan naki? bari dai na bin cike ki sai hankalina yafi kwanciya!"zaro manyan idanunta tayi tace"amma dai ba allura zaka mun ba ko? yace"haba my jewel ya kamata ace kin daina tsoran allura tunda kinga fa kin kusa girma!'bata gane abinda yake nufi ba dan haka sai tayi rau-rau kamar zatayi kuka,cikin sauri yace"nifa bance zanyi miki allura ba,duba ki kawai zanyi!'hakan da yafaɗa sai ta hakura yayi mata duk wani binciken da yakamata,bata ankara ba sai ji tayi yana juyi da ita a tsakar dakin tare da bin ko inan ta da wani zazzafan kiss,wanda har sai da ya ruɗa ya sauya mata yanayinta abinka da dama wadda take kusa saboda cikin da ke jikinta yana ɗan sata jin bukatar mijinta,ai kuwa dai biye masa tayi suka jika junansu da ƙauna mai tsayawa a zuciya da ruhi,bayan sun sami nutsuwa ne ya mamayeta da dukkan jikinsa yayi mata rumfa da faffaɗan ƙirjinsa, kana cikin so da kulawa yace"my ukty sai ki shirya dan kin kusa zama Ummu nan da wata takwas!' ya faɗa yana yi mata nuni da yatsunsa,ganin kamar bata fahimceshi ba sai ya kama kunnen ta yayi mata raɗa dariya ta saka tare da ƙanƙame shi tana mai jin farin ciki na mamaye duka nin ruhinta.

Wata sabuwar kulawa da soyayya Abdallah ke bawa Bintu yayin da duk gida ya ɗauka kowa murna da farin cikin ƙaruwar da suka samu yake,burin Alhaji Baba ya cika zuri'arsa ta kasance cikin walwala da jin daɗi,

Abdallah ya samu nasarar aikin da yaje yi, acikin wata takwas dan haka ya zauna Bintu ta ƙarasa karatunta kafin nan suka jiyo gida naija,


Taufiƙa ce ta fara sauka ta haifi dan ta namiji sai Rahima, daga nan kuma sai Ummi Laila,kamar layi abin sai ya zama abun burgewa saboda yadda suke ta haihuwa ajere,Anty Asma'u ma ta haifi ɗanta namiji,sai Anty Samira da ta haifi namiji itama,Bintu dai itace karshe dan da akwai tazara tsakanin su,


Alhamdulillah masha Allah bayan wata uku Bintu ta san kato yarinyar ta mai kama da Abdallah da Ammi,bazan iya fada muku irin farin cikin kin da bayin Allah nan suka shiga ba, sai dai kawai mutaya su da addu'a,an sakawa yariyar suna yusra,

Bayan daidai tuwar al'amurane,Alhaji Baba ya Tara dukkan alhalin sa,ya sanar da su cewa duk ana so su bada shawara, mai kyau akan diamon ɗin,yace"na zauna nayi dogon nazari akan al'amarin diamon ɗin na kuma na gano cewa cigaba da zamansa acikin zuri a ta ba karamar fitina bace"dan haka nake neman shawarar ku akan yadda za'ayi,amma kuma Ina so ku tuna cewa diamon ɗin nan ba mallakina ne Ni kaɗai ba,nida Abubakar ne dan haka inajiran shawarwarinku!'Baffa Hashir ne ya ɗanyi gyaran murya tare da ƙara daidaita zaman sa,kana yace"Ni dai aganina tunda abun ya zama haka me zai hana a kira masana sirrin diamon ɗin a sirran ce su siya tunda kai kasan kan harkar in yaso sai ku kasa kuɗin gida biyu kowa abashi haƙƙinsa!'alhaji Baba yace"wannan shawarar tayi ko da wani mai magana ya tambaya yana bin ƴaƴan sa da matansa da kallo,kowa dai ya yi na AM da shawarar da Baffa Hashir ya kawo,bayan Alhaji Baba ya tabbatar da gamsuwar su,sai ya dora da cewa,to Ni kuma insha Allahu idan An bani kasona zan rabawa iyalina duka!'Dady Abubakar yace"Alhaji Baba ni idan anbani me zanyi da ita?dan haka na bar maka ka haɗa duka ka rabawa zuri'ar ka!'gaba ɗaya falon yayi tsit ana jiran jin ta bakin Alhaji Baba,cikin nuna daddako yace"a'a Habu baza ayi haka ba ai kaima kana da magada, ga matarka ga ƴaƴan ka har da mahaifiyar ka dan haka baza a shiga haƙƙin su ba!'cikin sauri Hajiya zulaihat tace"wallahi Alhaji na yafe dani da yara na baki daya har ga Allah!'cikin tabbatar da hakan su Abdallah suka jinjina kai, dan haka sai ya juya gurin Hajiya Babba dan fitar da nata haƙƙin,kafin yace"komai ta rigashi da cewa haba Alhaji yanzu dan Abubakar yayi maka kyauta sai na amince zaka karɓa? bayan ina da tabbacin cewa bakai zakayi amfani da ita ba,kuma Hausawa suna cewa da kai da kaya duka mallakar wuya ne!'murmushi yayi cike da farin ciki,kana yace"za araba kudin da aka sayi diamon ɗin nan gida uku,kashi ɗaya za akai gidan marayu,kashi daya zamu gina asibitoci da masallatai da kuma makarantu, ɗaya kuma zan kasaftawa dukan ahlina ban cire kowa ba har surukai!'gaba ɗaya falon suka dau kabbara,a hankali ya kuma maida duban sa kan Dady Abubakar tare da cewa habu a ina wan nan diamon ɗin yake?so nake ka faɗa da bakinka kamar yadda akaso ka faɗa ɗin!'Hajja ji tayi kamar ƙasa ta tsage ta shige dan tasan bakar magana Alhaji Baba ya yaba mata,Dady Abubakar cikin bin umarnin mahaifinsa ya ɗanyi gyaran murya tare da cewa a bayan ɗakin Hajja muka binne shi Ni da kai kuma har rana irin ta yau yana gurin,kuma a yau da izinin Allah na tanoshi!'ya faɗa tare da ɗauko diamon ɗin ya nunawa dukan al'ummar dake zaune a gurin Hajja kuwa kamar ta nitse dan har gobe bata daina nadama da danasanin abin da ta aikata ba, tabbas ko yanzu Allah ya kuma nuna mata ishara ashe duk wahalar da ake kan diamon ɗin yana cikin wannan estate din kuma abayan ɗakinta,gaba ɗaya falon ya dauki kabbara saboda imanin da ya kuma shigar su,idan ba Allah me ƙudura da irada ba waye zai yi haka,(gashi dai duk sun gama bulayi da daukar zunubi kuma ƙarshe abin ya dawo wajen su su zasu amfane da dukiyar,Hakika hakuri shi yake tadda rabo,kuma duk abinda haƙuri bai baka ba,tsiya bazata taɓa baka shi ba, Allah ya kiyaye mu da aikata mummunan aiki, Allah ya bamu ikon tuba tun bamu rasa damar tuba ba Amin) addu'oi sukayi kana daga nan suka watse kowa jikinsa a sanyaye.

To alƙawari dai ya cika duk abinda suka shirya akan diamon Allah ya basu ikon gabatarwa, Alhaji Baba ya cika alƙawarin da yayiwa iyalansa,dan kowa sai da ya tashi da kusan miliyan biyar biyar,to Allah dai ka bamu dukiya mai amfani.

BAYAN SHEKARA HUƊU,,,

Abdallah ya cikawa Bintu burinta dan kuwa ya bude mata dan kareta gidan abinci wanda suka zuba masa manyan ma'aikata.


Bintu ce zaune a cikin gadin ɗin da yake mamaye da korayen ciyayi da fulawowi, rubuce-rubuce take tayi tana lissafin kayan da za ayi mata order na restorent ɗin ta wanda a yanzu ya zama guda uku saboda nasara da cigaban da aka samu a kasuwancin abincin,Bintu bata zuwa ko ina ta ɗora mutane masu amana wadanda suka karanci abun,wasu daga danginta ne na ɓangaren ummin ta,wasu ƴaƴan ƴan uwa ne aka tallafa musu,shi yasa kullum har kokinsu suke ci gaba ita da jigon ta uban ƴaƴan ta wato Abdallah Abubakar Balarabe,A,A,B ke nan,duƙufar da tayi ne har bata san sanda yusra ta zo gurin ba, Sai dai tashin rigimar ta da taji,ɗago kanta tayi cike da gajiya tace"o my yus Ina abbun naki kika taho nan ki dameni bayan guduwa nayi saboda ku!'kin gudu baki tsira ba ke nan!'abdallah ya faɗa yana takowa inda take,ɗan tura bakinta tayi kana tace"kai ya Akey ku ɗan barni mana na kusa gamawa fa!'zuwa yayi ta bayanta ya zagayo da hannayen sa kan cikinta yana shafawa a hankali,yusra kuwa ture takaddun da suke kan cinyar ummin ta tayi ta haye cinyar tana cewa, Ni ci kaini gidan cu fadil jamuyi washa!'dan matsa bakinta Bintu tayi, tana cewa aike ce washan, baga Abbunki nan ba sai ya kaiki!'lumshe idanunta tayi jin tafiyar tsutsar da yake mata kan cikinta,yace"hi my princess zuwa mukayi mu ganki sai mu koma,amma kiyi haƙuri da distorbing ɗinki da mukayi,kin san idan bamu ganki ba ne baza mu sami natsuwa ba,ga kuma new baby dake son jin muryar Abbun shi da yayarshi!' ya faɗa yana tura hannun shi ikon mararta,shafa kyakykyawan sajen shi tayi tare da cewa,shi ke nan anyi muku AFUWA,kana ta janye hannun shi daga jikita tanayi mishi nuni da yusra,ɗan shafa sumar shi yayi,kana yace"zan kai yusra wajen su fadil,dan haka sai ki shirya tarbata!'tace"naji kuje kafin ku dawo na gama shirya order ta!'lan gaɓar da kanshi yayi,kamar wani maraya tare da hade hannayen shi,yace"ai baki ce kin yafe mana ba!'tace"na faɗa mana, Sa dai idan mai-maici kikeso?dage mata gira sukayi shida ƴar tashi,lumshe idanunta tayi tana jin farinciki na shigarta ta kowane ɓangare,a hankali tace"My zauji and my princess yusra,kuje nayi muku AFUWA,amma SANADIN ƘADDARAR MU DATAZO DA HASKE!"yeeh shi da ƴar tashi gaba ɗaya suka saka ihu,dariya Bintu tayi tana mamakin Abdallah da yadda rayuwar shi ta canja,duk da cewa wannan halin nashi yana nan amma sam ita baya yi mata,ya maida kanshi yaro soko a gabanta,ita kam babu abinda zatace da Allah sai godiya Alhamdulillah masha Allah,a fili ta faɗa sai suma suka ɗauka da faɗin Alhamdulillah masha Allah,nima Fatima y Adam nace Alhamdulillah masha Allah,

Godiya ga Allah subhanahu wata'ala da ya bani ikon kammala wannan littafi Mai suna ƙudurar Allah,ina fatan mu amfanu da darasin dake cikin sa,kuskuren dake cikin sa kuma Allah ya yafe min, Allah ka yafewa dukkan al'ummar musulmi, Allah ka bamu ikon bin abinda yake daidai,

Sai mun haɗu a sabon littafina mai suna ƘADDATA SANADIN HASKE, I DAN ALLAH YA BAMU ARAN RAI DA LAFIYA,,,,

INA ƘAUNARKU MASOYANA ADUK INDA KUKE,,,,

KADA KU MANTA DA SUNAN SA NA KUƊIINE AKAN FARASHI MAI RAHUSA ,,,,ƘADDATA SANADIN HASKE.....ZAIZO MUKU NAN BADA JIMAWABA.....


TARE DA ALƘALAMIN✍🏽 FATIMA Y ADAM

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login