Showing 66001 words to 69000 words out of 184937 words

Chapter 23 - KUDURAR ALLAH COMPLETE BY FATIMA Y ADAM

21 Jul 2024

16907

duk da bazai fahimci komai aciki ba haka yayi gaba dasu batare da nasan abinda zaiyi dasu ba.

Da gudu ta ƙara sa ta tankoɓe hannun sa dayake shirin kai wa bakinsa, kallon ta yake cike da mamaki,ita kuma abincin tabi da idanu,cikin wani irin tashin hankali da ruɗani tace"kaci abincin? cikin mamakinta yace" ke meye hak...murɗawar da cikin sa yayi shi ya hanashi ƙara sa tambayar da yaso yi mata,ƙara riƙe cikin yayi cikin jin matsanan cin ciwo, Bintu wani irin kuka tasaka mai tsuma zuciya,kafin ta ankara Abdallah ya faɗo daga kan kujerar dayake kai yana wani irin juyi na tsananin azaba,riƙe shi tayi tana cigaba da kuka cikin matsanancin kuka tace"wayyo Allah na shiga uku yazanyi da rayuwata Ni Bintu wa zai fitar dani daga wannan mugun zarge?Allah kafitar da Ni banji ba bangani ba,bani da laifin komai ga bawanka da baiyi wa kowa laifi ba suna san ganin bayansa me yasa kuke san kasheshi me yayi muku? saboda tashin hankalin da take ciki har bata san lokacin da suka baiyana a falon ba Dady Habib ne yayi saurin cicciɓar Abdallah yana cewa maza muje asibiti Yakamata mu fara kaishi kar gubar tafara aiki har tayi ajalin sa!'Dady Mansur yace"kuje Ni ina nan saboda na kira police,inno kuwa dasu Taufiƙa harda Hauwa'u da bata jima da dawowa gidan ba,Dady jafar da Dady Habib ne suka tafi dashi asibiti, Bintu kuwa gaba ɗaya kukan ma ta neme shi ta rasa, sai yaune ta tabbatar ashe duk kukan da takeyi abaya na rahmane ashe kukan ma akwai ranar nemansa? Alhaji Baba ta kalla da tunda ya shigo ya zauna ya sunkuyar da kansa ƙasa,baice uffan ba,Hajiya Babba kuwa cikin nutsuwa ta ƙarasa kusa da Bintu ta dafa kafaɗarta wanda sai alokacin Bintu ta kula da ita,tace"Bintu gaya mana abinda ya faru kinji? ki kwantar da hankalin ki!' Dady Mansur yace"haba Hajiyarmu ai ba anan zata amsa tambayoyin ba sai taje can police station tukun dan mu baza ta gaya mana gaskiya ba!'Hajjah tace" kai bana san shashanci,ka bari yarinya tayi mana bayanin abinda ya faru kafin zartar da ko wane irin hukunci!'Hajjah ce tai mata magana a wannan karon cikin taushin lafazi tace"Bintu,gaya mana abinda ya faru? rawar murya ta farayi saboda ita bata san me zata ce ba,amma dai kawai zata faɗa musu gaskiya duk da dai tasan Allah ne kawai zai ƙwaceta daga wannan mummunar zargi,cikin tashin hankali tace" wallahi ban san komai ba Hajjah ɗakina na shiga na tarar an ajiye min wasiƙa,da na duba wasikar sai naga an rubuta an saka guba A cikin abincin Abdallah wallahi shine na fito da gudu dan nazo naga ko baici abin cin ba na zubar shine na haɗu da Sayyid ya bani wayata!'Dady Mansur yace"to lauya munji wannan ƙaryar shi kuma saƙon da Sayyid ya gani anturo miki fa? cikin mamaki tace" wane saƙo Ni ba wani saƙo da aka turan,(sanadin karbar wayarta da Abdallah yayi sai tayi tunanin tunda haka ta fara faruwa gudun tsautsayi gara ta goge duk wani saƙo dake cikin wayar,shi yasa Sayyid bai ga ko wane saƙo ba sai wanda aka turo A lokacin kuma da ɓoyayyar nomban)Bintu tayi mamaki ƙwarai dan bata san ta bar wani saƙo a wayar ba, Sayyid ɗin ne yace"Hajjah A karɓi wayarta a duba in dai bata goge ba za A ga saƙon wallahi ba sharri nayi mata ba!'Hajiya Babba ce ta karɓi wayar da kanta kana ta lalubo saƙon wan da bata sha wahalar ganin sa ba saboda dama Sayyid bai fita daga kan enbox ɗin ba,ga abinda saƙon ya ƙunsa Bintu kin tabbatar kin zuba masa gubar nan? bana so yau Abdallah ya kwana a duniya,shike nan abin da aka rubuta,wani irin juwa da layi Bintu ta shiga yi kan ka ce me sai gata yaraf aƙasa babu alamun numfashi,Abin mamaki babu wanda yayi ƙoƙarin tallafawa Bintu saboda dukkanin su sun shiga shock da jin wannan al'amari mai girma,wayar Dady Mansur ce tayi ringin ɗagawa yayi tare da cewa to to gamu muna ciki bari nasa a shigo daku!'kashe wayar yayi yana cewa maza jeka Sayyid kashigo da inspector lawan,da sauri ya fita dan shigowa dasu har zuwa yanzu babu wanda aka samu d yayi wani abu kan suman da Bintu tayi, Alhaji Baba ne ya miƙe tare da fita daga falon,har haɗa hanya yake kamar zai faɗi saboda har yanzu baya cikin nutsuwarsa, Siddiqa ce tayi saurin kamashi dan ta taimaka masa ita ta raka shi har part ɗinsa,

Sai da su inspector lawan suka shigo kana Dady Mansur ya ɗauki ruwa ya sheƙawa Bintu A fuska, ajiyar zuciya ta saki kana ta buɗe idanunta da sukayi mata nauyi, Dady Mansur yace"to gata nan ku tafi da ita na gaya maka kisan kai take ƙoƙarin yi yanzu dai yaron yana asibiti bamu san halin da yake ciki ba duk abinda ya kamata zakuji daga baya!'wata ƴar sanda ce ta ƙara sa kusa da Bintu tare da kama hannun ta,batare da wata gaddama ba Bintu ta bita saboda tariga tasan bata da sauran kalamin kare kai ko da da akwai ma baza su yadda ba,suna kallo aka tafi da Bintu ba tare da sun iya dakatar wa ba,jiki A saɓule suka fita daga falon zuciyoyinsu cike da tunanika iri-iri.


Tunda suka kaita suka rufe babu wanda ya ƙara bi ta kanta,saboda baza a fara taɓa fayal ɗin ta ba har sai anji sakamakon lafiyar Abdallah tunda su dai yanzu sun tabbatar Bintu mai laifi ce,ƙarewa gurin kallo tayi wai yau itace akarufe cikin magarƙama yanzu gaba ɗaya tunanin ta yana wajen san sanin halin da Oga Abdallah yake ciki, wani irin tsorone yake kamata idan ta tuna Abdallah zai iya mutuwa,ba kuma wai dan za'a kasheta ba kawai shiɗin ne bata san yabar duniyar yanzu,to wai waye yake san ganin bayan ta ita da Oga Abdallah shi waye acikin gidan? A cikin mutanen da suke nuna mata tsana bazata iya cewa ga wanda zai aikata haka A garetaba idan tayi duba da cewa wannan karon Abdallah suke so su kashe,to ko Anty Nafisa ce'zatayi mata haka saboda taƙi karɓar tayin ta? Anya kuwa itace? mugayen gidan nan fa suna da yawa ga hajiyar Dije ma da babu wanda yasan ta,ko ita ma zata iya aikata haka,to kuma waye ya kawo mata paper ya Ajiye dan ta gani? dafe kanta tayi saboda matsanancin sarawar da yake mata bata san wazata ɗorawa wannan alhakin ba zata iya zargin wanda bashi bane kamata yayi kawai ta barwa Allah shi zai saukar da ƙudurar sa da girman ikonsa kuma shi zai kawo mata ɗauki,tayi yaƙini wannan duk jarrabawa ce A gareta dan ya gwada imanin ta kuma zatayi ƙoƙarin cinyewa insha Allah.


Likitoci ne akan sa kusan guda biyar ko wannensu da binciken da yake yi ƙoƙarin su shine suga sun fitar da gubar tun kafin tayi masa illah, to Alhamdulillah anyi nasara saboda bai kai ga cin ta da yawa ba shi yasa ma har akasamu rayuwar sa, allurori sukayi masa daga nan suka fita suka barshi dan jiran farfaɗowar sa,sunyi wa su Dady Habib bayanin komai dan haka suka samu nutsuwar da suka sami damar tattaunawa a kan al'amurin.

What Nafisa wace irin magana kike yi ne hakaguba fa kikace? Aunty Nafisa ta dubi Hajiya ladidi tace" wallahi Hajiya da gaske nake gaba ɗaya yanzu ESTATE daga jiya zuwa yau zan can da ake yi kenan, Hajiya na shiga ruɗani dalilin da yasa kika ganni da sassafen nan kenan saboda ina tunanin koke kika bawa Bintu aikin nan ban sani ba!'Hajiya ladidi tace"wallahi Nafisa bani nasa ta ba,sam ban san da wannan maganar ba, Nafisa tace"idan kuwa hakane tabbas A kwai ƙura Bintu mu zata yau dara, taura biyu ta haɗa abakinta,nasan tunanin ta bazai taɓa bata kashe Abdallah ba sai dai A sakata,zama bai kama mu ba dole mu binciki Bintu ta gaya mana wanda yasa ta aikin nan, Hajiya ladidi tace"ta yaya bayan kin ce tana can A kulle!'Hajiya ganin ta ba zai bada wahala ba!' Nafisa kinsan kuwa laifin kisa kike cewa ganin ta bazai wahala ba? sai dai kawai ki jarraba amma ki kula dan zaki iya shiga cikin zargi!'ɗan jim tayi can kuma tace"hakane fa Hajiyata hankali na ne gaba ɗaya atashe,amma dai zamu jira muga abinda zai faru,tunda sai munji sakamakon da asibiti suka bayar akan lafiyar Abdallah.


Har yanzu babu wanda yace wani abu tunda ƴansanda suka tafi da Bintu ba asami wanda yaji zai iya zuwa inda take ba bare yayi tunanin taimakon ta, shuru kake jin estate ɗin ta ɗauka sakamakon abinda ya faru,kowa kuma jira yake yaji labarin abin da yafi ƙauna a ransa,shin Abdallah ya mutu ne ko bai mutu ba?


Alhaji Baba babu wanda zai ce ga halin da yake ciki,saboda tunda ya shige ɗaki ya rufe yaƙi bari kowa ya ganshi balle asan halin da yake ciki,inno ma kusan hakane ta ɓangaren ta duk cikin su dama Hajjah ce me iya magana to itama bakinta ya mutu dan batasan me zatace ba,a ɓangaren su Rahima kuwa tunda taji labari take kuka wanda baza ta iya cewa ga taka mai mai abinda yasa ta kukan ba tasan dai ta damu da Ya Abdallah matuƙar damuwa,haka kuma zaren tunanin ta yakasa tsaida ita A guri ɗaya,Ammin ta kuwa baza ka taɓa gane me take ciki ba wannan sirrin zuciyarta ne.


Sayyid ya dubi Taufiƙa da take ta kuka kamar ranta zai fita yayin da su Farida suke ta bata baki tamkar wadda aka sanar da ita mutuwar mijinta,yace"Ni kaina duk sheɗancina bazan iya aikata makamancin abinda yarinyar nan tayi ba,ashe yarinyar nan kallon mu kawai takeyi babbar ƴar ta addace ɗaga mana ƙafa kawai takeyi!'Siddiqa ce tace"a'a fa Sayyid duk irin takun saƙar da kake da mutum karka sake kayi masa ƙazafin kisa saboda komai daran daɗewa sai hakkin ya dawo kanka!'cikin mamakin ta yace"to me kike nufi da wannan maganar Siddiqa?ok nagane me kike nufi kina tunanin kice Ni nayiwa Bintu ƙazafi ko? har yanzu dai bata bashi amsa ko ɗaya ba,gyara zamansa yayi kana yace"Siddiqa wallahi wallahi wallahi kinji rantsuwa so uku ko to ban san komai cikin lamarin nan ba sai abinda nasanar daku tun farko,nasan da akwai irin wannan tsakanin mu kuma ban Musa miki ba Bintu bata bar komata ba,kuma ba ƙyaleta nayi ba sai dai Ni ba wannan ne nawa tsarin ba dan Ni sam Abdallah bai dameni ba duk da dukan da naci a hannun sa balle har nayi tunanin kasheshi,dan haka ki dai na min wannan zargin, Bintu ita tasaka kanta cikin matsala, yanzu matsata ƴan sanda zasuyi kawai ta faɗi wanda yasa ta kashe oganta faƙat!'yana gama bayanin sa ya tashi ya fita daga falon.


Anty Nafisa ta kasa hankalin ta biyu tana son ganin Bintu kuma tana tsoron kar ace ita tasakata, ko kuma idan wanda yasaka Bintu aikin yafita shu'umanci da iya barazana sai kawai Bintu ta ɗora mata,kan uba amma danayi asarar zuwa duniya na koma babu ɗa babu dukiya ai bazan ma ga wannan rana ba, dole na haƙura da zuwa police station har sai naga abinda hali zaiyi,da wannan tunanin ta samu mafita.


Baba nura hankalin sa a tashe yace"wallahi Baffa, wannan lamari ya ruɗani,me yarinyar nan take nufi wai ma shin waya turota cikin estate?a kwaifa lauje cikin naɗi, tabbas,a kwai waɗan da suka fimu wayo da shiri A kan wannan al'amari,dan a iya tunani na tun farmakin farko da muka kaimasa bamu ƙara wani yunkuri na kasheshi ba!'Alhaji Salisu yace"dole ne fa mu samu yarinyar nan mu tursasa ta ta faɗi wanda yasa ta sakawa Abdallah guba!' wayar Alhaji Sama'ila ce tayi wani ɗan sauti na alamun kira na shigowa,tashi yayi ya fita yana ɗagawa daga can ɓangaren Samirace ta ja ajiyar zuciya tare da cewa, haba dear Ina kashiga nake ta neman ka tun jiya da dare nakasa samun ka ina fatan dai lafiya? cikin yanayin damuwa yace"ke dai bari wallahi mun ɗan shiga ruɗani ne akan wani harkar kasuwancin mu shiyasa kika jini ba dai dai ba!'ayya sorry to ina fata dai yanzu an gyara komai?ina fa muna dai kanyi dan yanzu haka ma miting muke na fito amsa kiranki!'to shike nan amma idan ka dawo ya kamata mu haɗu ko dan kagayamin damuwar ka koda A kwai abinda zan iya taimaka maka dashi duk da nima ina da tawa matsalar kuma dalilin kiranka kenan,Samira wace irin matsala ce kike da ita haka? a'a karka damu ai nace zan gaya maka saboda abokin kuka ba aɓoye masa mutuwa,kuma yadda nake jinka araina bazai bari na ɓoye maka komai akaina ba,dolene kasan Ni wacece saboda aure zamuyi,dan haka mu haɗu a copy,anjima sai muyi magana!'to shike nan zan kiraki anjiman, kashe wayar yayi ya koma,a inda ya tarar Baffa Hashir yana cewa yanzu dai bamu da ƙwarin gwiwar tun karar yarinyar nan A police station dole ne mu tsaya muga yadda zata kasan ce amma fa abin da ɗaurewar kai saboda ina tunanin kamar itace wadda akace Alhaji Baba zai aurawa shi Abdallah ɗin to gashi kuma tana ƙoƙarin kashe shi!'Alhaji Kabir da sai yanzu zai ce wani abu yace"kawai muje kowa ya baza ido muyi matuƙar saka ido a cikin dukkanin motsinta,tunda dai yanzu tana hannun hukuma dole mujira, Alhaji Sama'ila yace"to amma kun san ba lallai ne ta dawo gidan ba dan nasan daga can sai gidan kaso za a wuce da ita, laifin kisa ne fa ko da Abdallah bai mutuba tabbas hukuma ba zasu rabu da ita taci bulus ba!'waw to ai inaga mu kuma da wannan damar zamuyi amfani mu ɗauke ta tasanar damu wanda suka saka ta aikin kaga a ƙarshe ma mune da ribar aikin, wannan maganar taka tayi dai dai Salisu, cewar Alhaji Kabir kenan,da wanan maganar suka samu matsaya.


Samira ta kalli Dady jafar bayan gama wayarta da Alhaji Sama'ila,tace"kaji dai komai da kunnen ka! jinjina kai yayi tare da cewa Samira kina ƙoƙari amma dagewar da zakiyi yanzu idan kun haɗu ki tabbatar kin jiyo mana sirrika masu yawa mafi mahimmanci ma shine ki jiyo mana idan dasa hannun su A kan zubawa Abdallah guba,idan ma babu sa hannun su na tabbatar sai sun bi hanyar da zasu binciko wanda yasa akayi,kinga mu kuma mun ƙara samun wata damar da sun sani sai mu sani,ya juya ya kalli Sabir yace"kai kuma Sabir kaci gaba da bibiyar Alhaji Nasir wannan abokan Alhaji Baban mugaye ne zasu iya cutar mana dashi,kai kuma samuyal aikin ka dama lura da shige da ficen duk wanda zai shiga ya fita daga cikin ESTATE,da lura da abinda suke aikatawa dan haka ina mai ƙara tunatar daku da bakin ogan ku,saboda haka ku kula kuyi aiki bisa amana da gaskiya,gaba ɗaya suka amsa da ƙarayiwa ogan nasu fatan samun lafiya.

Tunda ya farka bai cewa kowa uffan ba sai zuwa duba shi suke yi, amma A cikin su bazai tan tance wanda yazo dan Allah ba,sallolin sa yayi yayi wanka ya kimtsa tsaf dashi kai bakace mara lafiya bane,tun lokacin yaso su barshi ya tafi sai kuma sukace da A kwai buƙatar ya ƙara samun hutu koda na awa ɗaya ne Dady jafar ne kawai ya samu ya lallaɓashi ya haƙura,dole likitoci suka dakatar da shiga inda yake sai Dady jafar kawai da yake tare dashi,Dady jafar ya ɗan zubawa Abdallah ido na ƴan wasu daƙiƙa,kana a hankali yace"wai Abdallah me kasani game da wannan batun ne?shiru yayi batare da ya amsa masa tambayar sa ba,idanunsa A lumshe tamkar mai bacci,Dady jafar bai daddara ba ya kuma cewa, kasan cewa tunda abin nan ya faru Bintu tana hannun ƴan sanda babu wanda ya leƙa bare asan hali...ganin Abdallah kawai yayi batara da yasan lokacin da ya yun ƙura ba,sai tsintar sa yayi yana ƙoƙarin fita daga ɗakin, cikin sauri Dady jafar ya riƙo shi,amma yadda yaga fuskar Abdallah lokacin da ya juyo shi kansa sai da ya razana matukar razana tunda yake da Abdallah bai taɓa ganin mummunan ɓacin rai tare dashi da kuma tashin hankali ba sai yau,wani irin kallo ya shiga watsawa Dady jafar wanda bai san ya a kai ya sake masa hannu ba,fita yayi cikin wata irin gaggawa kana ganin sa zakasan cewa a kwai gagarumar damuwa, me napep ya tare yace" kaini duk wata station da kasani,daga haka ya faɗa Napep ɗin me Napep yaja suka fara kewaya station,

Saboda tsabar zuciya bai san station ɗin da aka kaita ba amma ba zai iya tambaya ba,a wannan lokaci bazan iya misalta muku zaɓaɓɓakar da zuciyar Abdallah take yi ba,tun shida suke abu ɗaya sune har takwas sallah ce kawai take tsaida su,yanzu ma sallar isha sukayi daga nan ne me Napep yace" da Abdallah to Oga Ni fa yanzu station ɗaya ta rage da nasani!'wata irin tsawa Abdallah ya buga masa tare da cewa to yanzu me kake jira ne?ai da wani irin gudu me Napep yaja jikin sa na rawa bai ƙara gangancin yiwa Abdallah magana ba,har suka isa station ɗin.

A dai dai wannan lokacin kuwa Bintu tana cikin cell cikin wani irin yanayi me matuƙar ban tausayi, babu wanda ya dubeta da idon tausayi babu abinda taci ko tasha sai azabar kuka wanda shi ya zama ruwan shan ta, A halin yanzu ma tana zaune can loko ta haɗa kanta da gwiwa kuka takeyi me cike da tausayin Abdallah da kuma fargabar halin da yake ciki, wani ne ya taso ya daka mata tsawa, miƙe wa tayi a firgice,wata ƴar sanda mace ya kira tare da cewa dpo yace mu fara tuhumar yarinyar nan ta faɗi wanda yasa ta wannan mugun aikin!'to tace" tare da ɗauko wata sanda da suke dukan masu laifi....
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 30 ```



Wayyo Allah na dan Allah karku dake Ni bana son duka!'ɗan sandan yace"au dama wayake don duka ai sai dole, idan kika bamu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login