Showing 21001 words to 24000 words out of 184937 words

Chapter 8 - KUDURAR ALLAH COMPLETE BY FATIMA Y ADAM

21 Jul 2024

16856

kai dalla dubesu duk kun wani rikice da ganinsa sai kace baku gansa jiya ba!'amna ce tai zakal tace" kai ya najib kaima ka rikice da ganinsa bare kuma mu mata, kuma jiyan ince kinbari yay aga fuskarsa tunda ya sunkuyar da ita har akatashi ataron bai dagoba!'rahima da zuciyarta take mata wani irin mugun bugu tace" kai amna baki sani ba dai irin wadannan ko kallo zasuyi basa bari afahimta, dan haka baki da hujja akan cewa bai dago ya kalli kowa ba!' abdurrahim ne ya kallesu cikin jin haushin maganganunsu yace"yanzun dan Allah wannan tarbiyace? kudinga yi da mutum agabansa kuma babu wanda yay tunanin gaidasa, karfa ku manta da jawaban Alhaji baba koma kai tsaye nace" umarninsa akan mubi Yaya abdallah domin shine babba ayanzu da zai tsawatar mana!' fa'iz ya harareshi gami da cewa to uban tsari kai yanzu gaidashin kayi? komu cewa akayi maka bazamu gaidashin ba me tarbiya!'yakarasa zancen
da mikewa kai tsaye ya nufi kujerar da abdallah yake hakimce akai, ya kwantar da kansa idanunsa alumshe tamkar bayajin muhawarar da ake tafkawa akanshi,sallamar da fa'iz yayine yasashi dan bude idanunsa, nutsuwa fa'iz ya kumayi ganin tsabar kwarjinin abdallah, amsa sallamar yayi kamar wanda yake koyan magana,dan durkusawa fa'iz yayi tare da cewa barka da asuba ya abdallah!'barka dai ya fada asaman labbah danma fa'iz din yana kallon bakinsane da tabbas cewa zaiyi bai amsa ba, ahankali kuma suka dinga tasowa daya bayan daya suna gaidashin cikin kula da taka tsantsan tamkar ansanar musu halinsa sai dai kuma atabangarensu ba komaine yasasu wannan nutsuwar ba illa tsabar kwarjini da kamala irin nasa da kuma rashin ganin fuskar wasa,

Tunda ya zauna ya hanasu sakewa karshe ma ahankali suka dinga zare jiki suna guduwa daga falon ba fada ba duka balle harara su da kansu sukaji sunyi tsarara abdallah yana zaune aguri suma suna zaune babu mai iya wannan karfin halin duk cikinsu,sai dai yan matanfa yau hirarsu ta canja zani dan gaba daya ayinin ranar hirar abdallah ce abakunansu karma amna da hauwa'u da kuma farida yar Alhaji habib suji labari...



Da dai matar nan taji bintu takiyi mata shiru sai ta kuma juyowa afusace ta kwaza mata wata azababbiyar tsawa wanda nan take bintu ta kuma rikicewa, tsoro ya kuma da baibaye zuciyarta, saboda ta kaici matar figarta tayi sukayi ciki bintu kuwa binta kawai take batare da tashiryawa hakan ba saboda matukar tsoro,suna shiga tafkeken falon mai matukar haduwa da tsaruwa,wani dattijo wanda akiyasce zai iya kaiwa shekara hamsin da bakwai,yace'haba ladidi kiyi mata ahankali mana bakya ganin yarinyace karama,kinsan da nafisa ta haihu da yanzu kina da jikan da ya girme mata sosai!'sakin hannun bintu tayi tana cewa haba Alhaji ya daga ganin yarinya akwararo zakace lallai sai munshigo da'ita kai kana ganin kafurin kyau irin na yarinyarnan kasan ba abin arziki ta fito shukawa ba dan bana raba dayan biyu karuwancine ya fito da ita sannan gaka ganinta kaga balarabiyar karuwa!'
Alhaji munir yace" ashsha haba ladidi bazaki daina aibata yayan al'umma ba kenan kullum Ina gayamiki Amma bakyaji, ki bar ganin daya kawai kika haifa...kafin ya karasa ta tari numfashinsa da cewa kaga ni banason wannan mugun bakin naka kaima dai yarkace na gani idan kayi mata baki ta lalace bani kadaice da asaraba harda kai ehe,!' jinjina kansa kawai yayi batare da yakuma cewa da 'ita komaiba, dawo da hankalinsa yayi kan bintu da kukanta ya mutu tun sa'ilin da kamilalliyar fuskar Alhaji munir tayi mata maraba,cikin nutsuwa yace yarinya ya sunanki? cikin Jan ajiyar zuciya ta wanda yaci kuka ya koshi tace"zahra ta sami kanta da canja suna wanda itama baza tace ga dalilin yin hakan ba, ya kuma cewa to zahra daga Ina kike kuma me ya zaunar dake kofar gidana kusan awanni hudu?bintu kasa tayi da kanta ganin irin buhu-buhun harar da hajiya ladidi take aikamata,tagane daga dazu zuwa yanzu matar da aka kira da hajiya ladidi bata kaunarta, itama kuma hakanan taji matar bata kwanta mata ba, Alhaji munir ne ya katse mata tunani da cewa muna jinki zahra!'hajiya ladidi tai zaraf tace"yo ba dole tayi shiruba tana kirkiro karyar da zata shimfida mana!' Alhaji munir yayi mata kallon ki kiyayeni ladidi.........
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

Aunty hasana (maman nuur)wannan page din nakine kiyi yadda kikeso dashi Ina kara mika dunbin godiyata agareki Allah ya kara mana zumunci Amin ya Allah

```Page 12 ```


Alhaji munir ya juya yana dada fuskantar bintu tare da cewa Ina saurarenki zahra!'bintu cikin tsoron hajiya ladidi, tace"ni marainiyace iyayena duk sun mutu kuma a bauchi muke zaune, Ina zaune wajen kishiyar mamana na tsawon shekara daya da babana ya rasu, itace cina shana duk da Ina azabtuwa ahannunta,katsaham rana daya ta tada balli akan ta gaji da wahala dani alhalin babu dangin iya bare na baba dan haka saina bar mata gida wai itama tashi zatayi ta koma garinsu, hakan yasa na bar gidan da garin ma baki daya, Ina fita na nufi tashar garinmu dake bamu da nisa sosai da kafa naje, lokacin da na isa cikin tashar naji ana cewa Abuja dan haka kawai sai na hau motar Abuja ba tare da nasan kowa ba idan nazo, wata matace ta biya min kudin mota da muka sauka take tambayata inda zani ta ragemun hanya kasancewar anzo daukarta amota, shine kawai sai sunan anguwar nan ya fadomun da suka saukeni sai ta kuma taremin napep yakaraso dani nan, akofar gidan nan ya ajiyeni shiyasa na zauna awurin tun dazu har kawo yanzu da kasa aka shigo dani!' tayi saurin yin kasa da kanta ayayin da takawo nan akaryar da tasamu kanta da iya shararowa, Alhaji munir cikin tsananin tausayawa yace" ayya zahra karki damu insha Allah zaki zauna damu na dan wani lokaci kafin muyi shawara da mai daki na akanki!' bintu ta hada hannuwanta biyu tace"Abba na gode Allah ya saka maka da alkhairin sa ya kara tsawon kwana!' cikin tsananin jin dadin addu'ar ta yace"amin amin,!'tare da juyawa gurin hajiya ladidi da tayi wani irin sakalo tana kallonsa cike da mamaki da kuma takaicin wannan abu da ya aikata batare da neman amincewarta ba, batare da ya kula da kallon takaicin da take masa ba yace ladidi dan Allah kuje kisa iya talatu tayi mata duk wani abu da ya kamata, kama daga abinci wanka dakin da zata zauna,da duk dai abinda zata bukata awannan lokacin, yanzu zansa bawa driver yaje store yasamo mata kayan da zata bukata!'ya gama maganar da dauke kansa dan baya bukatar ta kawo masa wani buwaginta akan abinda ya bukata, hajiya ladidi ta saki wani dan murmushi, wanda da gani kasan da wani abu aranta,cikin ranta take fadin haba Alhaji nice fa ladidi idan kasan wata ai bakasan wata ba, bana aikata komai sai da manufa kuma wannan abun dakayi ni kaiwa danni zai amfana,

Ganin yadda yabawa banza ajiyartane yasa ta mike ba dan ranta yasoba a fuskarta, kallon bintu tayi da wani irin kallon tsana ta rasa da lilin da yasa taji bata san yarinyar, ita kanta ta fara da sawa kanta ayar tamba tabbas akwai dalili amma babu kira mai zai kawo gawayi,ganin takiyiwa bintun magana yasa Alhaji munir yace" da bintu tashi maza diyata kuje kinji Allah yayiwa rayuwarki albarka!'bintu ta amsa da Amin tanajin kaunar mutumin da ganin girmansa da kuma mutuncinsa arayuwarta, sumi-sumi tabi bayan hajiya ladidi tamkar zakace kyat ta arta na kare.


Can side din yan aiki suka nufa,wani daki taga hajiya ladidi ta konkwasa, wata dattijuwar matace ta fito daga dakin, tana yin arba da hajiya ladidi jikinta ya fara bari, kokarin rissinawa take hajiya ladidi ta dakatar da'ita cikin takama da izza, tace" talatu ga yarinya nan kiyi mata duk abinda ya dace!' daga haka bata kara ko'alif ba ta juya tai tafiyar ta,daga bintu har talatu bin bayanta sukayi da kallo,har sai da tabacewa idanunsu kana suka juyo alokaci daya suna duban juna, ahankali bintu ta durkusa har kasa ta gaida baba talatu,baba talatu ta'amsa cike da jin dadin girmamawar da bintu tai mata,sannan tace muje ciki kiyi wanka kafin nan na kawo miki abinci,bintu tace"na gode!'kana suka shiga cikin dakin na baba talatu, bayan ta nuna mata bathroom din sai ta fita dan samo mata abinda zataci,

Zama bintu tayi akasa bayan tayi wanka ta fito ta maida kayan jikinta, tagumi tayizuciyarta cike da sake-sake da fargaba,to wai ita yanzu yaya zatayi?guduwa zatayi taje neman estate din nan Koko yaya? gashi ta manta sunan mai gidan balle tayi tambaya, to kuma idan ma tasani ta yayane zata kai ga matsayin da zata iya zama acikin gidan?rumtse manyan idanunta tayi, tana mai rokon Allah ya kawo mata mafita akan al'amuranta,bude kofar da akayine yasa tayi saurin bude idanunta, baba talatu ce ta shigo da leda ahannunta, mikawa bintu ledar tayi gami da cewa ga wannan kayane inji Alhaji sai ki cire wannan na jikinki kisaka sabbin!'karba tayi cike da ladabi tana mai yin godiya, zata shige bathroom kenan dan saka kayan, baba talatu tace a'a yar nan zo kisa kayanki anan ni fita zanyi na kawo miki abinci!"tana gama fadar haka ta juya tare da barin dakin, tashi tayi tasaka doguwar rigar wadda ta matukar amsar dirarren jikinta tabi kirarta ta cokacola tayi daram,komawa tayi ta zauna, tana zama talatu ta dawo hannun ta rike da plet shake da jolof din taliya wadda taji uban kifi kusan rabin abincin,ajiyewa tayi gaban bintu tana cewa ga abinci nan kici sai ki konta ki huta, aikinyi sallar isha'i ko?bintu ta daga kanta tare da cewa nayi sallah, baba talatu tace" to masha Allah maaza kici abincin kada ya huce!'bintu ta kuma amsawa da to na gode!'sannan ahankali ta sauko ta saka fock ta faracin jelop din supergatty, bata wani ci da yawa ba tacewa baba talatu ta koshi, baba talatu tace haba yar nan har kin koshi kenan? bintu ta jijjiga kanta batare da ta'iya cewa komaiba, da baba talatu ta fahimci dai bintu bata son yawan magana kawai sai taja bakinta ta dinke tare da dauke abincin ta fita dashi, konciya bintu tayi asaman gadon da take kai tare da lumshe idonta dan so take tayi tunanin mafitawa rayuwarta duk da bacci takeso tayi sosai.


Hajiya ladidi tana shiga bedroom dinta ta dannawa aunty nafisa kira, tana dagawa batare da ta saurari gaisuwarta ba, tace"nafisa inason ganinki gobe da sassafe, arikice aunty nafisa tace"hajiyata me ya faru?meyasa kike nemana da gaggawa? Hajiya ladidi tayi murmushi mai fidda sauti tace"na samo mana dogon tsanin da muke nema dan hawa mu kai inda mukesan kaiwa da kuma hanyar dai-daita al'amuran rayuwarmu, ke dai kawai kiyo sammakon zuwa gida agoben!'jiki asanyaye aunty nafisa tace"to Allah ya kaimu!'amin hajiya ladidi tace gami da ajiye wayar,


Zagaye dakin ta shigayi tare da cewa nafisa naga so kike ki lalata mana shirin mu da mukayi tsawon shekaru muna ginawa dan haka bazan taba barin haka ta faruba lallai so nake sai na cimma burikana bazan bari sanadin soyayya shirina ya wargaje ba domin kece tsanina awannan tafiyar to gashi yanzu na kuma samun wani tsanin, wani murmushi tayi mai cike da ma'anoni masu yawa,

Waya takuma dauka tai kiran wata nomber kana ta danyi Jim, sai kuma tasaki wata mahaukaciyar dariya, alokaci daya kuma tana saurin sa hannu akan bakinta tana mai cewa' kai agida fa nake, kasani nake wannan dariyar kalan Alhaji ya jiyoni!'dan shiru tayi tana sakin murmushi sai kuma tace albishirinka!' batare data saurari abinda na wayar zaice ba ta cigaba da cewa munsami ma'aikaciya hargida burinmu ya kusa cika, zamuyi abinda mukeso nan kusa, yarinyace karama ta kawo kanta hargida, da ita zamuyi amfani dan cika burinmu da manufarmu sai dai akwai Abu daya danake tsoro!'ta dayan bangaren aka tambayeta da cewa mekike tsoro?tace"Ina tsoro kar nafisa taki bamu hadin kai da wannan shegiyar soyayyarta ta, shiyasa nace da ita inason ganinta gobe da sassafe!'a daya bangaren akace hajiya kin tabbatar yarinyar zatayi mana abinda mukeso batare da musu ko jayayyaba? hajiya ladidi tace" na tabbatar maka babu matsala saboda yarinyar tana da matukar tsoro kuma Ina matukar jin tsanar yarinyar araina shine ma babban dalilina, na tabbatar zamu juyata yadda mukeso idan mukai amfani da tsoronta!'yace tom shikenan karki damu da matsalar nafisa ni zanji da lamarin kawai ke dai ki sanar da ita tsarinmu sannan ni da kaina zan kai yarinyar estate dama nace zan nemowa inno yar aiki!' hajiya tace yauwa kaga shikenan babu mai zarginmu akan duk abinda zai faru!' daga haka suka yanke wayar.


Alhaji baba yayi dan murmushi, lokacin da yagama sauraren maganar da dady jafar keyi masa,yace jafar indai akan samowa abdallah mai dafa masa abinci ne ni na dau wannan nauyin zansa abinciko min yarinya ko dattijuwa mai tsafta da amana saboda inno ma tana bukatar mai aikin da zata dinga gyara mata bedroom dinta, tace" jikokina dukkansu san gartattune!' yakarasa maganar yana mai fadada murmushin fuskarsa, daddy jafar shima murmushin yayi yana mai cewa' to babu damuwa baba hakan yayi Allah ya saka da alkhari!' Alhaji baba ya tari numfashinsa da cewa jafar na gaya maka kaida danka kude nai min godiya akan duk abinda yashafi abdallah saboda shima jikanane!'dady ya jinjina kansa yana jin wani abu yana taba zuciyarsa na tausayin Alhaji baba.


Hajiya wai mene ya taso haka da gaggawa kike nemana? hajiya ladidi tayi saurin Jan aunty nafisa can karshen dakinta, ta kuma komawa tasawa kofar dakin key, kana ta dawo ta zauna tana fuskantar aunty nafisa wadda ta maida hankalinta kacokan akan gajiyar.

Cikin kara san bawa maganar muhimmanci hajiya ladidi tace nafisa na samo yarinyar da zatayi mana aiki agidan Alhaji balarabe, abun nufi anan shine inason zaman zahra acikin estate saboda tadinga dauko mun duk wani abu dake faruwa acikin ahlin, sannan ni kuma ta dingayi mun duk wani abu da nasata batare da anzargeki ko anzargeni ba dan haka nake baki umarni da ki amince da wannan tsarin nawa!'ta karasa maganar da zubawa nafisar Ido, ga mamakinta sai taga nafin tayi dariya kana tace"haba hajiyata dan wannan yar maganar ne duk kikabi kika daga hankalinki bayan kinsan duk abinda kika umarceni dayi zanyi batare da musuba, karki damu akwai hanya mai sauki da zamubi batare da da wani zargi ba,!'cikin tsananin farinciki hajiya ladidi tace yauwa yar albarka shiyasa ako da yaushe nake alfahari dake amatsayin yata ta cikina, gayamun da sauri wace hanyace wannan? aunty nafisa tace"yanzu da zan fito saida na biya ta bangaren inno, shine take sanar dani wai Alhaji baba yasa anemo musu yar aiki mai tsafta da amana zata dinga da fawa wannan shegen yaron mai fi'ili da nunkufurci yawa fir.auna abinci, ita kuma inno zatana gyara mata bedroom shine tace" wai nima idan na samu ta bangarena na kawo duk sai azaba!'hajiya ladidi tai shiru tana dan wani tunani, nafisa batasan hajiya ladidi tana hada hannu da daya daga cikin yayan Alhaji balarabe ba dan haka dole ta dakatar dashi, akan cewa da yay shi zai kaiwa inno zahra, inyaso sai su mikawa nafisa wannan alhakin,firgigigit tayi lokacin da aunty nafisa ta girgizata dan tayi magana har kusan sau uku Amma no response shiyasa ta girgizata tace"hajiya wai lafiya kuwa? naga kinyi zurfi cikin tunani? me kike tunani haka? hajiya ladidi taja ajiyar zuciya kana tace" nafisa Ina tunanine akan yaron nan da kikace sunansa abdallah, ina tunanin Anya kuwa Alhaji dafar ba da wata manufa ya kawo dansa gidannan ba?nafisa ta danyi Jim kana tace tabbas hajiya na dade ina wannan tunanin kamar da kamshin gaskiya a maganarki Amma kina ganin kai wannan yarinyar zahra da kikace bazai bamu wata dama ta bincikar abinda suke nufi ba tunda kinga shine jigon wanda zatayiwa aiki kuma zata iya samun kusanci dashi inaga kamar zamu jefi tsuntsu biyu da dutse daya fa hajiya!'hajiya ladidi batasan sanda ta rungumo aunty nafisa jikinta ba saboda tsabar farinciki dan kuwa da gaske abdallah ya tsole musu ido, tace"kwarai kuwa yake yata mai basira da hngen nesa Ina matukar alfahari dake Allah yay miki albarka!'aunty nafisa ta amsa cikin jin dadin ganin farincikin mahaifiyar tata, sannan tace hajiya kirawo yarinyar na ganta Amma dai tare zamu tafi ko? Hajiya ladidi tace yanzu ma kuwa me zaki zauna kiyi nan din ? bakisan da zafi ake bugar karfeba, idan kuma wani ya rugamu fa?kin san dai mafarmakan gidan Alhaji balarabe suna da yawa dan haka bazamuyi sanyin jikiba!'

Waya tayiwa baba talatu tace"kizo mun da yarinyar nan yanzu!'baba talatu ta amsa da to ranki ya dade!' batare da ta gama jin amsar talatu ba ta kife wayar.


Kwankwasa kofar da akayine ya katse musu tattaunawar da suka cigaba dayi, aunty nafisa ce ta tashi ta bude kofar wanda budewarta ke da wuya suka hada idanu da bintu dake gefen talatu cikin shigar doguwar abaya wanda tayi matukar amsarta, tamkar dan jikinta akayo rigar, zuciyar aunty nafisa ce ta shiga wani irin bugu da karfi har sai da takai hannunta ta dafe saitin kahon zuciyarta,bin bintu da Ido kawai takeyi takasa tantance halin rudanin da tashiga ita dai tasan bata taba ganin bintu ba arayuwarta, kuma basu da wata dan gantaka ta jini, to miye hakan takeji aranta?me yasa take jin wata irin fargaba akan yarinyar? hajiya ladidi tace nafisa ya kuka tsaya ku shigo ke da zahra ke kuma talatu ki koma kan aikin ki!'talatu ta amsa da to hajiya na barku lafiya tare da fita daga dakin....
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

Aisha Ina godiya Ina jin dadin comment dinki, dan haka wannan page din nakine Ina godiya sosai.

Yan group din KUDURAR ALLAH Ina godiya sosai Ina sonku irin sosai dinnan.



Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login