Showing 162001 words to 165000 words out of 184937 words

Chapter 55 - KUDURAR ALLAH COMPLETE BY FATIMA Y ADAM

21 Jul 2024

16881

zaka iya fara gabatar da dalilin da yasa kasa aka tarasu!'rufe bakin Alhaji Baba dai dai yake da ƙara ƙarfin bugun zuciyoyi,sai kuma nutsatstsiyar Muryar Abdallah ta ƙara sa ruguza ɗan ragowar ƙarfin halinsu,yace"Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Ubangijin halittu,sai kuma ya ɗan yi shuru yana tunanin ta inda zai fara,idanunsa ne suka sauka akan Dady Habib dan haka ya cigaba da cewa'Alhaji Baba ina fata zakayi min afuwa game da abubuwa masu yawa da suka faru ba tare da saninka ba,san nan ina fata ka zama jarumi mai ƙarfin hali da yadda da duk wata ƙaddara da ta zo maka mai kyau ko akasin haka!'wani ɗan murmushi Alhaji Baba yayi kana yace"Abdallah baka da damuwa dani akan haka ai duk Musulmin ƙwarai dole ya kasance mai yadda da ƙaddara dan haka ka faɗi duk abinda yake tafe da kai insha Allahu zan kasance mai haƙurin ɗauka!'ya faɗa yana maida kallon sa kan matansa dan ya tabbatar da cewa suma haka take agaresu, Hajjah ce ta saki murmushin ƙarfin hali duk da bata da tabbacin zaman ya shafe ta ko bai shafeta ba,amma ya zama dole ta cigaba da yin pritendin dan tsira da ragowar mutuncinta,Anty Nafisa kuwa ji tayi zaman ya fara gundurar ta tunda yanzu ta fara hasaso wani abu daban,tunaninta ya fara bata cewa lallai wannan taron bai dangance ta ba kuma bai shafeta ba,tunda taga alamun duk mutanen cikin falon basu da wata masaniya akan abinda za a tattauna a wannan taron gaggawar, muryar Abdallah ce ta dawo da ita cikin hayyacinta inda ya cigaba da cewa,a kwai abubuwan mamaki wanda zan fara gabatar maka dasu yanzu,amma sai dai kuma banga Abba Umar ba ko bai ƙarasoba?wata mummunan faɗuwar gaba ce ta samu Anty Nafisa sai dai tayi saurin shiryawa abinda zata faɗa game da mutuwar Umar ɗin idan har saƙon bai tarar dasu ba,sai dai kuma Muryar da taji daga bakin ƙofar falon ALHAJI BABA ita taso zautar da tunaninta,Abba Umar ne yake shigowa cikin ɗan gaggawa tare da cewa afuwan ku gafarceni na makara ne saboda wani dalili mai ƙarfi!'mutanen da suka biyo bayan shi su kaja hankulan mutanen dake cikin falon har da Bintu wadda tayi saurin miƙewa cike da farin ciki ta rungume Hajjo da Anty Asma'u,take kuma kallo ya koma sama hatta da shi kansa Abba Umar ɗin da mamakin inda Bintu tasan su Hajja yake kallonsu, Abdallah kuwa wani irin murmushi ne ke fitowa daga bakinsa zuwa saman leɓansa,Alhaji Baba ne yace"Batula kin san sune?da sauri tace"Baba wannan kakata ce,da yayar ummina!'wata irin zabura Anty Nafisa tayi tare da cewa ƙarya kike wannan abun ba zai taɓa tabbata ba,bazaki taɓa zama ƴar Umar ba,kamar yadda ban taɓa haifa masa ɗa ba!'Abba Umar kamar wani dolo haka ya tsaya yana bin Bintu da su hajjo da Nafisa da kallo,gaba ɗaya ya rasa tunanin da zaiyi komai nashi ya tsaya,

Murya yaji daga bayanshi Muryar da ba zai taɓa mantawa da itaba Muryar da ko a mafarki yajita sai ya ganeta,Muryar da yake kwana yake tashi da begen sake jinta,itace take cewa ƙarya kike yi Nafisa ba'a taɓa canja Ƙudurar Allah,kuma baza a taɓa sakewa tuwo sunaba,kin yi sake domin kuwa Bintu ta zama zakanyar dake juya akalar rayuwarki, Bintu Umar Balarabe kenan ƴar da kika so salwantar da rayuwarta,itace ta dawo gareki domin tona asirin ki na mugun nufi akan bawan Allah!'cewar fafi kenan da ya ɗora maganarsa daga inda Ammi Laila ta tsaya,tashin hankali wanda ba'a sa masa rana Hajja dai bata san sanda jikin ta ya jiƙe da fitsari ba saboda tsabar tashin hankali dan tasan zuwan Dije taron nan tare kuma da su Laila ba Alkhairi bane a gareta,wato dama Dije ce ta gudu da su Laila ke nan?daɓas haka Nafisa ta koma ta zauna yayin da zufa ke ta zubo mata tamkar wadda ake ruwan sama akanta,yayin da fafi ya rugume Bintu tare da mahaigiyarshi da matar shi ciki kewa da shaukin ganin juna,shi kuwa Abba Umar sunkuyawa yayi tare da yin sujjadar shukurr,yana ɗagowa ya tarar da Bintu tsakiyar su shi da Laila ta rasa wajen wanda zata fara nufa,sai wasu irin hawaye da take fitarwa wanda ta tabbata na tsananin farinciki ne,yau gata ga iyayenta duka biyu babu hijabi tsakaninta dasu,ba ta ankaraba taji sun lulluɓeta duka su biyun sun rungume ta atsakiyar su,baka jin komai sai koke koken dake fita ƙasa ƙasa, wasu kuma da yawa mamaki ya hanasu kataɓus wasu kuma har yanzu basu fuskanci kan lamarin ba,Alhaji Baba kuwa yana zaune yana kallon ikon Allah, sai kuma ya jiyo da kallon sa kan Abdallah tare da cewa, Abdallah me nake gani haka mai ke faruwane?ya kamata ku FAHIMTAR dani, na shiga ɗimuwa da ruɗani na kasancewar ganin Umar ɗina da ɗiya har da mata idan banyi kuskuren fahimta ba!'Abdallah yace"Alhaji Baba ka kwantar da hankalin kazaka fahimci komai dan kuwa yanzu za a warware maka zare da abawa kuma abinda ka fahimta ba kayi kuskure ba,Bintu jikarka ce ta cikin jinin ka ɗiyar ɗan ka Abba Umar!'kabbara akasa tare da tu ajjubin wannan al'amari,inno da Hajiya Babba kuwa kukan farinciki suka saka,ko wacce na san ƙarajin Bintu ajikin ta A matasayinta na cikakkiyar jikar su,shima Alhaji Baba ɗagowa yayi ya kalli iyaye da ɗiyar tasu da suke cikin wani irin shauƙi na kasancewa da junan su,yace"Umar ku zauna kayi min bayanin abinda ka lulluɓemin!'zama sukayi gaba ɗayansu sai dai Abba Umar ya kasa haɗa ido da mahaifin nasa domin yasan shi ɗin mai laifine a gareshi.

Acan gefe kuma Hajiya zulaihat ce rabe babu abinda take sai kukan tunawa dana ta iyalan kuma gudan jinin ta,tausayin Bintu da ƙaunarta take ji har cikin zuciyar ta,yayin da Abdallah yakeji kamar ya tashi yaje ya rugumeta ya lallasheta yace"yi haƙuri Ammina kema naki farincikin yana kusa dake,amma ya fisan gabatar da komai daki daki idan ba haka ba abun zai cuɗe da yawa har a rasa abinda za 'aji dashi,amma dai ai sannu bata hana zuwa,mai da idanunsa kan Bintu yayi wanda yaji ajikinshi cewa itama idanun ta na kansa,ai kuwa suna haɗa ido yaga tayi masa wani irin kallo mai haɗe da wani irin shauƙi da kewa da bege gami da jinjina,lumshe idanun yayi tare da aika mata da sakon da ya kusa shiɗar da ita, Muryar Abba Umar ce ta karaɗe falon da fara bawa mahaifinsa hakura da neman gafarar sa dana mahaifiyar sa,kana ya ɗora da basu ainahin cikakken labarin haɗuwar sa da Laila da aurensu,kamar dai yadda Fafi ya sanar da Bintu,yana rufe bakin sa,Anty Nafisa ta zunduma wani irin ihu tamkar wata zararriya, Abdallah ne yayi mata tsawar da tasaka ta nutsuwa ba tare da ta shiryawa hakan ba,kana ya ɗora mata da cewa,muna jiran jin ta bakin ki ki sanar damu yadda akayi kika sa aje a kashe Bintu da mahaifiyar ta harma da Fafi?shuru tayi tamkar wadda ake magana da kurma,daga ƙarshe ma tace"ita sam sharri za ayi mata bata san komai akan wannan batu ba,kallon Bintu yayi tare da yi mata wata alama,cikin ƙan ƙanin lokaci kuwa akaji sautin Muryar Anty Nafisa ta cikin waya tamkar alokacin take magana,tsit falon yayi masu al'ajabi nayi masu fargaba nayi dan Hajjah ƙiris ya rage ta fara zawo bayan fitarin da ta lantaya,ta riga ta saddakar da cewa yaufa babu mafita kuma ranar tonon sililice,ranar jin kunya ranar nadama wadda bata taɓa tunanin cewa zata risketa ba,haka abin yake a ɓangaren Dady Habib da sauran makiran estate.


Wani irin kuka Nafisa takeyi kukan kaico da nadama,babu abun da ya kuma haukatata da wani irin fitinan nan kuka sai labarin da taji ya ɗora musu akan yadda yayi da saban aikin da ta bayar na kashe su shida su Hajjo da Bintu,da yadda ya kuɓutar da rayuwar su dake Allah yayi da sauran rayuwar su agaba sai ya bashi dabara da tunani da nasara akan mutanen har yayi nasarar juyar da hankalin su.

Tsit falon ya yayi baka jin komai sai fitar numfashi, wasu mai daɗi wasu na fargaba wasu kuma na tunanin makoma,kamar dai Anty Nafisa da tata ta riga ta ƙare acikin ESTATE ɗin Alhaji Baba,gyaran murya Alhaji Baba yayi tare da cewa zo nan ƴata Laila nasa Miki Albarka!'a hankali Laila ta ja jikinta ta matsa kusa da Alhaji Baba Wanda ya ɗan dafa hannun sa akanta ya shiga yi mata addu'oi da fatan Alkhairi arayuwarta baki ɗaya,haka abin ya kasance a wajen Hajiya Babba da inno,sai dai Hajjo ta kasa kataɓus bare ta samu damar sawa Lailan albarka kamar yadda sauran ƴan uwanta ko tace kishiyoyin ta sukayi,itama Lailan bataji zata iya kar ɓar Albarkar bakin Hajjah ba dan haka sai ta koma mazaunin ta ba tare da ta ƙarasa gaban Hajjan ba,masu ƙarfin halin magana ne suke iya tofa albarkacin bakinsu,Alhaji Baba yayi gyaran murya tare da ɗan gyara zaman sa kana yace"Abdallah ka gama gabatar da abinda kake son GABATAR wa ko da sauran bayanai a tare da kai?jinjina kansa yayi cikin ɗan motsa bakin sa yace"Alhaji Baba a kwai abubuwa masu tarin yawa da kuma mamaki acikin wannan zaman namu ƘUDURAR ALLAH CE take kan bayyana har yanzu da sauran mu,sai dai yanzu na miƙa ragamar bayanin Hannun Baffa Hashir ko Alhaji Nasir ga kuma Alhaji Kabir duk wanda yayi magana acikin su ya wadatar tunda bakin duk ɗaya ne!'yayi shuru yana mai zubawa kyakykyawar fuskar Bintu idanu,sunkuyar da kanta tayi saboda yadda kallon nasa ke tasar mata da duk wata tsiga ta jiki da kasala,yayin da su Alhaji Nasir suka shiga share zufa wanda basu san ma ta inda take zubo musu ba,haka kuma gaba ɗaya falon su aka sawa idanu Baba Ahmad da dai sauran ahlin Baffa Hashir duk tsumayi suke suji abinda tosffin nasu su kuma suka aikata,dan kuwa ga alamun rashin gaskiya nan tsaf akan fuskokin su,shima dai Alhaji Baba ido ya sawa ɗan uwan nasa da kuma aminan sa guda biyu mafi kusanci agareshi,Dady Mansur ne yace"ku muke sauraro ku wakilta ɗaya daga cikin ku idan kuma bazaku iya fada ba muna da hanyar sanin komai ba tare da mun wahalaba!'Abdallah yace"Dady inaga kawai a kunna wayar!"Dady jafar ne ya miƙowa Dady Mansur wayar dake hannun sa,karɓa yayi tare da kunnata cikin sakanni sai ga muryar Alhaji Sama'ila na fitowa tun daga farkon fara aikin da Samira tayi na sirri har zuwa inda ya sanar da ita komai akan diamon,wayar tana tsayawa falon ya rude da surutai daga masu Allah wadai sai masu fatan shiriya iyalan su kuwa kuka suke sosai da irin wannan tozarcin da Baffa Hashir da Baba nura suka janyo musu,gaba ɗaya sai sukaji duk sun mozanta acikin mutane,da ƙyar Alhaji Baba ya tsawatar falon ya kuma ɗaukar shuru na wasu ƴan sakanni kana cikin wata irin murya wanda take nuni da tsananin halin baƙin ciki da takaicin da yake ciki yace"sannu Nasiru sannun ku Hashir!''' ɗan shuru yayi saboda wani abu mai ɗaci da ya tokare maƙogaran sa,daga bisani yaci gaba da cewa, abokai na da ƴan uwana sune suka zama masu ha intata muna fukaina masu san ganin bayana,hannu yasa ya ɗan goge ƙwallar dake son fallasa halin da zuciyar shi take ciki,kana ya cigaba da cewa nasan akan wannan dalilin ne na rasa gidan jinina ɗan da babu kamarsa sai dai kwatankwacin sa zan iya yafe komai amma banda wanda ya rabani da ɗan da kuma jikana,amma ku kuje babu komai rayuwace,na barku da Allah tunda yanzu ma ba dabarata ce ta fallasaku ba ƙarshen makircin kune yazo,dan Allah ba ya barin mai zalinci,na gode Allah da rahamar sa agareni na gode Allah da ya kawo min Abdallah cikin zuri'a ta!'ya faɗa yana sakin wani ɗan murmushi na samun sukuni da yayi azuciyar sa a sakamakon yawan ambatan Allah.


Baffa Hashir cikin tsananin jin kunya da nadama wadda take neman karya garkuwar jiki da ruhin sa, yace"ɗan uwa ina mai neman gafarar ka da kafemin cin amanar da nayi maka duk da cewa ban cutar da rayuwarka ko wani daga cikin ahlinka ba, amma naci dukiyar ka kuma naso aikata babban kuskure akan abinda ba nawa ba ba kuma na ɗana ba,a yanzu ina mai cikin tsananin nadamar abinda na aikata,tabbas na kasance maci amana mai saka Alkhairi da sharri,ka yafe min ɗan uwana ina cikin wani hali na na rashin samun yafiyar ka!'ya ƙarasa maganar da rushewa da wani matsanan cin kuka wanda har saida Alhaji Baba ya runtse idanun sa,daga nan suma suka samu damar neman gafara da yafiya magiya da kukan da suke shi ya tabbatar wa da jama ar gurin cewa sunyi taubatun nasuha,dan haka Alhaji Baba yayi gyaran murya tare da cewa haƙika kunyi kuskure a cikin tafiyar da al'amuran duniya da rayuwarku,kamar ba kuyi karatuba kai Hashir kamanta da hadisin da mahaifina yake yawan yi mana maimaicin sa,cewa Annabi Muhammad (s.w.a) yace"duk jikin da ta ginu da haramun ba zata shiga aljanna ba,haka kuma duk mai annami manci ba zai shiga aljanna ba,kai kuma gashi a wannan gaɓar duk sai gashi ka aikata waɗan nan laifukan,dan haka ina mai jan hankalin mu anan da mu gujewa cin haram komai ƙan ƙantar ta,mugujewa ha'inci,da cin amana,domin Allah baya yafe laifin da akayiwa bayinsa,daga ƙarshe ina mai tunatar daku muhimmancin gaskiya da rikon amana,na yafe muku Allah ya yafe mana baki ɗaya,amma ku sani duk wanda yake aikata wani mummunan laifi to ya dinga tunawa da mutuwa san nan kuma duk abinda yake yi Ubangijin sammai da ƙassai yana kallon sa,ko da ka mutu asirin ka bai tonuba to tabbas a lahira za a nuna maka dukan aiyukan ka,da kunyar lahira kuwa gara ta duniya,zanso idan ina aikata mugun aiki asirina ya tonu ko hakan zai iya zama sanadin shiriyata, Allah yasa mu dace ya kuma karemu daga ruɗin zuciya ya tsare imanin mu!'da Amin suka amsa yayin da jikkuna su kayi sanyi zuciyoyi suka mutu hankula suka fara dawowa jiki,kiran sallar da akayi shi ya dakatar dasu daga ci gaba da gabatar da al'amuran da suke faruwa,Alhaji Baba yace"ya kamata muje muyi sallah ina yaso sai mu dawo mu ɗora daga inda muka tsaya idan akwai wani abun kenan!'Abdallah ne ya fara miƙewa idanun sa suna shawagi akan Dady Habib da Hajjah gani yake kamar zasu iya guduwa dan haka kawai sai yace" da Dady Mansur da Dady jafar su tafi suyi Sallah da Dady Habib saboda yanayin jikinsa su sun fahimci abinda yake nufi,yayin da wasu sukayi tunanin ko Dady Habib ɗin bai da lafiya ne,a hankali aka shiga watsewa daga falon, Abdallah yana fitowa ya kira wayar Safwan yace"su ke waye gaba ɗaya estate din Nan kar su bari ko ƙwaro ya fita,har gefan Hajjah bai bari ba sai da ya tabbatar da tsaron wajen.

A bangaren Anty Nafisa kuwa tunda ta fita sai taji bata da kwarin gwiwar shiga ɓangaren ta,tunanin makomar ta a wajen Abba Umar shine abinda ya da baibaye ƙwaƙwalwarta,jikin ta asanyaye haka ta shiga falon tana mai jin tsananin faɗuwar gaba akan abinda zai biyo bayan tonuwar asirin ta,

Duk da cewa kowa ɗokance yake da ya keɓe da iyalan sa,tsakanin Abba Umar da Fafi,amma hakan suka hakura suka nufi masallaci bayan sunyi alwala da tunanin ai yanzu komai ya wuce babu abinda zai kuma rabasu da iyalansu idan ba mutuwaba,lokaci lokaci zaka ga murmushi kan fuskar Abba Umar wanda yake nuni da tsananin farincikin da yake ciki ga matar shi Laila ga gudan jininshi Bintu babu abunda zaice da Allah sai godiya Alhamdulillah masha Allah.


Su inno dai da Hajiya Babba su sukayi ma sauƙin baƙi,Hajiya Babba kamar yadda ta saba tayiwa inno kara da alkunya ita tabarwa ragamar karrama surukar tata tare da ririta ta tamkar basu taɓa yin suruka acikin ESTATE ba,Hajiya zulaihat ma tana manne da Laila,dan ko ɓangaren ta bata koma ba,Bintu kuwa gatan har nema yake yayi mata yawa sai dai duk da haka ta kasa sukunin rashin ganin Oganta Abdallah maganin kukanta,wata irin kewar sa takeji tare da tsananin bege,wanda har kawo yanzu ta kasa fassara hakan da cewa ƙauna ce mara algus,

Bayan idar da sallar ne mazan duk suka hallara a falon Alhaji Baba,yayin da ya bada umarnin akawo abinci a fara ci kafin ci gaba da tattaunawa,a lokacin ne kuma ya saka waya yayi kiran Alhajin Nafisa ya sanar dashi yana buƙatar ganin sa tare da Hajiya ladidi,kowa yana sabga cikin walwala amma banda Dady Habib wanda bugun da zuciyarsa take yi tafi ƙarfin a misalta,yanzu yafi kowa shiga tashin hankali tabbas da ya samu hanya sai ya gudu dan yana ganin guduwar ita ce kadai mafita
agareshi da kuma samun sauki a gareshi.


Hajja kam tun komawarta bangaren ta take zawo har sai da Nana karama tace"wai Hajja lafiyar ki kuwa naga sai sunturin banɗaki kike?bata iya bawa ƴar tata amsa ba sai komawa da tayi ban dakin dan ta ga alama zaman cikin sa sai yafi mata sauƙi,a kwai abinda take ɓoyewa wanda babu wanda yasan shi kuma tana ganin lallai lokacin tonuwar wannan sirri yayi shi yasa abun ya haɗe mata bata jin cewa duk sanyin zuciyar Alhaji Baba zai iya yafe mata wan nan al'amari,a yanzu kaico da nadama take,shin tayaya zata iya fuskantar Alhaji Baba da wannan sirrin wanda tasan cewa koda su Abdallah sun san wancan to tabbas basu san wannan ba,yaya duniya zata kalleta da sauran ƴaƴan ta idan sukaji abinda ta aikata,dole tasa ta ci gaba da zaman banɗakin domin tun yanzu ta fara jin kunyar haɗa idanu da iyalanta,

Oga Abdallah kuwa mai gaiya mai aiki duk yadda ya kai ka san yin juriyar hakura da ganin Bintu abun gagara yayi, cikin rashin sukuni ya nufi ɓangaren inno,yana shiga falon yaci karo da Dije zata shiga kiching inda suke hada hadar dafa abinci,tsayawa tayi tare da cewa,a'a yallaɓai ko kana buƙatar wani abunne? cikin ɗan basarwa da farincikin da yaji na samun dama yace"ki bawa Bintu ruwa ta kawo min!'daga haka yayi saurin faɗawa falon sa,wani ɗan murmushi tayi tare da shigewa ɗakin inno inda Bintun suke tare da su Laila da Hajjo,yafito Bintu tayi,suna fita ta miƙa mata ruwan da ta ɗauko,ba ta haɗa da komai ba,dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login