Showing 135001 words to 138000 words out of 184937 words

Chapter 46 - KUDURAR ALLAH COMPLETE BY FATIMA Y ADAM

21 Jul 2024

16877

da wata leda,miƙawa Bintu yayi tare da cewa sauri ki saka zamu tafi!'tashi tayi tana ƙoƙarin shigewa toilet sai taga ya juya ya fita daga ɗakin hakan ne ya bata damar saka rigar tare da yana mayafin ta asaman kanta,fita tayi falon gidan wanda suka ci karo da Abdallah shima ya fito cikin shigar sa ta ƙananun kaya wadda sukayi masa matukar kyau suka kuma fito da zallar kyawun jikin sa,ɗan kallon sa tayi kana ta ɗauke kai,yayi mata kyau sosai amma ita yanzu tsoron kallon sa ma takeyi dan kar yayi mata wata fassarar,


Sarai ya gano ta amma bai magantu ba,fita sukayi tare, Daniyal yana ganin su yayi saurin buɗe motar suka shiga baya,ya rufe tare da komawa mazaunin drever,a hankali ya fara jan motar har suka fita daga gidan,fita yayi ya rufe get din kana ya dawo suka dauki hanyar zuwa gidan Hajjo.


Hankalin shugaba azukyi idan yayi dubu to duk sun tashi,wai mai yasa nanu yake son zama sanadin mutuwar kasuwancin su ne?anya kuwa ba cire shi daga harkar zaiyi ba dan karya jawo musu abinda zaizo ya tarwatsa jin dadin rayuwar su ba,nanu ne ya dawo da shugaba daga duniyar razanin da ya fara shiga akan mummunan karshen da yake son jawo musu,yace"shugaba kayi magana mana, wannan al'amari fa ba ƙaramin abu bane sun riga sun karya Ni sun rusani sun kai rayuwata ƙasa tunda suka riga suka ɗauke Abubakar suka sami Abigirl a hannun su,na tabbatar da cewa duk sanda Abigirl ko ABUBAKAR suka farfaɗo daga suman sihirin da mukayi musu ƙaryar mu ta ƙare daga Ni harku dan haka dole mu haɗu mu nemowa kanmu da rayuwar mu mafita!'shugaba yace"lallai nanu ka haukace da waɗan nan kalaman naka ai yanzu kai wan nan ta shafa bamu ba, tunda dakin nan ba ajiyar muce acikin sa ba,kuma Abubakar da tarkacen dake cikin ɗakin basune tasirin mu ba kowa tasirin tsafin sa daban,kamar yadda kowannen mu matsalarsa da ban,yanzu ka gaya min taimakon da kake so muyi maka dan ayanzu shi kaɗai ne abinda ya rage tsakanin mu da kai!'duk da cewa nanu baiji dadin maganar shugaba ba amma sai ya danne abinda ke taso masa ya kwantar da kai yace"yanzu so nake asato min yarinyar nan daga nan zan janyo shi mijin nata yazo inda muke,kaga kashe su duka bazaiyi min wuya ba!'Shugaba yace"nasan saboda rufin asirin ka kake son yin duk wan nan abun ko?kamar wani gaula haka nanu ya daga wa shugaba azukyi kai,dariya shugaba yayi tare da cewa shi kuma Abubakar ɗin ya zakayi dashi?kasan idan ka kashe su baka kashe Abubakar ba tamkar ka sare reshe baka kashe miciji baka sare kansa bane?yayi shuru tare da zubawa nanu idanu yana jiran amsarsa,wani wahalallan numfashi ya fesar kana yace"shima Abubakar ɗin kashe shi zanyi!'ka haƙura da dimon ɗin ke nan!'cewar shugaba,shuru nanu yakuma yi cike da zurfafa tunani,can ya ɗago kansa da idanun sa da sukayi jajur saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki,shuga rasa dimon ɗin nan tamkar rasa rayuwata ne bazan iya haƙura dashi ba,zan sace wannan shegiyar yarinyar da ita zanyi garkuwa Abdallah yakawo min kansa da mahaifin sa!'idan kuma bai aminta da haka ba fa? tambayoyin shugaba fa neman zauta ƙwaƙwalwal nanu sukeyi duk hanyar da ya samo sai shugaba ya kawo lalacewar ta,wata irin zufa ce take karyo masa ta ko ina,yayin da zuciyar sa babu abinda take sai bugu, wanda kuma tsabar fargaba ce tasa hakan,da ƙyar ya tattara miyan da ya daskare cikin bakin sa ya haɗiye shi tare da cewa,shugaba zamu gwada wannan ɗin amma daga baya zan iya haɗawa da yaudara!'wata shegiyar dariya shugaba ya sheƙe da ita har da riƙe ciki kana ya ɗan saurara tare da cewa shegen kaya nanu ai dama in dai yaudara ce ka iya ta,tunda ka yaudari mahaifinka waye bazaka iya yaudara ba,amma dai yanzu na gamsu da wannan tsarin tunda naga yanayi,abinda ka faɗa ɗin shi za'ayi amma kasan wannan yarinyar baza mu hada ta da tsafi ba tunda tun farko dama ta gagaremu ballan tana kuma yanzu!'sai yanzu nanu yaji dan dama tunda shugaba ya bashi dama da kuma goyan baya.


Sun ɗanyi nisa da fara tafiyar ya dube ta cikin dawowa yanayin sa na kullum yace"bani nombar inno a wayar ki mu kirata dan kar hankalin ta ya tashi!'miƙa masa tayi bayan ta duba sunan innon,ɗauka yayi awayar dake hannun sa ya kirata,ringin ɗin farko kuwa ta ɗaga,lokacin suna tare da Dady Habib,a hankali Abdallah yace"inno Barka da safiya!'cikin sauri inno ta amsa tana ɗorawa da cewa wai Abdallah ina kuka shiga kaida Bintu yau tun safe nake cikiyarku a cikin gidan nan?inno karki damu wani aikine ya taso mun cikin dare kuma tace bazata iya zama ba tana jin tsoro shine na tafi da ita!'jinjina kai inno tayi tana mamakin wai Abdallah ne da jero wannan dogon zan can duk saboda Bintu,cikin kulawa tace"aiyo ai hakan yayi kai da matar ka Allah dai ya baku nasara,saikun dawo,daga wannan sukayi sallama,juyowa tayi tana kallon Dady Habib da yayi shuru yana sauraren ta,tace"dama ai duk wanda ya samu mace kamar Bintu tabbas sai rayuwar sa ta canja tare da godewa Allah!'Dady Habib yayi murmushi tare da cewa jikokin naki ne?dariya tayi cikin farin ciki tace"sune kaga har sun hada kan su tamkar ba haɗa su akayi ba shi yasa nake cewa ita ma Taufiƙa zata haƙura duk ranar da taga bata da kowa A gefanta sai Sayyid, Allah dai ya baiyana mana shi cikin ƙoshin Lafiya!'da sauri Dady Habib ya amsa da Amin kana yace"to kuma ai baki tmbayesu inda sukaje ba!'inno tace rabu dasu mata da miji ne,kasan dai miji ba zai sace matar sa ba ko? murmushi kawai yayi b tare da yace"komai ba.


A ɓangaren Anty Nafisa kuwa tuni ta bada aikin gamawa da Abba Umar amma tace aɗan saurara zata faɗa musu ranar da take so aikin ya kasance,ba dan komai ne yasa ta jinkirta ba sai dan tana son ta fara bibiyar sa dan ta tabbatar da ko su Laila suna raye suma ta aikasu tare gaba ɗaya, ko hankalinta ya gama kwanciya tasa mu tayi rayuwar ta cikin farin ciki ba tare da fargaba ba,wan nan shine tunanin Nafisa,

A can kuma ɓangaren su Abdallah lokacin da suka gama waya da inno kallon Bintu yayi cikin haɗe gira dan karma ta kawo masa wasa cikin tambayar da yake son yi mata,ganin haka kuwa yasa ta nutsu tare da maida kanta daya ɓangaren,kamar daga sama taji maganarsa yana cewa Bint ke dawa kuke magana a cikin ɗakin nan kuma waya sanar miki da cewa Dady yana cikin dakin?kuma me yasa baki gayan ba tun asali kafin faruwar Al'amarin?cikin san tabbatar masa da gaskiyar abinda zata faɗa tace"wallahi ban santa ba kuma nima da farko ban sani ba saida ta sanar dani kuma yau baifi kwana uku da fara mafarkin da ita ba,tun ranar dai da mukaje wajen Malam ta fara zuwa kuma ita tace kar na gaya maka har sai mun shiga ɗakin munfito,kuma ita take min magana acikin ɗakin,Rimi Rimi ta faɗa masa maganganun da sukayi acikin ɗakin,cikin sheshsheƙar kukan da yake cinta tace"amma bata gayamin inda ummi na da fafina suke ba,inaso bagan su,amma bata gaya min ba,hannun sa har rawa yake gurin ƙoƙarin janyo Bintu jikin shi,ƙara shigewa tayi tana goga fukarta akan ƙirjin sa kamar yadda ta saba,rufe idanun sa yayi yana jin wani irin matsanancin tausayin bintu tare da wani abu mai girma da yake ratsa duk wata zuciya da gangar jikin shi,yana mamaye duk wata kafa mai muhimmanci dake cikin rukunin numfashin sa,hannu yasa ya ture ɗan mayafin dake kanta ya shiga shafa lallausar sumar kanta mai matukar santsi da ƙamshi,rufe idanun ta tayi wanda take anan bacci yayi awan gaba da ita,cikin mintunan da basu fi biyu da yin baccin Bintu ba suka ƙara so ƙofar gidan Hajjo.


Hajjah ta zubawa Habib ido dan san gano halin da yake ciki, amma hakan ya gagara,cikin ƙaunar ɗan nata da ya zamar mata ɗaya tamkar da dubu tace"Habibu mai yake damunka ne naga duk kayi wani sukuku da kai kamar bakajin dadi,ɗan murmushi yayi tare da cewa Hajjah kin san dai yanzu bani da wani abu wanda yake saka Ni damuwa face maganar Mansur shi kaɗai ne damuwa ta,ina jin abin har cikin raina, wannan halin nasa ina fata ALLAH ya canja masa shi.


Alhaji Baba ya kalli Alhaji Hashir cikin tsananin damuwar da ta taso masa a cikin wannan rana da tunawa da haziƙin ɗansa,wanda ya manta dashi tun bayan da akarasa shi, duk da cewa damuwar rasa shin yana tare da zukatan su,amma babu damar furtawa da baka,sai yau da yaji tamkar antashe shi daga bacci,ya tashi da azabar kewa da raɗaɗin rashin Abubakar ji yake tamkar yanzu aka neme shi aka rasa,so da yawa yakan kwana ya tashi da jin zafin abin amma ya rasa ta yaya akai ya kasa koda fita waje dan neman inda ɗan nasa ya shiga,abinda matuƙar mamaki ga kuma jikan sa da ya ɗauki soyayya ya ɗora masa shima ya rasa shi bayan rasa mahaifin sa,yanzu abin ne yake dawo masa tare da kaicon abin da ya hana shi yunƙurin neman ɗan sa da jikan sa,ɓatan Sayyid shi ya kuma saka zuciyar sa cikin wasu wasi da saka ayar tambaya akan lamarin gidan nasa,me yasa ake ɗauke masa zuriya?taɓa shi ɗan uwan sa Alhaji Hashir yayi tare da cewa ya dai Balarabe ka kiramu dan yin magana mai muhimmanci amma ka barmu kasa mana ido kai kuma ka tafi duniyar nazari,shin meke faruwa duk da nasan maganar bazata wuce akan ɗakin nan da aka tashi da gobarar sa ba!'ya faɗa yana duban dan uwan sa Alhaji Sa'ad da shima ya zubawa Alhaji Baba Ido dan son jin maƙasudin kiran da yasa akayi musu,Dady Mansur da Dady Habib da Abba Umar sai Baba nura da Ahmad da dai sauran ƴaƴan sa da ƴaƴan ƴan uwansa da suke tare aguri ɗaya cikin estate,yayin da kowa da abinda yake son ji daga bakin Alhaji Baba,wadan da suka san sirrin dimon suna fata ace abin da zai sanar dasu ke nan,wasu kuma saɓanin haka ne aran su.


Hajjah ce tace"ya kamata ku bar Alhaji ya nutsu tunda ya kiramu kun san zaiyi magana mai muhimmanci ne,kuma duk lokacin da mutum zai furta wata magana anaso ya tattaro tunanin sa da nutsuwa da kuma nazari akan abinda zai furta,saboda tuntuɓen harshe,dan haka Dan Allah karku rikitashi!'wani mugun kallo Baffa Hashir ya wurga mata tare da cewa to ƴar iya,dama nasan ko kowa baiyi magana ba ke saikin yi!'murmushi Hajjah tayi dan tasan dama can kanwarsu bata juƙuwa da Baffa Hashir,


Gyaran muryar da Alhaji Baba yayi ita ta sakawa kowa nutsuwa,tare da maida duk hankulan su kansa,cikin nutsuwar da bata hana damuwar sa baiyana ba,yace"duk hasashen ku bai zama daidai ba,domin nasan abinda zan fada muku bashi kuke tunanin zan faɗa ba,saboda nima yau tunanin ya fito daga zuciya ta zuwa kan harshena,ɗan shuru yayi,yayin da zuciyoyi suka ƙagauta da jin wannan batu,duk iya tunanin su akan dimon ne saboda su waɗan da suke abun sun san cewa Alhaji Baba bai san maganar dimon ɗin ta fita ba,balle yasan muguwar rigima da cutar data haifar a cikin zuri'arsa,Alhaji Baba yaci gaba da cewa,shi yasa zan sanar daku dan mu haɗu muyiwa kanmu da zuriar mu maganin abinda yake damunta,dan fitar da iska yayi ta bakin sa tare da sauke numfashin damuwar dake cunkushe a zuciyar sa,kana yaci gaba da cewa maganar Abubakar ce,,,wata irin zabura Dady Mansur yayi yayin da sauran mutanen ɗakin sukayi ɗif kamar babu wata halitta a falon,kowa da irin bugun da zuciyar sa keyi masa, Hajjah kuwa wasu hawaye ne suka sauko mata tana cewa Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah wanda yayi zuciya,kawai sai ta fashe da kukan farinciki nanatawa take Allah kasa lokacine yayi da gaskiya zata bayyana!'kowa ka kalla afalon nan da akwai abinda ke damun sa na matukar ruɗani da firgicin jin maganar Abubakar ta taso lokaci ɗaya, Dady Mansur kuwa kuka ya saka sosai wanda kana ji kasan kukane da yake fita tun daga ƙarƙashin zuciyar sa,ya kasa cewa komai sai sautin kukan sa dake fita gwanin tausayi,Dady Habib ne ya ɗan goge fuskarsa kana cikin nutsuwa yace"haba yaya bai kamata ba da girman ka kadinga abin yara!'wani Irin mahaukacin kallo me cike da fassarori da ma'anoni masu yawa Dady Mansur ya jefawa ɗan uwan nasa,ba tare kuma da ya iya ce masa komai ba,karon farko ke nan da yayiwa Mansur irin haka batare da ya tanka masa ba,ɗauke kansa yayi cike da mamakin wannan kallon da Mansur yake masa,ko me yake nufi da haka?


Alhaji Baba yayi wani ɗan murmushi na takaici kana ya cigaba da cewa,a yau kuma a yanzu nasa afara rokon ALLAH ba dare ba rana idan Abubakar yana lafiya Allah ya baiyana mana shi idan baya cikin haicinsa kuma Allah ya bashi lafiya ya dawo min dashi cikin gidan nan,idan kuma ya mutu,,,,,kukan Hajiya Babba ne ya dakatar da shi daga barin abinda zai faɗa,cikin kuka da matsanancin tashin hankali tace"dan Allah Alhaji karka ƙarasa,inason ganin jagora araye (dake sunan da take gaya masa mafi lokata acikin mutane saboda karar ɗan fari)taci gaba da cewa Wallahi inaso yazo gidan nan araye inaso naga waɗanda suka gurgunta min rayuwar sa akan abin ɗun,,,,bata ƙarasa ba inno ta rufe mata baki tare da girgiza mata kai,alamun kar ta faɗi abinda ke cikin zuciyar ta,tunda shi Alhaji Baba baƙo ne akan sanin hakan,zai iya zurfafa bincike akan al'amarin,shurun kuwa tayi bata sake cewa komai ba,sai dai kukan da taci gaba dayi ƙasa ƙasa,yayin da Hajjah ta zuba musu idanun ayar tambaya da wannan sabon Al'amarin, wai meke shirin faruwa a gidan nan ne haka? Alhaji Baba yace"dama abinda nake son sanar daku kenan kowa zai iya tafiya!'daga haka ya miƙe ya shige can cikin ƙuryar ɗakin sa,jiki asan yaye suka dinga ficewa daga falon kowa ya kasa magana dan sun rasa abin cewa,wasu farin cikine ya hana su magantuwa wasu kuma bakin ciki,kowa ya fita daga falon sai Abba Umar da Aliyu,da kuma Dady Habib,sai su inno,Abba Umar yace"Hajiya Babba ku daina kuka komai ya kusa wucewa insha Allah tun da har muka samu Alhaji Baba da kansa yayi maganar yaya,kuma daga nan nima gurin wani malami na zan wuce Musa aƙara tsanan ta rokon Allah!'Dady Habib yace"tabbas maganar Umar haka take nima ina da malaman da zan saka cikin lamarin, san nan a ganina ya kamata a hada da cigiya gidajen rediyo ko za a dace!'Hajjah tace"hakan yayi Allah yayi muku albarka!'shi Abba Aliyu ma atake nan ya fara kiran malaman sa kasan cewar shi malamin addinni ne ya fara shela yana sanar dasu asaka almajirai sauka,yanzu zai taho da kayan sadaka,inno tace"masha Allah Ubangiji Allah ya baiyana mana shi cikin farin ciki da cikakken lafiya!'gaba ɗaya suka amsa da Amin summa Amin.


Tunda ya fito yaji wani irin jiri na san kayar dashi,amma duk da haka sai da ya nufi ɓangaren ƙonannen dakin,zubewa yayi agurin yana cigaba da wani irin kuka mai matuƙar ciwo da saka mutum zazzafan zazzaɓi,Dady Mansur fa ya haukace da wannan al'amarin,shin ina Abubakar yake?ina kuma aka kaishi yanzu?kukan ya cigaba da yi,ya kuma kasa koda motsawa daga wajen,ji yayi an tsaya akan sa,da sauri ya juyo ganin Dije yasa shi saurin tashi tsaye yana kade jikin sa, ƙoƙarin barin gurin yake ta dakatar dashi da maganar ta data kusan saka shi fitsari a wando,shin yallaɓai Mansur wai meye haɗin ka da dakin nan ne?can kwanaki kai ne ka fara hanani zuwa gurin nan dan cika umarnin uwar dakina kuma har kayi min gargaɗin sake ganina agurin,san nan ina yawan ganin ka a gurin shin me ka ɓoye acikin ɗakin da yanzu rasashi yasa ka irin wannan kukan da tunda nake ban taɓa ganin magidan ci kamar ka nayin irinsa ba?Dady Mansur kallon Dije kawai yake amma bai bata amsar ko ɗaya daga cikin tambayoyin ta ba,saima kaucewa da ya kuma yi dan barin wajen,cikin sauri Dije ta kuma cewa,Mansur kaji tsoran Allah ka bayyanawa mutane abinda kake aikatawa!'ko da bai bayyana ba ai yanzu mun gane shi kuma ko baka faɗa ba Mansur a kwai mugun abinda kake aikatawa!'cewar Dady Habib ke nan da isowar sa gurin kenan,Dady Mansur sakato yayi yana buɗe Habib da wani shegen kallo,tsawan sakanni shuru ya gifta ratsa tawajen,daga baya kuma Dady Mansur ya ɗauke kan sa daga kallon Dady Habib,tare da cigaba da tafiya ba tare da ya tanka musu ba,yanaji Dady Habib yana cewa tabbas anfara yin walƙiya acikin estate ɗin ALHAJI BALARABE kuma da sannu zamu ci gaba da binciko irin ku!'ya faɗa yana mai juyawa dan barin gurin.


Cikin sauri Dije ta koma ɗakin ta,ba abun da take sai kaiwa da kawowa, tabbas itama lokacin da tayiwa uwar ɗakin ta alƙawari yayi,so sai take son ganin ta dan sanar mata da abinda ta daɗe tana nema,yayin da ita kuma nata burin ita da Bintu zai cika na tona mata asiri dan sun riga sun shirya mata gadar zaren da baza ta iya fidda kanta ba,tun tuni wannan ranar take jira dan tabbas tasan idan ta kaiwa uwar ɗakinta wannan labarin ita kuma zata cika mata alƙawarin ta na bayyana mata fuskarta da kuma sakar mata yaran ta,ita kuma tuni ta shirya yadda wasan zai kasan ce,dan tasan yanzu matar ta sakan kan ce akanta dan kwantar da kanta tayi ta nuna mata tabbatas tana tare da ita ɗari bisa ɗari,dan haka tona asirin ta ba wani abun wahala bane agurin ta,wayar ta takalla tare da cizon yatsa dole sai dai ta jira kiranta,amma tasan dole zata kirata a cikin tsukin nan dan haka tana nan tana addu'a tare da jiran kiran ta ako da yaushe.

A hankali ya ke tashin ta har ta buɗe idanun ta dasu ka kunbura saboda kuka da damuwar da take ciki, tashi tayi tana ɗan duban wajen da suke ,amma dai batace masa komai ba,ganin damuwar dake cikin fuskarta ne yasa duk yaji jikin sa ya mutu,haɗa goshin sa yayi da nata sai ya zamana dogon hancin sa na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login