Showing 105001 words to 108000 words out of 184937 words
ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 41 ```
A hankali ta buɗe bakinta ta fara da gaya masa yadda sukayi da Anty Nafisa ba tare da ta ɓoye masa komai ba,shuru tayi bata kuma cewa ko mai ba,wanda shi kuma Abdallah so yake kawai yaji ta bashi labarin ta,
Zuba mata ido yayi yana jiran jin ta ina zata fara,dan a haƙiƙanin gaskiya ya zaƙu da yaji wacece Bintu, wanda tun jiya shine aransa so yake ya tabbatar da abinda mutumin nan ya faɗa,idan har abinda ya faɗa yazo dai dai da wanda Bintun zata faɗa masa,to kuwa tabbas dole su san duk yadda zasuyi dan janyo hankalin Anty Nafisa ta buɗe musu sirrin da take ta ɓoyo, dan yana da yaƙinin cewa sirrin baya rasa na saba da Bintun,yana ji ajikin sa Nafisa itace sanadin komai,itace mafarin dukkanin abinda ya faru,dan ga dukkanin alamu tasan da zaman ɗiyar Umar ɗin,idan ba haka ba ba yadda za ayi ace ta tashi hankalinta kamar yadda Bintu ta sanar dashi,tabbas akwai lauje cikin naɗi akwai wani ɓoyayyan al amari me girma wanda ita Anty Nafisa bata son kowa ya sani, shine kuma sirrin datake muƙu-muƙun ɓoyewa,kuma da izinin Allah su sai sun sata ta faɗa ko ma meye da bakin ta,da kanta zata ɗauki wuƙa ta bur mawa cikinta,koma ace ta burma,tunda gashi bata iya aiwatar da komai batare da shawarar Bintu ba,wanda tabbas wannan wata alama ce data ke nuni da cewa ƙarshen Anty Nafisa ya zo,
"Ganin yadda ya zuba mata ido yasa tashiga ƙif-ƙifta nata idanuwan saboda ta rasa ta ina zata fara, ita sam bata iya bada dogan labari ba,wani tunani tayi a ranta wanda yasa ta ɗan kalleshi,kana cikin sanyin muryar ta tace"zan ɗauko maka deary ɗin da fafi ya bani sai ka duba,ina ga zaifi sauƙi!'ta faɗa tana lumshe idanunta,cikin alamun nuna gamsuwa da Maganar tata yace"kije ki ɗauko yanzu ina jiranki!'ya faɗa yana ɗan kwanciya jikin makarin gadon,wanda shima faɗa kawai yayi amma yasan Bintu baza ta iya fita a wannan lokacin ba,shuru tayi a wajen batare da ta motsaba,juyowa yayi yana fuskantar ta tare da yi mata alamar me take jira?tura ɗan ƙaramin bakinta tayi batare da tace"ko mai ba,har zai share ta sai kuma yaji ba zai iya ba yana so a daren nan ya karanta labarin Bintun,dan haka ya tashi yana mai zura silifas ɗin dake bakin gadon wanda akayi shi da yadin dake shimfiɗe saman gadon,tashi muje! ya faɗa yana wucewa gaba.
A hankali take bin bayan sa, wanda hakan ma ji take kamar za a ruƙota ta baya,lokacin da suka fita falon inno ne taji kamar anabin bayanta,tun tana daurewa har dai ta kumaji kamar an taɓota ta baya,cikin wani irin razana da tsinkewar zuciya ta ruƙo hannun sa yana juyowa ta faɗa jikin sa tasa hannu ta zagaye shi ta rikeshi katamau idanunta a runtse,hannu yasa ya ɗago fuskar ta,yana mamakin abinda ya tsorata ta lokaci ɗaya haka,sam taki bashi damar ganin fuskarta saboda yadda ta shigar da fuskar cikin ƙirjin shi, dalilin kusan cin su da juna ne yasa har yana iya jiyo bugun zuciyar ta wanda suke bugawa tare da tasa zuciyar, A hankali yasa hannun sa A gadon bayan ta yana ɗan partin bayan nata a hankali dan samar mata da nutsuwa,tana manne ajikin sa ya cigaba da tafiya da ita har suka kai cikin ɗakin ta,zama yayi da ita ajikin sa,cikin san yayi calming ɗin ta yace"buɗe idanunki, ki gani ba kowa mun shigo ɗakin ki,tashi ki nunan inda littafin yake!'A hankali yake mata maganar kamar wanda yake tsoran tashin jaririn da ya rasa uwar sa tashi daga baccin da yake,a tsorace ta ɗago kan nata tana bin ɗakin da ido a sace,kana cikin ƙara maƙale shi tace"yana cikin durowar can A cikin wata baƙar jaka, idan ka buɗe jakar zaka kuma ganin wata ƴar leda baƙa to aciki yake!'duk maganar nan da takeyi tuni ta daɗe da mai da kanta ta ƙunshe cikin jikin sa,ba dan Allah yayi masa ƙarfin ji bama da ba zai ji abinda take cewa ba,saboda yadda take yin maganar ƙasa ƙasa,kuma cikin tsoro.
Zuba mata ido yayi ganin bata da alamar zata sake shi yaje ya ɗauko littafin,sai aukin yi masa kwatance da takeyi,ganin lokaci sai tafiya yake basuyi abinda ya kamata ba yasa shi fara ɗan janye ta daga jikinsa, haƙura tayi ta rabu daga jikin nasa amma bata rabu da binsa kamar jela ba,har sai da yaje ya buɗe durowar da ta kwatanta masa,ya ɗauko jakar tare da buɗeta ya ɗauko ledar itama kana ya maida su inda suke ya rufe,tana ganin haka tayi saurin matsawa jikin sa wanda dama jiran sa take ya gama abinda yakeyi ta ɗora daga inda ta tsaya,duban ta yayi cikin fuskarsa da take a haɗe yace"Bint wai wannan wane irin tsorone haka?ki rage tsoron nan yayi yawa!'ya faɗa yana ɗan janye ta daga jikin sa,ba dan taso ba ta rabu da jikinsa tare da raɓe a gefe kana ganin ta zaka gane cewa a matuƙar firgice take, durowar kayanta ya bude tare da ɗauko mata kayan bacci da hijabi, kana ya kama hannunta suka fita,har suka koma ɓangaren sa jikin Bintu bai daina ɓarin tsoro ba,wanda shi Abdallah atunanin sa kawai irin tsorone irin na Bintu,amma a haƙikanin gaskiya a kwai wani abu da shi Abdallah bai sani ba.
Suna shiga ɗakin sa yasaki hannunta tare da miƙa mata kayan da ya ɗauko mata,karɓa tayi batare da ta motsa daga inda take tsaye ba,tana ta dai jujjuya kayan a hannun ta,ganin kamar bata gane abin da yake nufi ba yasa shi cewa kije ki canja kayan jikin ki idan bazaki iya yin wankan ba!'kamar wadda ƙwai ya fashewa haka take taka ƙafaunta dan zuwa toilet ɗin, zuciyar ta kuwa kamar zatayo waje saboda tsananin tsoron da ke cikinta,ƙoƙar tawa tayi ta fara karanto addu'oi bayan tashiga toilet ɗin,haka nan takejin wata kasala a cikin kwana biyun nan wanda ta rasa da lilin hakan,bata iya yin addu'oin ta yadda ya kamata, ko da ta fara sai bacci ya kamata,ga wani irin tsoron da take yawan ji,wanda ta san da ba haka take ba,duk da cewa tasan tana da tsoro amma ba kamar yadda takeji yanzu ba,cikin san dakewa da kalato jarumta ta cire kayan jikin ta,so takeyi ta ɗan yi wankan dan bazata iya bacci batare da tayi wanka ba,da tai makon addu'ar da ta samu ta zauna abakinta tayi wankan tare da ɗaura alwala kana taja ƙaramin tawul ta ɗaura ajikin ta,tana gab da fitowa taji kamar anja tawul ɗin da ta ɗaura ajikinta ta baya,ai da wani irin gudu ta ƙara sa fitowa jikinta yana wani irin rawa,
Ganin ta yayi kawai kamar anjeho ta,da gudu ta faɗa jikin sa tare da ruƙun kumeshi,zuba mata idanunsa yayi zuciyar sa cike da saƙe saƙe,anya kuwa yariyar nan lafiya take?yasan cewa tabbas Bintu tana da tsoro amma kuma bai taɓa ganin tsoron ta kamar na wannan lokacin ba,take zuciyar shi ta fara kaikawo akan wannan al'amari,jin yadda take ta shigewa cikin jikin sane yasa shi dawowa daga nazarin al'amarin da yake,cikin nutsatstsiyar Muryar sa yace"lafiyar ki kuwa? me yake damun ki haka?alokaci ɗaya ya jero mata waɗan nan tambayoyin yana mai son ganin fuskar ta, ta hanyar ƙoƙarin ɗago da kanta da ta cusa a cikin kirjin shi,
Zuba mata narkakkun idanunsa yayi A yayin da yasamu nasarar ɗago kan nata,itama kallon shi takeyi,da idanunta da suka cika da ƙwalla,cikin taushin murya yace"Bint gayamin meke damunki?girgiza kanta tayi saiga wasu zafafan hawaye sun sauka kan kumatunta,atare suka kai hannuwan su kan fuskar ta dan share hawayen,shi yana ƙoƙarin share mata itama tana ƙoƙarin gogewa,sai ya zamana hannun sa yana saman nata,kallon juna suka cigaba dayi cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa,itace tayi ƙoƙarin fara janye idonta akan sa tare da janye hannun ta,kana shi kuma cikin sanyin murya da kasalar da tausayin ta yasaka masa ya yace" da ita,faɗa min damuwar ki!'salon da yayi magana dashi shine ya kuma karya wa Bintu zuciya kawai sai ta saki wani ɗan marayan kuka cikin muryar kukan da takeyi ƙasa ƙasa, tace"bana jin daɗi tsoro nakeji zuciya ta wani irin bugu take,ban taɓa jin abin da nakeji yanzu ba na kasa yin addu'a kayi min addu'a kaji Yahh Abdallah!'ta faɗa tana saka duka hannayen ta saman funkar ta tare da girgiza kanta,wani irin tausayine wanda yake gauraye da wani irin yanayi da ba zai iya tan-tance na meye ba ya rufe shi,cikin yanayin da bai sake shi ba ya gyara kwanciyar shi sosai kana itama ya gyara mata kwanciya ajikin sa tare da sa blanket ya rufeta,kana ya shiga tofa mata addu'oi har sai da yaji ta daina jan ajiyar zuciya tare da shaahsheƙar kukan da takeyi,kana ya janyo littafin da dama yana kusa dashi ya buɗe tare da Bismillah,ya fara karantawa,
"Wani mudubi ne a gaban sa yake kallon duk abinda suke yi, amma Abdallah yana fara yiwa Bintu Addu'oi sai hotan su ya ɓace masa kamar walƙiya,dariya yayi tare da cewa,duk abin da zakayi nasara na gareni tunda har nayi nasara a kan matar ka to kai ma bazaka gagari dodo jack ba!'juyawa yayi ya dubi Alhaji Abubakar dake cikin wani irin yanayi na sihiri,yace"na gaya maka Abubakar sai nayi nasara akan ku,sai naga ƙarshen ku kaida duka zuri ar ka,wani shu'umin murmushi yayi tare da shafa ƙeyar shi da ita kawai nake gani yace"Bintu banyi niyar biyo miki ta haka ba ke kika jawo,saboda kina son ganin ƙarshe na kina son ganin bayana,koshi Abdallah baya ƙoƙarin kai kansa wannan ɗakin amma ke kullum burinki ki tona sirrin dake ɗakin,bayan kuma shine rayuwata shine garkuwa ta,bankaɗa ɗakin nan tamkar bankaɗa sirrina ne,tabbas duk ranar da nabarki ki ka samu nasara akan ɗakin nan to kamar kin samu nasara a kaina ne,wanda Ni kuma bazan taɓa baki wan nan dama ba,dan haka zan saka rayuwarki cikin wasi-wasi da halin razana, wannan tsoron da nasa miki shi ne zai rage miki ƙwarin gwiwa da tunanin tun karar ɗakin,ya kuma ƙyalƙyalewa da wata mahaukaciyar dariya yana cewa yarinya baki san wuta ba sai kin taka Ni ƙi gudune maganin sa gudu,murucin kan dutse ban fito ba sai da na shirya,ƴan jakar uba kwayi kwa gama rana ta tana nan zuwa,ranar da zan ganni gani ga burina a hannu na,Hhhhhh.
" A ɓangaren Anty Nafisa kuwa tana cikin halin ƙaƙa niƙayi,ta kasa zaune balle tsaye,burinta gari ya waye taji abinda Bintu zata kawo mata,sai dai fargaban ta ɗaya,bata so Bintu ta kuma yi mata batun san jin mafarin al'amarin tana tsoron jin hakan daga gareta,lallai wannan shi ake kira ga ƙoshi ga kwanan hanya,wani ɓangare na zuciyar ta yace"to meye ne idan kin gaya mata abinda kika sani, bake kika ce kin yadda da ita ba,ai kamar babu wani abu dan kin sanar da ita ɓoyayyen sirrin ki wanda babu wanda yasa Ni daga ke sai ALLAH da ya halicce ta,zama ta ɗan yi tare da tallafe fuskar ta,wata kuma zuciyar nayi mata gargaɗi da aikata wannan gangancin,to ita dai tafi yadda da ɓangaren dayake mata gargaɗin sanar da Bintu ɓoyayyen ƙullin da ta ƙulla tsawan shekaru batare da ta kwance shi ko warware shi ba,to amma dai yan zu bari ta jira Bintu dan jin abinda ta yanke akan shawarar da ta nema ɗin.
Tunda ya gama karanta littafin babu abinda yake yi sai tasbihi da ƙara kaɗaita Allah assamadu,tabbas ya shiga cikin ruɗani da wani irin tausayi me tsanani na gaba ɗayan su ahlin,tun daga kan Baffan sa Umar da mahaifiyar Bintu Laila da fafi da iyalan sa,sai uwa uba Bintu wadda yakejin tausayin nata har kamar zai saka shi kuka,kallon fuskar Bintun yake da take ta shaƙar baccin ta,ganin yadda take ta ɗan yatsine fuskane ya tabbatar masa da ba wai daɗin baccin take ji ba, addu'oi ya kuma tofa mata kana ya tafi duniyar tunanin yadda zaiyi ya nemo kakar Bintu wato Hajjon su Laila ita da iyalan fafi,wanda kuma yasan hakan ba zai taɓa yiwuwa ba har sai da tallafin Baffan nasa saboda ya riga ya tabbatar da cewa a yanzu haka Baffan sa Umar yasan inda suke, saboda bashi da wata hanya da zai iya sanin abinda ya faru da su Lailan sai ta hanyar su Hajjon,to ta yaya zai yi hakan batare da shi Baffan nasa yasan komai ba?wata zuciyar tace"dashi haba Abdallah sai kace" ba aikin ka ba, wannan ai ƙaramin aikine a wajen ka koda baka bi ta hanyar Baffa Umar ba zaka iya lalubo inda su Hajjo suke,da izinin mai duka da wannan tunanin ya samu ƙwarin gwiwa,to su kuma su fafin suna ina? A hannun wa suke?tunda dai ga dukkanin alamu suna raye,to ko suna wajen wannan tsinan nan da yake batun wai ba dan ba da ya faɗa musu inda su Lailan suke,lumshe idanun sa yayi yana mai jin kansa na sara masa saboda tsabar yawan tunani,cikin nutsuwa ya zame Bintu daga jikin sa ya tashi ya shiga toilet ya ɗauro al wala,har zai tashi Bintu sai kuma kawai yaji gara ya barta taɗanyi bacci,shimfiɗa sallaya yayi tare da fuskantar alƙibla dan kaiwa Allah ƙadiran ala manyasha'u kukan sa domin ya jiɓanci dukkan lamuransa na zahiri da na baɗini, Allah kabamu dacewa duniya da lahira.
Tunda ya tasheta tayi sallar asuba tana cikin yin azkar bacci ya kuma surarta,a haka ya dawo daga masallaci ya same ta,ɗan tsayawa yayi akanta yana kallon ta cike da tunanin abinda yakamata yayi,ya fara tunanin ko dai asibi zasuje aduba lafiyar ta ɗan tabbas yana tunanin akwai matsala cikin wannan sabon Al'amarin na Bintu,da wannan tunanin ya nufi toilet da tsaf tace jikin sa,
Tayi kiran wayar sau ba adadi amma duk abu ɗaya dai wannan matar ke sanar da ita,lambar bata yin aiki,cikin ɓacin rai Hajiya ladidi ta jefar da wayar can gefe tana cigaba da zabga tsakin da tayi shi yafi sau goma,yau kimanin kwana goma ke nan tana kiran mutumin nata wan da yayi mata bad da bami amatsayin wancan shu'umin mutumin,ta rasa dalilin da yasa ta kasa samun shi a waya,sai yanzu ne take ganin waw tar ta na kasa sanin komai akan sa,sai waya da nomber da ayanzu bata da wani amfani a gurin ta,to wai ita tun farko ma mai ya shiga kanta ne da ta kasa yin abinda yake daidai har ta bari wani ƙato can yana sarrafa tunanin ta?gashi ko Nafisa bata san komai akan tarayyarta da ɗaya daga cikin ahlin ALHAJI BALARABE ba,anya kuwa batayi shirme ba? ita da take neman dukiya sai gashi bata samu ko doki ba, tana nan daga zaune duk abin nan da tayi yana son tashi a banza,anya kuwa zata yadda ta tashi atutar babu?babu wan babu ƙanin,taɓ ai kuwa hakan ba zai taɓa yiwuwa ba dolene Nafisa ta cigaba dayi musu yaƙin neman dukiyar cikin ESTATE ɗin nan,tunda dai tana ji tana gani wan nan damar ta kufce mata, yanzu kuwa dole saban lale za a sake tunda suna da Bintu a hannun su,da wannan shawara ta ɗauko wayarta dan kiran ƴar tata dan su tattauna.
A hankali ta zare ta gumin da Ammin nata ta rafka,tare da zama a kusa da ita tana kuma ƙoƙarin san taga sun haɗa ido,sai dai ina hakan bai samu daga gurin Hajiya zulaihat ba,ɗan shuru Rahima tayi tana kallon yadda Ammin ta haɗe mata girar sama da ta ƙasa,ta san ba dan komai takeyin hakan ba sai dan tayi garkuwa daga manyan tambayoyin da tasan zata yi mata,ƙara matsawa tayi kusa da ita kamar zata koma Cikin ta,abin da ya fusata Ammin ke nan,cikin hasala tace"waike kam Rahima meke damunki haka? gotai-gotai dake kin zo kina neman komawa ciki!'ta ƙara sa maganar amatuƙar fusace,dan so take ta kaucewa tambayar da Rahiman take son yi mata a duk lokacin da ta risketa cikin wannan yanayin,cikin marairaice fuska Rahima tace"kai Ammi ke ko irin kewan nan nawa bakyayi,tunda kika korani gurin Hajiya Babba baki taɓa cewa Rahima na ina kewarki yau kizo min mana ko kwana biyu kiyi min sai ki koma ,Ni kuma na gaji da kewarki da rashin ki nazo amma nazo kina korata da hantara!'ta faɗa tana mai goge hawayen da suka zubo mata akan fuska, Allah sarki uwa,sai kuma duk Ammi taji rashin daɗin abinda tayiwa autar ta ta,cikin sanyin murya tace"haba auta ya za ai nace bana kewarki,kema kin san faɗa ma ɓata bakine kawai dai inayin nesa dake ne dan bana son damuwata ta shafeki har ta sakaki cikin wani hali!'ta karasa maganar tare da jin tasowar wani ɗaci mai haɗe da zafi dake ƙunshe cikin zuciyar ta,kama hannun ta Rahima tayi tare da cewa,Ammi idan damuwarki bata saka min damuwa ba to rashin ki zai sa tabbas nima A rasani,domin tabbas kikaci gaba da ɓoye abinda yake ranki tare da baiyana damuwar ki to wataran sai dai nazo na tarar da babuke,yawan damuwarki ya kai mizanin da komai zai iya faruwa dake, Ammi Ni ban ce sai kin faɗa min damuwar ki ba,dan tunda na san bakya son faɗa min na haƙura, amma dai ina so ki rage yawan damuwar ko da ba duka bane nasan lafiyarki zata iya inganta!'murmushi Ammi tayi mai matukar ciwo kana cikin tausayin kanta da ɗiyar tata,tace"wallahi Rahima na rage damuwa tuni na fauwalawa Allah dukkan lamurana,dan da ace ban daina ba da bazan kai yanzu ba,to amma na riga nayi tawassali da tsarkakan sunayen Ubangiji na kuma san cewa ƙaddara jarabawar rayuwace,ta wani tafi ta wani ta wani bata kai ta wani ba, haka kuma ta wani kyakykyawa ta wani kishiyar hakan,dan haka ki daina damuwa,nima na daina damuwa tunda nasan Allah baya bacci yana ji yana kuma gani,kuma na roƙe shi cikin bacci na roƙe shi cikin ido biyu na roƙe shi da rana da dare da safe,haka kuma na roƙe shi cikin sakanni da mintuna da awowi,dan haka ina nan ina jiran Ranar da ƙudurar sa zata haɗu da irada,ranar da zaice ta kasan ce ita kuma ta kasan ce,domin nayi yaƙini tuni