Showing 81001 words to 84000 words out of 184937 words

Chapter 28 - KUDURAR ALLAH COMPLETE BY FATIMA Y ADAM

21 Jul 2024

16869

suka ɗauke mu kika kasa gano babban shu'umin da kuke takara dashi wajen yaƙin neman Abu ɗaya to kuwa tabbas baki kai inda ya kamata kikai ba, kamata yayi kije cikin ESTATE ɗin ku ki binciko wannan takadarin da ya buwayi ahlinku tukun na, sannan kizo ki kama ƙananun ƙwari irin mu,kuma gashi duk kirarin da kike yiwa kanki kin kasa sanin inda mutum daya yake wanda dole shine zai haska miki hanyar samun cikar burinki, kinga kuwa kina da babban aiki agabanki tunda baki san inda ALHAJI Abubakar yake ba,kuma Allah ba zai taɓa baki nasara ba,dan haka ki sani wannan abun da kike kamar bulayi kike kina lalube a cikin duhu!'cikin matuƙar jin zafin maganganun Laila ta fita daga akurkin ɗakin, yayin da ta bada umarnin ci gaba da azabtar da Laila.


Misalin ƙarfe bakwai na yamma ya dawo saboda yana son jin ƙarshen tattaunawarsa da Bintu, dan yasan baƙaramin aikin tane da ta gama abinda takeyi ta yi bacci ba,sai da yayi sallar isha kana ya nufi ɓangaren inno,yana dab da shiga hanyar da zai kashi ɓangaren wan da dole sai ka wuce ɓangaren wannan ɗakin kafin ka ƙara sa saboda shi wannan ɗakin ya kasan ce a tsakiyar ɓangarorin, sai ya zamana duk ɓangaren da zaka shiga sai ka wuce ta ɓangaren ɗakin,


Kamar iska haka yaji wuce war Abu, juyawa yayi sai kuma yaga giftawar inuwar mutum al'amarin da yasa shi dakatawa daga niyar sa ta shiga ɓangaren inno,zubawa wajen ido yayi tare da ƙara nutsuwa ko zai kuma ganin wani abun, amma shuru kake ji sai da ya ɗauki kusan mintuna uku kafin ya bar wajen,amma zuciyar sa cike take da san ganin zahirin wannan inuwar,hakan ne yasa yaƙara sauri dan haɗuwa da Bintu tare da fatan Allah yasa batayi baccin nata na fama ba.


A dai dai lokacin Bintu ta gama duk wani abu da ya dan ganci ogan nata,yayin da su Taufiƙa kuma tuni sun canja shirin su saboda sunyi tunani dukan Bintu ba mafita bace domin abin kansu zai'iya dawowa,wani yaron maƙotan su na ESTATE suka kira ya samo musu karara a makarantar su, dan haka sun shiryawa Bintu mugunta ta rashin mutunci kuma sun fasa barin gidan a cewar su dole su kalli rawar duskon da Bintu zatayi a cikin wannan dare,lokacin da suka zuba mata tana kiching dan haɗawa Oga Abdallah abincin sa,

Tana shiga ta zame kayan ta, tare da waɗawa toilet, batare da tunanin ko maiba ta dauki sosanta wanda shima sai da suka zazzaga masa karara bayan wanda suka saka mata cikin bahon wankan,zuciyar ta ɗaya ta shiga cuɗa jikin ta, kaɗan kaɗan ta fara jin ƙaiƙayin sama sama tun tana daurewa har taji dai abin kamar gaba yakeyi,sauri tayi ta ɗauraye jikinta tare da ɗaukar tawul ta ɗaura,fita tayi daga toilet ɗin tana sosa dukkanin jikinta cikin ƙanƙanin lokaci ta fara fita daga haiyacin ta,gwanin tausayi haka ta shiga goga jikinta a bangon ɗakin ta rasa inda zata tsoma ranta gashi duk inda ta sosa sai ya tashi yayi wani irin ja kamar wanda zai tsatstsafo da jini,kuka ta farayi sosai tana kiran sunan Allah.


Duk abin da ya kamata yayi ya gama sai dai kuma shiru kake ji Bintu ba ita ba alamar ta duk da dama yasan bawuyacin Abune tazo ɗin batare da ya kira taba,cikin azalzalar da zuciyar sa keyi masa ya yunƙura ya tashi,wata zuciyar tace masa mene ne dan kashiga dakin Bintu bayan tariga ta zama mallakinka, ɗan dafe kansa yayi tare da runtse idanunsa, haka nan yake jin wani irin yanayi atare dashi kamar ana taɓa wani ɓari na jikin sa,me ya hana yarinyar nan zuwa ne?ɗan takawa ya farayi har yaje bakin ƙofar sai kuma ya tsaya yana jin nauyi inno ta ganshi wanda shine dalilin da yasa ya kasa yi mata waya ta turo masa Bintun dan kar tayi wani tunani na daban ko ta fassara hakan da wata manufa,har ya juya zai koma amma sai yaji ba zai iya aikata hakan ba,dan haka ya juya tare da buɗe ƙofar yafita kai tsaye hanyar ɗakinta ya nufa wanda da ba dan yana ganin shigar taba da bazaice ga ɗakin ba.


Kuka tayeyi sosai har da birgima duk ta yi wata iri shikansa tawul ɗin da ke jikinta gab yake da fita saboda duk cinyoyin ta a waje suke,gashi har ta rasa inda zata sosa, da ta sosa nan kafin ta ɗauke hannu wani ya fara,kai duk wanda yaga Bintu a wannan lokacin sai yaji ƙwalla cikin idanun sa.

A hankali ya murɗa handle ɗin ƙofar tare da saurin faɗawa ɗakin saboda kukan Bintu da ya fara cin karo da shi cikin kunnuwan sa,a hankali ya ɗan lumshe idanunsa saboda yadda yakejin kukan can cikin jikinsa da zuciyarsa,ci gaba yayi da buɗe ƙofar har ya buɗe ta gaba ɗaya ganin da yayiwa Bintu cikin wannan halin shi ya gusar masa da duk wani tunani da rayuwar da ake yi cikin gidan da rikicin ahalinsa, cikin wani irin taku mai cike da ƙarfin izza wanda ya haɗu da fushin da yasame shi cikin wasu sakanni ya ƙarasa inda take kwance tana burgima tare da soshe soshe,durƙusawa yayi agabanta cikin wata irin murya me cike da sirri kan da har yanzu bai gane su ba,yace"me yasameki? Bintu da batasan da shigowar Oga Abdallah ba tayi wata irin zabura tare da afka masa kana cikin wata irin murya irin wadda take nuni da halin raɗaɗin da mutum yake ciki tace"wayyo Allah Oga Abdallah ka taimakamin jikina ko ina ciwo ƙaiƙayi ciwo zafiii!'ta ƙarasa faɗa cikin wani irin yanayi tare da ƙara shigewa jikin sa tana ƙara mustsika jikinta a cikin nasa, cikin wani irin yanayi da ya saukar masa alokaci ɗaya yace"ƙaiƙayi kuma a ina kika samo ƙaiƙayin!'cikin kuka ta kuma cewa wanka nayi ina cikin yi naji jikina yana ƙaiƙayi!'ta faɗa tana mai ɗaukar hannun sa tare da kaiwa jikinta tanaso ya sosa mata,shi kuwa Abdallah gaba ɗaya yanayin sa ya sauya da wani irin fillin da bai san daga ina ya taho masa ba, mamaki ne ya rufe shi to kuma me ya kawo ƙaiƙayi cikin toilet ɗinta?jin yadda tasakar masa wani azababban kuka yasa shi aje wannan tunanin a gefe ya fara neman hanyar magance wa Bintu wannan ɗan yan muguntar da akayi mata,

Ɗaukar ta yayi cak tare da nufar ƙofa da sauri ya fita daga ɗakin yana dab da shiga falon sa yaji muryar Inno tana cewa Abdallah lafiya kuwa me ya faru da Bintu?cikin sauri yace" mata inno ƙaiƙayi aka sa mata cikin ruwan wanka!'bai saurari innalillahin da innon take zabgawa ba ya shige falonsa da Bintu ɗauke a hannun sa,

Kai tsaye ɗakin sa ya nufa da ita ya shim fiɗeta saman tattausan gadon sa,da sauri ta riƙo hannun sa tare da cewa Ni dai ka sosa min zafi ƙaiƙayi wayyo fafina Bintun ka zata mutu Allah ka taimakeni na daina jin wannan azabar!'zama yayi gefanta yana cewa ke matsalarki ce kin cika raki idan kika ƙyaleni zan haɗo miki abin da zai gusar da kaiƙayin!'noƙe kafaɗa tayi tare da cewa Ni dai banaso ka sosa min kawai!'a hankali ya kai hannun sa kan wuyanta da yaga tana ta sosawa, shafawa ya shiga yi a hankali, cikin karaɗi tace"wayyo Ni dai sosa min zakayi ba shafawa ba!'dafa goshinsa yayi cikin yanayin damuwa yace"Ni ban iya susa ba saboda bani da farce!'ya faɗa tare da ƙoƙarin janye hannunsa cikin sauri ta riƙo hannun tare da mai dashi saman wuyanta, wanda saboda tsananin ƙaiƙayin da take ji bata san a yanayin da take ba na daga ita sai tawul, shammatar ta yayi ya tashi cikin sauri ya haɗa allurar gusar da ƙaikayi duk abinda yake bata lura ba sai da yazo ya kuma zama gefan ta ya ruƙo hannunta tare da janyo ta jikinsa gaba ɗaya, kafin tayi wani yunƙuri ya tsira mata allurar,kuka ta kuma fashewa dashi tare da bugun ƙirjinsa cikin yanayin anyi mata ba dai dai ba,kawai rungumota yayi tare da bubbuga bayanta a lokaci ɗaya kuma yana gyara mata gashinta da ya hargitse,a hankali wani irin bacci ya fara surar ta, sai can kuma ta firgita tare da saka wani kukan cikin haɗe fuska yace"meyene kuma dalla Malama ki mana shuru duk kin cika min kunne da wani shagwaɓaɓɓen kukanki!'cikin kukan tace" Ni dai ƙaiƙayi ka sosa min!'kafin ya ankara zafin ciwon ƙaikayi yasa Bintu ɗaukar hannun sa wanda lokaci ɗaya yaji shi cikin wani abu mai taushi da santsi,wanda a iya tarihin rayuwarsa bai taɓa jin abu mai taushin sa ba....


Ina mai ƙara nusar daku da cewa comments ɗin ku shine ƙwarin gwiwa ta,an fara shiga gundarin labari idan ba kwayin comments zan tsince waɗan da sukeyi na dinga tura musu ta pc


More comments
More confidence

Alkalamin✍🏽

Fatima y Adam
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 34 ```


Runtse idanunsa yayi tare da kiran ya Allah me take shirin yi min ne? ƙoƙarin cire hannunsa ya farayi wani irin kuka ta kuma sawa me ƙarfi wanda dole yasa ya haƙura da ɗauke hannun sai dai ya rasa ta ina zai fara sosa mata wannan abu mai shegen taushi,yayi zurfi cikin tunanin ta yadda zai sosa mata,bai ankara ba yaji ta shiga mussika hannun sa akan bres ɗin ta, tare da cewa Ni dai kasosa min ƙaiƙayi nake ji!'cikin ɗauke numfashi Abdallah ya fara zagaya ya tsansa akan bres ɗinta, tabbas Bintu da tasan halin da tasaka bawan Allah aciki da batayi wannan sakalcin ba,tsayin mintuna biyu ya ɗan dakata tare da duban fuskarta dake kan cinyoyin sa,ashema tayi bacci wata doguwar ajiyar zuciya ya sauke,kai wannan yarinya akwai shegen raki da shagwaɓa shi mamakin yadda akai yake biye mata wannan shirmen yakeyi,tunda yake bai taɓa tunanin zai iya tsayawa ya biyewa mace ba balle kuma me irin wannan shirmen,to amma kawai shi yana ganin dan zuciyarsa na tausayawa Bintu ne na kasancewarta marainiya wadda mugayen mutane suka kewaye ta da salon kaidin su,yana tunanin wannan shine dalilin.

A hankali ya ɗauke hannun sa daga jikin ta tare da gyara mata ɗan ƙaramin towel ɗin dake jikin ta,yayin da idanuwansa suka kasa daina kallon kyakykyawar surarta me tsananin ɗaukar hankali baran ma wannan ƴan madai daitan lemukan da tasa ya sosa mata masu tsananin taushi da sheƙi, a hankali ya ɗan saki tsaki tare da cewa ƙwailar yarinya kawai babu abinda ta sani sai shirme da tsoro yanzu yauma ba zai ji komai daga bakinta ba kenan?Aikuwa insha Allah da safe baza ta bar ɗakin nan ba sai munyi magana!'zame ta yayi daga jikin sa tare da tashi ya faɗa toilet dan yin wanka,bayan ya fito ya saka kayan bacci masu kyau da taushi kalar sararin samaniya ya feshe jikin sa da turarukan sa na bacci masu cike da sirrika,falo ya fita ya ɗanci abinci kaɗan ya ɗora da kayan marmari kana ya koma ɗakin da Bintu take,fulo ya ɗauka ya sa a ƙasa ya kwanta can kuma yaji dai ba zai iya ba sai ya koma saman kujera nan ɗin ma kasa bacci yayi sai da ya dan gana da gadon kana ya samu nutsuwa,fuskan tar fuskar Bintu yayi tare da tsurawa ɗan ƙaramin bakinta ido wan da yasa yaji take yanayin sa yana sauyawa,wai meyasa kallon yarinyar nan yake dagula masa lissafi ne!'wan da shi bai ga abin damuwa a kan wannan ƙwailar yarinyar da ko ƙirgar dangi bata gama ba?rufe idanun sa yayi dan samun kariya daga kallon nata da yake saka shi cikin wani rikitaccen yanayi,sai dai kuma kafin ya gama mitar dake ransa, Bintu tayi wani kyakykyawan juyi wanda take ta nutse cikin yalwataccen ƙirjin sa tare da sa hannun ta gaba ɗaya ta zagaye ƙugun sa ta kuma ɗora fuskarta kan ɗan kewayayyen sajensa sai ya zamana goshinta yana kan haɓarsa,wayyo yarinyar nan da gaske so take ta kasheni ban cika burukana ba,numfa shinsa ya shiga saukewa kan goshin ta wanda ɗumin hucinsa yasa Bintu farkawa daga baccin ta,


Zaro manyan idanunta tayi tare da saurin miƙewa zaune buɗe idanunsa yayi A hankali lokacin da yaji ta fizge jikinta daga nasa wani kallo ya shiga watsa mata,tura bakin ta shiga yi cikin gunguni tace"sai karinga barina ina kwana nan ɗakin ba sai ka tasheni na koma ɗakina ba!'nuna mata hanya yayi alamun ta tashi ta tafi ɗakin nata, ɗan satar kallon sa tayi taga yadda ya haɗe fuska babu alamun wasa, hakan yasa A hankali ta sauka daga kan gadon, har ta fara tafiya sai kuma ta tsaya cak kamar ance kalli jikin ki tana ganin a yadda take ta saka wata ƙara wadda sai da Abdallah yasa hannu ya toshe kunnuwan sa da idanun sa,da gudu ta dawo kan gadon tare da yaye bedsheet ɗin ta kanan naɗe jikinta cike da kunya da tsoro,gaba ɗaya ta rufe kanta bata ko san ƙara kallon Oga Abdallah,yanzu ke nan dama tun ɗazu A haka yake kallonta,A haka ya rugumeta ba kaya? na shiga uku ta faɗa da ƙarfi tare da sakin wani marayan kuka me cike da tsananin kunya da nadama yayin da ta tuna abinda tayi ɗazu cikin yanayin fitar hayyaci,hannunta tasa kan bres ɗin ta ta dafe shi tana mai jin tsananin ta kaicin kanta da har tayi sake Oga Abdallah ya taɓa mata bres, wayyo Ni wace irin yarinya ce haka ya Allah ka dubeni!'a fili take ta sakin maganganun ta, tana mai ƙara jin takaicin kanta dana oganta,

Abdallah tun yana jin haushin yarintar Bintu har sai da abin ya koma bashi dariya haka nan ya dinga jin wani nishaɗin kallon diramar Bintun,jin shuru yasa ta ɗan leƙo da fuskarta amma sai karaf idanuwanta cikin na Oga Abdallah ai da sauri ta mayadda kan ta cikin bedsheet ɗin tare da ci gaba da kukanta,kwanciya yayi yana sakin wani ɗan muskilin murmushi wanda yayi matuƙar ƙawata fuskarsa da wani hasken annuri,tabbas Abdallah ya san idan yayi murmushi zai dinga kashe zuciyoyin mata da yawa ina ga shi yasa yake daga cikin abinda bai cika yi ba arayuwar sa,rufe idanun sa yayi kamar mai bacci tsawon mintuna uku yana sauraren sheshsheƙar kukan Bintu,ita kuwa jin shurun yayi yawa yasa ta kuma leƙo da kanta ganin kamar yayi bacci sai ta kuma tashi a hankali cikin sanɗa ta leƙa idanun sa har da sa hannu ta ɗan fifita idanun wai ta tabbatar yayi baccin ganin bai motsaba yasa ta kwashi fululluka ta shiga jerawa a tsakiyar su ta raba musu gadon biyu,ɗan kallon sa tayi tare da cewa dan ina jin tsoro ne amma da yanzu zan gudu ɗakina,tare da murguɗa bakinta,ko mawa tayi ta kwanta tare da runtse idanunta tayi addu'a ta tofa sai ta samu kanta da yiwa Abdallah addu'a shima ta tofa masa,kasancewar Bintu bata da wuyar bacci yasa cikin mintuna biyu ta koma baccin ta,

A hankali ya buɗe idanunsa tare da zuba su kan saitin fuskar Bintu dake rufe cikin tattausan bargo,wani ɗan munafukin murmushi ne akan leɓanshi yayin da yake bin filon da ta jera da idanu yana ƙara mamakin sakarcin Bintu, amma kuma wani lokacin sai yaga kamar tana da tunani sai dai idan akace abu ya haɗa da yarinta dole sai a hankali,a hankali yasa hannu ya cire fulullukan ya maida su mazaunin su kana ya kwanta tare da lumshe idanun sa, shima addu'o'in yayi ya tofa mata, Bintu fa tana da matukar san jiki shiyasa take da yawan juyi cikin bacci matar da ta saka fulo tsakanin su sai gata garin juyi ta dawo da kanta har cikin ƙirjin wanda tayi kariya da fulo saboda shi,rungume ta ya kumayi tare da jan blanket ya rufe su daga haka shima wani bacci mai daɗi yayi awan gaba dashi,asuba ta gari Abdubint.


Tun tana sauraran jin sakamakon abinda suka aikata wa Bintu har dai taji shurun yayi yawa, tashi tayi da niyar dubawa taga ko dai suma tayi saboda ƙayƙayin, zuciyar ta taji tayi wani irin fari tare da ƙara saurin shiga ɗakin tana fatan ganin Bintu cikin mummunan yanayi,turus tayi ganin babu kowa ɗakin toilet ta shiga ta duba nan ma babu Bintu babu alamar ta cikin sauri ta nufi kiching nan ma bata nan sai kawai tunanin ta ya bata Bintu ta gudu saboda azabar da taji tasan wannan ƙaiƙayin zai iya zautar da mutum na wani ɗan lokacin, da sauri ta koma ɗakin inno tana shiga taga inno tana nafilar dare ɗan zama tayi tana jiran ta ta idar da sallar,bayan inno ta idar ta dubi Taufiƙa tace"yaya dai cikin daren nan ince dai lafiya ko? Taufiƙa tace"Bintu nake nema bangan taba!' cikin wani tuhumammen kallo inno tace"mai zatayi miki Bintun ko kina tunanin muguntarku zatayi tasiri a gurin Bintu ne?idan ma wannan tunanin kike ki dai na dan Bintu kainuwace Allah ya riga ya kareta daga dukkan sharrin mai sharri,yanzu haka tana hannun mijinta yana can yana jinyar matar sa!'wani irin zufa ne ya shiga ke towa Taufiƙa tare da wani irin mummunan tashin hankali kallon inno tayi tare da cewa inno me yasa bakya ƙaunata me yasa kika fifita bare a kaina? inno ta katse ta da cewa mugun halinki shi na tsana bake ba da zaki gyara halinki da kinga soyayyata, Bintu kuma ba bare bace agurina kuma dalilin da yasa na fisonta halinta ne yaja mata dan haka dole naso Bintu fiye dake,kuma daga yau karki kuma yin tunanin zaki goge Bintu daga zuciyata saboda ta riga takafu na kuma yadda da ita ɗari bisa ɗari ki tashi ki bani ɗakuna zanyi bacci!'cikin wani irin kuka na tsantsan baƙin ciki da takaici tare da tsana me tsanani ta tashi ta fita daga ɗakin inno, tsayawa tayi saitin falon Abdallah kallon ƙofar takeyi tamkar wadda zata zuƙo Bintu ta ciki,wai me yasa rayuwa tazo mata da hakane me yasa duk lokacin da tayiwa Bintu wata mugunta take dawo wa kanta me yasa idan taso ganin Bintu cikin baƙin ciki da damuwa sai abin ya juya kanta?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login