Showing 84001 words to 87000 words out of 184937 words
hannu ta ɗora a kanta tanajin kamar tayi ta zunduma ihu,to wai dama Abdallah yana son Bintu ne ko Yaya?me sukeyi idan suka shiga ɗakin?tunanin da tayi ne yasa ta zubewa a wajen tana mai ƙara sakin wani rikitaccen kuka mai sosa zuciya (wanda koni naji tausayin Taufiƙa wannan shi ake kira ƙaiƙayi koma kan masheƙiya haka nan kuma ramin ƙarya ƙurarrene kuma ƙarshen ta idan ka haƙa ramin mugunta kai zaka zurma)
A wajen gari ya wayewa Taufiƙa har lokacin da Abdallah ya fito dan shiga ƙofar part ɗin Alhaji Baba dan tafiya msallaci,cike da ɗunbin mamaki yake bin Taufiƙa da kallo wanda sai yace tunda yake da ita da kuma haukan da takeyi akan sa sai yaune zai iya tan-tance kamanninta,ɗauke kanshi yayi lokacin da yaga ta zubo mashi jajayen idanunta da suka kumbura suntum ga rashin bacci ga kuka,ji takeyi kamar ta cinyeshi kowa ya huta Allah ne ya jarrabe ta da wannan ƙaƙƙarfar ƙauna me zafi dasa ta fita daga hayyacinta,cikin sauri ya bar gurin tare da waɗawa ƙofar da zata kaishi part ɗin Alhaji Baba,yana maiyiwa Bintu addu'ar neman tsari da wannan azzalumar yariyar,Taufiƙa ji tayi kawai gara ta shiga ɗakin taje ta kashe Bintu koda kuwa ita ma za a kasheta ta gwammace hakan da ace dai tana gani Bintu tana rayuwar farinciki ita da Abdallah,yunƙurawa tayi ta tashi ta ƙarasa bakin ƙofar falon, tana saka hannunta taji alamun a rufe ƙofar take wanda bata sani ba shi kuma Abdallah ya rufe Bintu ne dan kar ta tashi ta gudu bai samu labarin dayake buƙatar samu daga wajen ta ba,wata irin ƙwafa tayi wato ma har wani kulle kofa takeyi saboda samun waje,juyawa tayi cikin fushi da ƙuncin zuciya.
Ita kuwa Bintu tunda ta tashi ta ta buɗe ƙofar falon yaƙi buɗuwa hakan ne ya tabbatar mata da cewa rufeta yayi,to ita yanzu da wane ido zata dubi Oga Abdallah me zata iya ce masa?gaskiya baza ta iya kula shi a halin da take ciki ba
babu yadda zatayi haka taje ta ɗauro alwala tazo ta zurma doguwar jallabiyar sa wadda tayi mata tsayi sosai dubawa tayi ta ɗauki wani sabon towel babba ta rufa ta tayar da sallar ta,
Tana idarwa ta cire rigar saboda yadda take taɗeta, towel ɗin ta mayar ta ɗaura kasancewar wannan babbane shi yasa ya rufe mata har ƙaurinta,zama tayi abakin gadon wanda tasan da aɗakin ta take da yanzu ta faɗa kiching,dole a yanzu tayi tagumi zaman jira, ko karatun da takeyi bata samu ba tunda babu suttura ajikinta sai dai tasbihi da sauran lazumukanta da tacigaba dayi cikin zuciyar ta,
A wannan halin ya shigo ya sameta wanda bata san shigowar sa ba sai sallamar sa da taji akanta, wata irin zabura tayi tana neman gurin tsira daga tarkon da Abdallah ya ɗana mata,yana tsaye hannun sa soke cikin aljihun sa yana kallon yadda take ta dubi-dubi dan neman mafaka da ta rasa mafakar kawai sai ta fara tsiyayar da hawaye dan a hakikanin gaskiya tana matuƙar jin kunyar haɗa ido da Oga Abdallah,zama yayi kusa da ita wanda hakan ya kuma jefa zuciyar ta cikin wani irin bugu da fargaba,kawai sai ta sukuyar da kanta tana ta faman jajjan towel ɗin dake jikinta dan ya ƙara rufe mata jikin ta,cikin muryar sa da take fita ɗaɗɗaya da yanayin sa na muskilin namiji me tsananin aji da kwarjini yace"a karo na biyu zan kuma tambayarki idan kuma kika kawo min wasa sai na zaneki anan gurin tare da allura mai zafi guda biyar!'ɗagowa tayi ta ɗan saci kallon sa sai taga ashe idanunsa suna kanta,maida kanta tayi tare da cewa zan faɗa maka duk abinda ka tambayeni!'wai kuma sai yaji wani abu A ransa ganin yadda tayi magana cikin rauni, ya rasa me yasa yake da rauni da yawa akan yarinyar nan, cikin tausasa murya yace"ki nutsu ki cire tsoron ko mai ki bani amsa yadda ya kamata!'jin jina masa kai tayi tare da cewa to cikin rawar muryarta,ɗan gyara zaman sa yayi kana yace"wane irin aiki Nafisa ta sakaki kiyi mata san nan wanene mutumin da kike zargi suna aiki da Hajiya ladidi?da sauri ta dube shi cike da mamakin yadda akayi yasan abin da take ɓoye masa,ɗan ɗage mata gira yayi ganin yadda take masa kallon mamaki, sunkuyar da kanta tayi cikin jin kunya tare da cewa,Hajiya ladidi bata buɗe min zan can ba kawai tayi suɓutar bakine shiyasa nayi tunanin bayan Anty Nafisa a kwai wanda suke shirya wani al amarin tare, amma kuma nayi mamakin yadda akayi suke munafuntar junansu ita da Anty Nafisa,daga baya kuma nayi tunanin yadda zuciyoyin su suke babu abinda bazasu iya aikatawa junansu ba indai akan burukan sune,cikin ƙara yin ƙasa da murya ta fara bashi labarin yadda sukayi da Anty Nafisa tun daga farko har ƙarshe,cikin tsananin mamaki yake duban Bintun shi dama bai san komai a kan Nafisa ba kawai dai cikin salon aiki ne ya bigi cikin Bintun dan kar tayi tunanin ɓoye masa ko bashi labarin ƙarya,tashi yayi ya shiga zaga ɗakin hannun sa a dunƙule cikin juna kan sa ya kulle to amma idan hakane anya kuwa babu hannun Nafisa a saka masa guba?to kuma ta yaya zata kashe shi bayan cewa tayi sai Bintu taƙi yadda ko kuma ta gayawa wani sirrinta san nan zata aikata mata wani mummunan abu?kuma idan yayi la akari da yadda ita ma ta nunawa Bintu tana san sanin wanda yasa ta aikata wannan aiki sai kuma tunanin sa ya juya,kai wannan al'amari da matuƙar ɗaure kai yake dole ne ya bin ciki wanda ya saka masa gubar nan dan yana da yaƙini cewa shima zai zama jigo cikin binciken su zai ƙara faɗaɗa musu hanyar bincike cikin sauki tare da samun nasara,komawa yayi ya zauna inda ya tashi tare da duban Bintu da itama take ta binsa da kallo,yace"kin san me nake so dake? Bintu ta girgiza kanta ya ɗora mata da cewa inaso ki rage tsoro dan hakan shine zai kawo mana nasara cikin aikin mu,cikin sanyin murya tace"babu abinda zan iya taimaka maka dashi akan kyakykyawar niyarka ta binciko ruɓaɓɓun ƙwayayen dake cikin ahlinku?kallon bakinta yake dan baya iya jurar kallon ƙwayar idanunta,yace"kina ganin zaki iya taimaka mana?zan taimaka maka saboda raina fansane ga waɗanda aka cuta acikin ahlin nan!'a yanzun kallon idanun ta yake kai tsaye saboda yadda yaga wutar fansa na ci daga cikin kyawawan idanun ta yayin da suka cika da ƙwallar da take dauriya dan kar ta zubo saboda tun daga yanzu take san zama jaruma me yaƙi afilin daga,tunda yanzu ta samu tallafin gwarzan miji jarumi mara tsoro,dan haka ita ma ya zama dole ta cire duk wata fargaba domin fuskantar gagarumin yaƙin dake gabansu, cikin tausasa harshe yace"kin tabbata dai kin karɓi aikin da Nafisa ta baki ko?jinjina masa kai tayi,yace da kyau kin fara naki aikin tun daga yanzu da wannan ƙudurin nata zamu mamayeta,san nan ina so lallai zamu haɗu da Dije amma ba yanzu ba saboda haɗuwa da ita sai an saka lura da taka tsan tsan,ita kuma Hajiya ladidi cikin wayo zamu sa ta faɗi wanda suke tare dashi!'Bintu tace"oga a kwai tunanin da nayi akan mu amalar sirri tsakanin Hajiya ladidi da Anty Nafisa,taci gaba da cewa me zai hana tunda dukkan su basa son ɗayan su yasan sirrin ɗayansu mu kuma mubi wannan hanyar dan haɗa su faɗa, wanda Ni aganina zamu iya samun wasu muhimman sirrika ta hanyar tunzura zuciyoyin su,wanda zamuyi hakan ne cikin dabara batare da sun san daga inda abin ya fito ba!'duban ta yake cike da mamakin basirar ta tana da kaifin tunani tabbas ba karamin ci gaba zata kawo cikin wannan tafiyar ba,amma haka nan yake jin tsoron zaƙewarta cikin lamarin yana gudun kar wani abu ya yasame ta saboda ita yarinyace mai cike da ƙuriciya,hannu yasa ya shafa fuskarsa tare da jan dogon numfashi kana yace kinyi tunani mai kyau amma bake zakiyi wannan aikin ba!saboda me to wazaiyi?,ta faɗa duk alokaci ɗaya,haɗe fuskarsa ya kumayi tare da cewa kar su cutar dake kuma wadda ta san kan aiki zan saka tayi!'sakato tayi tana kallonsa yayin da ya tashi yana ƙoƙarin shiga toilet,har ya shige bata daina mamakin sa ba ita dai a iya sanin ta da shi bai cika bawa abu muhimmanci ba ballantana bada amsa amma yau shine ya zauna yake doguwar magana da ita har da su bata amsa kai harda ma ƙarin iyayi wai kar acutar da ita,ko da ike ai ɓangaren aikin sa aka taɓa wanda shi dama idan kaga dogon zan cen sa to akan aikin sane, taɓe baki tayi tana mai tuna ranar da tasan aikin da yake bayan aikin asibintin da tasan shine aikin sa, tasha mamaki lokacin da taga ID card ɗin sa tare da cikakken sunansa shi yasa abin bai dame ta ba tunda dama ta riga ta sani,ta shi tayi ta ɗauki ƙaramin tawul ɗin ta ta rufa kana ta fita daga ɓangaren.
Wata irin mahaukaciyar dariya ya bushe da ita, tare da cewa lallai yaro bai san wuta ba sai ya taka yan zu aka fara wasan su atunanin su zasu iya rusani?tabbas kunyi gan yancin fara yaƙata domin bazaku taɓa cin nasara akaina ba,haƙiƙa naji daɗin wannan himma taku domin ta haka ne zan cimma burina dole kune ginshiƙin burina daku zanyi garkuwa domin sanin inda wannan ɓoyayyan sirri yake wanda ake tunanin bamu san dashi ba,hhhh ya kuma bushewa da wata ibilishiyar dariya tare da cewa Ni da nake da Jack ga kuma shugaba ai babu abinda zai gagareni samu adunayar nan (wa iya zubilla Allah ka shirya waɗanda suka ɓata dan Alfarmar shugaba)duk ta inda kuka ɓullo sai na ɓullo muku, Abubakar dole ka buɗe baki kasanar dani inda sirrin nan yake a ina aka ɓoyeshi?lokacin faɗarka yayi saboda fansar rayuwar yaronka da ƴar ɗan uwanka, lokacin ta shinka ya kusa saboda biyan buƙatata da nasamu kuma shikenan zan ƙara saka domin nasamu abinda ya hanani kasheka,ɗan taɓa kan kyakkyawan mutumin da yake a daskare kamar ƙanƙara yayi,sai ga wani irin farin hayaƙi na fitowa daga jikin sa idanun sa ne kawai keyin motsi sai bugawar zuciyar da ita ke nuni da har yanzu yana raye, zagaye shi ya shiga yi yana tafa hannayen sa ya cigaba da cewa babu wanda zai mallaki wannan abu idan har ina numfashi,duk masu bulayi da neman inda kake kallon su kawai nakeyi waɗan can mutanen da wani shu'umin ya sace su babu abinda zasu karan kawai dai ina ƙoƙarin rage yawan sune saboda zasu iya zama bara zana cikin samun farin cikina, Laila da ɗan uwanki duk ranar da na haɗa ido da wanda ya ɗaukeku gaba ɗayan ku zan haɗa na kashe bana so ki bayyana cikin ahlin ALHAJI BALARABE dake da shegiyar yariyar ki,duk da cewa ita ta bayyana amma tunda babu wanda yasan da labarin auren uwarta babu ta yadda za ayi ajingina ta da ahlin ESTATE ,kafun suma lokacinsu ya ƙara so ita da gwarzan mijinta,dariya yakeyi cike da farin cikin yana samun duk yadda yake so, tsarin sa yana tafiya dai dai da yadda ya buƙata,wani farin cikin ma sai nan gaba.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 35 ```
Tun ranar da Laila ta gaggaya mata maganganun nan masu zafi da nusar da ita abinda ta manta, bata ƙara samun nutsuwa ba gaba ɗaya hankalin ta atashe yake, tabbas ta amince da maganar Laila basu ya kamata ta tsare akan wani ƙaramin dalili ba ko da yake shima wani jigone sanin wannan mugun mashirikin na cikin ahlin ALHAJI BALARABE to amma ita Laila da ɗan uwanta sun ƙi bata haɗin kai su sanar da ita ko waye wannan mutumin dan sanin sa shima yana da matukar muhimmanci dan tana da tabbacin zai iya sanin inda aka ɓoye Abubakar, duk iya takunta a wannan karon ƙwaƙwalwarta bata aiki duk wanda zata yi tsammanin yasan inda Abubakar yake ba sannan inda zata lalubo shi ba bayan wannan dai shi umin da takasa gano waye duk iya binciken ta kuwa, da hakan ta jinjinawa taƙadirancin sa,ta riga ta sani kamar yadda ta iya takun ta haka suma ragowar masu neman suka iya nasu takun,babu wanda ta iya ganowa sai ƴan tsirarin mutanen nan su Alhaji Nasir da kuma Hajiya ladidi,to amma kuma yanzu duk bata tasu take ba dan ta riga ta gama bincikenta akansu tasan suma har yanzu lalube suke,shine dalilin da yasa ta kuma riƙe wuta gurin su Laila dan tayi yaƙinin sun san mutumin nan sai dai ta rasa dalilin su na ƙin gaya mata ko wanene,iska ta fesar daga cikin bakin ta dole Sayyid ya kamata ta kira tunda shi yayi mata binciken Bintun da waɗanda suka kawota gidan ta dalilin hakane yasa ta gano Hajiya ladidi da ƴarta Nafisa,wani shu umin murmushi tayi yayin da ta tuna shikansa Sayyid ɗin bai san fuskarta da Muryar ta ba balle ya gane WACCE ITA,dole shi zata saka yasawa ubansa ido cikin hikima zata sashi yayi mata aiki akan ubansa,har yanzu da akwai ragowar ƙwarin gwiwa atare da ita kuma baza ta taɓa sarewa ba har sai taga abinda ya turewa buzu naɗi,
Ta ɓangaren su Alhaji Nasir tare da tawagar sa su Baffa Hashir sun miƙa cikin binciken kishiyoyin su, kamar yadda Samira ta tunatar dasu sai dai kuma basu manta da ci gaba da neman inda mukullin samun sirrin su yake ba wato Alhaji Abubakar,haka kuma sun kasa ɗauke ido daga kan Abdallah saboda suna matuƙar tsoron sa,kowa nema yake yi ido rufe, yayin da ta gefe Samira ta cika da ɗaukin san Alhaji Sama'ila ya sanar da ita wannan sirri,kamar dai yadda suka saba yauma sun haɗu a mahaɗar da suke haɗuwa,Samira cikin yanayin jimami tace"har yanzu babu wani da kuka samu wanda kuke tunanin yana da hannu cikin yaƙin nema,ɗan shuru yayi kana ya ɗan numfasa tare da cewa a kwai wanda muke zargin ana sashi bibiyar mu da kuma saka mana ido a dukkan al'amarin mu!'wani irin bugu zuciyar Samira tayi tare da zaro ido waje,Alhaji Sama'ila ya cigaba da cewa abinda yasa nace miki saka nace miki sakashi akayi shine saboda bai san komai akan wannan sirrin ba sai dai idan faɗa masa akayi,cikin zaƙuwa da kuma fargaba Samira tace"to waye wannan?kai tsaye yace" da ita Sayyid ɗan gidan Mansur!'wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ta saki dan da atunanin ta ko ya gano wanda Oga Abdallah yasa shi aiki akan su ne,cikin mamaki tace'Sayyid kuma? tare da ƙara duban wayarta adabarance dan ta tabbatar bata kauce daga kan recording ɗin da take yi ba,yace"Sayyid shine wanda nake zargi abinda bansani ba kawai shine Mansur ɗin ne yake saka shi kokuwa wasune daban?jin jina kai Samira tayi tare da cewa shi kaɗai kake zargi yanzu?yace shikaɗaine kafin binciken mu ya kuma samo mana wani!'da kyau Alhajina yanzu zakaga komai naku yana tafiya kan tsari daga nan ma sai kuga kun samo wannan abu mai mahimmanci da kuke nema!'yace"tabbas hakane amma kuma wani abu da ban sanar dake ba Samira shi wannan abu da muke rububin nema mutum ɗaya ne yasan inda yake kuma an sace shi kusan shekaru talatin kuma tunda aka ɗauke sa ba akuma jin ɗuriyar sa ba hatta da ESTATE babu Wanda ya kuma tunawa shi,to a yanzu dole sai mun same shi kafin mu sami abun da muke hari dan shi kaɗai ne zai nuna inda aka killace abun!'jinjina kai kawai Samira takeyi saboda Al'amarin yayi matuƙar taɓata,tace"baku san inda yake ba kenan?da mun sani Samira ai da tuni an wuce gun kuma da yanzu wani labarin akeyi ba wannan ba!'hakane to yanzu wane mataki kuka ɗauka dan cigaba da neman sa?Samira kenan ai baza mu zauna ba saboda duk abinda kikaga munyi dan shi mukeyi da zarar mun sami inda Abubakar yake,shike nan kakarmu ta yanke saƙa!'to Alhaji meye tabbacin ka na za a sameshi a raye?wani makirin murmushi ya saki kana yace"ai Samira Ina tabbatar miki da cewa da ankashe Abubakar da yanzu an fara kashe ƴan uwansa da mahaifin sa,Bama shi kaɗai ba duk wanda yake da ƙudurin samun wannan abu to wannan shine shirin sa na gaba koma waye ko su waye,dan magadan wannan abu su za akashe ko muma burinmu kenan,shi yasa nace miki ba akashe Abubakar ba,kuma Abubakar yana da matukar taurin kai ba zai faɗi inda abun nan yake da wuriba ba!'Samira da al ajabi yaƙi barin fuskarta da zuciyarta tace"ya akayi ku kasan da wannan abun kuma meye shi wannan abu haka da ake irin wannan ta asa akan sa? murmushi yayi tare da cewa Samira bazaki gane ba wannan amsar ba yanzu zaki san ta ba,amma,abinda zan gaya miki shine shi kan sa me abun bai san sirrin ya fita ba bayan Abubakar bai sanar da kowa ba, yadda akayi muka sani shima zaki sani nan gaba!'batayi masa musu ba saboda gudun karya ganota, wannan ma da ta samu ba ƙaramin babban nasara suka samu ba yanzu za ta kaiwa Oga Abdallah sai suji mataki na gaba da Yakamata su ɗauka,daga nan ta daure suka ɗan sha copy tare amma ji take kamar tayi tsuntuwa ta ganta office ɗin Oga Abdallah.
Babbar macece wadda zata iya kaiwa sa ar inno zaune take bakin madafa daga dukkanin alamu dai girki takeyi,amma kana kallon fuskarta zaka iya hango ɓoyyayyiyar damuwar da ta kasa bushewa daga zuciyarta,wata makiman ciyar matace ta fito daga wani ɗaki a ƙiyasina baza ta wuce talatin da biyar zuwa da zuwa da bakwai ba,da sauri ta ƙarasa gaban matar dake gaban madafi tare da cewa haba Hajjo me yasa baki bari na fito ba kin san ba lafiyar idone dake ba amma kike zuwa gaban hayaƙi!'kama hannunta tayi tare da miƙar da ita tsaye sai da ta kaita har kan tabarmar dake shimfiɗe a makeken tsakar gidan,zama