Showing 171001 words to 174000 words out of 184937 words

Chapter 58 - KUDURAR ALLAH COMPLETE BY FATIMA Y ADAM

21 Jul 2024

16886

kammala shirina,salamatu reza karuwar gida wadda take cin karenta a lokacin,ita najewa da buƙatata amatsayin ta na karuwa,ai kuwa tun alakocin ta sanar dani ai faduwa tazo dai dai da zama dan kuwa tayi sake a wannan karon ta ɗauki ciki,dan alokacin zubar dashi take ta faman yi yaƙi zubuwa,daga nan dai muka shirya me yuwuwa,muka tsara komai cikin dabara,dan haka lokacin da naje Maiduguri dan aihuwa,sai na sharawa mamana ƙaryar cewa a gidan mai magani zan haihu,na nuna mata ina da matsala kuma nice na samo mai maganin likitace ƙwararriya,ita zata karɓi haihuwa ta kuma ba aso haihuwar tazo babu ita akusa saboda matsalar da ka iya faruwa,ras ƙaryata ta yi tasiri azuciyar ka da na mamana,daga nan na shirya muka koma gidan da na karɓi hayar kwanaki, cikin ikon Allah kuwa sai salamatu reza ta haihu a cikin satin sai dai kuma tana haihuwa tace ga garin ku nan,duk da cewa naji mutuwar ta amma hakan bai hana Ni farin cikin cewa bani da wata sauran barazana arayuwata ba,babu wanda yasan me na shirya daga Ni sai ita sai Allah da yafimu sani,na dawo gida da yarona,daga nan kazo kayi masa huɗuba kace kuma mu zauna muyi arba'in saboda bai kamata nayi tafiya mai nisa ba,ka sakawa yaron suna Habibu!'

Innalillahi'wa'inna ialaihi raji un abinda yake fitowa daga bakuna mafi hankali kenan, daga ciki harda uban gayyar Alhaji Baba,wata irin zabura Dady Habib yayi kamar mahaukaci ya nufo Hajjah yana cewa ke muguwace Hajjah yanzu kina so kice Ni ba ɗan Alhaji Baba bane?Ni dan ban zamo ɗan ki ba ba abin damuwata bane,amma dan Allah kar kice Alhaji Baba ba mahaifina bane,duk irin mugun halina Ina fatan zama ɗan mutum na gari kamar Alhaji Baba!'sai ga Dady Habib yana zubda waye kamar ƙaramin yaro, Hajjah tace"Habibu sai dai kar a kuma domin kuwa ba kazamo ɗan Alhaji ba san nan kuma baka zamo ɗana ba,domin Allah bai bawa Alhaji gurɓataccen ɗa ba,kasancewar sa mutumin da yatsaya ga Allah,kuma ko ban fada ba dole anzo gaɓar da zaka sakawa mutane kokwanto azuciyar su,domin abinda kayi ya wuce hankali ya ɗauka cewa ɗan uwa zai iya yiwa ɗan uwan sa irin abin da kai kayi,Ni kaina habibu na ji daɗi da yakanance bani ce na haifeka ba domin mugun halinka ya zarta nawa nesa ba kusa ba!'wani irin kuka ne ya kufce mata tana mai cigaba da basu labarin abinda ta aikata ba ta ɓoye komai ba, ta ƙare da ɗurƙushewa gaban Hajiya Babba tana kukan neman gafarar ta, Alhaji Baba kuwa ya kasa cewa komai,sai kansa da yayi ƙasa dashi Allah kaɗai yasan halin da zuciyar sa take ciki,a hankali ya miƙe ya fara ratsa taron ƴaƴan sa da jikokin sa ya wuce can cikin ɗakinsa ya kulle,babu wanda yayi ƙoƙarin dakatar dashi saboda sun san a wannan lokaci dole ayi masa uzuri dan ma ya kasance mutum mai tsananin tawakkali,da juriya akan ƙaddarar da tasameshi.


Kuka Dady Habib yake da idanun sa wanda bai taɓa tunanin zaiyi shiba, wannan lamarin shi kaɗai ya karya lagon sa,tabbas idan yace ya ya taɓa jin makamancin wannan tashin hankalin yayi ƙarya, cikin kukan yake cewa Hajja kin cuceni,me yasa baki barni na taso a hannun dan gin uwa ta ba koda kuwa za a dinga yimin girin uba?yanzu duk taran mutanen nan da da suka kasance ƴan uwana yanzu na zama bare acikin su kenan?maganganun da yake yi har sai da takai da cewa wasu sun fara tausaya masa karma Dady Mansur yaji labari,dan abun shi yawa yayi masa ya mutukar razana da jin wacece Hajjah da iri n abinda ta shuka,kallon Habibu yake cike da haushi da kuma tausayi Sa dai shi kansa yasan cewa Habibu ba abin tausayi bane,saboda ya cutar da mutane masu yawa arayuwar sa,wanda kuma alhakin sune ya fara bibiyar sa,tun da gashi har ƙaddarar sa ta juya sama ta koma masa ƙasa,tabbas duk wanda bai ji tsoran Allah ba ɗaiɗaicewa tana tare da rayuwarsa,Dady Habib yana cikin halin nadama wadda ta zame masa ƙeyar baya, yaji an damƙi hannun shi yana ɗagowa yaga Safwan ne da ankwa a hannun sa da alamu dai zai koma inda ya fito ne,dan Nana ne kaɗai ya fi dacewa dashi kafin ya fara ganin sakaiyyar Allah,saboda tsananin tashin hankali da zaucewar tunani bai iya yin musu ba haka ya tashi ya bishi idanun sa na zubar da zafafan hawayen nadama.


Duk wanda ka gani afalon Alhaji Baba zakayi tunanin mutuwa akayi masa mai shiga jiki,sai dai kuma sam ba haka bane tsabar damuwa da tashin hankali da kuma tsinkewa da al'amuran duniya ne,Hajiya ladidi da akayi komai agaban idanun ta,tuni jikinta yayi sanyi nadama ta shigeta,tare da fara itgfari akan abun da taso yiwa rayuwarta,Alhajin Nafisa ne ya ɗan ja numfashi kana yace"ai wannan al'amari wanda ya shafi ahline,bai kamata kuyi kirana ba,duk da dai ban san dalilin Alhaji Baba nayin haka ba!'Alhaji Rufa'i ne ya ɗan share gumin dake saman goshinsa,kana yace"ai Alhaji kaima wannan zama ya shafeka matuƙa,kawai dai Alhaji ya ɗan shiga cikin wani yanayi ne da ya kamata ya keɓe kansa shi yasa bai iya tsayawa yayi maka bayani ba,to amma tunda wakilan sa suna nan na kuma su ai nahin waɗan da abin ya faru akansu to ai ina ganin za a iya sanar da kai komai!'ya rufe bakin sa yana mai duban inda Abdallah yake kwance idanunshi a lumshe dan bazaka taɓa iya fahimtar halin da yake ciki ba,Dady jafar ne ya karbi zancen dan yana ganin waɗan nan ahlin yanzu dole ayi musu uzuri dan suna cikin halin da a yanzu bazasu iya wata doguwar magana ba,har sai lokacin da zuciyar su ta fara mantawa da gagarumar ƙaddarar data keto cikin rayuwar su,babu wanda ya motsa ko yayi wani ƙwaƙwƙwaran tari,har sai da Dady jafar ya dire ƙarshen labarinsa da yake bawa Alhaji munir na abinda gudan jinin sa Nafisa ta aikata,sai gashi shima yabi layin kurame,dan tunda ya ɗora tafukan hannun sa akan fuskarsa,bai ce komai ba har na tsawon wasu mintuna,sai daga can ne kuma ya saki ajiyar zuciya tare da cewa,kuyi haƙuri dan Allah kuyi Allah ya huci zuciyarku,bansan da irin bakin da zan rarrashi zuciyarku ba,haƙika Nafisa tayi min ƙarshen tozarci a rayuwata,ta kuma aikata mummunan kuskuren da bazai taba kankaruwa ba!'yana maganar yana share hawayen da ya kasa hana su zubowa,miƙewa yayi ya bawa su Alhaji Hashir hannu kana ya nufi hanyar waje yana cewa Umar kayi haƙuri ka'ida dukkan iyalanka,amma bance sai ka yafewa Nafisa ba,kabbarta taje ta koyi darasin rayuwa,kuma karki sake ki nufo gida na,ki haƙura dake har abada!'wani irin kukan ihu Anty Nafisa ta saka tana magiya wa Mahaifinta da ya yafe mata ya bawa Umar hakuri,amma ina tuni shi yayi ficewar sa,yana ƙara goge ƙwallar idanunsa,Abba Umar ne yace"Abdallah ya kira Safwan ya tafi da Nafisa dan barinta ba tare da ankoya mata darasi ba hadarine, Abdallah kuwa kamar jiran umarni yake haka ya kira Samuyal,yace"yazo cikin falon,yana shigowa ya zo gaban Abdallah ya duƙa kansa a ƙasa yace"Oga kafin inyi abinda ka umarceni inaso na fara karɓar kalmar shahada a bakinka,domin naje nayi bincike akan addinin Musulunci na kuma gamsu cewa shine addinin gaskiya,dan haka ina so ka musuluntar dani!'gaba ɗaya falon ya ɗauki kabbara, Abdallah kuwa bazan iya ce muku ga halin farin cikin da ya shiga ba,ba tare da wani jinkiri ba,ya bawa Samuyal kalmar shahada,yana faɗa har saida ya maimaita sau uku,kana aka kuma yin wata kabbarar, Abdallah yace"wane suna kake so?kai tsaye yace"Abubakar!'dady ya miƙa masa hannu cikin murmushin farin ciki,yace"Alhamdulillah masha Allah, Ubangiji ya sa musulunci da musulmai su amfane ka,ya kuma baka ikon kiyaye DOKAR sa!'da Amin suka amsa kana Abdallah ya bashi umarnin ya tafi da Nafisa har sai ya nemeta.

Wannan abun da yafaru na karɓar kalmar shahadar Samuyal shi ne ya sanyaya musu zuciya har aka samu damar tattauna abinda ya faru,sai dai har yanzu babu wanda ya kula Hajjah hatta da ƴaƴan ta sunƙi duban inda take, addu'oi masu yawa aka gabatar kana kowa ya fara watsewa jiki a sanyaye,Dady jafar ne ya ciro madaukar da yasaka ya bawa Dady Mansur saboda waɗan da basa nan,domin wannan zaman yana da muhimmanci ace duk wani ahlin ALHAJI BALARABE ya san abinda ya faru acikin ESTATE ɗin sa,

Hajjah kam ta zama tamkar wata mujiya dan kaf ƴaƴan ta waɗan da suka sami halartar taron basu koma ɓangaren ta ba kowacce sai ta wuce gidan mijinta,domin a halin yanzu basa jin zasu iya fuskantar mahaifiyar tasu,duk da cewa itama Nana ƙarama da mijinta a cikin maha intan,to amma dai tanajin gwarashi tunda har ya samu yafiyar wanda suka zalunta,Abba Umar kuwa matarshi ya janye suka nufi sashen sa,Dady Abubakar ma Ammi yabi, dukkanin su suna maijin sabon farin ciki tamkar a lokacin suka mallaki junan su,inno dai itace ta wuce dasu Hajjo bangaren ta,ita kuma Hajiya Babba sai ta janye Bintu saboda dalilinta na cewa sai sunyiwa BINTU auren gata,dan haka da ga yau tabar zaman ɗakin Abdallah,Dady jafar kuwa kai tsaye yacewa da Abigirl ta san inda dare yayi mata dama shi yanzu basu da wani haɗi da ita,ya daiyi mata taimako daya ya bata kuɗin mota ta tafi garin su.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 61 ```


Alhaji Baba kuwa tunda ya shige ɗakinsa ya saka fuskarsa gabas ya shiga miƙa lamuaransa ga Allah,bayaso yayi wani abu da zaisa ace ya zama daga cikin mutane marasa tawakkali da yarda da ƙaddararsu, wannan dalilin ne yasa ya tsaya tsayin daka domin nemarwa kansa nutsuwa,tabbas yasan ko bai fada ba an san cewa dole ya koka da irin wannan lamari da ya samu ahlinsa, amma kuma yanzu dole ne ya zama mai godiya ga ubangiji domin kuwa yanzu ba dabarar sa ce tasa ya warware masa matsalolin ba,yana ji cewa yanzu lokacine da ya kamata ya ƙarfafa zuciyarsa ya janyo farinciki dan farincikin iyalansa,dan kuwa yasan kasancewar sa cikin walwala shine zai basu damar mantawa da mummunar ƙaddarar da ta same su,tun da su sukayi hakuri ai yana ganin shi ba komai bane,ganin cewa su ne jigon waɗan da akayiwa laifin tare da cuta mafi muni, wannan tunanin da yayine yasa shi sakin wani ɗan murmushi tare da faɗin Alhamdulillah aka kulli halin, Allah ya karemu daga sharrin zuciya ya mana tsari da shaiɗan,ya kuma bamu farinciki mai ɗaurewa ya kuma kawar da duk wani abu da zai ƙara cutar da rayuwar iyalina!'Alhaji Baba yayi ƙoƙari sosai gurin cire abinda Hajiya Babba tayi masa a ransa tare da kitsa irin hukuncin da ya kamaceta,Habibu kuwa bashi yayiwa laifi ba Allah yayiwa laifi mai girma, laifinda ya faɗa cewa ba yayiwa bawansa a fuwa akan waɗan nan abubuwa, laifin wani akan wani laifin shirka,to shi kuma Habibu duk ya aikata waɗan nan laifukan,ba zaice yaji daɗi ba dan Habibu ya kasance ba ɗan shi ba,saboda ya riga ya sawa ranshi Habibu ɗan sa ne dan haka yanzun ma bata sauya ba,sai dai yabishi da addu'ar fatan shiriya da neman sassauci gurin Ubangiji.


Tsakanin Dady Abubakar da Abba Umar ban san wanda yafi wani dokin amarcewa ba,dan kuwa tunda suka kule a ɓangaren su babu wanda ya kuma jin ɗuriyar su,suna can suna sabunta soyayyar su,Nafisa kuwa ba zan iya misalta halin da ta shiga ba,saboda rashin tsuntsu da tarko,kuma gata a kulle cikin gurin da ko tafukan hannayen ta bata iya gani,gurin da bata taɓa tunanin zata zoshiba,(to dama Nafisa ai ƙarshen mugun abu kenan, Allah dai ya tsare mu daga masu irin halin ku)

ESTATE ɗin tayi shuru tsawon kwana biyu,kafin kuma su koma da walwalar su, Abba umar tuni ya maida su Hajjo gidan da ya kaisu kasancewar gidan babban gidane,sai ya miƙa wa Fafi takardun gidan yace"ya bar masa ya cigaba da zama da iyalan sa,ƴan biyu kuwa tunda suka ƙyalla idanu suka ga ƴar uwar su Bintu shike nan suka samu nayi duk da cewa sun girmewa Bintun,Hassan ya zama macen dole a cikin su,sunƙi barin estate ɗin gaba ɗaya sun tare anan sunce sai angama bikin Bintu zasu koma gida,fafi dai yana can shima shida ma'unsa ana sabunta soyayya.


Yayin da duk ake wannan budurin Abdallah yana can yana fama da soyayyar da a yanzu yake kokarin gasgata ta,ya rasa dalilin da yasa a ka hana Bintu dawowa sashen sa,shi kuma tsabar miskilanci ya kasa tambayar ko Ummi Laila ce,wadda a kwana biyun kusan kullum yana bangarenta,haka yake sunturin zuwa wajen Alhaji Baba ko da zaiyi masa maganar Bintu amma shuru kake ji,sai yayi tunanin ko dai baisan abinda yake faruwa bane?tun yana daurewa zuciyar sa har ya fara bin iyayen nasa maza amma,duk yawan zaman da zasuyi tare baya jin maganar Bintu abakin su,to wai me ake nufi da wannan abun ne?sai kuma ya shiga fargaba kar dai ko Dady jafar ya faɗa musu abinda yace"akan cewa da yayi idan komai ya daidaita zai saketa ta auri wanda takeso,tunawa da hakan yasa yaji zuciyar sa na bugawa da ƙarfi,kamar zata faso ƙirjinsa ta fito.

Ita kuwa Bintu tana can Hajiya Babba da Ammi da inno kai harma Hajjo da bata gidan suna faman yi mata gyaran da bata samu ba,gyaran gata wanda suke san zautar da jikan nasu a ɓangaren fadamar Bintu,tana yawan tunawa dashi tana kuma mararin ganin sa,sai dai kuma yadda su Inno suka kasa suka tsare yasa bata da hanyar ganin sa ko da daga nesa ne.


Yau kimanin kwana biyar kenan da warwarewar ƙullin dake cikin gidan Alhaji Baba,hankula sun fara kwantawa farinciki ya fara wanzuwa a zukata,yayin da wasu suke cikin halin tsaka mai wuya,kamar dai su Hajja ke nan,wadda tunda abun ya faru babu wanda ta kuma gani a ɓangaren ta,tun daga kan ƴaƴan ta har zuwa ƴaƴan kishiyoyinta da surukanta,dan kuwa Alhaji Baba yayi jan kunne mai tsauri akan kowa dake cikin estate din,duk wanda yaji koda labarin ya kalli hanyar ɓangaren Hajja to bai yafe masa ba, wannan shine hukuncin da ya fara zartarwa akanta,a halin yanzu kuwa kaf ahlin ALHAJI BALARABE babu wanda labarin abinda ya faru bai same shiba,su abdulraman da abdulshakur duk sun dawo cikin ahalinsu farin cikin ganin mahaifinsu da ɗan uwansu shi ya saka su cikin farin cikin da ya hana su alhinin abun alhinin da ya faru,kowa ya dawo da iyalan sa ya kafa sabuwar rayuwar tafarinciki tare da ƴan uwansa,a ɓangaren Taufika kuwa tunda labarin ya sameta ta rude tare da shiga wani irin hali na damuwa, wato dai yanzu ana nufin ace Ya Abdallah ya haramta a gareta,bata jin zata iya wannan jihadin hakan ne yasa ta tattaro daga ziyarar da suka kaiwa mahaifansu suka dawo Abuja cikin ESTATE.

Abdallah ya koma bakinsa,kamar yadda ya saba a baya,ya na cigaba da tafiyar da asibitin sa,amma duk wannan abun da yakeyi ƙarfin hali yake,dan dai kawai Abdallah ya kasance muskilin mutum ne,amma fa haƙika zuciyarshi tana cikin wani yanayi na rashin Bintu, wanda a kwana kin ne ya tan-tance tsakanin ƙarya da gaskiya,ko yanzu dawowar shi daga asibiti kenan,ya shiga shawagi a tsakanin part ɗin iyayen nasu ko Allah zaisa yaci karo da Bintun,sai dai har ya gaji ya yada zango a part ɗin Hajiya Babba wanda ya fi bada tabbacin cewa Bintu tana nan bai ga ko usainar fafi ba bare kuma buntu,yana kwance jikin ƙatuwar kushin ɗin falon idanunshi a lumshe kana ganin sa kasan da akwai gajiya a tare dashi gakuma ƙishin ruwan Bintu da ya addabeshi,Muryar Hajiya Babba ce tasa ya ɗan bude gajiyayyun idanun sa,kai kuma lafiyar ka kazo nan ka kwanta cikin kin kayan aiki?bai kulata ba,sai dai can kasan zuciyarsa yake cewa ina fa lafiya Hajiya Babba kun kama matar mutane kun riƙe,amma a fili sai yayi mata banza dan gaba ɗaya haushin su yake ji,bata nuna ta gane komai a tare dashi ba, tace"ai ya kamata kaje ka kwanta ka huta tunda da alama yanzu ka dawo!'tamkar ba dashi take ba,ko kallon inda take baiyi ba, sai ɗan gyara kashingiɗar shi da yayi,hakan da yayi ne yasa ta gane bai da niyar tashi,ƙwafa tayi tana cewa dani kake zan can!'ta tafi tana ƴan miticinta,bata san kunnen Abdallah da ji ba, har da su cewa ita sam bazata yadda da zaman Bintu dashi ba,dan Bintun bazata iya da wannan halin nasa ba,a saman laɓɓan shi yace"da data zauna dani har zuwa yanzu ke kika zauna mata dani?

kamar anjehota haka ta ta fado cikin falon,dawowarta kenan ko hutawa ba tayi ba,tazo ganewa idanunta abinda taji,turus tayi ganin wanda yake hakimce acikin falon,sai kuma take jikinta ya shiga rawa,har ta ma manta abinda ya kawota,itafa bata jin zata iya daina san Ya Abdallah sai dai idan mutuwa tayi,duk lokacin da ta ganshi saitaji tamkar ana ƙara mata wutar sanshi,cikin sanyin jiki ta ƙaraso tsakiyar falon,kana ta nemi guri kusa da inda yake ta zauna,tare da gaida shi cikin kiɗimewar murya,da lafiya ya amsa mata shi ma badan kallon ƙuril ɗin da take binsa dashi ba,da bazata san cewa ya amsa ba,sai kawai ta samu kanta da ƙarfin halin fara yi masa jaje akan abinda ya faru da kuma fatan Allah ya tsare gaba.

Buɗe idanun ta tayi a hankali,idanun ta nadan komawa suna lumshewa,ita kam ta rasa wannan abu na magani da meyene,gaba ɗaya nema suke su zamar da ita ƴar ƙwaya daga sun banka mata wancan sai wan Nan,wai duk maganin sanyi ake bata,a fadarsu dai,gashi wasu da yawa idan ta sha sai sun sata bacci kamar dai yanzu da wannan ya sakata baccin yamma,saida ta ɗan huta kana ta miƙe har zata shige toilet,sai kuma taji jikinta ya dauki wani sanyi,haka zuciyarta ta shiga bugawa da sauri da sauri,fasa shiga tayi ta juya akalarta zuwa ƙofar da zata maida ita falon Hajiya Babba,a hankali ta buɗe tare da cusa kanta,sai dai kuma tozalin da tayi da Taufiƙa durƙushe gaban Abdallah shi ya nemi hautsina tunaninta,da sauti ta ƙarasa fitowa,sai a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login