Showing 33001 words to 36000 words out of 184937 words

Chapter 12 - KUDURAR ALLAH COMPLETE BY FATIMA Y ADAM

21 Jul 2024

16865

gaidasu,haka Rahima itama tayi, Dady ane ne ciki yanayinsa na zafi da rashin sakin fuska, yace"ke Rahima ina kuma kika samo wannan kalar zabiyar? cikin yanayin tsoron sa da ya sabar musu Rahima tace" inno aka kawowa ita dan ta dinga taimaka mata kuma tana dafawa ya Abdallah Abinci da gyara masa sashe!'tana direwa Dady ane yasaki wata banzar dariya me ƙurar da zuciya, yana cewa ayyo haka zaki ce ƴar aikin inno ce kawai amma ba sai kinyi wani dogon bayani ba!' Hajjo ta ɗan gyara kashin giɗarta kana cikin girma da nuna isa tace" wai Mansur meyasa baka girma? wannan wane irin zance ne shi ɗan Adam ai ba abin tozartawa bane kadinga kiyaye harshen ka idan ba haka ba wataran zakayi da nasani!' dawo da hankalinta tayi kansu Bintu cikin sakin fuska tace" yarinya meye sunanki? Bintu ta amsa da cewa sunana Fatima zahra amma anfi kirana da Bintu!'Hajjah tace masha Allah Bintu suna mai daraja!'gani kawai Dady ane ya tashi fice A fusace,inno ta girgiza kai tana binsa da addu'ar shiriya,Rahima tace Hajjah bari mu kewaya sashen Hajiya Babba!'Hajjah tace"to madalla amma ku kujirani kaɗan ina zuwa,tana barin falon sai ga Yaya sagir ɗan gidan Alhaji mansur kasance war dashi da Nabil ɗan gidan Anty Asiya da take kaduna A wajen Hajjah suke, turus yayi ganin su Rahima zaune, A hankali ya ƙara so cikin falon yana da ɗa ƙure Bintu da kallo, zama yayi kana suka gaida sa,Bintu duk tabi ta takura da kallon ƙuril ɗin da yake Binta dashi, cikin ikon Allah sai ga Hajjah ta fito tana cewa na barku ku kadai ko? ko da ike ma ga Aku nan Sarkin zance zata ɗebe miki kewa!' tana mai nuni da Rahima datake ta zunɓura baki dan tasan da ita take,Ya Nabil yayi zaraf ya amshi zancen da cewa,aiko Hajjah kamar kin sani tana nan ta dami friter da shegen surutu!'gaba ɗaya suka dubeshi Rahimace tayi saurin tambayar sa wace kuma haka!'ɗage gida ɗaya yayi kana yace gatanan Bintu ko ke baki taɓa ganin kamar su ba?Rahima ta ƙyalƙyale da dariya tana cewa Wallahi kuwa Ya Sagir so saima sai dai Bintu har tafi friter kyau!' yauwa ƙanwas ashe kin gane!' Hajjah tace karɓi nan kinji faɗima idan kika biye waɗan nan bazaki taɓuka ko mai ba zani ce ta tadda mujemu!'gaba ɗaya dariya sukayi har Bintun, karbar ledar tayi tana yi mata godiya, Hajjah tace" karki damu duk wanda ya shigo Ahlinmu yazama namu Allah yayi muku Albarka!'gaba ɗaya suka amsa kana sukayi mata sallama, har Sagir ya yunƙura zai bisu Hajjah ta dakatar dashi da cewa ina kuma zaka bayan kasan neman ka nake!' dole ba dan ransa yaso ba ya koma ya zauna.

Cikin kulawa Rahima ta dubi Bintu tace"gaskiya Fatima na fahimci kina son sunan ki!' ɗan kallonta Bintu tayi, kana tace"saboda me kika ce haka? Rahima tace kawai dai nayi la'akarine da yadda idan an tambayeki sunanki kikan faɗi duk wanda yazo bakinki, Amma mu meyasa baki gaya mana ana kiranki da Bintu ba? Bintu ta saki ƙawataccen murmushin ta wanda har sai da gefan kuncinta duka suka loɓa,kana cikin sautin muryar ta me daɗi tace" kai Anty Rahima to bagashi yanzu kin saniba,kuma kin riga kin bawa kanki amsa,dan haƙiƙa inason sunayena duka ko Batula kika kirani dashi zan amsa!' ta ƙarasa maganar fuskar ta ɗauke da ƙayataccen murmushi,Rahima ma dariya tayi tare da cewa to Ai hikenan nima duk wanda yazo bakina dashi zan kira ki!'da wannan hirar suka ƙarasa sashen Hajiya Babba.


Lokacin da suka shiga kimtsetstsen falon Hajiya Babba wanda yake cike da wani mayan ƙamshi mai sanyaya zuciya, samun ta sukai zaune akan sallaya da hijabinta fari ƙal sai casbaha dake hannunta tana ja, har gabanta suka je suka durƙusa suka gaida ta, Rahima cike da soyayyar kakar tata ta raɓa jikinta ta kwanta,cikin nutsuwa Hajiya Babba tasa hannu ta jawo Bintu jikinta tana cewa' ke kam Rahima anyi babbar kobo yanzu ai bakece autar jika ba,faɗima ce!


Bintu tayi luf jikin Hajiya Babba, yayin da wata irin ƙauna me haɗe da kewa ta lulluɓe zuciyar ta tanajin kamar ta dauwama tare da wannan mata mai tsananin kyau kamala kirki da nagarta, muryar Rahima ce ta katse mata tunani da cewa kai Hajiya Babba dama nasan haka zaki min shi yasa tunda kike cewa na kawo miki Bintu naƙi kawota nasan fada zata ƙwacen A gurinki!'Hajiya Babba tayi ɗan murmushi irin nasu na manya tana ta ɗan shafa kan Bintu, yarinyar ta shiga ranta sosai tanajin shauƙin ƙaunarta tamkar su Raihana.

Sun daɗe A sashen Hajiya Babba, Bintu ta sake sosai da ita saboda yadda Hajiya ta sakar mata fuska ta nuna mata ƙauna ta zahiri da ba ɗini, haka da zasu tafi Hajiya ta Haɗa mata kayan amfani sosai kana sukayi sallama, Hajiya taji kewar yaran sosai.


Kewayawa sukeyi cikin Babban ESTATE ɗin, Raihana tana nuna mata kowane ɓangare da kuma me shi, sunzo dai dai ta wajen hanyar da zaka miƙa ka koma ta cikin wannan ɗakin, Bintu ta da kata, yayin da ta zubawa hanyar ido tana tuno abinda ya faru ranar tamkar A lokacin yake faruwa,sai da Raihana ta taɓata kana ta dawo haiyacinta tare da cewa Raihana gurin nan ya burgeni muje ta wajen mu zaga, naga kamar lambuneee......
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 17 ```


A tsorace Rahima take duban Bintu cikin tabbatar mata da abinda zata faɗa, tace" ke Bintu ki rufa mana Asiri kin san kuwa babu wanda yake iya bi ta wajan nan!' Bintu cikin tsananin mamaki tace" to saboda me? kuma waye ya hana zuwa gurin?Raihana tace" babu wanda ya hana, hasalima ba A taɓa yiwa kowa gargaɗi da zuwa wajen ba, nima haka nataso nagani ba wanda yake iya zuwa, sai dai ban taɓa tunanin yin tawajen ba kuma bantaɓa ganin wani yaje ba ko zancen babu wanda ya taɓa yi balle musan dalili!' tunda ta fara magana Bintu take kallon bakinta cike da maɗaukakin mamaki da tarin al'ajabi,to ya akayi ita taje wurin harma take tunanin ƙara kusan tar wurin? wai meyake faruwa A cikin gidan nan? dole ta saka ido akan ɗakin nan dan ita ɗin cikakkiyar shaida ce A kan rashin gaskiyar dake tattare A cikin ɗakin,dole tasan waye mai shi da yadda akayi aka samar da shi,

Rahima ce ta dubeta cikin nutsuwa tace"yaya dai koda matsalane? Amma idan kinji kina san zuwa zaki iya zuwa amma Ni dai bazanje ba, da sauri Bintu tace a'a nima bazani ba muje kawai.


Cikin takunsa na ƙasaita yake tun karar ƙofar da zata sadashi da office ɗin sa wayar sa dake ringin ya ɗora A kunnen sa kana ya fara magana cikin ingantacciyar muryar sa me daɗin saurare, yanzu zan shiga office ɗin inaso katuran dukkan bayanan ta cikin e-mail ɗina zan duba!' abinda yace kenan ya katse kiran, A dai-dai lokacin kuma ya ƙara so office ɗin da sauri sakatariyar sa ta tashi ta buɗe masa ƙofar tare da cewa good morning sir!' kamar dai kullum bai saurareta ba yay shigewarsa,binsa tayi da ido kana tayi ƙwafa tare da cewa kai Dr Abdallah matarka ta shiga uku da nunƙufurci,( niko nace ke kibar irin su Abdallah idan suka tashi basu iya soyayya ba)


Bayan ya ɗan yi wasu muhimman abubuwa sai kuma ya janyo laptop ɗinsa ya shiga duba baya nan da Aka turo masa,lumshe idanunsa yayi A yayinda ya gama duba duk bayanan da aka turo masa akan binciken Bintu.


Yarinyar nan kenan duk labarinta da ta bayar na ƙaryane? to me hakan yake nufi?gashi dai an binciko masa komai akanta sai dai Abu ɗaya ne basu samu ba, shine A salin inda suka fara zama,wato daga inda suka tawo,A yadda samu bayanan ance ba asan inda fafinta yayi ba kawai anwayi garine anga baya nan, daga nan ita ma Bintun ko kwana ɗaya bata ƙaraba ta gudu daga garin, hatta da gidan da suka zauna sai da aka ɗauka aka turo masa.


Jinjina kansa yayi cikin takaicin da ya tokare masa maƙoshi yace"dolene nasan koke wacece!' ƙofar office ɗin aka turo tare da yin sallama, A hankali ya buɗe idanunsa dake alumshe har sun canja kala saboda ɓacin rai,Dady jafar ne ya shigo yayin da yake ƙoƙarin zama yace"Abdallah banaso kasaka damuwa mai yawa A cikin ranka har yayi maka sanadin wata cutar,ka riga da kasani koda ba Ahlinka bane bincike yazaman maka dole tunda aikin kane, kariga da kasan cewa aikin likitacin nan kaje kayi shine musamman dan ɓatar da hankalin mutane akan ainihin aikin ka amma kuma kaga hakan yazame maka aikin lada ta ɓangarori biyu, ga ladan nemo lafiya ga na nemo gaskiya,dan haka Abdallah ina baka shawara kasaki jikinka da mutane gidan nan musamu abinda muke nema, ko ita wannan yarinyar Bintu kamata yayi ka ɗan sake mata ko yayane dan hakan shine zai bamu damar sanin abinda yake tare da ita!'

Ɗan furzar da iska yayi daga bakinsa kana yace" Dady bazan iyaba mukin dake cikin zuciya ta bazai bari ba ina jin ƙuna da gaske bazan iya sakar musu jiki ba Dady,ita kanta yarinyar mamakinta ƙara cushe min tunani yake!'Dady jafar ya dafa hannunsa kana yace"Abdallah karkayi saurin zargi dan bashi da kyau kafini sanin hakan,Ni inaji kawai kamar da abinda ya kawota gidan na daban bawai Abinda kake zargi ba,amma dai bincike shi zai nuna mana komai,bari na koma office ni!'Abdallah yace" nima fita zanyi Ni da Yahya akwai aikin da zamuje!'ok to ba damuwa sai mu fita tare kawai,


Gaba ɗaya Bintu ta saka kanta cikin tunanin yadda za ai ta san wace ce dije,zama tayi A gefan gadonta,tana mai cigaba da lalubo mafita, can kuma sai tunanin wannan matar ya faɗo mata, to ita kuma wannan ko wace?gashi tun ranar bata kuma ganin ta ba, kamar an mintsine ta haka ta miƙe da sauri,tana ganin cewa tunani daga zaune bazai yi mata ba gara ta fita ko Allah ya taimaketa taci karo da abinda zai warware mata gaddama,


Kai tsaye ta fita bayan ta sanar da inno zata ɗan zaga ta gaji da zaman guri ɗaya, har inno tana cewa ko duk kewar Ƙawarta Rahima ne ya dameta, saboda Rahiman sunje mai duguri ita da amna da Hajjah yayar amna ɗin ta haihu, murmushi kawai tayiwa inno ta fita daga ɗakin da cewa sai na dawo inno!'
tafe take tana saƙa da warwara,cikin ranta harma batasan ta bangaji mutum ba sai dai taji kalmar subhanallah,da sauri ta maida hankalinta kan matar,wani irin farin cikine ya rufeta yayin da ta haɗa ido da matar nan,wanda hakan sai da ya nuna A kan ƙawa tacciyat fuskarta,Dije ma murmushine ɗauke A kan fuskarta,cikin fara'a Bintu ta duƙa har ƙasa ta gaida Dije,cikin farin cikin girmamawar da Bintu tayi mata ta amsa tare da cewa sarkin kuka ina kukan? Bintu tayi ƙasa da kanta tana murmushi, yayin da take tunanin ga mafita Allah ya kawo mata,to' amma ta ina zata fara wannan tambaya ba tare da tayi mata wani mummunan zargi ba, Dije ta katse mata tunani da cewa ƴan mata meye sunanki? wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya Bintu ta sauke saboda jin tambayar da matar tayi mata,A hankali tace" sunana Bintu kuma Ni ƴar aikin inno ce,cike da gamsuwa Dije tace masha Allah duk da tariga tasan komai game da Bintun amma bata nuna mata haka ba, gabas ta duba ta dubi yamma kana cikin ta ka tsantsan dije ta miƙawa Bintun hannu kamar zasu gaisa amma sai Bintu taji ta bar mata wata yar takadda A cikin hannunta lokaci ɗaya Bintu ta fahimci Abinda Dije take nufi wato tana son isar mata da wani saƙo ne shiyasa tayi hakan,juyawa Dije tayi da niyar tafiya,Bintu tayi saurin cewa dan Allah mama meye sunanki? Sunana Dije! yayin da taci gaba da tafiya batare da ko waigeba,


Abin baƙaramin mamaki ya bawa Bintu ba, dama wannan ce Dijen da take ta nema? Ita kam wace irin me Sa'a ce da A duk lokacin da take neman Abu sai taga ashema abin yana kusa da ita ko tana tare dashi, lallai wannan shi ake kira da ƘUDURAR ALLAH.


Tana shiga ɗakinta kai tsaye toilet ta faɗa ta ɗaura alwalar azhar, bayan tayi sallah tayi addu'o'inta tare da ƙara miƙa godiyar ta ga sarki Allah jalla wa'azza mai iko buwayi gagara misali haƙiƙa tayi yaƙinin cewa Addu'ar Umminta da fafi da Baffa Jauro sune suke tasiri A kanta da kuma wadda take cigaba dayi dare da rana batare da ƙosawaba,kuma tayi yaƙinin Allah zai ci gaba da kareta da bata nasara A rayuwar ta har ta kai ga cin nasara A kan kyakkyawar manufarta,daga nan kiching ta nufa ta kama aikin shiryawa oganta Abdallah Abincinsa tanayi tana tasbihi, zuciyar ta na ƙara samun ƙarfi da nutsuwa.


A can ɓangaren Hajiya ladidi kuwa ta hana Aunty nafisa yawan zirga zirga A ɓangaren inno, duk dan kar A gano tsakaninta da Bintu dan A cewar Hajiya ladidi yawan tsanar da tayiwa Bintu ma zata iya sawa A saka musu ido tunda bata iya ɓoye tsanarta wa Bintu ba,yayin da kuma take jin daɗin yadda Bintu ta karbi aikin hankali kwance batare da ta ƙara nuna musu rashin amincewa ba yake matuƙar yi mata daɗi, har tana ganin kamar dan Bintun taje taga daula ne yasa ta canja ra'ayin ta,tana ganin indai hasashenta ya zama gaskiya to lallai nan gaba idan aikin Bintu yanayin kyau batare da wani kuskureba zata iya jawo ta cikin tafiyar, saboda ta fahimci yarinyar tana da matuƙar baiwa ta basira da kaifin tunani.



Tunda suka shigo farfajiyar gidan idanunsa suke kan hanyar ɗakin nan, in dai kuma idanunsa ba gizo sukayi masa ba sai yaga kamar giftawar inuwar mutum ta can bayan ɗakin, har Yahya ya buɗe masa ƙofa bai sani ba saida yahyan yace" sir Bismillah! kana ya zuro dogayan ƙafafuwan sa da suke sunƙe cikin wani arnan takalmi sau ciki sai sheƙi yakeyi,taku yake me cike da zallar ƙasaita kai kayi zatan sarkine, ko mai na Abdallah abin burgewane da ƙayatarwa,dai dai hanyar da zai ɓullah ya shiga ɓangaren inno sai ga Dady ane,(Alhaji mansur)kamar an jefoshi,ɗan kaucewa Abdallah yayi tare da cewa Barka da yamma Dady!' washe baki yayi tare da cewa Abdallah ne?ya naganka yau ka dawo da wuri? Abdallah bai samu damar bashi amsaba sai ga Dady nan ya ƙara so(Alhaji Habib)da murmushi A kan fuskarsa,yace"yana ganku anan ba shiga zakuyi bane?gaba ɗaya suka shiga falon inno bakunansu ɗauke da sallama,
Inno suna zaune ita da Bintu harda ma Hauwa'u,ta amsa tana cewa sannunku kamar duk tare kuke!' Alhaji Habib yace"A'a inno duk Haɗuwar ƙoface yana maganar yana zama,ga mamakin Bintu da inno kai Harma Hauwa'u da tunda ya shigo ta daina gane na kusa da ita,zama yayi shima yana gaida inno da sannu da gida, Abinda suka sanine haka kawai bai cika zaman falon inno ba idan ya shigo ƙarƙarinsa ya gaidata ya wuce part ɗinsa,mamakin bai gama sakin su ba saida yasa tsadaddiyar muryarsa yace" ke ki kaimin wannan falona!' yadda yayi maganar bazaka taɓa fahimtar da wa yake ba ko kuma kayi tsammanin idanunsa abuɗe suke, saboda kansa jingine yake A jikin kujerar yayin da idanunsa suke A lumshe tamkar mai bacci,Hauwa'u ce tayi saurin tashi taƙarasa har inda yake, tasa hannu zata ɗauki jakar laptop ɗin kenan yace" bake nasa ba! cak Hauwa'u ta da kata yayin da wani irin haushi da takaici ya turnuƙeta,haka ta koma mazaunin ta jiki a saluɓe,

Bintu kuwa tun sanda yace da Hauwa'u bake nasa ba, jikinta ya shiga baburashin dan ita kwata kwata bata san abinda zai kusanta ta dashi, dan ita kaɗai tasan irin bugun da zuciyar ta keyi da yadda take rikicewa duk saboda tsoronsa,A hankali ta miƙe kamar an zare mata lakar jikinta,zuwa tayi ta duƙa ta ɗauki jakar yayinda zuciyar ta kamar zata yi tsalle ta faso ƙirjinta,sai da ta raba kanta daga kusa dashi kana taji komai nata ya dawo daidai.

Duk wannan diramar da sukayi hankalin Dady ane yana kansu, yayin da Alhaji Habib suke ɗan tattaunawa da inno,inno ta dawo da hankalin ta kan Abdallah yayin da take ce' masa yaya dai Abdallah naga ka dawo da wuri ince dai lafiya?ɗan motsawa yayi kana yace" inno ai yanzu zan dinga dawowa da wuri saboda na ɗauki hutun Asibiti yanzu ina ɗan wani aikine dan haka wataran ma babu inda zani zama zanyi muyi hirar soyayya!'yana gama faɗa inno ta ɗauka da wata shewa irin ta dattijan da sukaji daɗin wata magana, tace"haba ɗannan kamar bansan halinka ba,kaine zaka zauna nan kayi hira sai dai kaita lum-lumshe idanuwa kana taɓa waya!'murmushi kawai yayi batare da ya kuma tankawaba dan wannan ma da yayi ba ƙaramin ƙoƙari yayi ba, muryar Dady ane ya tsinkaya yana tambayar sa wane aikine kuma zakayi shi a gida dan fi'ili? Alhaji Habib ya tari numfashinsa da cewa haba yaya bai kamata ba dan yace yana da aiki sai kaji ko wane irine? Afusace ya miƙe ya na nuna shi da yatsa yace" mansur ka dai nayi min katsalandan A cikin lamurana, ban isa na tambaye shi bane ko yaya?kana ƙoƙarin fa kadinga ganin ka zubda min da girma a gaban yara amma babu damuwa!' yayi ƙwafa tare da ficewa daga falon,inno ta dubi Alhaji Habib tace dan Allah Habibu ka daina shiga dabgarsa kasan dai ɗan uwan kane yadda Allah yayi mutum babu yadda za ayi wani yace zai canja shi!'numfasawa yayi kana yace" wallahi inno idan nayi kamar zan dinga ƙyale yaya mansur da halinsa sai naji sam bazan iyaba saboda yana zubarwa da kansa ƙima a idon mutane ba daga nan gida ba har can waje!'tace"to addu'a zamuci gaba dayi masa Allah Ubangiji ya shirya mana shi da dukkan zuri'a baki ɗaya!'da Amin ya amsa kana ya miƙe yace inno bari na shiga wajen Alhaji Baba!'to madalla afito lafiya, yace" Amin gami da fita daga falon.


Yana zaune har suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login