Showing 120001 words to 123000 words out of 184937 words
iskancin ba,fitowar sa ce tasa ta yin shiru tare da hayewa saman gadon batare da ta saka rigar ba,rufe kanta tayi gaba ɗaya da tattausan blanket ɗin sa,bai kalleta ba yayi abinda ke gaban shi cikin nutsuwa ya gama shirin sa,fita yayi daga ɗakin,jin fitar tasa ne yasa ta tashi cikin sauri ta zura rigar tare da sake komawa ta rufe kanta ruf,dama sun tsaya a hanya sunci abinci dan haka bata da yunwa,tana jin lokacin da ya dawo, batayi wani motsi da zai nuna masa cewa idanunta biyu ba,amma shi yasan ba bacci tayi ba,a zuciyar sa yace"yanzu zanyi maganin ki,allurar tetonous ya haɗa asirinji kana ya dauko tofinta da malam ya bayar da magungunan da zai zuba aciki ya nufo kan gadon batare da ta san abin da yake yi ba,dan har bacci ya fara ƙoƙarin ɗauke ta,ji tayi kawai ya yaye,bargon yana cewa taso kisha magungunan ki!'a hankali ta buɗe idonta tana kallon hannun sa,sai a san nan ta gane maganin da yake nufi,shi yasa batayi musu ba ta tashi zaune tana ta faman jan bargon jikinta dan kar ya ganan mata jiki,haka kuma ta kasa kallon fuskar sa, shi ko gogan naku ko ajikin sa sai ma haɗa fuska da ya kuma yi,yana haɗa mata magungunan da zata sha,miƙa mata yayi tare da cewa tayi Bismillah tasha ta kuma shafa ajikin ta.
Sai da ta gama shan tofin, har tana ƙoƙarin komawa ta kwanta,ya dakatar da ita,ɗan tsayawa tayi ba tare da ta dubi inda yake ba,shi kuma hakan ne ya bashi damar soka mata allurar batare da ta ankara ba,runtse idanunta tayi saboda jin shigar allurar cikin fatar ta,hannunta ta ɗora kan nasa hawaye wani na korar wani,sai da yagama ya leƙa fuskar ta,yaga yadda ta caɓe da ruwan hawaye,yace"yarinyar nan yaushe zaki daina kukan allura ne?tura ɗan mitsitsin bakinta tayi tana gunguni,kafin ta maida shi taji wani sabon Al'amarin daga ɗan gidan ABUBAKAR jikan BALARABE,kuma yayanta garkuwar ta mijinta Abdallah,sarrafa harshenta ya shiga yi cikin bakin sa da wani irin salo mai matukar tsayawa a rai da zuciya,yadda yake tsotsar bakinta har abin saida yaso fin ƙarfin tunanin ta,kokowa take dashi dan ta ƙwaci kanta,amma da abin yafi ƙarfin ta tuni ta miƙa wuya ga jikan BALARABE,har da saƙala hannunta ta ratayo wuyan sa,saiga Bintu da cafke ɗan madaidaicin laɓɓan Abdallah tana masa wata iriyar siɗa da ita kanta bata san ya akayi ta iya ba,dan sam bata cikin hankalinta,wani irin sweet bakin nasa yake mata kamar wadda aka lasawa zuma haka take ji akan harshen ta, Abdallah kuwa shi baya cikin wannan duniyar ma domin halin da yashiga da shauƙin da yake ciki ba Abune da zai iya kwatantawa ba, wannan yanayi da wannan rana ya barwa zuciyar sa da gangar jikin sa sanin halin da yake ciki,sun fi ƙarfin mintuna ashirin cikin wannan zazzafan yanayi me cike da sirrika da kuma tarihi a gare su dan dukkan su baƙi ne a wan nan fagen kuma a wannan ranar ne suka taɓa ɗanɗana garɗin soyayya,duk da su basu san da haka ba, bakuma su san cewa wannan abun da sukayi shine ƙauna ba,sun dai can ja masa suna daga tausayi zuwa shakuwa,e mana shaƙuwa ce tasa suka manta duniyar da suke ciki,(inji Abdallah da Bint ɗin sa fa,ba inji Fatimah ba)ɗaga kan sa yayi yana kallon ƙawatacciyar fuskar ta da take ta ƙyalli da sheƙi bacci take yi sosai tana tsotsar bakinsa da take jinsa tamkar zuma ana ta bakin, A hankali ya zame bakin sa tare da tashi zaune, tsura mata idanu yayi yana tunanin da duk koƙarina ban gano komai ba a wannan karon,yunƙurawa yayi ya tashi,toilet ya faɗa tare da sakar wa kansa shaya sai da yayi wanka daga nan,ya ɗauro alwala ya fito,dadduma ya shimfiɗa ya tada nafila,duk da cewa yaso tashin Bintu amma sai ya ƙyaleta,saboda tofin da zaiyi mata tana cikin bacci,asuba ta gari Abdulbint.
A cikin wannan daren da Abdallah da Bintu suka samu nutsuwar zuciya,a cikin sane wasu kuma suka kasa bacci,kamar dai yanzu da nanu yake ta zagaye cikin ɗakin sa shi ɗaya,fargaba ce taf cikin ransa,da tashin hankali tabbas idan yace baya tsoron yarinyar nan yayiwa kansa ƙarya,dan gashi ga dukkanin alamu tana son ganin bayan shi,shin mai zaiyi a wannan karon dan dakatar da ita daga shirin ta na tunkarar ɗakin nan?yaya zaiyi duk ranar da ta samu nasar bankaɗa ɗakin nan?me yasa ƙarfin gwiwar shi yake sarewa ne?me yasa yake jin faɗuwar gaba duk sanda ya haɗu da yaran nan?shi da yake son su zamar masa garkuwa gurin samun mafarkin sa,to me yasa yake jin tsoron su? tabbas dole ne yayi gagagawa gurin cimma burin sa idan ba haka ba kuwa ko mai zai iya faruwa,cikin tashin hankali yace ABUBAKAR dole ka faɗa min inda mahaifin mu ya binne ajiyar nan,bazan ƙyaleka ba kai da iya Lanka, har sai na ga na samu abinda nake nema,badan ina da tabbacin ba a cikin ESTATE aka binne ba, ai da tuni na kashe kowa na tarwatsa estate din domin bin ciko abin da nake nema.
A ɓangaren Nafisa ma dai kusan haka din ne,tarasa abin kamawa,ta kai mari ta kai gauro,duk wani shirin ta neman kwancewa yake,shin ya akayi ta bari har Umar yake zargin ta?wane irin sakaci tayi haka,da balli yake neman tsinke mata?shar ce hawayen fuskar ta tayi tare da cewa me yasa al'amuran suke ƙoƙarin dagule min?shin basu Babe sun bani tabbacin sun mutu ba,me ya jawo duk wan nan?idan sun mutu ai bai kamata na dinga jin tashin hankali irin haka ba!'wayar ta tayi saurin rarimowa lambar da tayi shekara kusan goma sha takwas rabon ta da ita, ita ta dan nawa kira a yanzu,bata jima tana ringin ba aka daga,cikin matuƙar ƙasa da murya tace"da Babe nake magana?wata irin dariya irin ta cikakkun ƴan daba akayi tare da cewa hajjaju Nafisa gaskiya baki da amana,ko dan kiran nan a gaisa baki taɓa yi mana ba tun bayan da buƙatar ki ta biya,yanzu ma wata buƙatar ce ta taso miki ko?cikin sauri ta dakatar dashi tare da cewa,babe ba wannan ne abinda yasa nakiraka ba,tambayar ka zanyi,shin a wan can ranar baka ce min kun kashe matar nan da ɗiyar taba? tabbas haka na gaya miki amma nima sai kwanakin nan naji yarana suna hirar gaskiyar yadda abin ya faru, ashe nima muna funtata suka yi,a taƙaice dai basu kashe su ba dan ɓace musu sukayi suka rasa su,dan haka gaskiya bani da tabbacin sun mutu ko basu mutu ba,,,wata razanniyar ƙara ta saki tare da sakin wayar ta faɗi ta tar watse,zubewa tayi tana wani irin kuka mai cike da tashin hankali da tunanin makomar,shike nan su baku kashe su ba Ni kun kashe Ni ƙarshe na yazo, tabbas tunda Umar yace"zai nemosu sai ya nemo su in dai suna raye,yanzu ya zanyi?kaicona,me ye amfanin abinda nayi tunda ban samu riba ba,yanzu kam anzo gaɓar da dole sai na gayawa Bintu abinda na aikata, da bakina,domin ta samo min mafitar da zan tsira koda da rayuwata ce,ranar idanun Anty Nafisa basuga bacci ba duk iya satar sa kuwa.
Washe garin safiyar kuwa Umar ko ƙeyar Anty Nafisa bai gani ba,bai kuma neme taba shima, haka ya gama shirin sa na tafiya suleja,ai nahin inda ya mayar da su Hajjon Laila,shi yasa zuwa baya yi masa wuya,tunda ya dawo dasu cikin Abuja, ɓangaren Hajiya Babba ya fara zuwa su kayi sallama kasan cewar ita kaɗai ce tasan inda zashi,daga nan ya wuce sauran sashen suka gaisa, ya ɗan jima a bangaren inno dan kawai yana son ganin su Bintu sai dai ganin lokaci na ja basu fito ba yasa ya haƙura yayi sallama da inno ya ɗauki hanyar suleja, tare da ɗan rakiyar da bai san da yana bin sa ba.
A can ɓangaren Samira kuwa yau ta tashi ne cikin farin cikin babbar nasarar data ke tunkaro su,don kuwa a yau ɗin ne misalin ƙarfe huɗu na yamma zasu haɗu da Alhaji Sama'ila,kuma da alƙawarin zai gaya mata abinda suke nema suke yaki suka hana idon su bacci dare da rana,suka zalinci wasu suka ha inci wasu duk akan sa,yayi alƙawarin saboda yar dar da yayi mata da kuma gudummawar da ta kawo masa,zai gaya mata wannan abun da suke nema,wanda Ni kaina na ƙagu da naji ko menene wannan abun da ake ta zaluntar bayin Allah akansa.
Alhaji Baba ne ya zubawa kyakykyawar fuskar matar sa Hajiya Babba ido cike da son gano wani abu atare da ita, sam ya kasa gane mata kwana biyu kamar tana cikin damuwa,cikin taushin murya yace"meke damun ki ƴar Agadez?ɗan murmushi ta kalato wanda kana ganin sa kasan na yaƙe ne,tace"babu abinda yake damuna, halin rayuwa ne kawai,bai takura ta ba ya rabu da ita,sai ma can ja maganar da yayi da cewa,kin san dalilin kiran danayi miki? girgiza kanta tayi,yace"akan wannan ajiyar da na binne ne kin san dalilin da yasa naƙi gayawa kowa inda take,kuma bayan ke da Abubakar bana tunanin wani yasan da ita,duk saboda gudun fitina,to yanzu lokaci yayi da nake ga zan sanar da sauran ƴaƴana da matana, inda na ajiye wannan d....ɗan shuru yayi ganin kamar yaji motsi a tabayan ɗakin nasa,dan haka yace"Safiya mu bar maganar da sauran lokaci ban yadda da wajen nan ba kamar anyi mana laɓe a ta wajen nan....
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 46 ```
Hajiya Babba tace"shike nan Allah ya baka ikon sanar da zuri'arka wan nan sirrin,tunda kaga dai dani da kai duk ba dauwama zamuyi a duniyar ba,shekaru ja suke yi,shi kuma wanda ya sani bashi ba labarin sa Allah ne kaɗai yasan halin da yake ciki!'ta ƙara sa maganar cikin fashewa da wani irin kuka wanda daga ji kasan ya daɗe yana cin ranta da zuciyar ta,ta kuma jima tana son yin sa,Alhaji Baba shuru yayi yana kallon ta bai katse mata kukan ta ba,dan ji yake inama shine ya samu damar yin wannan kuka da ya ji sauƙin abinda yake cunkushe a zuciyar sa,ɗan jingina yayi da jikin gadon yana fidda wani irin nishi mai fita da tsananin wahala da damuwa,baka jin sautin komai sai kukan Hajiya Babba da takeyin sa cikin wani irin baƙin ciki da tarin damuwa,cikin rawar murya tace"ya Allah ya Ubangiji na roƙeka ka bayyana min farin cikina kafin ƙasa ta rufe idanuna,ina roƙon ka bayyana sirrin dake ɓoye,ka fiddani daga cikin duhun da na shiga,ka kuma kawo farin ciki acikin rayuwar ɗana Umar ka bayyana masa sashin sa farin cikin sa, Allah ka nuna min ranar da zanga farin ciki da walwala a kan fuskar sa wanda yake daga cikin zuciyar sa!'amin Alhaji Baba yake ta cewa yana jin tururin dake kwance cikin zuciyar sa na lafawa,saboda tasirin addu'ar dayake ta nanatawa a duk lokacin da wata damuwa ta taso masa,allahumma la sahlan,itace addu'a mafi sauƙaƙa damuwar zuciya.
Dadyn Sayyid nifa na gaji da gafara sa har yanzu kuma banga ƙaho ba,kullum cewa kakeyi Sayyid zai dawo,amma har yanzu da muke cikin kwana na uku da ɓatan sa,babu wani labari mai daɗi akan sa, gaskiya ka nemo min yarona dan na gaji da wannan daɗin bakin naka!'Dady Mansur ya zaburo cikin masifa yace"au Nine nake miki daɗin bakin?ko kina tunanin kin fini shiga tashin hankalin rasa shi?ke baki san ko mai akan abinda nake tunani ba shi yasa bazaki gane tashin hankalin da nake ciki ba,amma saboda wuyan ki yayi kauri har Ni zaki duba kice ina miki daɗin baki!'ya faɗa yana ƙureta da kallon sa,bata ce masa ko mai ba sai da taje bakin step ɗin da zai kaita ɗakinta,ta juyo kana tace"ai dole hankalin ka yafi nawa tashi tunda kasan baka shuka gaskiya ba, yarona yana can za aɗauki fansar abinda kake yi akan sa,to kasani shi Allah babu ruwan sa, dan da wanda yayi zina da wanda ya tsaya akayi agabansa yana kallo duk ɗaya suke,tunda cewa yayi la taƙrabuzzina kada ku kasanci zina,to kaga kuwa baka da wata mafita laifin duk ɗaya ne kuma hukun ci daya,Ni dai kawai kasa waɗan da suka ɗauke min ɗana su dawo min dashi tunda shi baiji ba bare gani!'tana gama faɗar haka ta haura dakin ta da gudu,dan tasan kaɗan daga aikin Mansur ya faffalla mata maruka,a lallai wuyan ki yayi ƙauri,to zan ɗauki mummunan mataki akanki kuwa,da idan ba tsoro ba ki tsaya mana,da kuwa kin sha mamakin abinda zai biyo bayan waɗan nan mugayen kalaman naki!'fita yayi ran sa amatuƙar ɓace.
A ranar nan ne dai kuma Abdallah yayiwa gidan sirri tsinke wanda tunda aka kai masa Sayyid aka ajiye bai waiwayen shi ba sai yau ɗin,zama yayi agabansa bayan Faisal ya saka masa kujera,kallon Sayyid ɗin yake wanda duk ya fita daga haiyacin sa duk da cewa ba dukan sa ake ba, kuma ba A hana shi ci da sha ba,kawai dai babu maganar wanka sallah dai ko ba yayi dole yayi ta,sai dai babu sakewa kuma ɗakin da aka saka shi aciki babu haske ko kaɗan,waɗan nan abubuwan sune suka sauya Sayyid tamkar ba Sayyid ɗan gayu da wanka ba,zuba masa ido yayi bayan yasa an haska masa wajen da wada taccen haske, Sayyid ɗin shima kallon sa yake cike da mamakin dama shine yasa aka kawo shi gurin nan,ɗan ɗage girar sa yayi kamar yadda ya zame masa jiki,kana yace"kayi mamaki ko? Sayyid yace"me nayi maka kuma da ka rabani da jin daɗi na?sai da Abdallah ya shaƙi ƙamshi,na ɗan wasu sakanni,kana yace"tambayar ka zanyi me by kasamu amsar taka tambayar acikin tambayar da zanyi maka, Sayyid bana so kayi min gaddama,saboda aikina na gaggawa ne,idan kuma har kana son fita daga gurin nan kaje kaci gaba da shaƙar iskar duniya kusa da mahaifin ka to ka gaya min gaskiya karkayi min karya!'kawar da kai Sayyid yayi tare da cewa me kake so ka tambaye ni?in dai na sani zan baka amsa!'ɗan tafa hannu Abdallah yayi tare da cewa yauwa kasamawa kanka lafiya,kana yace"waye yasaka shiga rayuwar Bint?kallon sa yayi da alamar bai gane Bint ɗin da yake nufi ba,gane hakan ne yasa Abdallah cewa Bintu my wife u understand,wani kafurin murmushi Sayyid yayi kana yace"au cewa zakayi bagidajiyar ƴar aikin inn...kafin ya kai ga ƙarasa abin da yake son faɗa Abdallah ya ɗebe shi da wasu mahaukacin marika hagu da dama wanda Sai da duniyar ta tsayawa Sayyid gaba ɗaya, lokaci ɗaya hancinsa ya fara zubda jini,cikin kakkausar murya Abdallah yace"tare da nuna shi da yatsa,kar ka sake ka bari wannan ruɓaɓɓen bakin naka ya kuma furta ƙazaman kalamai akan kyakykyawa mai kyakykyawar aniya kamilalliya mai kamilalliyar zuciyar matata,bana son raini ka mutunta Bintu tamkar yadda zaka mutunta iyayenka,koma fiye da haka,domin na tabbata tafisu kyan zuciya da mutuncin da za a mutunta ta,amsa kawai nake buƙata a gurin ka ba wasu ban zayen kalaman ka ba,ina sauraren ka,kabani amsar abinda na tambaye ka,saboda ina da abinyi!'ya faɗa yana duba tsadadden agogon dake ɗaure A tsintsiyar hannun sa,cikin wahala da nadamar shiga hurumin Abdallah da yayi Sayyid yace"nima ban san ta ba,a flazer muka haɗu da ita ta bani kwangilar sawa Bintu ido da kawo mata rahotanni akanta,amma wallahi ban san ta ba!'kamar ya baka santa ba?baka ga fuskar ta bane ko kuma kaga fuskarta sanin tane bakayi ba?girgiza kai Sayyid yayi cikin fitar da wahalallan numfashi yace"niƙabi ne a fuskarta, da ɓaƙar doguwar riga ban gane ko mai atare da ita ba,ban san komai A kan ta ba!'to meye manufarka ta karɓar tayinta? Abdallah ya tambaye shi cike da takaicin wawancin sa,nima saboda ina da manufa akan Bintun shi yasa na karɓa!'meye manufarka akanta? Abdallah ya kuma jefa masa tambaya,sunkuyar da kansa Sayyid yayi kana cikin rawar murya yace"sonta nake taƙi bani dama saboda tana da matukar kamun kai da nutsuwa,hakan ne yasa ko fuskar da zan yi mata wasan banza ban samu ba shi yasa Ni kuma nake jin haushin ta,kuma shine dalilin da yasa nayi saurin karɓar tayin matar saboda nima na ida manufata akanta,kamar dai ranar da ka ƙwace ta a hannuna!'ya ƙara sa faɗar maganar cikin fargaba,ji yake kamar Abdallah zai iya maimaita masa irin dukan da yayi masa ranar, wani ɗan huci Abdallah ya furzar batare da ya kuma cewa komai ba ya miƙe daga kan kujerar yana ƙoƙarin barin ɗakin,cikin saurin baki Sayyid yace"dan Allah tunda na gaya maka abinda kake so ka fitar dani daga nan gun!'Abdallah yace"da sauran lokaci daga haka ya ficewar sa ba tare da ya saurari surutan da Sayyid ɗin keyi ba.
Tunda ya fita Bintu tana ɗakinta bata leƙa ko ina ba saboda bata jin fita ko ina ga kuma addu'oin da malam ya bata su ta yini tana yi,ko inno tunda suka haɗu da safe bata kuma ganinta ba,sai dai innon tana leƙawa ɗakin Bintu dan tabbatar da lafiyar ta,sai bayan sallar azhar ne ta fito falon dan samun abinda zata sakawa cikin ta,tana fitowa taci karo da bayan matar da take shirin shiga part ɗin Alhaji Baba,ta cikin ƙofar dake falon inno,zubawa bayan matar ido tayi zuciyar ta na bugawa da sauri da sauri wacece wannan da ta shiga ɓangaren Alhaji Baba?wata zuciyar tace mata wacece take da ikon shiga idan ba inno ba,dafe ƙirjinta dake dukan tara-tara tayi,cikin sauri ta nufi ɗakin inno dan ganin ko tana cikin ɗakinta,sai dai abinda ya kuma tada hankalin Bintu sam bata ga inno a cikin ɗakin ta ba,hatta da toilet sai da ta duba amma bata ganta ba,kanta ta dafe,cikin tsinkewar zuciya tace"nashiga uku wacece wannan me irin takun matar nan da yanayin bayan ta, tabbas daga bayan matar nan ƙirar waccen shu'umar matar ta gani,to me hakan yake nufi?ji tayi kamar tabi matar sashen Alhaji Baba, Allah na roƙeka kar ka tabbatar min da abinda idanuwa na suke gani, Allah kar kasa zargi na ya zama gaskiya,haba inno anya kuwa zata iya aikata haka ta faɗa cikin yanayin