Showing 102001 words to 105000 words out of 184937 words
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 40 ```
Shuru officce ɗin ya ɗauka na dan wani lokaci,kana daga bisani Alhaji Rufa'i ya ja doguwar ajiyar zuciya tare da maida duban sa kan Dady jafar,yace" jafar akwai al'amari mai matukar ruɗarwa a cikin rayuwar iyalan mai gida,ɗan gyara zaman sa yayi tare da ƙara fuskantar Abdallah ya cigaba da cewa,tun a shekarun baya na fuskanci yadda al amuran ahlin ALHAJI BALARABE yake sauyawa da wani irin san zuciya da san duniya,kasan cewar Ni ba mazaunin Abuja bane ballantana na sa ido akan wasu miyagun abubawan da suke faruwa cikin ESTATE ɗin,to kuma ina cikin taraddadi da tunanin hanyar da zan ɓullowa al'amarin kawai saiga tayin da su Alhaji Hashir suka kawo min na san in shiga cikin su saboda sun san nima zan taimaka, kuma akwai manyan kadarorin Alhaji Baba A hannuna,ganin wannan ma wata dama ce na samu ta samun zaƙulo abinda ake ta ɓoyan sa da kuma makircin da ake son ƙullawa uban gidana kawai sai na amshi wannan tayin cikin nuna farin ciki,nan kuma aka shiga gwagwarmayar dani da faɗi tashin yadda za a samu wannan ajiyar da kowa yake harinta, A lokacin na samu na tara wujjoji masu yawa akan su Alhaji Hashir,sai dai har kawo rana irin ta yau na kasa gano abin da ake nema,duk iya bincikena da bin diddigina amma hakan ya gagara,kuma abinda na fahimta kamar dai nine kawai acikin su ban san wannan sirrin ba Ni kaɗai suka rufewa wanda nakasa gano dalilin haka, har ma na fara tunanin ko sun harbo jirgina ne nasan tona musu Asiri,sai kuma na lura sam ba haka bane kawai dai har yanzu basu gamsu dani bane,ba yanzu suka shirya sanar dani ba har sai sun gamsu da gaskiyata acikin su,kuma ina zargin Alhaji shamsi yasan ko mai akan abinda suke fafutukar nema, wanda shine baya cikin wannan kungiya tasu hasali ma nuna musu yake baza a haɗa baki dashi aci amanar ALHAJI BALARABE ba, duk da cewa zargina bai tsananta A kansa ba amma ya kamata abi sahunsa dan ina da tabbacin zamu sami wani abu daga ɓangaren sa!'yana tsayawa nan A bayanin sa Dady jafar ya ɗauka da cewa, Alhaji Rufa'i duk wan nan bayanan dakayi mana kamar tuni ne a wajen mu sai ɗan abinda ba A rasa ba,da kuma manufar ka ta shiga cikin su Alhaji Mansur,saboda ba a zaune muke ba kuma in Sha Allah muna gab da tonawa kowa asiri!'miƙewa Abdallah yayi tare da duban Dady jafar,gane abinda yake nufi da yayi ne yasa yace"Abdallah baka ce komai ba kuma kana shirin tafiya,ko baka yadda da gaskiyar Rufa'i ba?ɗan jim Abdallah yayi tare da cewa zan neme shi idan na tabbatar da abinda ya faɗa gaskiya ne!' daga haka ya fita daga officce ɗin ya barsu,Dady jafar yace" da Alhaji Rufa'i kar ka damu nasan zaiyi nazarine akan maganarka,saboda Abdallah mutum ne da bayayin abu cikin gaggawa komai yana yinsa cikin nutsuwa ne shi yasa ba zai saurin baka yarda nan take ba!'Alhaji Rufa'i yace" wannan shine halin manya,kuma hakan Abune mai kyau kayi dacen haihuwa yaron ka yana da ƙwazo da himma da kuma uwa uba san tabbatar da gaskiya, murmushin jin daɗi Dady jafar yayi,batare da yace komai ba,kana yaji daɗi da Alhaji Rufa'i bai san matsayin Abdallah a gurin sa ba,hakan yana masa nuni da cewa har yanzu su Alhaji Hashir basu san waye Abdallah ba,kuma hakan yana nufin sune da nasara akansu Alhaji Nasir ɗin.
Fitowar sa daga officce ɗin kai tsaye mota ya shiga Yahya yajashi zuwa asibiti,duk da yadda ƙwaƙwalwar sa ta ɗauki zafi da wannan al'amari hakan bai hanashi nutsuwa ya duba marasa lafiyar da suke buƙatar sa ba,duk da a can ƙasar zuciyar sa ji yake kamar ya koma gidan awan nan lokacin ko dan duba lafiyar Bintu, sai dai kuma hakan ba mai yuwuwa bane dan da akwai ayyuka da yawa da suke gaban sa,wayar sa ya zaro daga gefan aljihun rigar sa, danna wa yayi tare da ɗora ta akunnen sa,ba ayi minti ɗaya ba aka daga wayar,cikin lafiyayyar Muryar shi yace"sani idan kana cikin Kano ina so kayi min wani aiki A nan!'banji mai akace ta ɗaya ɓangaren ba naji dai Abdallah ya ɗora da bashi bayanai akan Alhaji Rufa'i,ya ɗora da cewa inaso bayanan shigo da da sauri,ok kawai yace"tare da kashe wayar ya turata ma zaunin ta..
Dije kin san dalilin da yasa nace ki dawo ko?ba tare da ta jira amsar Dijen ba ta cigaba da cewa,gagarumin aikine ya taso min wanda dole sai da mataimaki,dan haka ina so ki maida hankali kan abinda zan sanar dake, ban ɗaukoki dan kici amanata ba ɗauko ki nayi dan kiyi min aiki,Dije lallai ina buƙatar ki shiga jikin Bintu ba dan kanki ba sai dan kaina da biyan buƙatata,danƙo kunnen Dijen tayi cikin ƙara yi mata kashedi da gargaɗi tace"wallahi wallahi wallahi Dije in dai na sameki da kuskewa daga kan maganata ko cin amanata to ki tabbatar da cewa ƙarshen rayuwar iyalan ki yazo ke nan,ke kuma sai na ƙarar da rayuwarki ta hanyar gana miki azaba iri iri wadda ita kaɗai ta ishi mai irin halinki na cin amana izina,salon da kika fara dashi nakeso ki ɗora ki barta a yadda tasan ki,sonake ki lulluɓeta da kalaman yaudara ki nuna mata kinatare da ita, ki tayata yaƙin nemo wancan shu umin,ni kuma abinda nake buƙata ke nan daga gareta tunda ita da mijinta suna da baiwar gano mugu to Ni kuma da ita zan jingina dan cimma burina!'babu abinda Dije take sai kuka wanda yake tafe da wani irin baƙin ciki na kasancewar rayuwar ta a haka, tabbas da tana da damar canja ƙaddarar ta ta zuwa aƙasan wannan shu'umar mata,sai dai ina, bakin alƙalami ya riga ya bushe Allah da yayo rayuwarta ahaka shi yasan dalilin haɗa ta da wannan mata,insha Allah sai ta zama sanadin bankaɗuwar asirin wan nan makirar mata,duk duniya babu abinda yafi ƙarfin Ubangiji dan haka bazata karaya da waɗan nan mugayen kalaman nata ba,ta riga tayiwa Bintu alƙawari kuma tayi alƙawari ita da Ubangijin ta saita tona asirinta,koda kuwa shine abu na ƙarshe da zatayi arayuwarta,wata gigitacciyar tsawa ta dakawa Dijen wadda har sai da ta toshe kunnuwanta,tare da runtse idanun ta tana kuma mai fatan Ubangiji ya bata dama da nasara akan wannan azzalumar mata,koma wacece,matar tace"kinaji na kina kumajin alwashina akanki dan haka ki tabbatar da cewa ba asamu matsala cikin wannan aikin ba domin shine kwanciyar hankalin ki da rufuwar asirinki da cigaban rayuwar zuri arki!'ki tashi yanzu ki koma cikin ESTATE ki gayawa uwar ɗakin ki cewa kin dawo daga zaman jinyar da kika tafi,daga karshe ina mai kuma tunasar dake muhimmancin amanata!' cikin sanyin jiki da kuma ƙwarin gwiwar rusa rayuwar ta, Dije ta miƙe tare da kama hanya ta fita daga gurin wanda kullum zasu haɗu sai ta canja gurin haɗuwar tasu kai wannan mata ta iya takunta.
Dide ta dawo cikin ESTATE da kyakykyawar niya,da kuma burin hada hannu da Bintu dan su cimma kyakykyawar manufarsu wadda abaya ta dakatar dasu,zasu ɗora daga inda suka tsaya, saboda yanzu tana da cikakken ikon tarayya da Bintun zasu kashe su binne batare da tasani ba ta yadda ita take yiwa aiki amma ta wani gefan aikin rusa rayuwarta da farin cikin ta zasuyi ita da Bintu,cikin ƙudurar Allah gashi ita da kanta ta bata damar fallasa sirrinta da kuma rusa duk wani shiri da takeyi dan cimma mummunar manufar ta,ita da kanta ta bata lasisin tarayya da Bintu,tabbas lokacin karya alƙadarin waɗan nan azzalumai yayi lokacin banƙaduwar sirrin su yayi,zatayi abinda ya dace dan kuɓutar da bayin Allah da basuji ba basu gani ba,ko dan haka tasan Allah bazai taɓa bawa wannan tsohuwar azzalumar ikon cutar da ita ba,dan haka da ƙwarin gwiwar ta ta koma aikin ta ka in da na'in.
Baƙaramin mamaki Bintu tayi ba lokacin da tajiyo Muryar Dije a falon inno,cikin sauri ta ɗauraye hannun ta datayi kwaɓin alkubus,haka kawai taji tana sha awar yiwa Oga Abdallah alkubus,duk da tasan ba gwanin ta ake masa ba amma tunda yana son waɗan nan nau'ikan abincin wataƙil idan yaga dama yaci batare da ya gwasaleta ba,fita tayi daga kiching ɗin cikin wani irin farin ciki dayakasa ɓoyuwa daga zuciyar ta har saman fuskarta,cikin wata dariyar farinciki ta zube A gaban Dijen tare da kama hannun ta,inno tarike baki yayin da taga itama Dijen fuskarta ta cika da farincikin ganin Bintun,tace"kai Bintu irin wannan farin ciki haka,Dije tayi saurin cewa ai inno Bintu tana da shiga rai saboda biyayyar ta ga manya kinga dai ba wani haduwa muke sosai ba amma mun shaƙu da juna!'inno tace"Dije haka maganarki take kuma kema ɗin Dije ai akwai daɗin zama kin san ance sai hali yazo ɗaya ake kulla abota shi yasa kuka shaƙu da Bintu!'Bintu da bakinta yaƙi rufuwa tace"Allah mama Dije nayi kewarki gashi kuma na rasa wanda zan tambaya ina kike,kullum sai nayi cikiyarki a raina nace Mama Dije balakuro babu sallama!'dariya sukayi gaba ɗaya inno tace"ai bakin kine balakuran!'ɗan tura baki tayi cikin yanayin ta na sakalci tace"Mama Dije mai zan kawo miki?Dije tace"babu komai ai ba yanzu na dawoba na ɗan jima a gidan kinga kuwa ai aƙoshe nake!'inno tasa baki da cewa Dije sai dai idan baƙunta zakiyi mana, ke Bintu je ki kawo mata ko lemo ne ta jiƙa maƙoshinta!'da sauri Bintu ta koma kiching ta haɗowa Dije ƴan kayan taɓa taɓe,tana ajiye mata tace"gaskiya Mama Dije ki dinga zuwa koni na dinga kawo miki ziyara!'inno tace" idan mijinki ya baki umarni ba!'Dije da bata san da batun auren da aka yiwa Bintu ba, ta ɗan zaro ido cike da san ƙarin bayani tace"kai haba yaushe akayiwa Bintu Aure?kunya ce ta kama Bintu dan haka ta gudu kiching dan karasa aikinta tabar inno da yiwa Dije bayanin Auren gaggawar da akayi mata,Dije tayi mamaki sosai da wannan al amari lallai wannan shi ake kira da ƙudurar Allah ƴar aiki da auren ɗan gida amma dai tayi musu fatan Alkhairi tare da kumajin matsuwar keɓewar ta da Bintu,to amma tasan ayanzu dai hakan bazai samu ba tunda dai sun riga su gaisa,sai dai zuwa gobe dan bata son suja lokaci batare da sun tattauna abubuwa masu mahimmanci da ita ba..
Ɗaya bayan ɗaya saida Dady Mansur yabi su ya kare musu tanadi da kuma basu tabbacin in dai basu fito masa da ɗan sa ba zaiyi abinda zai tada hankalin kowa da kowa,mutum ɗaya ya kasa tun kara wanda kuma yasan ko amafarki ba zai taɓa iya tun karar sa da makaman ciyar maganar nan ba haka ya dinga ɓaɓatu shi kaɗai yana harbin iska,
Taufiƙa ce zaune A barandar ɓangaren inno,ta zauna ne a inda duk wanda zai shiga ko ya fita sai ta ganshi kuma ya ganta,tun bayan sallar magriba take zaune agurin,wanda ba kowa take jira ba sai Abdallah,shiga tayi take ce raini da ɗaukar magana wanda take ganin dashi zata karkato da hankalin Abdallah zuwa kanta,tun zaman yana mata daɗi har ya gundure ta,miƙewa tayi ta koma falon tana mai fatan Allah yasa inno bata nan dan dama saboda ita ta fito waje,fatanta ya tabbata dan kuwa babu inno a falon sai Bintu wanda hakan ba ƙaramin daɗi yayiwa Taufiƙa ba,aganinta tasamu hanyar da zata rama bakin cikin da ta daɗe tana ƙunsa mata akan Abdallah, saboda a yanzu dai tayi yaƙinin Abdallah ba zai taɓa kaucewa tarkonta ba,dan shigar da tayi ba irin wadda lafiyayyan namiji zai gani ya kauda kai bace,bata kula Bintu ba itama Bintun bata kulata ba,zama tayi akujerar da take dab da ƙofar shiga falon,
Cikin ƙasan maƙoshi yayi sallama tare da zuge ƙofar glace ɗin falon alokaci ɗaya yana sako dogayen ƙafafunsa kan tattausan carpet ɗin dake shimfiɗe a bakin ƙofar falon,cikin wani irin yanga da yauƙi Taufiƙa ta miƙe tare da cewa waw broth ur welcome iknow ka gaji sosai,tana faɗa tana karɓar bag ɗin laptop ɗin sa,shi bai masan wacece ba dan har ga Allah bai gane Taufiƙa bace,dan haka saboda gajiyar da yayi kawai ya sakar mata jakar tare da ƙarasawa falon sa, Bintu kuwa tana zaune tana kallon Taufiƙa da iyashegen da takewa Oga Abdallah,lokacin da taga tabishi falonsa,sai taji ta kasa jurewa,tashi tayi tabi bayan su,wanda shi Abdallah ma bai san tanayi ba dan baima san ta biyo shi ba, Taufiƙa baƙaramin kiɗemewa tayi da ganin haɗuwar falon Abdallah ba, ƙoƙarin zama take Abdallah ya ɗan juyo dan atunanin sa Bintu ce,cike da mamaki yake dubanta,yana tunanin wannan kuma wace zararriyar ce,kafin yasamu abin cewa Bintu ta shigo tana wani ciccin magani,wanda ita kanta batace ga dalilin da yasa takejin wannan yanayin ba.shigowar Bintu sai ya ɗauke masa hankali lokaci ɗaya ya tuna halin daya fita ya barta aciki,dan haka sai ya zuba mata lulu eyes ɗin sa,yana so ya tambayeta amma ya rasa ta ina zai fara, kawai sai ya ɗan ɗaga mata girar sa ɗaya,sai hakan ya bada wani salo na musamman,haka nan taji wata shagwaɓa tare ƙwalla sun cika mata idanu,ɗan duban Taufiƙa da tayi mutuwar tsaye agurin tayi tare da cewa to kace ta tafi mana,alamu yayi mata waye take nufi? da ido tayi masa nuni da Taufiƙan,ɗan duban inda take kallo yayi,lumshe manyan idanun sa yayi tare da cewa ba tare kuke ba?hararar gefan ido tayi masa kana tace"Ni ban san ta ba ma!'tafiya ya shiga yi dan shiga ɗakin sa yana cewa na gaji sosai zan ɗan huta!'daga haka ya shige ɗakin tare da kullowa, Bintu ta ɗan murguɗa ƙaramin bakin ta tare da cewa kin ji yace"zai huta,samun kanta tayi da binsa cikin ɗakin tare da yiwa Taufiƙa gwalo,
Taufiƙa hannu tasa ta ɗan goge ƙwallar da suke san fallasa tarin bakin cikin dake kwance cikin zuciyar ta,ita da taso ta sa Bintu kuka yau, amma shine reshee ya juye da mujiya,anya kuwa Bintu ba asiri tayiwa Abdallah ba?dan taga kamar ma idonsa rufewa yakeyi idan Bintun na waje,baya tuna kowa sai bayan bata nan,anya kuwa zatayi nasara a wannan gaɓar ma?tunda gashi tunkan aje ko ina ta fara sarewa,wai bai ma gane taba ga kuma ita ƴar iskar yariyar da tasamu waje,wai itama bata santa ba,wata zuciyar tace"da ita Taufiƙa kawai kiyi haƙuri da Abdallah dan tuni yayi nisa bakuma yajin kira,cikin rushewa da wani mahaukacin kuka ta fita daga falon,
A can dakin Abdallah kuwa, Bintu tana shiga taga yayi tik daga shi sai dan boxa ihu tasa gami da rufe idanun ta da duka hannuwanta,banza yayi mata bai ce mata komai ba, gashi ita kuma baza ta fita ba saboda kar Taufiƙa tace"korota yayi,ta gwammace tai ta zama da hannu saman fuska,bata buɗe idan ta ba har sai da taji shigar sa toilet ɗin kana ta saki ajiyar zuciya tare da cewa, shi mutum sam babu kunya a idanunsa, da zan shigo ba sai yace min ehemm ba sai nasan abinyi amma ya kama ya barni na shigo naga... sai kuma tayi shiru,tare da fita daga ɗakin dan tasan yanzu Taufiƙa ta gaji da zama ta fece...
Zama tayi afalon tana jiran fitowar sa,kasancewar dare ya ɗan farayi sai garin yayi tsit ga kuma yanayin damuna dake sako kai,gari sai yayi kamar hadari,yanayin tsit ɗin da gari yayi shi yaɗan fara sakawa Bintu tsoran zaman falon, ƙoƙarin guduwa ɗakinsa take sai gashi ya fito,kai tsaye ya wuce tsakiyar falon ya zauna,tare da tanƙwashe dogayen ƙafafunsa,cikin miskilar muryarsa yace"kawo min abincin nan!'A hankali tace"yau kuma gargajiyar ce ta motsa? duk da yaji ta amma bai nuna mata alamun hakan ba tara ta kawai yakeyi duk ranar da ya rutsata baza taji daɗi ba,mata ɗin cin abinci ta shimfiɗa kana ta maido komai ta jera su cikin tsari da burgewa,har zata koma mazaunin ta sai kuma tayi wani tunani,dawowa tayi ta zauna gefansa tare da savin ɗinsa,loda alkubus ɗin tayi da yawa kana ta zuba miyar ta tura masa gaban sa,ɗan duban uban abincin da tazuba masa yayi tare da yin ƙwafa aransa, A hankali ya fara cin alkubus ɗin wanda take kunnen sa ya fara motsawa,tsayawa faɗar daɗin da Abincin yayi masa ma ɓata bakine,sai gashi yana neman cinye wanda ta saka mishi,gani tayi ya janyo kular ya kuma zubawa A tunanin ta daɗa wa zaiyi,har tana masa tsiya a ranta,sai taga ya turo shi gaban ta,zaro firgitattun idanunta tayi tare da cewa me za ayi?cinyewa za ayi!'ya bata amsa ba tare da ya dubeta ba,ɗan marairaice fuska tayi,cikin son ya tausaya mata tace"ai ya ai wannan yayi yawa na cifa nida inno!'juyowa yayi yana mai tsareta da kaifafan idanunsa wanda take suka saka mata nutsuwa,batasan sanda tashiga tura alkubus ɗin abakin taba,sai gani tayi kawai ta cinye wanda ya zuba mata tass,ganin ta cinye yasa shi miƙewa dakin sa ya nufa,zaro ido Bintu tayi dan ita dai har ga Allah tsoro take ji kuma sai ya ringa barinta ita kaɗai duk sanda tajita ta ita kaɗai, dakin nan take gani yana gilmawa ta cikin idanun ta,da gudu ta tashi tabishi cikin ɗakin,tana shiga ta shiga raɓewa kamar wata ƙadangaruwa,lokacin har ya gama shirin baccin sa,
Zama yayi a gefan gadon tare dayi mata alamar da tazo,ita fa abin nan yafara damunta wai shi baya gajiya da yin magana da jiki ne?ta fahimci sam hakan baya damun shi dan tsaf zata iya irga maganar shi arana,a hankali ta ƙarasa ta zauna akasan ƙafafunsa,cikin kamar yanayin gajiya da jin bacci yace"bani labari,kallon shi ta shigayi tare da san sanin wane labari yake nufi?,katse mata tunani yayi da cewa komai nake nufi maganar ku da Matar nan da labarin rayuwarki da ko mai ma wanda ban sani ba,kuma bana son ki ɓoyen ko mai akan Asalin ki,inaso ki gayamin keɗin wacece acikin wannan ahlin?
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y.