Showing 12001 words to 15000 words out of 184937 words

Chapter 5 - KUDURAR ALLAH COMPLETE BY FATIMA Y ADAM

21 Jul 2024

16850

zube gaban alh baba yana gaishishi cikin tsananin girmamawa,alh baba yace tashi jafaru kazauna Allah yayi muku albarka!'ya amsa da amin baba muna godiya Allah ya kara girma yajikan magabata!'alhj baba ya amsa cikin jin dadi hakanan yake ganin kimar alhj jafar da mutuncinsa yana kuma girmama alakarsu sosai ya daukeshi tamkar d'an cikinsa,cikin mutumtaka da kamala alhj baba yace da alhj jafar, nayiwa duk wani wanda yakamata atattauna dashi magana dan haka yanzu zasu karaso baki dayansu!' yan halak kuwa yana rufe bakinshi sai gasunan kusan duk atare, kasancewar yau weekend kusan kowa yana gida danshi alhj balarabe duk yayansa yan bokone kalilanne suke kasuwanci acikinsu.

Bayan gaishe-gaishe atsakanin su ne kuma alhj baba ya dubi alhj jafar yace"to jafar kace kana neman alfarma agurin ahlin gidan nan, kuma baza ka nema ba harsai na tara maka manyan yarana maza wanda dole sai da saninsu za'a'iyazartar da wani abu muhimmi acikin gidan nan,to gasu dan haka muna sauraronka!'alhj jafar yayi gyaran murya tare da gyara zamanshi kana yace"baba dama wata alfarmace nakeso ayimin acikin gidan nan wanda wannan alfarmar ba wani abu bane illa inaso d'ana abdallah zai dawo gidan nan da zama,wata zabura da alhj mansur yayi ita ta dakatar da dady jafar daga maganar da yakeyi, cikin wasiwasi da matukar shakku daddy jafar ya zuba masa ido dan yanaso ya karanto abinda yake kasan zuciyar mansur, alhj baba ne yace"munajinka jafaru kayi shiru!'numfasawa dady jafar yayi san nan yaci gaba da cewa"baba abdallah wani irin rikitaccen mutum ne kuma miskili me wuyar sha'ni,nayi-nayi ya fito da matar aure yakiya hasalima baya saurarona haka mamanshi duk wanda zaiyi magana ta bayan kunnenshi take wucewa,shiyasa na zauna nayi tunani me kyau akan abdallah naga dacewar kawoshi cikin ahlinka ko da bai samu macen da tayi masa ba zai dauki darasin rayuwa,kuma zai iya canjawa daga yanayin da yake ciki da kuma matsananciyar damuwar dayake ciki tunda nan wajene na jama'a da hada-hadarsu!'ya kare maganar yana mai tsurawa fuskar dady ane ido dan ganin yadda yake ta antaya masa harara tamkar idonsa zai fado,gyaran murya alhj baba yayi kana cikin nutsuwa yace"jafaru kan wannan dan batun ne kace sai na tara jama'a kamar gangamin daurin aure?kana ganin ko habibu kasamu da maganar nan bata isa ta wadatar ba?dady jafar ya sunjyiyar da kansa yana mai neman afuwa gurin alhj baba yace"baba ayi min gafara nayi kuskure amma naga kamar sai hakan yafi asanar da masu hakki!'alhj baba ya junjina kai,sannan yace"babu damuwa jafaru ni dai ta bangarena na amince abdallah jikana yazo ya zauna da yan uwansa, kuma duk yarinyar da yaga tayi masa indai babu maganar wani akanta to na bashi ita ya aura!juyawa yayi yana mai kallon yayan nashi da kuma yan uwanshi alhj Hashim da alhj mas'ud yace"idan da wani mai magana zai 'iya!' dady ane da dama kiris yake jira, ya zaburo cikin yanayinshi na zafi da ya shiga jikinsa yace"baba nifa Ina ganin kamar hakan bai dace ba bamusan manufarshi ta kullah wannan munafurcin ba to inba gulma ba haka kawai za'akawo katan gardi ace wai ya zabi mata bazai iya zuwa ya zaba ya koma inda ya fito ba!'ya karasa maganar cikin huci da hakilo shi adole baba ya fahimceshi, alhj hashir wanda suke kira da baffa ya dan numfasa kana cikin taushin murya da kamala irin ta manyan dattijai masu daddako, yace" haba mansur ya kana gima kana abun kananan yara duk ga kannenka nan zaune babu wanda yay irin wannan abun sai kai, dan allah ka dinga nutsuwa karka zama babban kobo meye abun tada hankali acikin wannan maganar, ka nutsu ka kwantar da hankalinka babu abinda zai faru sai alkhari insha allah!'abba mas'udu ma yace" hakane zancen ka yaya shi mansur baya daukar abu da sauki ne kamar yan uwansa, shiyasa kake jawowa kanka abubuwa da yawa ka nutsu dan Allah haka mansur kajiko!' ya fada cikin rarrashi da san kwantar mai da hankali,shi dai dady ane yayi shirune kawai dan anfi karfinsa amma ba dan yaji hankalin nasa ya kwantaba, Abba two wato alhj habib yace"to yaushe d'an namu zai karaso danni har na 'kagu naga zuwansa cikin ahlinmu!'ya fada yana sakar wa dady ane wani kayataccen murmushi tare da dage masa gira na irin to ya kagani din nan,dady jafar yayi dariya yace karka damu aboki insha Allah yana nan tafe!' Abba Ali yace" kaga sai asha shagalin biki dashi tunda yanzu baifi saura sati biyu ba bikinsu fa'iz!' abbi husain ne ya karbi zancen da cewa"tabbas zaisha hayaniya dan bikin mutum takwas ba wasaba!'nan dai suka cigaba da dan tattaunawarsu daga karshe kuma kowa ya nufi sabgarsa, dady jafar ma gida ya nufa kai tsaye da kudurin tunkarar abdallah da maganar komawa ahlin estate.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 8 ```

Yana zuwa yatarar da mom abigail zaune afalon idanunta sunyi jawur da alama taci kuka ta koshi, bai saurareta ba ya wuce apartment dinsa dan yasan ta tsuniyar gizo bata wuce koki,yasan abinda ta kawo ba mai yuwubane shi yasa ma bai fasa tun karar alhj baba da batun komawar abdallah gidan ba.

Saida ya gama duk wani abu da ya danganci rayuwar sa ta yau da kullum kana daga cin abinci wanka da dai sauransu. yana kokarin fitowa daga bedroom yaci karo da ita tana kokarin shiga bedroom din nasa, dan haka sai shi ya dakata da fitar, wato ta ga bai da niyar fitowa shine ita ta biyosa, dama baya sawa akansa lallai sai tazo ta kula da al'amuran rayuwansa dan bai saba da hakan ba,murmushi yayi kana cikin dan tsokana ya kama hannunta yana cewa mom abdallah ya akayine naganki wata iri!'aiko tamkar jira take tasake masa kukan daya ke ta cin ranta tun shigowarsa, kamata yayi ya zaunar da ita abakin gado kana shima ya zauna agefanta, cikin san lallaminta yace" to kuma daga tambaya sai kuma kuka dan dai ke bakya girma kina fa da yaro kamar abdallah!'cikin Jan numfashi tace"abban fatash da kanka kake kiran fatash da wani suna ba fatash ba? me hakan yake nufi ?nifa gaba daya awatannin nan nakasa gane inda ka dosa idan kayi kamar kana bayana sai kuma kayi wani abun da zai jefani cikin shakka kamar da wani abu da kake boye mun abban fatash!'ta zuba mishi Ido tana jiran abinda zaice mata, hannu yasa yadan share fuskarsa kana yace"abigail me kike tunanin zan boye miki?kina zargina da aikata wani mummunan abune?da sauri ta girgiza kanta tace"bawai zarginka nake da wani mugun abuba abban fatash,kawai dai Ina maka kallon wanda yake boyen wani abu ko kuma kake wani shiri wanda ni ban sani ba!'da sauri ya tari numfashinta dacewa haba Abigail wane magana kikeyi haka ni Ina can Ina fafutukar nemar miki mafita akan danki ashe ke kuma kina nan kina saka mugun zato akaina!'bakinta har rawa yake wajen furta da gaske kake abban fatash ? kasamo mana mafita akan wannan lamarin? kasan ni yanzu aduniyar nan bani da wata babbar da muwa da tawuce damuwar fatash,yace"calm down mana ki nutsu muyi maganar da fahimta mana' ke matsalata dake kenan gaggawa!'tace" to naji Ina saurarenka!'cikin nutsuwa yace"abigail nasamo inda zan kai fatash horo akan abinda ya shafi addinin mu babu abinda bazai koya ba hatta da yanayin rayuwar duniya zai koya harma mata zai'iya samu acan,ko yanzu ma daga gurin nake fatan mu da burinmu yanzu ya amince!'mom abi tace"cikin sanyin jiki anya kuwa fatash zai amince da wannan zancen?ni dai bazan kara fuskantar yaron nan da wani zance ba, Dan ba saurarata yake ba hasalima baya ganin mutumcina,amma bana ganin laifinsa komi ya faru nice sila!'yayin da wasu zafafan hawaye suke sauka daga cikin idanunta tana mai danasanin abinda ta aikata masa amatsayinta na wadda akabawa amanarsa,to amma ai tayi na dama ya kamata ya manta ya kuma karbeta amatsayin mahaifiya.abban fatash ya katse mata tunaninta da cewa" bakece zaki masa magana ba ki barni da shi kawai nasan zai amince domin shima tafiyar karuwarsa ce da kuma babbar mafita arayuwasa,za kuma ta zame masa haske mai haska masa duhun da ya mamaye idanunsa!' ita dai mom bata fahimci inda zaurencen mijin nata ya nufa ba amma ta sami salama daga zababbakar da zuciyarta keyi.

Baffa hashir ne zaune shida baba nura da kuma alhj nasir kana ganin yadda suka nutsu zakasan lallai tattaunawa suke mai matukar muhimmanci, baba nurane ya ce baffa kana ganin kuwa babu kamshin gaskiya akan maganar yaya mansur? kasan yaya mansur shine fitilar ganinmu mai haska mana hanya ni dai inaji kamar da alamar tambaya akan wannan jafar din!'alhj nasir ya dan muskuta tare da cewa"ni babu abinda yake dauren kai irin yadda yayi, yashiga jikin alhj baba yana matukar girmama jafar tamkar d'an cikinsa, alhj hashir yace abinda nakeso dakai nura lallai kayi kokarin binciko mana waye alhj jafar da kuma manufarsa ta kawo mana dansa cikin ahlinmu,dan tabbas kamar yadda ka fadane mansur shine fitilarmu mai haska mana hanya,kuma kasanarwa da salisu shima ya cigaba da yi mana binciken inda aka boye abubakar!'ismal yace maganar da nakeso nayi kenan nima dan wannan gabar ita tafi komai muhimmanci awannan zaman namu, ya kamata salisu ya kara azama akan wannan binciken, dan abubuwa karuwa suke kar lokaci ya kure mana!'dukka sunyi amanna da wannan shawarar,dan haka kowa yay damara dan aiwatar da kudurinsu me kyau ko akasinsa allahu a'alamu.


..... Bauchi.....

Har aka kira sallah gari ya fara yin haske bintu na kan zagaye gidansu ciki da waje dan neman fafi, amma ba wata alama datake nuni da fafi yana cikin garin bauchi ma bare cikin gidan,tarasa me zatayiwa kanta kukan ma yanzu ya gagara,idanunta sun rufe sam bata kula da dan karamin diary acan gefe akasan dakin ba saboda bata iya ganin komai aidanunta ta zama tamkar makauniya,acan wani bangare na zuciyarta, tayi wani tunani a inda fafinta yakan yawaita yi mata nasiha akan dukkan cakudewar lamura saukinsu yana ga Allah kar ta nemi temakon kowa sai Allah domin shi kadaine mai jin kan bawansa shi kadaine mai kudura da irada kuma majibancin lamura, tunawa da haka yasa tayi azamar zuwa ta dauro alwala ta gabatar da sallar asuba, tare da mika kukanta gun allah buwayi gagara misali,tayi kuka tayi addu'a ta tayi a sujjada tayi atsaye tayi azaune tanayi tare da yakini da tawassali, ko da ta'idar wani irin kwarin gwiwa takeji tare da jin bata rasa kowa ba tunda tana da Allah buwayi mai kowa da komai, ahankali ta bude idanunta da suka kumbura saboda yawan kuka duk sun kan kance dishi dishi ta fara ganin dakin saboda dadewar da tayi idanun akulle ahankali suke washewa, can tashiga wurga idanuwan loko da sako na dakin tamkar dai tana tunanin zata ci karo da fafinnata, har ta kawar da fuskarta sai kuma ta kuma juyawa da sauri dan karamin diary din nan ta gani ,cikin sauri ta rarrafa ta daukoshi tare da zuba masa ido,budeshi ta farayi kamar amarki taci karo da zanzareran rubutun fafi jere reras akan farar takardar ,cikin nutsuwar da ta dan samu ta fara karanta rubutun.


..... ABUJA.....

Sai misalin karfe 7 abdallah ya dawo, kaitsaye masallaci ya wuce saida yatsaya yay sallar isha kamar yadda yasaba kana ya shiga gida.

baisamu kowa afalon ba dama koda ya samu ba damuwar shi bane cikin sassarfa da almun gajiya atare dashi ya wuce side dinsa,kayansa kawai ya cire ya daura towel ya fada toilet, kusan awa daya yayi kana ya fito,shiryawa yayi cikin wasu tattausan kayan bacci ya feshe jikinsa da turarukansa da yake amfani dasu wajen bacci daga nan ya nufi falo dan shan copy.

da kansa yake hada kayanshi dan shi bai yadda wata kazamar arniya ta taba mishi koda kofar side ba bare taba abinda zaici, yana dora copy din akan tattausan lip dinshi aka murda handle din kofar, zubawa kofar ido yay yana tunanin ko momce tazo tacikashi da banzayen surutai,sai dai yayi kuskuren tunani, dady ne yashigo bakinsa dauke da sallama, ahankali ya sauke cop din copy daga bakinshi yana mai amsa sallamar dad din cikin taushin muryasa mai dadin sauraro,dady yace"abdallah ina fatan dai bakajin bacci dan magana nakeso zamuyi mai muhimmanci!'ya fada yayin dayake kokarin zama cikin daya daga cikin kujerun da suka kawata falon, abdallah yadan saki fuskarsa kadan amma ba murmushi yayi ba gata nan dai babu yabo babu fallasa,karasowa yayi kujerarsa dake fuskantar inda dad din ya zauna,ya hada hannunsa yana dan murzasu cikin salo da burgewa,kana ahankali yace da dady barka da dare!'dady ya amsa da alhamdulillah ya aikin naka?asaman labbah ya amsa dan wannan yar maganar har ta gajiyar dashi.

Dady ya dan gyara zama tare da gyaran murya, kana yace abdallah wannan zaman da kakeyi cikin kunci ya isa haka duk danasan cewa ba azaune kake ba atsaye kake dan ganin ka cimma magauta ka kuma yakesu to amma kasan har yanzu lalube muke aduhu bamusan ko mai ba duk da kutsawar da nayi cikinsu to amma na gaza gane komai,abinda nayi tunani shine abdallah banine ya kamata na shiga cikin wannan ahli ba kaine ya kamata kaje kayi yakin da kanka wannan ahli ahlinka ne abdallah kuma idan kana zaune anan ta yaya za ka gano makiyanka da kuma inda suka kai mahaifinka?na fahimci wani abu guda acikin ahlin alhj balarabe wato shine akwai wata makar kashiya da yasa kwata-kwata ba'atunawa da mahaifinka ban tabajin habibu yayi alhinin rashin dan uwansa abubakar ba ban tabajin alhj baba yayi batun batan dansa mafi soyuwa agareshi ba kai hasalima babu wata alama dake nuna anyi wani babban rashi aciki wannan zuria ba,ban kai ga batunka bama tunda kai kana yaro karami,bansani ba kuma ko dai da akwai hakan ata wani bangare!'dan nisawa yayi kana yaci gaba da cewa abdallah dole kashiga cikin ahlinka kodan tseratar da wasu rayuka da basuji ba bare gani bayan mahaifinka na tabbatar akwai wadanda suke bukatar tai makonka dan haka ka shirya gobe sunday zamuje na rakaka!'gyada kanshi kawai yayi batare da yayi wani doguwar magana ba yace na gode dady!'dady ya shafa kanshi tare da cewa karka damu abdallah dole na taimaka maka domin nima ka,tai makeni dan tasanadin ka na samu haske arayuwata,yau gani amatsayin musulmi mai alfahari da musulunci,dole na tayaka da laluben neman masu san halaka ku kaida mahaifinka!' daga haka ya nufi kofa dan fita, harya dora hannu zai bude kofar ya tsinkayo daddadar muryar abdallah yana cewa dady bazasu ganeni ba saboda kamanni?dady yayi murmushi yana aiyanawa aransa lallai abdallah ya karbi batunnan da muhimmanci harda su tambaya,yace karkadamu abdallah Allah bazai bawa kowa ikon ganoka ba idanunsu zai rufe insha Allah,kayi itihara yau kafin ka konta kajiko!' jinjina kai abdallah yayi cikin nusuwa ya kuma cewa dady akara kwanakin tafiyar har sai na gama istihara!'dady yace hakane abdallah hakan yayi kyau,daga haka yabar falon,


..... bauchi.....

Bintu kiyi hakuri abinda kikeso kiji daga gareni bazai samuba dan nima bansan komai ba amma abinda zan gaya miki yanzu shine fitilar da zai haska miki hanya, abu dayane zuwa biyu shine asalinki da kuma inda zaki nufa!'


Dafarko dai bintu banine mahaifinki wanda ya haifeki ba amma uba nake agareki dan ciki daya muka fito nida mahaifiyarki uwa daya uba daya nine babba sai ita mu kadai iyayenmu suka haifa!' mu cikakkun fulanin adamawa ne,iyayenmu ba yan boko bane amma sun samar mana da ilmin boko dana addini mu bamasu kudi bane amma muna da rufin asiri dan bamu nemi komai mun rasa ba nayi karatun digree dina a maleshiya anan ne muka hadu da umar balarabe wanda yazamo amini agareni,ko da muka gama karatu bamu bar zumunci ba,har bikinsa naje nayi kwana biyu sai da aka gama na dawo. daga nan nima ban jima ba akayi bikina da yar uwata asma'u alokacin Ina aiki a wata babbar kotu dake nan cikin yola.

Bayan shekaru kusan biyar Allah bai bamu haihuwa ba daga ni har aminina umar sai dai umar yafini shiga damuwa nine nake yawan bashi baki da yaci gaba da addu'a ,yana yawan cemun shi dai aure zaiyi da zarar yasamu matar da yakeso.


Ana cikin hakane kanwata lailatu ta dawo daga makaranta, kasancewar akano take karatu a b.u.k tana zaune a hostel, tunda umar yake zuwa bai taba haduwa da Laila ba sai alokacin da ta kare karatunta, ranar da tayi exam din karshe aranar tayo gida tunda umar ya dora idonshi akan Laila shike nan yawada zazzafar soyayyarta,tun daga lokacin umar baya cikakken sati bai biyo jirgi yazo yola ba tun muna jin tsoro nida ita da iyayenmu har muka saduda, ba komaine yasa mukejin tsoron dangantakar umar da Laila ba illah tsananin kishi mai matukar zafi kuma na hauka wanda matarsa nafisa ke dashi agabana tasha alwashi iri da kala munana akan duk wadda tayi gangancin auren mata miji dan umar natane ita daya, wannan shine babban dalilin dayasa bamason wannan alaka ta soyayya. ana cikin wannan halinne kuma mahaifinmu ya rasu,bayan wasu yan watanni da rasuwar ne umar ya kuma dago da maganar sa da Laila wanda ni atsammanina ya hakura ashe wai mutuwar bafface tasa ya danyi shiru da zancen.

Babban kuskuren da muka aikata alokacin ganin nine alwalin Laila yasa mukayi ganganci, nazo na kalallame hajjo mahaifiyarmu da zance mukace babu wanda zaisan da auren har sai ankwana biyu, umar ya kawo hujjar cewa idan alhj baba yasani kamar nafisa tasanine dan haka ayi auren daga baya sai ya kaita gida ya nunata yadda alokacin nafisa babu yadda zatayi dasu dole ta dangana,

Haka kuwa akayi. aure tsakanin Laila da umar ya dauru, ya siya musu gida mai shegen kyau anan cikin yola suka tare duk sati yake zuwa yayi kwana biyu ya koma bansan me yake gayawa mai dakinsa nafisa idan zauzo .


Haka rayuwa ta shuda har tsawon watanni biyar, alokacin matata asma'u ta haifa mun tagwaye harsuyi wayo. cikin ikon Allah Laila tasamu ciki acikin watansu na shida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login