Showing 138001 words to 141000 words out of 184937 words

Chapter 47 - KUDURAR ALLAH COMPLETE BY FATIMA Y ADAM

21 Jul 2024

16894

gogar tsinin nata hancin,cikin sanyin murya yace", Bint ba son damuwar Nan,na daukar miki alƙawarin kamar yadda kika zama sanadin farinciki na nima sai na zama sanadin farin cikin ki,bazan bari kiyi kuka ba zan toshe duk wata hanyar damuwar ki,zan kawar da duk wani abun cutuwa A gareki,Bint zan samo miki fafinki da ummin ki aduk inda suke a faɗin duniyar nan!'.....

Fatima y Adam✍🏽
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 51 ```



Ko yanzu ma na tanadar miki da abinda zai iya rage miki damuwa!'ya faɗa yana goga siririn hancin sa kan tsinin hancin ta,rufe idanun ta tayi tana ƙoƙarin maida hawayen da suke san zubo mata,A hankali yasa hannu yana goge mata fuskar tare da ɗan gyara mata ita,ɗage mata gira yayi tare da cewa har kin ɗan yi kyau,bana so su ganki cikin damuwa da yawa!'zata yi magana yayi mata alamar tayi shiru,haka ta haƙura da tambayar da take bakin ta,fita sukayi sai faman kallan anguwar take yi saboda har yanzu bata fahimci inda suke ba.

Duban ta yayi tare da cewa ki shiga sai kiyi min iso!:ɗan jim tayi kamar tana tunanin wani abu,sai kuma ta gyada masa kai tare da saka kanta cikin madaidai cin gidan na bulo,sallama tayi cikin sassanyar Muryar ta,HAJJO dake zaune jikin bishiyar mango dake girke a faffaɗan tsakar gidan tayi wata irin zabura har zanin ta na ƙoƙarin kuncewa,cewa take yi, wa nake ji kamar Lailata Allah Ubangiji ka amsa addu'a ta na ganin Laila araye,idan mafarki ne kuma ka barni a haka karka farkar dani!'ta faɗa tana ƙarasawa bakin ƙofar da Bintu ta cokare agurin,zaro ido Hajjo tayi tare da dafe kirji bakinta har rawa yake gurin kiran Asma'u, Asma'u dake cikin daki tana haɗa wanki ta fito da gudu tana cewa lafiya Hajjo me yasa mek,,,,maganar ce ta maƙale mata sakamakon tozali da tayi da Bintu.


Cikin kiɗima ta matso kusa da Bintu, ta taɓata tare da cewa Laila kece da gaske? Bintu dai ido tasa musu saboda ita bata fahimci abinda hakan ke nufi ba ta daiji suna ambatar sunan mahaifiyar ta, Asma'u ta jawo hannun Bintu tare da cewa Hajjo wannan ba Laila bece"sai dai idan yarinyar Lailace!'Hajjo ta kamo Bintu cikin wani irin kuka mai tsanani da ban tausai,ta rungume ta,tana cewa tabbas wannan jinina ce,ko aduhu na laluba naji wannan halittar sai nagane jinina ce saboda tsarin halitta da komai babu inda ta baro Laila,ta wani bangaren kuma sak Umaru!'Bintu jin an ambaci mahaifinta yasa taji wani kuka ya ƙwace mata, Allah sarki ko a wane hali yake yanzu,tunda ta san Nafisa tana nan tana shirin kashe shi,jin hon daga waje yasa Asma'u tace"kai Hajjo ko dai tare suke da yaya Umar ne?bari na da naje na gani tunda har yanzu baya iya shigowa gidan nan kai tsaye!'ta faɗa tana figar mayafi akan igiya,ta fita cikin sauri,Hajjo kuwa kama hannun Bintu tayi ta kaita har kan tabarmar datake zaune,tare da saka ta gaba tana kallo bata fata ace mata Bintu ba jikarta bace,


Sallamar Abdallah yasa Hajjo ta dawo da hankalin ta kan bakin ƙofar tare da amsa sallamar,zubawa Abdallah ido tayi saboda hango kamannin Umar atare da shi,wani tabarmar Asma'u ta shimfiɗa masa ya zauna,idanun sa kan Bintu da yake son gano halin da take ciki, ji yake kamar bashi da lafiya saboda rashin walwalar Bintu, yarinyar da bata da batabarin damuwa tayi tasirin da zata hanata farinciki da walwala amma yanzu gaba ɗaya duk ta sauya,babu kunya Bintu ta matsa kusa dashi tare da langaɓe wuyanta a kafaɗar sa,tana ci gaba da yiwa su inno kallon rashin sani, cikin girmamawa Abdallah ya gaishe da Hajjo kana suka kuma gaisawa da Asma'u,Hajjo tace"bawan Allah daga ina duk da cewa ina maka kallon sani amma ina so kayi min bayani,amma dan Allah kar kace min wannan yarinyar ba ɗiyar Laila bace!'ta ƙarasa maganar cikin matso hawayen da suke kwarin idanunta, Asma'u ma shuru tayi ta zubawa Abdallah ido da kuma fatan jin kyakykyawan labari daga bakin sa,ɗan ajiyar numfashi Abdallah yaja tare da fesar da iskar da yacika bakin sa da ita,kana cikin nutsuwar sa da kuma salon maganarsa mai ratsa zuciya ya fara bawa Hajjo labari tun daga farkon zuwan Bintu ESTATE da irin gwagwarmayar da tasha da na nasa labarin da irin abubuwan da suka fuskan ta har kawo wannan rana da suka samu kuɓutar da Dady Abubakar daga cikin wannan ɗakin.

Wani Irin mamaki da al'ajabi da kuma tsoron duniya shi ne abinda ya riski Hajjo da Asma'u ko magana sun kasayi sai taraddadi da kuma hawayen tausayin ƴaƴan ta dakuma jikokin ta,cikin zubar hawaye tace"zo nan Batula naji ɗumin ki , ki maye min gurbin kewar mahaifanki Sulaiman da Laila!'da gudu Bintu ta waɗa jikin ta saboda yanzu ta fuskanci komai,wato wajen kakarta mahaifiyar ummin ta da fafinta Yah Abdallah ya kawota,kwanciya tayi ajikin matar da takeji kamar ta kwanta A jikin ummin ta ne,wasu hawaye masu dumi suke ta sararowa bisa kyakykyawar fuskarta,goge fuskarta Hajjo tayi kana ta gyara zaman ta cikin nuna jinjina tace"Abdallah kayi ƙoƙari kunyi ƙoƙari kuma zamu cigaba da addu'a da sadaka domin Allah ya kuma ɗora mu akan maƙiya insha Allah nasarar na garemu kamar yadda kuka kuɓutar da Abubakar da taimakon Ubangiji suma su Laila zaku kuɓutar da su da izinin Ubangiji,Ni ai yanzu hankalina yafi kwanciya kan da, saboda yanzu ina ji ajikina kamar yadda Allah ya baiyana min Bintu to zai baiyana min Sulaiman da Laila!'Asma'u ta ɗora da cewa insha Allahu rabbi ya nuna mana wannan rana!'gaba ɗaya suka amsa da Amin,Hajjo tace"yanzu mai zamu baku irin naku na ƴan gayu? ta faɗa tana kallon Abdallah da murmushi akan fuskarta,shima dan murmushin yayi tare da cewa ai Hajjo sai dai ko Bint Amma yanzu nake son juyawa ina da aiyukan da zan gabatar dasu yanzu!'Hajjo ta riƙe baki kai ɗan nan da wuri haka? amma dai ko furar garin mu ka bari na dama maka zata rage maka wani abu inyaso ko tafiya sai kayi da ita!'shuru yayi bai ce komai ba sai murmushi da ya ɗan yi,yana duban Bintu da tayi zuru tana binsu da ido,kafin Hajjo tayi magana ma tuni Asma'u ta tafi dama furar dan haka sai ta kuma dawo da duban ta kan Abdallah tana cewa, amma dai anan zaka barmin kishiyata mudan kwana biyu ko?jin jina kai yayi tare da cewa gobe zanzo mu tafi idan Allah ya kaimu!'to goben nan to babu damuwa Allah ya nuna mana ai ganin ku yafi min komai!'ganin kamar Hajjon bataji daɗi ba yasa shi cewa Hajjo karki damu indai Bint ce har sai kun gaji da ganin ta, insha Allah baza mu dawo muku nan ba sai da fafi da Ummi Laila,Kinga yanzu zaman bint bazai yuwu ba saboda akwai abubuwan dake gaban mu!'cikin gamsuwa da bayanin Abdallah Hajjo tace"karka damu na gamsu da maganarka, Allah ya baku nasara akan aiyukan ku na alheri ya kuma baiyana mana su cikin aminci shi kuma Abubakar Allah ya tashi kaɗunsa ya bashi lafiya!'amsawa sukayi da Amin cikin rangwamen damuwar da tayi kaka gida A zukatansu.


Lokacin da sukayi sallama har zai fita sai kuma ya ɗan yi jim da alamu dai akwai abinda yake son faɗa, inno tace" da akwai wani abu ne Abdullahi?cikin kwantar da murya yace"alfarma ce nake so kiyi min!'Hajjo tace"faɗi matsalar ka tsakanina da kai babu alfarma!'cikin ƙara tausasa murya yace"dan Allah Hajjo karki faɗawa Abba Umar komai kiyi shiru da bakin ki saboda ayanzu sanin sa zai iya haifar da wata babbar matsalar wan nan yazama sirrin mu har zuwa lokacin da Allah zai kawo mana ƙarshen komai!'Hajjo ta ɗan yi jim kana kuma tace" idan kana ganin hakan zaifi to babu damuwa game da hakan kuma wannan tunani ne mai kyau, insha Allah bazai san komai ba!'yauwa Hajjo na gode da fahimta!'daga haka sukayi sallama ya fita,Hajjo tace"kije kuyi sallama mana Batula!'cikin sanyin jiki Bintu tabi Abdallah wanda har ya shiga mota.


A cikin motar ta same shi shi kaɗai,sai ta tsaya daga bakin ƙofar tana kallon sa idanuwan ta har sun cicciko da ƙwalla,miƙa mata hannun sa yayi alamar ta taho a hankali ta taka ta saka hannunta cikin nasa,janyo ta yayi cikin motar,yasa hannu ya rufe kana ya juyo da fuskarta gareshi,hmm gayamin wannan kuma na meye?ya faɗa yana lakato hawayen da suka zubo mata,fadawa jikin shi tayi tana ɗan sakin wata ƴar sheshsheƙa tare da ajiyar zuciya,shafa bayan ta ya shiga yi cikin ƙoƙarin samar mata da nutsuwa yace" ko bazaki iya zama ba mutafi?ɗan tura ƙaramin bakinta tayi tana ɗan bugun saitin zuciyar sa tace"kaima ka zauna mana sai goben mu tafi tare!'zaro idanuwan sa yayi tare da cewa kai Bint ya za ayi gan sameme dani na kwanar musu agida sai kace wanda mukazo wani garin!'shuru tayi batace komai ba,ɗago fuskarta yayi tare da ɗora bakinshi kan nata,A Hankali ya shiga tsotsa kamar mayunwacin da ya kwana baici ba,sun ɗau tsawon mintuna biyu kafin ya saketa,cikin muryar sa da ta sauya yace"maza shiga gida ina kallon ki!'cikin sanyin jiki kamar bata so, haka ta fita ta shige cikin gidan tana waiwayen sa, saida yaga shigar ta kana ya kira Daniyal,yazo su tafi,sai da suka fara tafiya kana yace"gidan sirri zaka kaini!'ok sir Daniyal ya faɗa yana ƙarawa motar gudu.


Sosai fa Anty Nafisa tasa ake mata bincike akan shiga da fitar Abba Umar, wanda garin haka ne aka binciko mata gidan su Hajjo,daga nan tace yaran da tasa su aikin su duba tanaso agano mata suwaye acikin gidan,to wannan aikin ne dai ya ɗan dauki lokaci dan har yanzu jiran sakamako take,sai kuma yau katsaham da aka tashi da gobarar wan can ɗakin da itama ta daɗe tana son kai masa ziyara dan sanin ko me aka ɓoye acikin sa,ana cikin wannan jimamin kuma sai ta samu kira daga yaran da tasa suyi mata bincike,suna tabbatar mata da cewa sunga baƙin fuska sunzo gidan har mutum uku,amma dai babu Abba Umar acikin su,cikin tashin hankali tace"wane jinsi ne?yaron ya sanar mata cewa mace guda ɗaya sai maza biyu take zuciyar ta ta hau bugu,cikin rawar baki tace"lallai kuma cikin gaggawa inaso ku turomin da fuskokin su,a yau ba sai gobe ba!'daga haka ta kashe wayar tare da yin jifa da ita,tana fitar da wani irin zazzafan hucin ta shin hankali, Allah dai yasa ba shegun nan ne suka dawo ba,duk da cewa bata tunanin hakan zai tabbata amma tana matuƙar jin tsoron faruwar hakan.


Yana yawan shiga ɓangaren inno dan kawai ya duba yaga ko su Abdallah sun dawo,sai dai kuma har yanzu da lokacin ranar ya kusa wucewa shuru kake ji babu alamar dawowar su,har inno sai da taso gane wani abu atare da shi saboda yawan shigo mata yake yi duk minti bayan minti,a shigowar sa ta wajen biyar ne inno tace" wai kai lafiyar ka kuwa ɗan nan ko dai da wani abu da kake jira ko kake nema?yace"ba wani abu inno kawai dai ina ɗan duba lafiyarki ne!'ya faɗa tare da ficewa daga falon,inno ta bishi da wani mugun kallo tare da fidda wani ɗan sauti kamar irin ƙwafa ɗin nan,a bayyane ta furta cewa komai ya kusa zuwa ƙarshe ayi dai mu gani!'


Samuyal yace"wallahi Oga tun da muka dawo taƙi yin magana daga ƙarshe ma sai ta yi suman da muka kasa gane kanta,tun jiya muke sheƙa mata ruwa amma taƙi farfaɗowa,gashi kuma tana numfashi da'a lama dai ba mutuwa tayi ba!'Safwan ne ya ɗora da bawa Abdallah labarin abinda ya faru dasu ajiya wajen tahowa da Abigirl ɗin,shuru Abdallah yayi tare da tsurawa fuskar Abigirl ɗin idanu,ɗan jin jina kansa yayi kana ya fita daga ɗakin,ɗakin Saiyyid ya shiga yaja kujera ya zauna yana fuskantar Sayyid ɗin,cikin matuƙar kaushin murya Abdallah ya shiga korawa Sayyid gargaɗi yace"wallahi Sayyid idan ka sake ka kalli inda nake Acikin estate to zakayi nadama balle kuma ka ambaci sunana,kuma bawai ina maka gargaɗi dan ina jin tsoro bane a'a sai dan kawai inason kammala aikina lafiya,zan mai dakai gidan ku amma idan kana sha'awar cigaba da zaman rashin ƴanci to ka gwada yin abinda bana so!'daga haka ya kira Daniyal tare da bashi umarnin ya ɗauki Sayyid ya maida shi ESTATE kar kuma ya bari aganshi yasan inda zai ajiye Sayyid ɗin, Daniyal ya amsa cike da girmamawa kana ya juya ya fita daga ɗakin,Yahya ya kirawo dan ya mayar dashi estate,


Hajiya zulaiha kuka take nasamun rangwamen abinda ke damun zuciyar ta,jin wannan al'amari take kamar almara wai yau Alhaji Baba da kansa ya tara mutane dan sanar musu zai sa afara neman ABUBAKAR,tabbas ta daɗe tana jiran wannan rana me ɗin bin tarihi,hakanan kuma take jin wani farin ciki tun bayan gobarar dakin can,wanda ta rasa dalilin haka, Rahima da bata jima da dawowa daga can egift wajen yayan ta ba,ta matso kusa da mahaifiyar tata,cikin tausayi irin na ƴa ga uwa tace"Ammi yauma dai har da kuka kuma duk da kince kar na kuma magana akan damuwar ki!'da sauri Ammi ta jawo ta jikin ta,tana cewa yau insha Allah zan baki labarin mahaifin ki da ɗan uwanki, alokuta da dama inason yin magana amma sai hakan ya gagara ban san meye dalilin ba, amma yanzu kamar wadda aka cirewa wata ƙaya daga cikin maƙogaro haka nake ji,amma ina fatan hakan ya zama silace ta warware mana dukkan matsalolin mu!'kuka Rahima take yi sosai kamar zata shiɗe bayan ta gama jin labarin mahaifinta da dannuwanta wanda ita a tunanin ta mahaifinta ya mutu,ta kanƙame Ammin kamar zata koma cikin ta,wayyo Ammi na dama wannan baƙar damuwar kike shaƙa shekara da shekaru ke kaɗai ban sani ba,dan Allah Ammi na ki yafe min gurguwar fahimtar da nayi miki Abaya,duk rashin sani ne wanda yafi dare duhu!'ta ƙare maganar cikin ƙara ƙanƙame Ammin,shafa kanta Ammi take cikin san lallashin ta,tace"ba laifinki bane nima kuma ba laifina bane,wan nan abinda ya sameni ba Ni kaɗai bace duk ahlin ALHAJI BALARABE ne,kamar anrufe baki da idanuwan mu babu wanda yake iya furta sunan mahaifinki acikin gidan nan,sai dai kabar damuwar ka cikin ranka tayi ta kassara lafiyar ka,dan haka yanzu godiya zamuyiwa Allah da ya bamu ikon tunawa dasu wanda hakan ma wata babbar nasara ce,a garemu,kinga zamuyi addu'a da bakunan mu mu roki Allah ya baiyana mana su aduk inda suke.


Ta gumi ta zuba ɗan duk sai taji ranta babu daɗi akan abinda Inno da Hajiya Babba sukayi ɗazu a falon Alhaji Baba,ko me hakan yake nufi kuma?dama da akwai wannan kishin tsakanin su?duk sai taji ta tsargu to me Hajiya Babba take shirin faɗa Inno ta tareta?miƙewa tayi tsaye tana cewa tabbas bazan iya haƙuri ba sai na je nasamu inno da maganar dan Ni ban iya ƙunbiya ƙunbiya da munafunci ba dan haka bazan bari ayi min ba,ta zari mayafinta tayi waje dan zuwa sashen Inno,

Daniyal yayi nasarar kawo Sayyid gida ba tare da kowa ya ganshi ba,daƙyar Sayyid ya iya ta kawa zuwa cikin estate ɗin saboda daure war da ƙafafunsa sukayi wajen zama guri ɗaya,yana shiga get ɗin farko ya cikaro da Dady Habib zai fita amota,ɗaga masa hannu yayi kasan cewar baƙin glace ne yasa shi Sayyid ɗin bai gano Dady Habib ɗin ba ya dai gane motar sa kawai,cikin sauri Dady Habib ya taka burki tare da fitowa daga cikin motar jikin sa har rawa yake saboda farin cikin ganin Sayyid, rungumo shi yayi yana duba jikin Sayyid ɗin tare da cewa Sayyidi ina fata dai kana lafiya babu abinda ya same ka suwaye suka sace ka?duk ya jero masa tambayoyin ajere, Sayyid yace"Dady nima ban san su ba,muje ciki a gajiye nake sosai!'cikin rawar jiki Dady Habib ya saka shi cikin motar kana ya zagaya ya shiga yaja suka nufi cikin estate ɗin.


Wata irin zabura Anty Nafisa tayi yayin da taci karo da hotan Bintu a kan scring ɗin wayar,jikinta da zuciyar ta babu abinda sukeyi sai rawa,zubawa hotan ido tayi tana kallon wata fuska acikin fuskar Bintu,shin WACECE BINTU,me tazo yi ESTATE kuma meye haɗin ta da waɗan nan mutanen da Umar yake zuwa wajen su, su ɗin su waye?wai mai ke shirin faruwa da Nine?yana ke ganin fuskar Bintu na juye min da wata fuska da na sani?me yasa tun farko ban fara buncikar yarinyar nan ba na yadda da ita haka?me yashiga kaina alokacin?cikin sauri ta ta danna kira,ana ɗagawa tace"cakewa kayi gaggawar buncikomin asalin mutanen da suke zaune agidan nan, da matsayin su agurin Umar bana son ɓata lokaci kamar yadda katuran hotan nan a yau shima ina so wannan ayau ka bincikon abin da nake da bukatar sani!'yace"angama Hajiya karki damu zaki samu yadda kike so!'ajiye wayar tayi tana ci gaba da kaiwa da kawowa aɗakin dan batajin yau zata iya zama batare da taji sakamakon binciken da tasa ayi mata ba.


Dady jafar ya dubi Dady Mansur cikin mamakin sa yace"dama wannan shine kiran da kayi min amma kuma me yasa kake son kasan inda Abdallah da Bintu suke,meye damuwarka da hakan, kuma me zakayi musu?Dady Mansur yace"Jafar bazaka ne komai ba yanzu amma dan Allah inaso ka taimaka kagayamin inda yake saboda ina buƙatar ganin su da gaggawa!'wani mugun kallo Dady jafar ya watsa masa kana yace"amma Mansur baka ji daɗi ba Nima ka biyoni ne dan kayi min yaudarar da kasaba yiwa mutanen gidan ku?to bari kaji na gaya maka Mansur tuntuni anyi walƙiya na ganka kuma sauran mutane ma zasu ganka insha Allah sai asirinka ya tonu a idon duniya,kuma zaka girbi abinda kake shukawa,saboda ɗan zaki ya riga ya girma shine zai cinye dukkanin mugayen kananun namun daji!'yayi wani irin murmushin takaici me ciwo ya cigaba da cewa Allah ya riga ya nufi zakaran da cara babu yadda zakuyi dashi sai dai kallo!'shuru Dady Mansur yayi saboda ayanzu dai bashi da ta cewa duk bakin sa amma yanzu ya baya iya maida magana,dan haka ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login