Showing 90001 words to 93000 words out of 184937 words

Chapter 31 - KUDURAR ALLAH COMPLETE BY FATIMA Y ADAM

21 Jul 2024

16890

yasa yace"ko kina da buƙatar wani abu ne? cikin san zubar da hawayen taɓara tace"Ni banyi wanka ba kuma gashi babu kaya anan!'bai ce mata komai ba, ya buɗe wata akwati mai kyau ya zaro wasu kayan bacci masu kyau da ɗaukar hankali,miƙa mata yayi tare da cewa tashi kije kiyi wankan!'cike da mamaki tasa hannu ta karɓi kayan, sauri yayi ya fita daga ɗakin dan yasan sai tayi masa tambaya shi kuma bai shiryawa jin shirman nan nata ba,jiki asanyaye ta shiga bathroom ɗin sai da ta haɗa turarukan wanka kala kala amma duk da haka ba taji yayi mata yadda take so ba saboda haɗin inno na musamman ne dan ma ƙamshin ya riga ya kama jikinta ko nan da wata biyar zatayi bata sake wanka dashi ba wannan mataya taccen ƙamshin yana yana tare da ita,bayan ta fito ta zura rigar da ya bata tare da fesa matattun turarukan sa masu sanyin ƙamshi da kwantar da hankali,kana ta jera musu fulo a tsakiyar gadon,kwanciya tayi ta shige cikin tattausan bargo tare da lumshe idanun ta,shigowa yayi bakin sa ɗauke da sallama lokaci ɗaya yana mai bin saman gadon da ta jera fululluka da olido,wani irin tattausan murmushi ne ya suɓuce akan leɓan sa girgiza kan sa kawai yayi tare da ƙara sawa ya haye kan gadon.

Hannu yasa ya fara zame fulon,cikin sauri ta buɗe idanun ta gaba ɗaya dan dama tana kallon duk abinda yakeyi takafar idanun ta da bata gama rufe shi ba,da hanzari tasa hannun ta ta riƙe wanda ya ɗauka yana shirin maida shi mazaunin sa,kallon ya bita da shi mai nuni da alamun tambaya,ɗan kawar da kanta tayi tare da cewa Ni kawai ka barshi anan raba mana nayi ba sai wani ya buge wani ba, kuma kai mirgin mirgin ne da kai!'kallonta kawai yake ya rasa ma abin da zaice mata wai shine yake mirgin mirgin lallai yarinyar nan taga gadon kwanan sa,bai ce mata komai ba ya cigaba da kwashe fulon yana gamawa yayi kwanciyar sa batare da ya tanka mata ba,gunguni tayi tare da ɗaukar fulon ta, ta komar da kanta wajen ƙafafun sa tana cewa to bari muyi sama da ƙasa!'still dai bai ce mata komai ba sai ma addu'a da yashiga yi,ganin haka yasa itama ta fara tofa tata addu'ar,


Shi dai bai san ya akayi ba buɗe idon sa yayi kawai ya gansu manne da juna karma Bintu da tabi ta wani kanainaye shi kamar tana tsoron kar wani ya ƙwace mata shi,a hankali ya maida duban sa kan agogon da ke gefan sa saman gadon, ƙarfe uku saura,a hankali ya zameta ya miƙe ya shiga toilet bai ɗau lokaci sosai ba ya fito,wanda fitowar tasa tayi dai dai da farkawar Bintu,binsa tayi da kallo ta ɗan hasken ƙaramar fitila ganin kamar alwala yayi yasa itama ta yunƙura ta sauko tare da shigewa toilet ɗin,lokacin da ta fito yana ƙoƙarin tada sallar,sauri tayi ta ɗauki ƙatan tawul ɗin sa sabo ta rufa akanta, kana tabi shi yayi musu jam'i.


Acikin wannan daren kuma su Safwan suka cafke Sayyid,ba tare da sun bari wani ya gansu ba kamar yadda Oga Abdallah ya gargaɗe su,


Anty Nafisa fa da gaske ƙaramar yarinya tana neman buga wasa da ƙwaƙwalwal war ta,so sai shawarar Bintu ta shigeta tare da girgiza tunanin ta,har ji take yi aranta kawai ta fasa shirinta na saka cikin ƙarya tana ganin ma ta huta da sake-saken tsumma da fargabar samun akasi,amma kuma anya yarinyar nan ba wani ne yake ƙunsa mata wannan tunanin ba?amma kuma ai dama can tasan Bintu da tunani mai kyau, ko ita shine dalilin da yasa ta sakota cikin al'amarinta,duk da haka tayi mamakin ƙwaƙwalwar Bintu ko ita da ta kusan jika da Bintu batayi wannan tunanin ba, bayan kuma shine babbar mafita agareta,kai amma dai ita baƙaramar mai sa a bace na yadda batayi saurin sanar da Umar tana ɗauke da juna biyu ba,ashe wannan jinkirin alheri zai zamar mata, gaskiya ta jin-jinawa basirar Bintu.

ɗan bin ɗakin tayi da kallo tana wani irin murmushi me cike da jin daɗi,tasan zata samu abin da takeso saboda mijin ta bai iya ɓoyo ba, dan haka tana da yaƙinin cewa bazata sha wahalar haɗa muhimman kadarorin sa ba,wani tunani ne ya faɗo mata wanda yasa ta ɗan cizan yatsa, ko wane abune Bintu zata gaya mata ta fasa? tabbas a kwai ayar tambaya akan wannan lamarin akwai abinda Hajiyarta ta gargaɗi Bintu da kar ta gaya mata shi,to meye wannan dahar Hajiyar ta zata iya munafuntar ta akan sa wane abu take son ƙullawa batare da sanin ta ba?wata zuciyar tace da ita kin manta halin ladidine? komai fa A kace ta aikata indai akan kuɗi ne tabbas zata iya ai katashi,to amma meye na ɓoye mata?wani ɓangare na zuciyarta ya kuma cewa da ita a'a Nafisa karkiyi saurin yanke hukunci ki bari ki lallaɓa Bintun ta sanar dake abinda yake da akwai, daga baya saiki yanke hukunci,da wannan tunanin ta tashi dan fara binciken abinda ya kasan ce shine burinta da buƙatar ta,


Wai shin ina Abigirl ta lula ne? Tunda ta tafi garinsu can inugu bata ƙara waiwayar Abuja ba balle kuma tunanin mijin ta, ita dai kawai tunda tana ganin ta tsira da rayuwar ta to shike nan,sai dai abinda bata sani ba shine,tuni Dady jafar ya sanar da Abdallah yana zargin Abigirl amma bai sanar dashi ainahin abin da ya saurara daga gareta ba, dan yasan Abdallah idan ya sani ba lallai ne ya barsu subi aikin A sannu ba,cikin zafin zuciya zaibi lamarin na Abigirl tunda dama yana ciki da ita Abigirl ɗin,kuma hakan da zaiyi, shi zai ƙara bawa makiyan su damar da zasu iya cutar dasu ba tare da sun ankaraba,dan haka ya ɓoyewa Abdallah komai,shi kuma Abdallah batare da ɓata lokaci ba yasa akabi masa bayan Abigirl tare da ɗauko masa duk wani bayanan ta, da duk wani motsinta.

Shi Dady jafar so yake sai Abigirl ta sakan kan ce kawai sai su sa aɗauko ta, dan ta amsa tarin tambayoyin da shima yake matuƙar buƙatar jin su daga gareta,lallai ya zaƙu yaji yadda akai tasamu Fatash wanda A yanzu ya koma Abdallah?kuma waye suke waya da shi?meye burinta akan Abdallah? me yasa kuma take ƙoƙarin kashe shi a halin yanzu? tunda tace kasheshi shine marufar asirinta,kuma gashi duk da haka sai da abin da take gudu ya faru,wanda shine dalilin da yasa tayi masa ƙaryar mutuwa ta gudu garin su?ɗan ƙara gyara kashingiɗar sa yayi tare da cewa, afili tabbas komai ya kusa ƙare muku duk wani munafiki an kusa yin walƙiya dan muga fuskokin ku,asirin ku duk ya kusa tonuwa,ɗan zakin da suka hana shaƙar numfashi tare da iyayen sa to shi zai ruguza tasirin su da duk wani makircin su,insha Allah lokaci ya kusa,shi kan sa ya ƙagu yaga ɓaƙaƙen fuskokin su,badan farin ciki ba sai dan san ganin ƙarshen su, insha Allah ƙudurar Allah ta kusa baiyana.


Akan idon Taufiƙa Bintu ta fito daga sashen Abdallah, jikin ta sanye da rigar baccin da yabata ta saka a daren jiya,Bintu da ta fito a saɗaɗe dan kar inno ta ganta, sai tayi turus ganin Taufiƙa zaune akan kujera tana watso mata wani irin kallon tsana mai cike da ɓakin ciki mara misali,A hankali Bintu ta ɗauke kanta tare da cigaba da ta kawa dan isa ga ɗakin ta,tsayuwar da Taufiƙa tayi agaban ta shi yasata ɗan ja da baya tare da zubawa Taufiƙa ido kamar yadda itama Taufiƙan take bin duk ilahirin jikin Bintu da kallo na tsan tsan tuhuma da san gano wani abu, Bintu gefe taja da niyar canja hanya da sauri Taufiƙa ta wani sa hannu ta finciko ta ta dawo baya,tana wani irin huci na tsan tsan baƙin ciki da hassada, Bintu tsayawa tayi tana kallon ta cike da jiran ko takwana dan ta ɗau alwashin ta daina ragawa kowa dake cikin gidan, dan da hakane kawai zata samu ƴancin yin abinda ya kawota batare da tunanin wasu shirgin ƙwarƙwata ba.


"Ke mahaukaya ƴar talakawa matsiyaciya,macijiya mai saran ƴaƴan masu gida da mugun dafin da yafi na kowace macijiya zafi da raɗaɗi,kinzo kin kanai naye wa mutane gida sai kace ramin macijin ubanta da na uwarta masu saran ɓoye,su noƙe su nuna tamkar basu taɓa saran ko wane ɗan adam ba,to ina mai tabbatar miki da cewa muddin baki fita hanyar ahlina ba saina kassara rayuwar ki yadda nan gaba bazaki iya moruwa ko ga makaho ba balle mai ido da cikakken lafiya,zan tabbatar miki da abinda nake faɗa in dai har baki san inda dare yayi miki ba!'wani mugun kallo Bintu take bin Taufiƙa dashi har ta kammala zantukan ta cikin wani irin huci da sauke numfashi,tsaki Bintu tayi tare da cewa,me kike da suna Taura ko Tofi? to inaso ki sani duk abinda kuke yi ba wai dan kun gagari Bintu bane yasa ta kasa yin komai ba, a'a sai dan ina da manyan kune ku kun yi min ƙanƙanta A sarah sai dai na sari na sama daku domin yaƙi na dasu nakeyi bawai daku ƙananan marasa kunya da abinyi ba,tabbas Ni macijiya ce amma inaso ki ɗan da ɗan lokaci dan in tabbatar miki da hakan, Taufiƙa Ni macijiya ce wadda idan tayi sara sai dai mutum ya mutu ko ya na ƙasa amma ba dai a warke ba,idan kina buƙatar sarana to ina so kibi ayari domin abin layin markaɗe ne bai zo kan ƙaramin kai irinki ba,idan na gama da manyan kawuna zan tsaya na saurare ki,kuma kisha kurumin ki ki daina haƙilo shi wanda kikeyi dan shi wallahi ko fuskarki ba zai tan-tance ta cikin ahlin ALHAJI BALARABE ba balle yayi miki duba irin na zumunci balle kuma duban soyayya, Oga Abdallah yafi ƙarfin ki dan ba dan irinku Aka halicce shiba Allah ya halicci bawansa Abdallah don mata masu kyakykyawar zuciya da tsoron Allah da kuma taimakon bayin Allah, zuciyar Oga Abdallah ta zinare ce ke kuma ta gawayi,to gaya min tayaya wannan haɗin gambizar zai yuwu,dan haka ki sawa zuciyarki shidin ba abokin rayuwar ki bane dan insha Allah Allah ba zai yi masa wannan jarabtar ta Auren ki ba ko iri-irin ki ba,ina so ki cigaba da saka ido akan wannan wasan Ni kuma insha Allah zanyi miki addu'ar tsawan kwana domin kiga ƙarshen wasan wanda zai zama gaskiya Abdubint for ever,ya kika gani?Taufiƙa ki kiyayi ranar na dama ranar da nasani ranar da sirrin ɓoye zai fito ranar da fuskoki da yawa zasu baiyana suna masu kaico da rayuwar da suka shuka,ki kuma kiyayi ranar da ƘUDURAR ALLAH zata baiyana,dan haka ina mai baki shawara da ki tuba tun kafin ranar dan karki kasance,cikin masu danasani wadda zata zamar miki ƙeya,kuma zaki kasan ce cikin mutanen da saran da nayi musu shi kaɗai ya isheki ba sai na kai ga asarar zubar da dafina ba!'har zata wuce sai kuma ta ɗan juyo dai-dai saitin kunnen Taufiƙa wadda ta tafasa kamar wuta saboda zafi da mamakin kalaman Bintu wanda suka matuƙar sakata cikin ruɗani da shakku mai tsanani akan Bintun,tace"abinda na manta ban gaya miki ba shine dafina baya cin wanda ya tsaya ga Allah ya kuma kiyaye dokokinsa,dafina ya tsaya ne akan mugaye ɓaragurbi masu ɗoyin baki da ƙwaƙwalwa,daga haka tayi shigewar ta ɗakinta tare da banko mata ƙofar da ƙarfi saboda ƙara tura mata haushi.


Tabbas idan taufiƙa tace"maganganun Bintu basu taɓa ta ba tayi ƙarya,sosai kanta ya kulle tare kuma da san neman ƙarin haske ga kalaman Bintun wanda suke kama da magana mai harshen damo,a kwai manufa A cikin kalaman Bintun,cikin mutuwar jiki da zuciya taja jikinta ta shige ɗakin su.


BaTaufiƙa ka ɗai ce ta shiga halin rikicewa da kalaman Bintun ba,hatta da Abdallah da Hajiya Babba da ta kawo kai dan sanarwa inno kiran gaggawar da ya same su daga Alhaji Baba sai da ta shiga wani yanayi na matukar zurfafa tunani,kasa shiga falon tayi ta koma saboda bazataso wani yaganta cikin wannan hali na kiɗima ba.


Tun dawo war sa daga masallaci da ya wuce tiraning sai lokacin ya shigo, wanda shigar sa ke nan kunnuwansa suka fara jiyo masa kalaman Taufiƙa, tsaki yayi zai wuce saboda bai ga amfanin sauraren shashan cin Taufiƙan ba,amma kafin ya saka ƙafar sa cikin falon sa ya tsinkayo ɗaɗdaɗar muryar Bintu tana maida wa Taufiƙa Raddi cike da kar sashi da kuma san zuwan wata rana mai ɗinbin tarihi agareta,tabbas shima ya shiga halin rikicewa da wannan sabon Al'amarin, tabbas ya daɗe yana tunanin abinda Bintu takeyi bai ci ace wai dan taimakon musulunci kawai take ba, idan yayi duba da ranar da ta bashi tabbacin zata taimaka masa da dukkan rayuwar ta,tabbas ranar ya hangi yadda wutar fansa ke ci a tsakiyar idanunta,to ga kuma wannan kalaman nata masu shige da har shene damo,meye gaskiyar tarihin wannan yarinya meye gaskiyar,abinda ya kawota ahlin nan?kai akwai wani abun da Bintu ta ɓoye wanda ita kaɗai tasan shi sai Ubangijin ta,ta yaya zaiyi ya gano wannan gaskiya da ta ɓoye masa?anya kuwa Bintu bata da alaƙa da ahlin ALHAJI BALARABE?dafe kansa yayi A yayin da yake zama ƙasan carpet ɗin dake malale tsakiyar haɗadɗan falon nasa,tare da runtse idanun sa,wai meye yasa abin mamakin cikin gidan nan baya karewa?kafin ya gama da wani al amarin wani ya taso, tabbas al al'amari Bintu wani babban al amarine da dole sai ya nutsu dan gano shi,kuma shi kaɗai zaiyi wannan binciken batare da sa hannun kowa ba kuma zai bar shi a matsayin sirrin zuciyar shi,


Hajiya Babba tunda ta koma ɓangaren ta take kaiwa da kawowa itafa a rikice take da wannan al amari na Bintu, tabbas A kwai wani ɓoyayyen sirri da Bintu take ɓoyewa,to me yasa takejin wani irin sabon kusanci A cikin jikinta game da Bintun? kuma tanaji ajikinta komeye agame da Bintu to Alheri ne,(Hajiya Babba macece mai matuƙar dogon hange da baiwa mai tarin yawa to ba wani abin mamaki bane dan shaidar Bintu jikar tace ta baiyana acikin jikinta da zuciyar ta duk da ita bata taɓa kawo wannan tunanin ba) amma tabbas tanaji ajikin ta Bintu haske ce ga ahlin ta kuma madubi mai haska baya,

"Zama tayi tare da ɗaga hannuwan ta sama tana mai addu'a tunda ga ƙasan zuciyarta har zuwa kan bakinta,ya Allah ka zama gatanmu kajiɓanci lamuranmu Ni da dukkanin musulmi masu tsoronka,ya Allah ka sakawa waɗanda aka aka zalunta ya Allah ka war ware mana ƙullin da aka ƙulla mai wuyar kwancewa,ya Allah ka tsare mu daga sharrin kiɗan shaiɗan ka kiyaye zuciyoyin mu daga faɗa wa halaka katsare mu da aikata saɓonka, Allah kakiyaye mu da aikin na dama kasa kar mu tozarta a duniya da lahira, Amin Ya Allah.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 37 ```



Wayar tace tashiga neman ɗauki, cikin nutsuwa ta shafa addu'o'in ta, tare da janyo wayar ta kara a kunnen ta,cikin girmamawa tace"Alhaji wallahi wani ɗan saɓani aka samu amma yanzu zan kuma gwada wayar tata idan batayi ba sai na koma ɓangaren nata!'ta ɗaya ɓangaren Alhaji Baba yace"kizo ai na samu wayar tata tuni ke muke jira, Hajiya Babba tace"to madalla gani nan tafe!'bayan ta ajiye wayar tare da tafiya dan amsa kiran megidan nasu, suji abinda yake faruwa da sammakon nan kuma.


Tana dosar coridon da zai sada ta da falon Alhaji Baban ta fara jiyo tashin Muryar Dady Mansur, a ranta tace"sababbe kaci kanka wato ma shine sanadin tarasu da wannan safiyar,to Allah Ubangiji ya shirya,ta faɗa tare da yin sallama cikin falon,amsawa sukayi gaba ɗaya kana sukayi gaisuwa a tsakanin su,cikin nuna halin dayake ciki na tashin hankali ya gaida Hajiya Babba, Dady Habib ma dake zaune ƙasan ƙafar Alhaji Baba yana ja masa yatsu ya gaida ta cikin tsananin biyayya, Hajiya Babba ta amsa fuskarta cike da ƙauna da kuma alfahari da yaron nasu wanda ya ya ƙwace girman Mansur tunda ya zubda girman to su sun ɗauka sun bawa Habib.

"Ɗan gyaran murya Alhaji Baba yayi tare da cewa kai Mansur tun yaushe ne baka ga shi Sayyid ɗin ba?cikin ƙara san zafafa abun yace" Nabil yace"sam baiga ya shigo jiya ba, ma ana dai bai kwana gida ba,da farko ma yayi tunanin yana sashena sai da aka idar da Sallah kana nake ce masa ina Sayyid,to shine yake sanar dani,gashi tun alokacin nasa aduban duk inda akasan yana zuwa amma babu wani labari!'ya ƙara sa maganar cikin yanayin fargabar abinda zai faru da ɗan nasa, Alhaji Baba yayi gyaran murya kana yace"to Ni dai aganina Sayyid ba yaro bane da za ace ya ɓata,sai dai wani abu daban dan haka Ni aganina mu jira zuwa jimawa idan bai dawo ba sai mu ɗauki mataki!'inno tace"gaskiya Alhaji Ni dai ashawarata gara ayi saurin fara neman yaron nan tun da kasan duniyar yanzu ta zama abin tsoro,ba zai yiwu ace har sai wani lokaci mu fara ne man sa ba,kuma dai kaga yaran nan duk runtsi sai sun kwana a gida,barantana muce sun saba yin irin haka!'tana ajiye maganar ta Hajiya Babba,ta ɗauka ita ma dai shawarar da ta bayar ke nan kamar yadda inno tace" ita kuwa Hajjah tayi musu kara amatsayin ta na kakar Sayyid,dan haka batace komai ba baya ga fatan Allah ya baiyana shi da gaggawa,Dady Habib yace"yanzu yaya katashi muje mu bayar da cikiyar sa gida jen ƴan uwa da abokan nan sa,idan ba a ganshi ba zuwa gobe sai mu sanarwa ƴan sanda,tun da yanzu bamu da tabbacin ɓata yayi kaga bai kamata muyi saurin sanar da ƴan sanda ba!'Alhaji Baba yace"to madalla hakan yayi, Allah Ubangiji ya kareshi aduk inda yake ya dawo mana dashi cikin ƙoshin Lafiya,Amin suka amsa gaba ɗayan su,daga nan Dady Mansur da Dady Habib suka fita dan fara aiwatar da abin da ya dace,Hajjah da Inno ma tashi sukayi suka koma sashen su kasan cewar yau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login