Showing 150001 words to 153000 words out of 184937 words

Chapter 51 - KUDURAR ALLAH COMPLETE BY FATIMA Y ADAM

21 Jul 2024

16900

ita bata taɓa sanin anayin fuskar wani asakaba,cikin ƙosawa Abdallah yake ɗan duban agogon hannun sa wanda yake traking ɗin in da mutum yake,lumshe idanun sa yayi wanda sai buɗe su yayi yaga mutane zagaye dasu an dasawa kowannen su bindiga,wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke,Muryar wani jami'in tsaro ne ya karaɗe wajen da cewa kar wanda ya motsa duk wanda ya motsa kuwa saina fasa kansa da bindiga! cikin mamaki Dady jafar yace"to me yakawo ku nan?ina tunanin gurin da ake aikata laifuka irin ku suke zuwa?to nan kuma naga tattaunawa ce tsakanin zuri'a ɗaya Dady jafar ya faɗa cikin nuna pretending!'Safwan da ya ɗorawa Bintu bindiga yace"babu ruwan mu da abinda kuke tattaunawa binciken mune ya nuna mana da akwai matsala babba a ta ɓangaren nan, dan haka gaba dayan ku abin tuhuma ne!'ya faɗa yana tafiya da Bintu wajen da Abdallah yake tsare da bindiga,yayin da Dady Mansur da Alhaji Rufa'i da basu san shirin su Abdallah ba hankalin su duk ya tashi,haka kawai Habib zai shafa musu jakar tsaba,cikin tsari da sanin makamar aiki suka dinga fita da yaran Dady Habib,sai da aka fita dasu gaba ɗaya sai shi kaɗai yayi ragowa, Abdallah yasa hannu ya ture hannun wanda ya ɗora masa kan bindiga kana yashiga takawa A hankali tamkar wani Basarake da yake kan ganiyar mulki,gaban Dady Habib ya ƙaraso tare da zuba duka hannayen sa cikin aljihunan dogon wandon jins dake jikin sa,wani irin kallo ya fara watsa masa wanda Dady Habib yajishi har cikin hanjin cikin sa,ganin Abdallah agaban sa baƙaramin kyarmar jiki yasa shi ba,tabbas kwarjinin Abdallah abun tsorone ga maƙiya da kuma marasa gaskiya,Dady Habib baisan sanda ya sunkuyar da kansa ƙasa ba,ya kasa haɗa idanu da shi,wani zazzafan huci Abdallah ya furzar kana cikin maganarshi mai fita ɗai ɗai da kuma salon iya sarrafa harshe,yace"Habibu ga ranarka nan, sakamakon ka kuma yana nan tafe,gashi dai ɗan zaki yazo har fadarka kuma zai tafi da kai cikin ƙasƙanci,kuma mutuncin da kake dashi zai zube a idon duniya,ina nan kuma zan aiko maka da ragowar mutanen ka da kuke aikata shirka dan babu wanda zai tsira a cikinku da izinin Allah!'yana gama faɗar haka yayi musu alama da su tafi dashi,hankaɗa ƙeyarsa Safwan yayi suka fita dashi cikin ƙasƙancin da yake gudu,bakin sa dai bai mutuma alwashi yake ci iri da kala akan sai ya ga bayan zuri'a Hajiya Babba gaba ɗayan ta.

Da wani irin gudu haɗe da kuka-kuka dariya dariya Bintu tazo ta waɗa jikin sa,ba su Dady jafar ba hatta Ni da nake sakaɗe abayan kofa sai da naji ajiyar zuciyoyin da suka sauke atare kamar an irga musu,riƙeta ya kuma yi ajikinsa yana shafa gashin kanta da duk ya watse a gadon bayanta,Dady jafar ne ya dubi Dady Mansur tare da cewa Mansur afuwa fa, saɓanin fahimta ne!'murmushi Dady Mansur yayi kana ya kama hannun Dady jafar yana cewa babu komai baka da laifi kai mutumin kirki ne, da duk mutane zasuyi koyi da halayenka da tabbas ansamu ƙaruwar jin dadi da zaman lafiya!'fita sukayi suna ƙara maida maganar.


A hankali ya kamata suka fara takawa yanayi yana duba lafiyar jikinta duk da ta tabbatar masa da cewa babu abinda ya same ta ko sukayi mata sai marikan da tasha,motar da su Abdallah suka zo da ita shine ya shiga shida bintu sai Safwan da zai ruƙasu,su kuma su Dady Mansur suka shiga wadda suka zo shida Alhaji Rufa'i da Dady jafar,cikin nutsuwa suka jero motocin suka fito daga wan nan mugun wajen.


A hankali ta matsa jikin sa tare da saƙala hannunta ta bayansa,ta kwantar da kanta A ƙirjinsa,ji take kamar wadda ta shekara ba tare da shi ba,ɗan tura ta yayi yana cewa matsa tsamin datti kikeyi!'a zubure ta ɗaga kanta tana kallon sa,sai kuma ta shiga ƙoƙarin ƙwace wa daga gareshi,riƙe ta yayi yana sakin wani sassanyan murmushi wanda yake fitowa tunda ƙasan zuciyar sa,da ta kasa ƙwacewa sai ta ɗago kanta dan yi masa magana,,,amma ina hakan ba ta samu ba sakamakon jin ya haɗe bakinsa da nata,a hankali cikin wani irin salo na ƙwarewar da bai san a inda ya sameta ba,yake sarrafa harshenta acikin bakinshi,tun tana son ƙwacewa har ta haƙura ta bada kai bori ya hau,sai da ya hango fuskar Safwan ta cikin miro kana ya ankarar da shi abinda yake gaban yaran sa,zare bakin sa yayi daga nata yana binta da wani kasalallan kallo,rufe fuskarta tayi akirjinsa tana tura baki,cikin gunguni tace"me yasa to kayi wannan bayan wari nakeyi?bai amsa mata ba sai kallon da yake ci gaba da yi mata,ganin haka kawai sai ta canja maganar ta,ta da cewa yanzu da Hajjo ta tafi da Dady ina zata kaishi?karfa ta kai shi ESTATE,bayan bamu shirya komawarsa yanzu ba?dan sunkuyawa yayi ya sumbaci goshinta kana yace"kar ki damu shi yasan yadda zaiyi zaiyi mata bayanin komai!'da wannan maganar ta gamsu duk da dai tanajin wani abu aranta game da tafiyar tasu,cikin sanyin murya ta kuma cewa dashi dan Allah ka kai Ni gidan Hajjo Ina son daukar wayana,kuma,,,,katse ta yayi da cewa shuru Malama da surutun!'tura baki tayi amma dai bata kuma cewa komai ba,

Ganin su A kofar gidan Hajjo ba ƙaramin farin ciki ya saka ta ba,sai dai kuma abin mamakin da suka tarar gidan babu kowa gashi abuɗe sakayoshi kawai akayi,cikin fargabar abinda zasu shiga su tarar suka shiga cikin gidan,a kideme Bintu ta kalli Abdallah tare da cewa to ina suka je dukan su haka?ɗakin Hajjo ta faɗa da gudu anan ta samu wayarta a yashe ƙasan ɗakin durƙusawa tayi ta ɗauka,cikin rawar jiki ta kunnata,tayi sa a kuwa da ragowar caji tunda mutuwa tayi,lambar da Anty Asma'u ta saka mata ita ta kira,zuciyar ta kuwa sai bugawa take saboda tsananin fargaba,ɗan matsowa yayi kusa da ita tare da kamata ganin yadda ƙafafun ta suke rawa, yace"Bint ki nutsu Mana me yasa haka da ruɗewa,tun kafin kiji dalilin barin su GIDAN!'kar ɓar wayar yayi yasaka ta a amsa kuwa,daidai lokacin da Anty Asma'u ta rangaɗa sallama,wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya suka saki atare kamar yadda suka saba,kana cikin nutsuwar sa ta kullum yace"Anty Asma'u mun dawo kuma bakwa nan!'da sauri tace"kai da waye?ina Batula hankalin mu ba akwance yake ba, Allah yasa kar kace mun ba a sameta ba? cikin ƙosawa da yawan maganar yace"tare da ita muke!'miƙawa Bintu wayar yayi ta karba da sauri tare da cewa'Anty Asma'u gani kuna ina ku?sai kuma taji Muryar Hajjo har da kuka tana cewa Alhamdulillah Allah abin godiya, Abdallah Allah yayi maka albarka tabbas kacika gwarzo kuma jarumi Allah Ubangiji ya taya maka ya dafa dukkan al'amuran ku,ya cigaba da kareku daga sharrin maƙiya da dukkan abin ƙi!'amin Hajjo me yafaru ne wai?'ya faɗa yana matsawa jikin Bintu don yaji maganar sosai,nan dai Hajjo ta bashi labarin abin da ya faru gaba ɗaya har yadda sukayi da yaran Anty Nafisa da Abba Umar,hamdala yayi,yana sakin murmushin farin ciki da nasarar da suke samu adukkan abinda suka tunkara, lallai Allah mai ƙudura ne,shi kaɗai yasan ta hanyar da zai kare bayin sa wanda suke tare da shi,cikin farin cikin da ya kasa ɓoyuwa akan fuskarsa ya da ɗa rungumo Bint jikin sa yana cewa to Hajjo Allah abin godiya ne ko da yaushe agaremu Allah ya ƙara wa Annabi wasila da fabila,gaba ɗaya suka amsa da Amin,Bintu tace"Ni kam ma Hajjo dama kukan gulma kikeyi bana rashina bane,tun da gashi har yanzu kin kasa yimin magana!'ta faɗa tana share hawayen da ba wahalar zubo mata sukeyi ba,dariya Hajjo tayi cike da madaukakin farin ciki,tace"wace ni naƙi kula ƴar lelena,mijin nawa ne dole na tsaya na yabeshi dan ya cancanta!'ɗan kallon Abdallah tayi wanda yake ta zuba mata wani munafukin murmushi da kallon da yake haifar mata da mutuwar jiki,abinda ya shiga yi matane yasa ta fara yiwa Hajjo in ina, tace"haj,, haj, Hajjo to zamu taho inda kuke kiyi mana kwatan ce!'karɓe wayar yayi yana cewa Hajjo ba yanzu ba kin san dai abinda nake shiryawa,dan haka sai mun sake waya!'daga haka ya kashe wayar, yana yiwa Bintu sigina A lokaci ɗaya kuma yana cigaba da yimata tafiyar tsutsa a gadon bayanta,kanƙame shi tayi jikin ta na wani irin rawa,cikin rawar murya tace"Ni Ni dai mu tafi gida!'cikin hura mata iska a kunne yace"nan A daji muke?a bazata taji wani irin sanyi cikin kunnen ta, ƙafin ta dawo hayyacin ta, Abdallah ya shiga tsotse kunnenta loko da saƙo,wani irin kyarma jikin Bintu yake yi, wannan abun da Abdallah yake mata wani baƙon al al'amari ne a gareta wanda take, taji duk wata tsiga dake jikinta tana miƙewa cikin biyayya da karban saƙonnin da Oga Abdallah yake basu,bata gama kiɗimewa ba sai da taji hannuwan Abdallah biyu akan nn,ta wanda yasa ta kusa shiɗewa,

Ringin ɗin da wayar ta tayi shi ya dawo dasu hayyacin su duk da cewa Abdallah yaƙi sakin ta,ganin lambar Dije ya sa ta ɗauki wayar da sauri,ajiyar zuciyar da Dije ta saukar shi ya shiga kunnuwan ta da Abdallah yayi musu wankin babban bargo da miyansa,Dije tace"Bintu ina kika shiga haka kwana biyu nayi kiranki har na fidda rai da samun ki!'Bintu tace"Dije na shiga matsala ne amma yanzu komai yayi daidai,ya ake ciki kuwa?Dije tace"sakon da nake ta son baki ke nan,amma yanzu a gurguje abu ɗaya mafi muhimmanci zan gaya miki sauran bayanin sai mun haɗu!'Bintu tace"ina jinki!'Dije ta ɗan ja ajiyar numfashi kana tace"kin san wacece wannan matar Bintu?cikin fargaba, Bintu tace"wallahi ban sani ba Mama Dije!'Dije tace"abin da matukar mamaki da ɗaure kai,ba kowa bace wannan shu'umar matar ba sai Hajjah matar ALHAJI BALARABE ta biyu,kuma uwa ga ALHAJI Mansur da Alhaji Habibu.......

Ɗit ɗit ɗit .... FATIMAH Y ADAM✍🏽

More Comment
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 55 ```


Wayar ta saki, ta faɗa ƙasa,ita kuma ta koma jikin Abdallah saboda jirin da ke neman kayar da ita,riƙe ta yayi,kana cikin taushin murya yace"Bint calm down Mana me yasa bakya ɗaukar abu da sauƙi? cikin kukan da yake tasan ƙwace mata,tace"ya Abdallah ta tafi da Dady fa,kuma kasan fa ita ma tana son ta ɗauki dimon ɗin nan,dan haka zata iya cutar da Dady!'A hankali ya shiga jijjiga ta kamar wata ƙaramar jaririya,sai da yaga ta ɗan nutsu kana ya kai bakinsa saitin kunnen ta yayi mata raɗa, wanda hakan yasa naga ta saki wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya tare da kuma ƙankameshi har da guzurin wani sassanyan murmushi,shima murmushin yayi tare da kama hannun ta suka fita daga gidan,kullewa sukayi kana suka dau hanyar komawa ESTATE,


Cike da farin ciki suka isa gidan da ta ajiye su Laila,shi dai Dady Abubakar yana kallon ikon Allah ne kawai amma baice komai ba, tun daga yadda suka ɗauke hanyar shiga cikin gari yasan cewa akwai wata manufar,

Fito dashi sukayi suka tura shi har zuwa cikin dakin da aka ajiye fafi,daga nan Hajjo ta yi musu kashedi da jan kunne akan su kula su kuma kiyeye kar suyi saƙen da zata rasa Abubakar akaro na biyu akan sakacinsu, dan akan wannan bazata taɓa raga musu ba, saboda samun Abubakar shine cikar burinta,da wannan kashedi ta tafi ta barsu da niyar sai gobe zata dawo saboda yanzu dare ya raba kuma bata son shirinta ya wargaje na yadda zatasanar dasu kufcewar ABUBAKAR daga hannun ta.


Kai tsaye falon inno suka nufa,wani abun tausayin inno suka tarar tare da Hajiya Babba daga dukkan alamu ko da rintse basu runtsaba,gaba ɗaya hankalin su atashe yake,da gudu Bintu ta ƙarasa ta zube jikin inno kana ta koma jikin Hajiya Babba wani shaukin kaunarsu ne ke da ɗa kwarara cikin zuciyarta,inno ta dubi Abdallah dake zama kusa da ita cikin damuwa da kulawa tace"Abdallah ina kuka shiga kwana biyu hankalin mu duk ya tashi? tun ranar da kayi min waya ban kuma jin duriyarku ba!'Hajiya Babba ma saka mashi idanu tayi suna jiran amsar da zai basu, jingina yayi da jikin kujerar da yake zaune tare da lumshe gajiyayyun idanun sa,kana A hankali yace"inno na gaya miki aiki ne ya fitar damu shine na tafi da ita!'kallon da suka ci gaba da yi masa ne ya tabbatar masa da cewa basu gamsu da abinda ya gaya musu ba,hakanne ya sa shi mikewa cikin nuna gajiyar dake tattare dashi ya nufi falon sa,da kallo suka bishi har sai da ya shige kana suka dawo da duban su kan Bintu dake kwance jikin Hajiya Babba idanun ta alumshe da alamun dai itama da gajiya da kuma bacci atare da ita, a hankali Hajiya Babba ta shafa kanta tare da cewa Bintu me ya same ki ne haka dubeki kamar wadda aka tsamo cikin shara duk kayanki sunyi datti ga idanunki sun faɗa,wai ina kuka je ne haka da kuke ɓoye mana?kallon jikin ta tashigayi wanda ta riga tasan ya Abdallah bai tsammaci zaiga su Inno a nan ba da tabbas bazasu shigo a haka ba,murza idanunta ta shigayi ta rasa abin cewa,kallon juna su Inno sukayi kana inno ta kuma dawo da dubanta kan Bintu tace"Bintu na nasan da akwai abinda kuke ɓoye mana kawai dai kuna tsoran faɗa ne saboda sirrin junan kune!'cikin sauri Bintu tace"a'a inno kar zuciyar ki ta raya miki wani abu mara kyau,sirrin mu sirrin kune,koda babu dangantaka tsakanin mu zan iya fada muku sirrina!''kallon da taga suna zurfafawa akan ta ne yayi saurin ankarar da ita katoɓarar da tayi,dan haka cikin dabara ta sauya zancen da cewa,inno wallahi kun riga kun zama dangina kuma iyayena shi yasa har nake manta koni wace a gurinku ji nakeyi tamkar nima daga tsatsan ku na fito dan haka babu wani sirrina da bazan iya sanar daku ba,amma kuyi haƙuri ku bamu lokaci!'ta ƙarasa faɗa cikin marairaice fuska,Hajiya Babba tace"shike nan tashi kije kiyi wanka ki kwanta!'tace to tare da tashi sai da tabi kowaccen su da runguma ta tsantsan ƙauna da farin cikin basu zamo daga cikin taɓaɓbuba,kallo suka bita dashi ganin ta nufi falon Abdallah hankali kwance ba tare da tasan suna kallon nata ba,sai da taje bakin ƙofa kana ta juyo tare da huro musu sumbata,san nan ta shigewar ta tana kuma yi musu sai sa da safe, murmushi sukayi kana inno tace"Hajiya Babba ki wuce na rakaki dakin Alhaji!'Hajiya Babba tace"yi kwanciyar ki ba sai kin raka Ni ba abinda ta kofar falonki kawai zan shige!'inno tace"to shike nan Allah ya tashe mu lafiya!'amin Hajiya Babba ta amsa tana shiga falon Alhaji ta falon inno, sai dai dukka su zuciyoyin su cike take da damuwa akan al'amura masu yawa, dake wakana acikin gidan kwana biyu.


A zaune kan sallaya ta tarar dashi kamar yadda ta tafi ta barshi,zama tayi a gefan gadon har ya shafa addu'a itama ta shafa, cikin nutsuwar sa ya juya ya dubeta kana yace"sun dawo?tace"sun dawo amma alamu ya nuna a kwai wani abu da suke ɓoyewa a junan su!'nan dai ta gaya masa yadda sukayi da su Bintu,ta ɗora masa da cewa, wallahi Alhaji haka nan nakeji araina kamar da wani gagarumin abu dake shirin faruwa acikin gidan nan,kuma zuciya ta tafi raya min Alkhairi shi yasa nakejin wani irin farin ciki!'murmushin su irin na kamilan mutane yayi,kana yace"kice munyi ɗaya dake amma Ni dai farinciki na baya rasa nasaba da irin mafarkan da nake yi da Abubakar wanda nake ganin sa cikin halin jinya amma duk kwanan duniya idan na kumayin mafarkin to sai na ga samun sauki da lafiya a tare da shi, kuma inaji ajikina ya kusa dawowa garemu,sai dai kawai mu cigaba da tsananta addu'a akan lamarin!'Hajiya Babba tace" hakane Allah ya shige mana gaba!'...


Turus tayi ganin Dady Mansur zaune a falon ta, ya zuba ta gumi kana ganinsa kasan yana cikin damuwa matsananciya,
cikin sanyin jiki ta ƙaraso cikin falon sai kuma duk taji damuwa da tausayin MANSUR ɗin ya kamata,tasan damuwar da yake ciki bata rasa nasaba da halin da ɗan uwansa ya shiga,to yake nan zaiji idan yaji cewar uwarsa ma tana daga cikin waɗan nan mutanen masu matukar san zuciya da san abin duniya?wane irin hali zai shiga duk ranar da ta bayyana cewa mahaifiyar sa munafuka ce mai fuska biyu?kai ina bata ma fatan zuwan wan nan rana, baza ta taɓa bari hakan ta faru ba,duk yadda zatayi zatayi dan rufuwar asirin ta,baza ta bari ta tozarta gaban mutanen da suke matukar ganin girma da darajar ta ba,zama tayi a kusa dashi tare da dafa kansa cikin san cire damuwa da fargabar da suke san rufeta tace"Mansur ya haka da zama mai makon kaje ka kwanta ka huta sai kazo ka zauna anan, ko kana nufin kwanan zaune zakayi?wata irin ajiyar zuciya yayi cikin sanyi jiki da murya yace"Hajja bazan iya bacci ba,ba na yau kawai ba har da na gobe da jibi,abun nan bazai taɓa fita daga raina ba,na dade ina tuhumar kaina dalilin da yasa ina ganin ana aikata ɓarna amma bazan iya kataɓus akan hanawa ba,Habibu ya cuceni ya cutar da ƴan uwan taka yaci amanar zumunci!'ya faɗa wasu zafafan hawaye na zubowa daga kwarin idanun sa, cikin mamaki Hajjo tace"kana nufin tun tsawon lokacin nan kasan abinda Habibu yake aikatawa kuma kasan ABUBAKAR yana hannun sa?jinjina kansa yayi tare da cewa tabbas Hajjo Ni ganaune kuma jiyau akan dukkan abinda Habibu yake aitawa,sai dai kuma sanin nawa bai da wani amfani tunda baiyiwa ɗan uwa na ABUBAKAR rana ba!'Hajjah tace"meye dalilin ka na rufawa wannan bugun asiri?cikin damuwa da tsananin takaici yace"Hajjah ban sani ba,amma yanzu na sani,nasha yunƙurin zuwa dakin nan dan fito da Abubakar amma sai hakan ya gagara,wanda nasan hakan baya rasa nasaba da ƙarfin sihirin dake tare dani ko nace tsafi dan yanzune nake da tabbacin Habibu tsafaceni yayi,nasha yunƙurin zuwa gurin, wanda tasanadin haka da yawa mutanen gidan nan suke zargina da alaƙa da wannan ɗakin,ranar da aka sace Sayyid ma nayi tunanin shine ya ɗauke shi saboda yasha min kashedin idan ban daina yunƙurin zuwa dakin nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login