Showing 99001 words to 102000 words out of 124070 words

Chapter 34 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

333

yabon kyan bayan kyan da hular da masa

Bakinsa ya dan tabe ya juya ya nufi baban falon da yake kyautata zaton a cen suke iyayen, domin gidan dai ba wani mai hargitsin gine gine bane

A hankali ya saka hannunsa ya tura kofar da salamar dake saman lebensa a lokacin da kunnayensa suka jiyo muryarta ta daga tana fadin" Auta walahi kar ki shanye min tuwon madarana, kin sha naki fa, bara na sauko daga doguwar kujerar nan na tardoki malama baki san hanyar kicin bane ki je ki yi naki mana........"

Daga ciki yake jiyo muryar Auta itama sama sama tana fadin " ki dirko mana ke da sai na tayaki sauka aman kulun sai kin taka kin hau, ba zan daina din ba ki yi abinda zaki yi , abin ne da dadi NURIYAH"

Dan kiciniya ta so yi dan sauka daga saman kujerar dake da tsayi sosai wace tana wajen ne dan ajiye litatafai ba dan hawa ba aman ita kulun sai ta taka abu ta dane sama wai dadin zama a samanta take ji

A hankali yake sake kallonta yana idasa shigowa ya nufi inda take zaunen
Wando ne dogo blue na jins a jikinta sai riga wace ta sauko mata har gwuiwarta, sai dai mai laushi ce sosai rigar

A hankali yake kare mata kallo gashinta a fili tana kara kiran Murjanatu da fadin ta zo ta kama mata kujerar ta sauko sai su raba tuwon madarar

Juyowar da zata yi idannuwanta suka shige cikin nasa a haukace ta diro kasa kan kafafuwanta tana zarro idannuwanta da sake kura masa ido hankalinta na neman tashi

Kansa ya so kawarwa sakamakon kirjinta dake sama yana kasa, da kuma kusancin da suka samu mai matukar wahala, sai dai ji ya yi ya kasa dan haka da sauri ya dawo da shi a saitinta ya kafeta da idannuwansa masu sakata barin jiki

A hankali ya kamo hannayenta ya karaso wajen kujera da ita gannin wajen da zata dafa take nema ya zaunar da ita a saman babar kujera mai tudu kadan kafin ya sake zubawa kafafuwanta ido da take ta murzawa kanta a kasa ta kasa kallonsa cikin ido dan dimuwa

A zabure ta zuba masa manyan idannuwanta a lokacin da ya kai gwuiwoyinsa saman kafet din ya masu irin tsugunin da ake saka yaro yi a school idan ya yi laifi, ya dauko hannayen nasa ya sake dora mata a saman cinyoyinta yana kallon irin kallon da take masa mai cike da fasarori kala daban daban

Sai da ya lumshe idannuwansa a hankali ya sake dubanta, muryarsa a fice zarrr yana dubanta ya furta" WILL YOU MARY ME NURIYAH?"

A yau sai da ta gwamace dama bata zurfafa a neman koyan turanci a harshenta ba, da ta tabata cikinta ba zai cure waje daya ba ta ringa ji kamar zata saki wani lamarin da idan har ya fito daga cikin ba zata kuma koda hada hanya da wannan bawan Allah ba bale har ta dube shi ido cikin ido,

Gannin ta yi shiru ya saka shi dan matsa cinyarta ta dama yana sake fuskantarta ya ce"



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
5?? 6??


Gannin ta yi shiru ya saka shi matsa cinyarta ta dama hankalinsa na nuna alamun zai tashi ya sake fuskantarta sosai inda kanshin turaren jikinsa da na bakinsa ke dukanta du idan ya budi bakinsa ya ce" Ki bani amsa, kar ki min shiru a matsayin amsa"

Hannayenta ta sake dunkulewa ta budi bakinta da nufin yin magana sai kawai t shiga inda inda

Hakan ya saka shi a tunani da rikita

Ya sasauta muryarsa sosai ya dago habarta yana kallonta a sanyaye ya ce" Shi kike so? NURIYAH shi kike so? Don't tl me yes i bg u........."
Sai kuma ya sakar nata habar ya kai hannunsa wajen goshinsa ya dafe, ya sake saki ya ce" Ba zai taba baki kulawar da nake tanadar maki a rayuwa ba.....u seee zan raine ki da hannuna, zan yi ta rarashinki da kaina, zan barki har ki kai wajen da zaki iya fahimtar komai a kaina.......Nuriyah babu wanda zai iya baki soyayar da zan baki a rayuwar aure...........kar ki ce min shi kike so"

Hawayen dake idannuwanta suka fara zuba, bakinta na rawa ta ce" Sir"

"MU'AZAM, AM MU'AZAM PLZ" ya fada a sanyaye yana kallon lebenta dake bari

Idannuwanta ta lumshe hawayen ya shiga bin kumatunta ta girgiza kai a haukace ta ce" Tausayina kake ji? Me yasa? Tausayi nake baka? Shine zaka rufan asiri ka zamo sirina? Aure fa kake cewa? Ni a wa? Ni a y'ar wa? Dan Allah dan Allah kar ka.......""""""""""
Idannuwanta gaba daya ta firfito a lokacin da ta ji wasu irin lalausan abubuwa a saman lebenta, lokaci daya ta dauke wuta ta ji ta saki fitsari a zaunen da take sannan cikinta ya bada wani kuuuuuuuu dan tsoro a tunaninta harda oga ba jira ta saki a lokacin da ta ji wasu irin tausasan lebunna sun cafki nata lokaci daya ya shiga bata wani irin lamarin da bata taba tunanin ana yi a duniya ba , duda bakinsa saman leben nata aman sai komai ya so kwonce masa har sai da lalausan hannayenta ke neman tura shi ya zarro idannuwansa ya zuba a cikin nata yana mata kallon da take masa lokaci daya kuma ya tsayar da abinda ya fara idannuwansa lumshe

A hankali ya shiga raba lebensa da nata kafin ya cire kwata kwata yana kallonta da irin kallon da take masa

Kunya, kunyar da bai taba ji a duniyarsa dan ya yiwa mace haka bane ya ji tana neman hanna shi kallonta cikin ido, a hankali ya kara ja baya ya zauna ya jingina da kujerar yana jan hularsa baya dan jin zufa na sin karyo masa

Ya kai mintina biyar a haka, wajen ya dauki shiru harta da muryar Murjanatu ta jima da daukewa tunda ta leko ta ga yayanta duke gaban Nuriyh ta koma da gudu ta ringa kwaso shoki tana jira ta ga yau da me Nuriyar zata bilo mata

Da kyar ya iya bude bakinsa, inda makoloton wuyansa ya yi sama ya yi kasa sannan ya tsaya a wuyansa a hankali ya ce" I'm sorry , I'm sorry da wannan abin............ban zo da wannan niyar ba, nd ban saka haka a tsarina ba sai kin kai shekara talatin..........."

Ya dakata yana kallonta yana jin wata bukatar sake koma mata na bijiro masa ya ce" NURIYAH im so sry......but........but i cnt, ba zan iya kallonki na barki ki auri wani ba...............blv me na fi shi cencentar samunki......... .................................., Ki ce masu kin daina aurensa, idanma auren zasu miki su yi da ni sai ki ci gaba da karatunki har ki kai lokacin amsar auren.......kin ji?"

Bata da wani zabin da ya wuce ta amsa masa tambayarsa ta ta ji, dan so take yi ta summa a bayan idannuwansa, so take yi ya tafi sai ta summa, bata so ta summa a haka, da ido ta raka shi bayan ya sakar mata murmushin da ya sake kashe mata jikinta baki daya sannan ya mike tsayinsa ya kama hanyar ficewa yana tafia irin ta wanda ya gaji da wani abin, kamar wanda ya sha duka

Bata san kallon hanyar da ya bacewa ganninta take yi ba har sai da muryar Murjanatu ta fargar da ita a lokacin da ta saka ihu tana juyi tana ambaton sunnan da ya sakata tsatsareta da ido tamkar bakuwarta

Murmushin saman fuskarta bai gushe ba ta duka a gabanta itama like yayanta ya yi tana kallonta ta ce" ni na san soyayar da nake maki mai karfi wace ta zamto ta yan uwantaka da wani gagarumin sirri da Allah ya boye kanki a tare da rayuwata, na kasa yarda duda na jima da fara hasashen hakan a cikin raina, u see kowani laifinki yafafene a wajensa, kowani motsinki abin kallo ne a wajensa, bafa dan bai isa ya salameki ba a ranar da kika zuba masa ruwa ya kyaleki, ba kuma dan rigimar hajia ba, a lokacin ni bana nan Hajia ta fara fada min yau ta ga wani baban lamari kuma bako a tatare da shi, tun a lokacin na takurawa mamana cewa zan zo, zan dawo dan na hadu da ke, NURIYAH matansa da suka haukace da yawan masa tambayoyi masu girma a kanki dan sun kula dukkan motsinki sai ya rakashi da ido, kiri kiri yayanmu yake nuna kishinsa a kanki NURIYAH"

"Ki yiwa girman Allah ki rufa min asiri da wannan maganar Auta, ki rufa min asiri da ita, kina ji wai abubuwan da ya fada kuma kuma ya...???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?.........." Sai ta samu kanta da kurawa waje daya ido sai kuma hawayenta da suka ki tsayawa sunna zuba shafshafshaf kamar an bude pampo ta ce" ina shi ina ni? , Auta ina shi ina ni? Yace wai za'a min aure na nuna bana so wai wai wai shi............. " Sai ta fashe da kuka tana yarfe hannayenta

Salamar mama Husaina ce ta sakata son hadiye kukan nata aman ta kasa domin ita kam tabarariya ce dama da kakarta, idan ta sha wahalarta tana fada mata tana hawaye ita kuma tana rarashinta kamar wata yar baby

"Subahanalah, Daughter wht happen?" Mama Husaina ta fada tana ajiye jakar hannunta saman table din dake falon tana nufarsu, daidai ana shigowa da kayayakin da suka je siyowa wajen bagwariyar matar da suka yi da ita zasu zo da sasafe dan fara hade hade kayan gyaran da suke da niyar yiwa y'ar ba tare da ta san dalili ba

Kanta take girgizawa a lokacin da suka yi ido hudu da su harda mahaifiyarta

A hankali ta mirgina ta tashi tsoro cike da cikinta na tunanin a dazu ta ji wani zirrrd a kasanta sannan tana jin dan jika kadan a jikinta kar a ga ta yi fitsari

Da sauri ta nufi dakinta ta shige ta nufi bayi ta barsu a nan a lokacin da Murjanatu ta shiga labartawa mamanta abinda ya faru

Da mamaki ta ce" Babyna kin tabata shine ya zo ? Kuma har kuka ji haka?"

Da dukkan gaskiyarta take tabatar mata da hakan, Mama Hasana ta samu kanta da sauke ajiyar zuciya a boye, ko ba komai yanzun ta san koda ba so akoy kula, ta kuma tabata za'a so yar tata dinma a hankali bi'izinillah, abinda ya fi dan damunta a kan kudirinsa na mace sai ta kai kaza ko kaza din nan ne ke dan damunta, sai dai abinda y'ar uwarta ta fada mata kan sakata jin kwarin gwuiwa harma itama zata saka kai da fata ta gabatarwa da NURIYAH abubuwan da ta koya a zamantakewarta da mutanen arziki, ciki zasu fara gabatar mata da wankin mara ne, su yi mata na sanyi, sannan su karra gyara mata fata domin b fari da kyalkyalin fata kawai ba ake so, ana son fata mai dumi da laushin gaske
Dan murmushi ta yi a lokacin da ta tuna tsumamen sabulun da za'a hadawa yarinyar tata wanda ta tabata idan har ta yi anfani da shi koda na kwana biyar ne sai an ga cenji mai girman gaske

Albishirin da Mama Husaina ta yiwa Murjanatu sannan ta ja kunnenta kar ta kama bakinta ya sakata kusan haukacewa, a nan ta shiga rigimar ba zata yi taro ba? Ba zata yi party kala kala ba? Rigingimu dai irin na tabarariya a gaban mamanta tana tarota

Murmushi Mama Hasan ta yi ta masu salama kan zata leka mai gidanta ya zo su gaisa kafin iyayensu su dawo, dama sun fita ne wani uzurinsu suma a yau din

Tun daga wannan ranar Nuriyah bata kuma samun labarinsa ba bale ganninsa, haka kuma babu wanda ya tada mata maganar nan ciki harda Murjanatu, sai dai ya mata kaka gida ne a kahon zuka, idan me take yi sai ta zabura ta tina abinda ya faru tsakaninta da sir Kan Giwa
A haka take amsar gyare gyaren da bata fahimtar komai a cikinsu, abinda ya hannata tambaye tambaye gannin harda Murjanatu ake gyarawa, duda bata san cewa banda ita ake ba abubuwan shan da ita ake bata ba, sai dai tana jin dadin abubuwan shan da take samu domin wani irin dadin mararta take ji fiye da tunanin mai karatu

A haka har ya zama saura kwana daya tak daurin aurenta

A ranar ne suka yi zama da kakarta domin a ranar kakanta ya bada umarnin a tafi da su gidan watau palace, dan kuwa ba a nan zai yi taro ba daurin auren kansa zai gabatu ne a baban masalaci

A gigice ta karasa dakin mahaifiyarta, a lokacin da take idasa ninke kayan Nuriyar da Hajia ta turo wa'inda za'a saka mata a goben tana mamakin kyansu da yannayinsu

Idannuwanta ta lumshe a lokacin da ta ji dumin jikin y'ar tata a bayanta ta rukunkumeta
A hankali ta saka hannunta ta rike nata tana dan shafa bayan hannun nata, muryarta a sanyaye sosai ta ce" Nuriy, menene? Kuka kike yi ne?"

NURIYAH kam shashekarta ta hanna mata magana

Mahaifiyarta a hankali ta ce" Bakya sonsa ne?"

Da mamaki ta dakata ta dago ta juyo gaban mahaifiyarta tana kallonta ta ce" Kennan kin sanni Umana?"

Murmushi ta yi mata mai taushi tana sake ninke kayanta ta ce" Tun ranar da aka yanke maganar na sani mana Nuriy, menene na tayar da hankali a nan?"

Nuriyah ta kamo hannun mahaifiyarta, ta yi kallar tausayi sosai ta ce" Mama, sir fa"

Ajiye ninkin ta yi tana kallonta da kallo irin na mamaki kadan, sai kuma ta ce" Haka zaki je kina kiransa da Sir? Ko shine sunnan sirrin da kika tanadarwa mijinki sirrinki ?"

Yanzun kam mamaki ke neman kasheta, ta kasa furta komai sai kikifta ido take yi a lokacin da mahaifiyarta ta ce" Kar ki zama kamar wata sakarai mana, ko wata wace ta rako mata duniya, yanzun ba koya maka kula da mijinka ake yi ba, Mu'Azam a waje yake soja, a dakinki mijinki ne Nuriyah, na san koda baki samu ilimin boko ba kin samu na adini, kin san me ake nufi kuma kin san me nake nufi......sannan kina da abokan zama, ba zan so ki saka shirme da kuka a gaba ba ki wayi gari ki rasa wacece ke balle wa kike aure, baki je da wuri ba baya nufin ba zaki rayu da mijinki ba, lalle gaskiya ne matarka ta farko itace malamarka, ama bai zama lalle ka ba kowace macen karatunta ba, kina da dama saka naki karatun a cikin wanda yake dauke da shi ta hanyar laluma, wani abin zaki same shi yadda kike so, wanin komai kwarewarki da iya zamanki da shi baki isa ki cenza shi ba, kalle ni da kyau! Jinnin mai dala an sanmu da hakuri da kawar da kai aman ba'a sanmu da zubar da makamanmu ba! U'r a mai Dala family Khalb, u'r a prncss, we lv u so much, nd muna nan tare da ke da addu'a da kwarin gwuiwa,yanzun ki fada min bakya sonsa ne?"

Ta jima tana kallon mahaifiyar tata da tunanin dama tana magana har haka? Har sai da ta maimaita mata maganar sannan ta shiga aaunata a zuciyarta
Ita kam gani take yi basu fahimta ba dan haka ta ce mata" Mama, ina ni ina siiii ina ni iba shi?"

Mamanta ta kureta da kallo ta ce" kin fi karfinsa ne?"
Da sauri ta girgiza kai tana zarro ido ta ce" Aa, Mama shine ya fi karfina, ina shi ina ni? Mama wacece ni? Idan gobe matansa suka san wanene mahaifina me zasu ce min? Shima idan ya ji wacece ni a me zai dubeni ?"

Mama ta tabe bakinta ta ce" ke ba shegiya bace NURIYAH, da mahaifinki bai yanka maki rago ba shi ya siyawa kansa............ni na yanka maki a lokacin da muka samu budi da Abanki muka yi sadaka, matansa su fada abinda yake bakinsu kema ki dube su ki rama domin ba zan baki damar ki ringa kuka gaban du wace ta zubar da girmanta ba! Wace ta zubar da girmanta ba zaki mace a yi mata kuka ba, sai dai ki mutunta wace ta mutuntaki ai kishi ba hauka bane!, Shi kuma da kike fadi ya rigayeki jin wacece ke kuma a haka yake so!, Wama ya ce maki namiji na fin karfin mace? Aljihunsa ko meye ne?"

NURIYAH ta ringa sauke ajiyar zuciya du hawayenta ya bushe a fuskarta, a lokacin da ta fito ta zata zata yi ta kuka ne har kanta ya fashe, sai dai abin mamaki kukan nata ya koma hira mai dadi tsakaninta da mahaifiyarta wace bata taba sannin ana iya yin haka ba, bata taba tunanin akoy abinda zai zakata dakatawa da kukan da take yi ta yi sauraron wasu abubuwa a irin wannan lokacin, domin ta tsinci kanta a hali na matsanancin tsoro da neman shiga uku da tunanin wa zata tarba ta fadawa damuwarta da tsoronta? A yanzu kuwa sai take jin wani irin abu mai kama da karfin zuciya da kwarin gwuiwa da jin amanar yarda da abin a cen kasan zuciyarta, duda ba zata fadawa kowa matsayar tunaninta ba

Tabas jikinta ba kwari, ama kuma zuciyarta ta tsaya a matsaya guda a lokacin da aka lulubeta cikin shigar alfarma a dakin hajia saman gadonta , kunnayenta na jiyo mata saukar Alkur'ani mai girma da ake yi har nanauyen barci ya yi awon gaba da ita tana karra jin a wau ne zata amsa kiran mata a wajensa........ ...........



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
5?? 7??



Tabas jikinta ba kwari, ama kuma zuciyarta ta tsaya a matsaya a lokacin da aka lulubeta cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login