Showing 60001 words to 63000 words out of 124070 words

Chapter 21 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

350

nesa kar mu juyo domin za'a diro a daren a mana fashi da kuma kudurin kashemu har kiyama ....ya fada cewa wani makusancin mahaifina ne, wanda ya ba yarda, yarda mai girman gaske, ya fada cewa kar mahaifina ya saki ya nemi kowa kawai ya tafi.....Nuriyah, wayo Allahna Uma Uma kar dai aje Lawali ne? Uma Lawali ne?"

Uma ta sauke ajiyar zuciya tana share hawayenta muryarta na rawa itama ta ce" Hasbunalahu wani'imal wakil, Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, aa, kar ki ce shine idan har shine to fa tabas da na guji duniya kennan har na koma kiyama, zan iya cewa zan tsorata da kowa, kin ga yarinyata ki yi shiru hakanan mana, ki daina kukan nan mana, na tabata wani ne daban azalumin da ya wulakantar da ahalinku, aman rashin imanin mijin y'ar uwarki ba zai saka shi aikata haka ba, to a kan me zai aikata haka ne?"

Kaka dake girgiza kansa cike da daci ya furta" DUKIYA, subahannalah a kan DUKIYA tabas komai na iya faruwa, ina tsoron soyayarsa da datin duniya ne ta saka shi aikata haka"

Aba dake gefen Hajia kansa a sade yana jin ciwon kukan matarsa sai dai ya san ba zai taba hannata kukan nan ba a sanyaye ya ce" Hasana, ki daina kukan nan haka mana, tunda an zo kan gabar nan ai an yi mai wuyar ko ina ta shiga a yanzun ai dole zai fada mana, idanma ya kawo mana tirjiya ai sai mu maka shi a kotu dan ya fada mana infa take, mu bamu da wata magana da shi da ta wuce wannan , abinda ya aikata kuwa ya je ya ci gaba da zaunawa a duniyar idan an busa kaho Allah ya sa shi din ya labe a wani waje mu gani"

Kai Hasana ke gyadawa tana kokarin tashi hadi da fadin" Yanzu zamu je? Yanzu zamu je ko? Dan Allah ku tashi mu je ya fada min inda y'ar uwata take, ku tashi mu tafi"

Gaba daya yanzun kowa ita yake tausayawa fiyema da Nuriyah, domin Nuriyah tabas ta ci kuka na gannin ashe itama tana da dangi? Danginma a irin gidan nan? Aman kuma ta riga ta saba da duka, ta sha dukan rana, ta sha na ruwa, ta sha na sanyi, ta sha na tsangwama da mugwayen kalaman jama'a, ita kam meye kuma za'ai mata ya girgizata? Ai kawai a dai tafi, abinda zai iya girgizata sake haduwa da mutumen da yake mahaifi a gareta, domun ta yi rantsuwar ta hakura hakanan, idan dan bata da uba a tsaye a kanta duniya zata juya mata baya kuma shikenan sai ta kilace kanta ta rayu kamar yadda kakarta ta yi

Ajiyar zuciya ya sake saukewa a nutse ya ce" KOTU?"

Gaba daya suka juyo domin a yannayin da ya furta kotun da fan karfi fa kuma alamun tambaya yana kallon mahaifinsa da mamakin sanyi irrin na mahaifin nasa

Abansa ya ce" Babana ai na kula mutumen takadari ne, ka ga fa ana wani hasashen a kansa wanda idan har haka ne dole kotun kanta na nemansa dan kama irinsu, ki yi hakuri y'ata ina maganar nan a gabanki aman a gaskiya ni ya tsorata ni, yarinyarka mace karama ka kora dan me to? Ai ko mahaukaci yana son d'ansa, koda yake da rasa hankali da rasa imani gwara rasa hankalin, yanzun ni zan fara zuwa na kai kararsa ka ga sai a yi komai a tsare ya fadi inda mahaifiyar yarinyar take idan kuwa ta rasu ya fada mana wajen da aka bineta sai mu je"

Murmushi ne ya subuce masa, har ga Allah abin dariya ya so bashi

Bakinsa ya tabe ya mike yana hadiye dariyar dan kar ya hasala iyayen nasa ya ce" Ba sai kin je ba, zan je kawai....maganar kotu kuwa zamu ga yadda hali ta kama"

Tunda ya mike du suka zuba masa ido , da sauri Hajia ta ce" Maigidana wannan ai aikin na kasa da kai ne, kar ka je da kanka kar ka daki mutumen nan fa"

Kallonta ya yi lokacin da NURIYAH ta zuba masa ido jin an ce kar ya daki babanta tana kallonsa

Bakibsa ya sake tabewa ya ce" Ke zo nan"

Yana gama fada ya juya , hakan ya sa da sauri du suka kalli NURIYAH, itama ta kalle su tana nuna kanta da fadin" NI?"

Murjanatu ta gyada mata kai tana sake tabatar mata da ita yake mana

Sai da gabanta ya sake faduwa sannan ta ciciba da kyar ta muke daga zaunen da take ta fice a hankali hankalinta a tashe, hakan ya sa kwata kwatama ta manta hijab din a cen gaban kujerar Hajia

Tunda ta fito take sake goge idannuwanta, nan da nan ta gige hawayenta tassss sannan ta sauke ajiyar zuciya ta hado dukkan jarumtarta ta shiga takawa a hankali tana ta waige waigen gannin inda ya nufa

A hankali ta karasa kusan wani soja ta gaishe shi da dan bakon turancin bakinta sannan ta masa tambayar inda sir yake
Shi dai kallonta yake da son gane ko wacece? Domin Nuriyar dake kai kawo tunda ta samu yancin saka hijab take bulumtunta da abinta, kafin ta samu yancin nan kuwa koda yaushe kanta a kinshime yake cikin dan kwali ga hula

Gannin bai santa ba kuma daga ciki ta fito ya saka shi juyawa ya nuna mata wajen da KAN GIWA ke tsaye jikin wata galeliyar mota kafarsa daya a saman abin takawa a hau , dayar kuwa a kasa yana kallon wajen da take tsayen

Wata jarumtar ta sake arowa ta nufo wajen tana adu'a a kasan zuciyarta da fatan kar Allah ya sa ta bata masa rai a yau, domin ta kula mutumen idan ba rai ka bata masa ko ka shiga sabgarsa ba yanada matukar saukin kai

"A wace anguwa yake? Ya fada a kausashen da ya sakata sake shiga cikin taitayinta har tana sake sada kanta kasa sosai tamkar ta zo bada shedar karya a kotu

Muryarta a sanyaye ta ce" A cen anguwar tamu ne"

Shiru ne ya wanzu a wajen na kusan minti daya, bata ji ya ce komai ba, bai salameta ba, haka kuma bata ji tashin motarsa ba bale ta yi tunanin ko ya tafi ne

A hankali ta dago idannuwanta ta sauke a saman fuskarsa
Ido hudun da suka yi ya sakata gagawar sake sada kanga jikinta na Neman fara bari

A hankali yana kawar da kansa ya ce" To ni na san anguwarku ne? Ki min kwatance dala dala yadda zan gane har kofar gidansa"

Wannan karron dole ta dube shi dan ta tino komai da yake so ta fada masan ba tare da ta hasalashi ba

A hankali ta shiga kwatancen da su idan ka zo nan ka sha kwana, ka mike a saman baban titin zaka irga shukokin maina bakwai, a bakin baban dalbejiya kofar gidan take mai kala ja mai ruwan jinni, kaf anguwar dai a barina da ita shine baban gidan masu kudi, kumama ka ga harda abin nan na TV kato a sama daga hakama zaka gane gidan......." Ta karashe tana sake kallon fuskarsa dan ta fahimci idan har ya gane ko aa

Kallon da yake yi mata na mamaki da tunanin lafiyarta kalau kuwa? Na wannan zane da ta masa cewa idan ya zo anguwa kwana ta uku zai shiga ya mike ya sha kwana ya yi waye waye wannan kwatance tamkar na aljannu? To shi ta yaya zai gane wannan kwatance nata?

Kansa ya sake kawarwa yana jan dan tsaki da tunanin sai iya kallon idon mutun bata ko tsoron hakan!, A bayane kuwa sai ya ce" Yaya sunnansa yake gaba daya?"

Sai da ta dan rike haba kafin ta furta" LAWALI MUNTAR dai na ji ana fada"

Wata ajiyar zuciyar ya sake fada yana tunanin a duniya idan bai wujijiga wannan bawa Allah ba ai an sha da shi

Da yan yatsunsa ya mata nuni da tana iya tafiya dan haka ta juya da sauri ta nufi hanyar tafiyar

"Ke" ya fada yana wara ido da kallonta da tunanin ya aka yi yau ta fito ba hijab kuma?

Dawowa ta yi da sauri ta nemi dukawa , ya yi gagawar dakatar da ita da hannunsa yana fadin" Ina hijab dinki?" Ba komai ya saka shi yi mata tambayar nan ba sai gannin ita din mutun ce mai son rufe suturarta wanda sanadiyarta kanwarsa take koyi da halayanta na rufe jiki ruff bata tafia jikinta a bude, a yau da ta fito a haka idannuwane ruuuu a kanta, zai iya cewa tunda ta karaso harta da yaronsa na hannun damansa ya saki dukan abinda yake ya zuba mata ido.....eh toh ai sojan kennan soja ba mace gawa.....

Sai a lokacin gaba daya dukkan wani abu da zai sheda mata cewa bata da hijab ya bayana a tare da ita, kama daga jin iska ya mata yawa da sauransu

Cike da matsananciyar kunya ta shiga hade jikinta spcily wajen kirjinta tana mamatse kafafuwanta sannan ta yi yannayin dake nuni cewa kiris take jira ta fashe da matsanancin kuka

Bakinsa ya tabe ya idasa shigewa cikin motar bai kuma ce mata komai ba direbansa kuma baban yaronsa na hannun damarsa ya warci motar suka wuce har jikinsa rawa yake yau ya samu abinda yake so watau su je su daki mai rabon dukan domin sir ne da kansa ya fada cewa zasu je horo, to fa yau zai yi duka mai lada

Da gudu ta juya ta nufi cen gidan, hakan ya saka shi rakata da kallo har ta shige fallon kafin ya sake tabe bakinsa yana kawar da kansa , haka kawai yana jin wani haushi haushin shirmen yarinyar a ransa

______________________________________

Wani irin hayaki da mitar tasa ke yi mai baki da kaurin nan zaka ce za'a tayar da wuta ne d amanyan itace da bakaken ledoji da roba irin ta faro mai bakin hayaki da kauri

Gaba daya ya bade layin motar kuma ta ki tashi

Aa dan hasale ya sake fitowa yana sake gyara rigar jikinsa malun malun ya daureta da kyau a jikinsa ya bude gaban motar ya saka abin dogarewa ya rike sannan ya wani duka ya zubawa karafunnan ido yana so a dole shima yau ya gane abinda ake gani a jikin hade haden motar shina ya gyarata ba tare da ya ci kudin gyara ba

Sake gyara tsayuwa KAN GIWA ya yi yana sake kallon mutumen a lokacin da ya dago ya zubawa wani Salisu ido da ya tsaya yana masa sannu

Rai bace ya ce" Kai Salisu aikin uban me ka ga ina yi ne da zaka tsaya min sannu? Ko sa idon ne ka zo yi yau a kaina? To bari ka ji ni naci dubu sai ceto ko ubanka ya san waye ni, idan kuma ka yi gardama sai na kasheka na kashe banza na bada toshiya a rufe maganar kamar na kashe kare?"

Murmushi KAN GIWA ya yi a lokacin da ya samu dalilin da zai tafi da mutumen ba tare da ya sanar masa a kan gaskiyar abinda za'a tafi da shi ba

Kallon yaronsa ya yi da ya ciro dorina wata irin murdediyar nan da suke dukan gagan barayi sai washe fuska yake shi sarkin keta yai zai zane wani
A dan kausashe ya ce" Je ka zo da shi mu tafi, aman ka yi anfani da ilar furucinsa da ya yi yanzu"



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
4?? 0??




Sai da ya saki Murmushin mugunta sannan ya juya da bulalar zai tafi

A hankali Kan Giwa ya ce" Me zaka yi da bulalar nan?"

Juyowa ya yi ya kalli Kan GIWA ya kalli Bulalalar hankali kwonce ya ce" Wai kar aje ya yi gardama Sir"

Kan GIWA ya gyada kansa yana fadin" Bani bulalar "

Bulalar ya miko masa ba dan ransa ya so ba ya karasa wajen da LAWALI ke ta masifa da duk wanda Allah ya kawo

Maganar da ya masa bayan ya fada masa cewa shi din soja ne sun zo zagayen anguwar ne dan an samu labarin akoy barayi a cikinta sai suka ji furucinsa dan haka zai bisu caji office a binciki gaskiyarsa , domin furucin kisa baban furuci ne

Da farko hankalinsa bai tashi ba, a lokacin da ya ga da gaske mutumen yake ga kuma yadda ya hade ransa tamkar zai masa dukan tsiya ya sake birkicewa, ya shiga kokarin iface iface da fadin ya san ko shi waye zai masa haka? Ya dora da fadin idan talaucinsa ne ya kunno shi zai zo ya masa badala bara ya bashi dan na kashewa ya bace masa da gani shi yanada wajen zuwa yanzun

Sai dai bai raina kansa ba sai da sojan nan ya yi raf da hannun nasa mai dauke da dubu daya kwalin kwal ya masa matsar mutuwa na yan sekwani wanda ya so ace wuyansa ya matsa haka sannan ya sake shi ne ya ringa zunduma ihu na wahala da hannu a rike domin bai taba jin azaba a hannunsa irin haka ba, a dole ya yi biyaya ya bi bayan sojan yana ayana su je in dai shine sai ya wulakantar da rayuwar sojan nan ko uban wa ya tsaya masa

Sai dai a lokacin da suka nufo motar sai ya ji ya fara tsorata harda tunanin kardai garkuwa za'a yi da shi? Kar dai magauta ne zasu ga bayansa a kaishi wani waje a kashe shi a yar?

Bai idasa girgiza ba sai da sojan ya tura shi bayan motar ya rufe ya shige gaba, a lokacin ya waiga dan ya ga mutumen dake zaune ne sai da y'ayan hanjinsa suka so zazagowa daga cikinsa

Muryarsa na rawa sosai ya furta" *GENERAL KAN GIWA ?* "

KAN GIWA ya kalle shi kadan na yan sekwani ya kawar da kansa yana ayana' Tabas wannan din baya tsoron Allah, kamarsa da y'arsa kamar ya yi kaki ya zubar, har farar fatar da komai na fuskarta nasa ne, aman yake wulakantarwa.....'

Shi kuma sai ya nutsu ya sada kansa kasa sosai ya hade hannayensa ya matukar nutsu ya daina koda kwakwaran motsin da zai saka shi doguwar magana da kan giwa
Nan da nan ya shiga baje dukkan abubuwan da yake yi na take dokar kasa yana aunawa da tunanin idan har dan sunne aka kawo shi ya mutu ya lalace ko yana iya kare kansa, shi baban tashin hankalinsa dama ace sojoji aka aiko aka saka masa ankwa da gannin wanda ya zo kama shi KAN GIWAR ne da kansa? 'Allah Allah ka rufa min asiri ka sa taimako zai bani' shine abinda ya fi lazumta a yanzun dan ya gama gane Idan a kan dalilin shigo da shinkafa ta barauniyar hanya da yake yi, ko a kan dalilin kwaya da yake dan siyarwa jifa jifa ne KAN GIWA ya damke shi ya kade har buzunsa

Kan nasa a sade suka yi doguwar tafiyar da bai san adadin lokacin da suka dauka ba, a cikin motar kuwa shiru ne ya wanzu babu mai motsin kirki a cikinsu sai yaron Kan giwar dake tukinsa yana so su isa a baje laifin mutumen cen a ba sojoji shi su masa cin naman soyen laya domin babu abinda zasu bari sai sun murje shi tas su watsar a bola, dan mutumen yanada kamanin munafukai


Wayar da ya daga ya amsa a mutunce sannan ya sake tambayar da ta saka LAWA???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?LI dan zuba masa ido yana mamakin irin yadda mutumen ya ci karfe ya amshe shi daidai misali bai masa mugun kibar nan ba, haka kuma ya amshi dukkan wata gaba da ta dace ta amsa ta fito dasss a jikinsa ya yi gagawar kawar da kansa gannin Kamar Kan Giwa zai kalle shi yana ayana' Ko ina ne nan kamar fadar shugaban kasar ingila?, Allah ka fitar da bawanka ka fitar da ni a hannun soja ya Allah daga wannan ba zan kuma aikata laifi ba ya Allah'

Kan GIWA ya fita a motar yayi dandaja yana kallon yaronsa da ya ce" Sir na wuce da shi dakin duhu ne?"

Har ga Allah dariyama ya so bashi, tsakaninsa da Allah wanda zai daka yake nema, ga dukkan alamu alurarsa ta motsa ne ya gaji da tsarin ba zai daka ba sai an bashi izini

Kafadarsa ya dan daka kadan yana fadin" Wannan da kake gani idan muka dake shi mun masa adalci"

Da mamaki ya waiga ya kalli mutumen ya yi tsomomo yana tunani, ya ce" Sir wani ya kashe ko? Ratayeshi zamu yi ne?"

"Kai Hamza ka daina gagawa mana, jeka abinka" KAN GIWA ya fada yana kallonsa ya juya yana ta waiwayen motar da LAWALI ke ciki har ya tafi

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya juyo yana kallon motar shima, da ace Hamza ya sani da shi abinda yake sakawa a ransa inama ace da hali ya kama wannan mutumen da hannunsa na hagu ya sheke shi yana kallonsa yana babala kafafuwa har ya bar duniya ne? Dama zai fara yanke hukinci kafin ya ji komai daga bakin mutumen da ya rike shi da igiya ya ringa tafka masa dorinar rakuma goma masu barkono a jikinsu jikon tulun kunnamu? Kai da ya dan kamanta adalci a kan abinda ya dace ya samu mutumen, aman zai fara kwatanta rikita masa kwakwaluwarsa da abinda ya dauki niya

Dan gaba ya yi kadan ya sake daga kiran da Aba ke masa a nutse Aba ya ce" ABANA, yarinyar nan ba zata iya pretending like ur wife ba, ka ga tunda aka fada mata gatanan jikinta sai bari take bama da na fada mata mahaifinta ne zaka shigo da shi zaka nuna masa cewa ita din iyalinka ce, ita kuma zata masa tambayar ina mahaifiyarta a cikin ruwan sanyi idan ya waiga ya ga me ta zama kuma matar wa ta zama zai gama sarewa duniya , ta yiwu da sin zuciya irin tasa ya so nuna mata so, wannan din du ba damuwa bane ka ce kai dai so kake ya fadi ina mahaifiyarta take a ruwan sanyi kafin ku tafi da shi, to dai gatanan ban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login