Showing 18001 words to 21000 words out of 124070 words

Chapter 7 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

325

matarsa

tayi murmushi lokacin da ta fito daga dakin hajiya ta hango sabin kyankyasar dawisun sun fara girma sosai sa? irin karar nan suke suna bin sahun uwarsu

? hankali ta matsa ta zauna ta zuba musu ido, sai ga hawaye ? ranta ta ce" wai daba ma ta san dadin iyaye to ina da mutun ? Mamana idan Kina raye Allah ya bayana min ke da yan uwanki

tana nan zaune Rislan ya tardota shima sai gani tayi ya kai zaune Yana cewa" Kawata bakida kirki, sai ki gudo nan Kina morewa ki barni ?

Firgigit tayi tana kalonsa Inda ya zaro ido ya ce" kuka ? Kukan mai kike ? Lafiya ? Mai yake miki ciwo ?

Da sauri ta Mike tsaye tana dan dingisawa dan ta jima ? zaune, haka jikinta ke Bari cikin muryar kuka da gajiyawa ta ce" Kai mai gidana ne, ni ba kowa bace sai yar aikinka baiwarka, wace koda tsakar dare sai ka sakani aiki nayi maka, ka daina yaudarar kanka dan kagan ni nan *NEMAN NA KAINA* na fito, bazan yarda dalilin muna gaisawa da dan masu gidan na rasa aikina, bazan taba lamunta nayi wasa da damar da ta rabani da yawon titi na dawo aiki ? kamilance ta subuce min ba, ka gane kai ba sa'a Yina bane, tsakanina da kai ka sakani nayi maka ne, ka daina nuna min nima inada darajar da zan iya zumunci da kai

Rislan ya zaro ido ya ce" ashe bakida hankali ? Nutsuwarki ta shirme ce ? Ashe musuluncinki ? baki ne ? Yau idan har baki iya banbance tsakanin talaka da mai kudi ba Wanda ya fi wani sai Wanda yafi Jin tsoron Allah ? wajen shi mai dukan ba to ki koma makaranta,
shin wannan abin ne ya cika maki ido wannan kyalekyalen duniyar ? Nuriyah ? My Nuriy, kin manta wannan kasar da kike takawa ita zata matseki, karshe ki zama ita ? Injin sallah kike, sannan kin yarda da kalmar innalilahi wa'ina ilaihi raj'une, daga shi muke, wajensa zamu koma, ina son Inda hali ki yarda da zumuncina har Allah ya cikan burina na alkhairi ? kanki Nuriy

gaba daya jikin Nuriya yayi wani irin sanyi Inda ta juya da gudu ta fada dakinta ta fashe da kuka

da baya baya ya fada samman tafkekiyar kujerar dake falonsa bayan ya kare kalon diramar Rislan kaninsa da wannan bakuwa da Hajiya kakarsa ta jajubo, ? hankali ya furta *wacece ke ?*





Toh fa
*>?&? @&>?&? @&>?&? @& NEMAN NA KAINA>?&? @&>?&? @&>?&? @&*


Marubuciya: *SAJIDA*


*P+


*(16)*

*Ummuta* plz i beg u ki suburbudo min *MUGUN BUTULCI* kiyi anfani da dumbin basirar da Allah yayi maki, cikin nutsuwa ki kara fadakar nishadantar da mu Auntyna, mu muna jiranki plz=??

Aunty *Batul* *Anfanin soyaya fa aure* mu kam ? zaune muke dan karin haske ? namu auren, plz ki motsa, iliminki yafi gaban nan my aunt,

Na sadaukar da wannan shafin wa *Aunty Ummun Safwan And Aunty Batul*

My masoyan usul ina mika sakon gaisuwa na da jinjina gare ku, domin Kuna cikin mutanen da nake farin cikin buda data dan na karanta sun tashi lafiya wato *MaMan Manal* nd *LEEMAT*








Karfe takwas na safiyar asabar wata jiniya tayi kara, wada ? karan da tayi na?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ga ikon Allah, kowa ya rikice, sai shige da fita suke kowa cikin rawar jiki Yana aikinsa harma da Wanda ba nasa

Shugabar kicin ce ta shigo tare da Nuriyah ? bayanta

Da sauri naga suna gaisheta da mutunci domin KO ba komai ta manyata,

Wata mai suna Bilki ce ta matso ta ce" mama, yau *KAN GIWA* zai shigo ne ? , munji karar jiniyar shaida hakan

wannan mata mai suna laraba ta ce" Eh, insha Allah yau zai shigo, sannan ba'a fadi lokacin shigowarsa ba

da sauri wani bature ya ce cikin turancin shima" Shin wani ya aikata wani laifi KO ?

Ita kanta laraba ta dan langwabar da kai ta ce" ? gaskiya nima ban san shigowar da zai yi KO na menene ba, domin ba'a fadi ba, ina fatan ba Wanda ya san yayi wani munafurcin, dan kuwa wannan karin KO da wasa bazan lamunci laifin wani ya shafeni ba, kunga dai abinda ya faru da jikata ta cikina yanzu shikenan an koreta daga aikin dan ta sakawa hajiya tatasai ? miya, du Wanda yayi garaje shi zai kwana ciki kar ku ce ban fada maku ba

Kasa kasa suke kus kus, kowa na tambayar dan uwansa ai dai ba abinda yayi, Nuriyah mamaki kokarin kasheta yayi, tana mamakin irin,, wannan tsauri, nan da nan itama tsoro ya kamata, duda tana nan lokacin da Hajiya ke shaidawa mijinta cewar Kan giwa zai ci abincin dare ? bangarenta, aman sai da cikin ya murda, dan kuwa ? jiyan nan ta daukowa hajiya ruwan sanyi bayan Bata sha ruwa mai dumi dumi ne ruwanta koda yaushe dan karin lafiya

a hankali ta sauke ajiyar zuciya ta bi Mayan laraba wace ta nuna mata babar kurar da zata jera gaba daya kayan abincin ta kai idan bakin sun Zo, hakama fannin abin sha ta dauko katuwar farar takardar da aka rubuta komai, tun daga jus da ruwa kowa da kalar Wanda yake sha, abin Mamaki ? sunayen sai ta ga Harda Isabel, ita kadai take rayawa ? ranta kenan ? zuriyar Elhaj Ibrahim akoy Christa

Idannuwa ta zaro daidai lokacin da baturen nan mai kula da yannayin suturar da za'a saka idan KAN GIWA zai shigo Yana mika mata wani sket daidai gwuiwa sai Riga chemise da cravate, sai yar hula baka wace zaka dan dora, sai wani dan farin zani an fitar da daidai wuya kadai an rubuta serveuse a jiki

bakinta na dan rawa ta cewa wannan bature " excuse me, aman ni musulma ce, ta ya zan saka wannan abin ?

Shima kalon mamaki ya bita da shi, Inda ya ce" to dan Kina musulma sai mai, su su Bilkiss ba musulman bane suka saka wannan ? jikin su KO Kina son ki nuna min ni banida adini KO aikin naki zaki yi wasa da shi dan kawai Kina musulma ?

Ido ta kara zarowa, hankalinta ya tashi, ita fa tunda take, Bata taba saka irin hakan ba, yauma kuma bazata saka ba, bayan wa'innan da take sakawa da kyar yanzu kuma ? wani kawo mata wannan abin mai shige da gyafto ace shi zata saka ?

? hankali ta koma taci gaba da kara kimtsa falon Hajiya, wace ita kanta sai murna take tana ta faman shiga daki tana fitowa


Tana gama salar isha'i ta dauko wani sket din baki Wanda ya saukan mata har kasa ta saka,

Tsaki ta ja lokacin da ta ga irin yanda yake rawa ? jikinta sannan harda wata tsaga ta dafe kanta >?&? @& cikin takaicin wannan dabi'a ta wannan gida, Jin wannan jiniyar ta dazu ta kwasa ya shaida mata fa lale zasu ISO, hakan ya saka ta da gudu ta saka rigar ta gyara cravate din kamar yanda ya koya mata, ta daura yar hular nan wace iya gaban goshinta kawai ta rufe, ta daura farin kyalen nan sannan ta saka baj din dake shaidar ita ma'aikaciyar gidan ce

Da sauri sauri gudu gudu ta karaso kofar falon Hajiya Wanda kadan ya rage fitsari ya zubo mata sakamakon wasu jibga jibgan bodyguard har hudu, biyu ? hakimce ? kofar sunyi kane kane, biyu suna dan zagayawa ? saman filin terrasse din

Rawa kafafuwanta suka kwasa lokacin da ya nufota da kansa ya ja bage din wuyanta ya karanta, cikin wata murya ya ce" ke kinyi lati daga kafa mun kusa hana shiga

da gudu ta kwasa ganin dayan ya bude mata kofar ta shige da salama ? bakinta

Idannuwan Nuriyah tamkar zasu fito su fado kasa dan kalo lokacin da tayi arba da Wanda take Kyautata zaton wannan shine *KAN GIWA*,

Da alamar shigowarsu kenan domin kowane sai kalar gaisuwarsa yake yiwa hajiya da Elhaj Ibrahim,

A hankali take kokarin zagayewa dan ta kai kanta kicin din Hajiya tun kafin ta fadi dan kalon iyalan KAN giwa, NADIYA ba'indiya ta sha doguwar rigarta mai shegen duwatsu, ta baza gashin kanta ? bayanta ta sha makup da wani digo ? goshinta, sai DJAmila Ibo, ta sha wata bugagiyar atanfa ta kafa daurin dan kwali ? kan uban atach din da ta dora ? kanta, sai Rislan ya sha kananun kayansa sun masa kyau sosai, sai Uban garin *KAN GIWA* Wanda ya saka wandansa na soja, sai farar Riga wace ta bayanar da irin yanda tarin kirjinsa da sauran jikinsa yake

Nadiya ta saka Nuriyah zaro ido daidai lokacin da ta rungume Kan GIWA ta mana masa peck ? kunci sannan ta ce" i miss u

Kan giwa ya dan kawar da kansa dan ya ga yannayin hajiya, bai ce da ita komai ba, aman ya cika da mamakin ina masu zuba abinci da jus na tarban baki

Cikin faduwar gaba Nuriyah ta turo wannan kurakurar ta shigo daidai lokacin da Isabel ta shigo itama wace ta sha dan karamin sket dinta KO gwuiwarta bai rufe ba haka ma rigarta yar karama ta daure jan gashin dake malale ? kanta, ta sha zako zakon faratunanta, haka gashin idanuwanta ta kara wasu zako zako, ga Kwayar Idannuwan tamkar na mage,

Tana karasowa ta dan daga hannu ta ce" hi mamy, hi papy

Direct ta karasa jikin *KAN GIWA* ? gaban matansa da kaninsa da kakaninsu ta dan rankwafa ta mana masa Kiss ? lebensa ta furta" Hi my hero, ta wani kashe ido daya ta dan girgiza kirji

Nuriyah da ta saki kurar nan ta dafe kanta ta furta *WAYo* cikin tsoro da mamakin wannan matar sannan tsoron juyowar da suka yi ? tare suka zuba mata ido ya dirar mata ? lokaci guda

Ta dora hannayenta ? saman kanta ta kuma cewa *Na mutu shikenan na kade*






Kadidi na kuma cewa *TOH fa* =?D?>?&? @&
*>?&? @&>?&? @&>?&? @& NEMAN NA KAINA>?&? @&>?&? @&>?&? @&*


Marubuciya: *SAJIDA*


*P+


*(17)*

Hajiya murja ta ce" Nuriyah kin bige ne ? Sanu fa, plz kiyi ? hankali

Da sauri Nuriyah ta tare ta shiga karanto du adu'ar da tazo bakinta sannan ta daina hada ido da kowa bare har ta rasa nutsuwarta

Ajiye takardun kalolin abincin da aka girka ta shiga yi Inda idan ta ajiye robar ruwa da kofi sai kuma ta ajiye takardar, ta ajiyewa Isabel wace take ta Binta da kalo ta juyo daidai Kan giwa, gabanta ya yanke ya fadi sakamakon dantsen hannunsa da tayi tozali da shi ? ranta ta ce" lale ka amsa sunanka *Kan Giwa*,

Ta mika hannunta ta ajiye babar robar ruwa ta dauko kofin kwalba ta ajiye, sannan ta dauko takardar ta ajiye ? dan gefensa Inda take dan shakar kanshin turarensa mai mugun kwontar da hankali(=?D?)

Muryar Isabel ta katseta lokacin da ta ce" Ke, wannan sket din da ya saka ki saka shi ? Idan za'a zubawa my hero abinci ba'a taba irin wannan shigar haka ba, sai kace wada kika je wajen karatun adini ?

Djamila dake gefe ta ja tsaki ta zabgawa Isabel harara aman bata furta komai ba

Nadiya ta dan kara yin kasa kasa da muryarta ta ce" i said i miss u husband

*Kan giwa* ya kara waigowa Yana kalonta ya ce" really ?

Ta dan lumshe idanuwanta, tana nufin eh
Isabel na lura da abinda ke faruwa ta kara matsawa ta kara shige masa ta ce" Hero, ina magana fa

Ya juyo ya zuba mata ido, sannan ya dan kali Hajiya Murja da ta kada kai ta ce" rayuwa

? hankali ya ce" Madame ya dai, ni yau kamar ba'a wani murnar ganina, sannan ya akayi na ga yar aiki kwaya daya ? Ina suke ne masu aikin ? Kuma haka ake taryen baki har yanzu ba'ayi serving Din mu ba, an karya min dokar idan zan Zo a tabatar an gama hada min komai, sannan maganar wannan bakin abin da ta saka shi ba'a bata Wanda ya dace ta saka ba ? Ni fa bana son kazanta, dan haka yarinyar nan gaskiya bazan zauna da ita ba

tunda ya fara magana a kanta ta lumshe ido tana Jin yanda muryarsa ke amo , irin voi rok din nan ne da shi, ? muryarsa babu irin alamar tausasawa cikin taushi, aman ba karamin caza kwakwalwar yan mata take ba, tana cikin adu'ar Allah ya kubutar da ita muryar Rislan ta farkar da ita Inda cikin ladabi ya ce" Eyah Yaya, laifina ne, ni na ce ta saka shi , i'm sorry ba laifinta bane


ido Ibrahim Kan Giwa ya zubawa dan Uwansa Yana nazartar maganar sa,

Muryar Hajiya Murja ta kuma fargar da shi, Inda ta ce" bama wannan ba, koda ba kai ka sakata ba, yarinya ni na zabeta, ni nayi niyar ta zauna ? wajena, bafa ka Isa ka koreta ba, sannan dan kaga ni kadai ce ? zaune ? wajen nan har wannan baturiyar mai sifar aljanu ke shiga jikinka haka, idan nayi magana sai kace kawarka ce dan ubanka kawar taka zatana yi maka wannan lalatar ? gaban matanka ? Shin Kan Giwa mai ka dauki Aure ? Sunnar fiyayen halitar ne kake wasa da ita haka ? Shin Kan Giwa kana fatan ka samu rabauta kuwa

sai kuka ya kubce mata Wanda gaba daya jikinta ke girgiza da gani tana Jin wahalar yanda ta tsinci kanta da lamarin jikan nata

idannuwa suka zaro, Isabel ta shiga tambayar whats happen , domin da hausa Hajiya murja tayi maganarta Djamila da Rislan da Kan giwa da kuma Nuriyah dake tsaye tamkar gunki ne kadai suka fahimci yarenta Inda su Isabel da Nadia suke binsu da kalo

kasa kasa *Kan Giwa* ya ce" ku tashi ku bar mu

sifsifsif kowa ya kama gabansa ciki harda Nuriyah da ta nufi kicin da sauri Rislan ya rufa mata baya

suna tafiya Ibrahim ya matso da kujerarsa daf da ta Hajiya Murja ya ja numfashi ya sauke tamkar bai son yin magana ya ce" Damuwar har ta ritsaki haka hajiyata ?, fada mini mai kike SO nayi miki ?

Hajiya murja ta juyo da ganninta daidai fuskarsa ta ce" ka nisanta kanka da Zina, Zina mugun aiki ce, Zina na gurbatar da rayuwar dan Adam, tana sakawa komanka ya ja baya sannan idan ka mutu ? halin Zina zaka hadu da fushin ubangijinka, Wanda ya haliceka, du isarka kai ba kowa bane a duniya da kiyama yanda Allah yayi niyar yi da kai zaiyi da kai ? lokacin da yayi niya, yau idan ka juya ka jika ? cikin kabari mai zaka bada hujar godewa Allah da wannan ni'imar da yayi maka ?

Ibrahim ya lumshe idannuwansa, tabas bashida Wanda ya kai wannan tsohuwa, wannan tsohuwa ita ce mai son farin cikinsa duniya da kiyama, abinka da rainon turawa basa boye Abu magana su kan yita ne kwaro kwaro ya ce" Hajiyata, ya zanyi ne ? Na kasance mabukaci

Hajiya murja ta kawar da kanta cikin kunya, aman ganin kunyar nan ba abinda zata kara mata sai kara ci baya ta ce" Matan ka aikin mai suke, yanzu tsakaninka da Allah yaushe rabonka da shinfidar matanka

kai tsaye ya ce" basu iya gyara shinfidarsu ba (=?3?), basu iya tarban mijinsu ba, su dai abinda suka iya su kashe kudi, su kwonta suyi baci, suyi wanka su taka jirgi yau suna wannan kasa gobe suna wancen kasa, ni kuwa ya zanyi, da na auri Nadia Ya kasance Sam bata iya mini, hakan ya sa na auro yar Ibo dan ana fadin sun iya tarban mijinsu aman itama kanwar ja ce, ya zanyi ne hajiyata

Hajiya murja daidai wannan lokacin kam ta kai makura ? Jin kunyar irin abinda yake fadi Aman ya ta iya ta kara shafawa idanuwanta toka dan burinta ya kasance cikenken namiji, ta ce" Ibrahim, dan matanka sun kasance ragwagin mata hakan zai baka damar bin wata matar KO nace wasu ? Ka kara Aure mana

Kan giwa ya zaro ido ya ce " Aure ? Wa zan aura ? Kinga dai bazan auri Isabel ba domin Sam musulunci baya cikin tsarin rayuwarta, dan na gwada sosai aman abin ya gagara

Hajiya murja ta girgiza kai tana mamakin zamani ta ce" ita kadai ce mace ? Du matan duniyar nan, idan kyan ne ka aura, idan asalin ne da arzikin ka aura yanzu ina bukatar kayi auren nutsuwa, ka SAMU nutsuwa nima KO na samu fa'ida ? cikin kabariba, shin ? tunaninka aikin da kake aikatawa mahaifiyarka bata samun nata kason na azaba ?

Da sauri ya kaleta fuskarsa alamar tsorata da furucinta
ta ce" kwarai kuwa, idan alkhairi kaci gaba da aikatawa khairin nan zai tarda ita du Inda take, idan shari ne zai tarda ita, dan haka ka kiyaye, Kan giwa, yau mutuwa KO yanzu KO yanzu idan ta daukeni zanso ace na barka cikin rayuwa mai kyau sannan ina adu'ar Allah ya nuna min yayanka, shekara wajen shida da Aure aman har yanzu mata sun tsuke ciki su yan gayu ? Ku gagauta komawa ga Allah tun kafin wuri ya kure

Kan giwa ya ce" yanzu dai Plz ki bar maganar nan haka, nayi maki alkawarin zan Sami mace na kara aure

Hajiya murja Tayi murmushi ta ce" Allah yayi maka albarka

Ya amsa Yana kokarin dane damuwar dake damunsa
Hajiy? ta Mike ta dauki waya ta Dana Kiran kicin Inda ta ce" Nuriyah ki hanzarta kawo abincin aman nawa da na *KAN GIWA* kadai dan sauran sun tafi








Nuriyah ta amsa da......
*>?&? @&>?&? @&>?&? @&

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login