Showing 81001 words to 84000 words out of 124070 words

Chapter 28 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

330

da yan matan da kansu suka yi wace suka abubuwa masu laushi suka hade baki dayansu sunna hirar yaushe gamo bayan sun gama dan jimamin irin farin cikin da muryar mahaifin Hasana da husainar ke fitarwa wanda ya tabatar masu yau yau zasu nemi abinda zai kawo su kasar dan gannin gudan jinninsu

Gefe daya kuwa Murjanatu ce da Nuriyah sun tankwashe kafafuwansu Murjanatu na mika mata sauran maganinta daya da ya rage sai karra kumbura fuskarta take ta amsa ta tura shi da sauri ta sha ruwan tana sauke ajiyar zuciya Hajia na kallonsu ta yi yar dariya tana girgiza kanta tana sake buga number KAN GIWA domin rabonta da magana da shi tun jiya batama san inda yake ba ta ce" Takwara kece da ba wani magani yau?"

Nuriyah ta juyo tana sake takwakwabe fuskarta ta ce" Hajia kina gani har cewa take yi wai sun yi kadan ya dace in sha da yawa dan na mike da kyau da kuma wuri bayan ita pain relief idan aka bata ta kama ihun daci bata so"

Husaina ta ce" To ku menene a maganin in ba rigima irin taku ba?"

Hasana ta yi dan dariya tana fadin" Kar fa mutun ya manta ta yadda yake shan magani fa?"

Husaina ta yi dariyar itama daidai lokacin da wayar Auta ta dauki kuka

Tana gannin mai kiranta ta daga tana yiwa NURIYAH Signal da idannuwanta

Sunna gama wayar ta kashe tana tunanin ta inda zata fara nema masa damar zuwa gidan zance? Damuwarta daya ce tak yayansu

Wajen hajia ta dan matsa tana fadin" Hajaju sirikinku ne fa, wai shi so yake sai ya fara zuwa zance"

Gaba daya wajen ya dan dauke hayaniyar da ake yi ana kallonta, hakan ya sa ta daburce tana fadin" Ba bafa ni na, na NURIYAH"

NURIYAH ta zarro ido tana mikewa hadi da tafa hannayenta tana fadin" Innalilahi baby ni kuma? Walahi ni dai ba ruwana..........." Gaba daya sai ta rikice ta kalli wannan ta nuna masa ba ita bafa, ta kalli wancen, sai kuma lokaci daya ta juya ta gudu bangaren Hajia tana jin kamar zata tashi sama dan kunyar abinda Auta ta mata

Da ido suka rakata, sai kuma suka juyo suka hada ido watau HAJIA da HUSAINA da duban dake nuni kamar wani abu na son taba zuciyoyinsu

Karasowar motarsa wajen ta saka Hajia zuba masa ido da duban da ita kadai ta san girman tausayi da kaunar jikan nata dake cikin zuciyarta

A yannayin dake nuna daga nesa yake sannan a gajiye yake ya sauko daga cikin motar, haka kuma fuskarsa babu fara'a ko disss a tatare da ita ya karaso wajensu yana kokarin sakin fuskar tasa kadan ya rage tsayinsa sosai yana gaishe da iyayensa da kuma kakarsa kafin ya idasa zama a gefen Hajia lokacin da mai aiki ta karaso da sauri tana kokarin zuba abinda zai tarbeshi da dadin rai

Kasa kasa ya kalli Hannun Auta mai dauke da wayarta tana gaishe shi fuskarta tamkar gonar auduga sannan ya cire kansa yana tuna abinda ya faru jiya da tunanin Allah ya sa bata kula da zubewar da ya yi ba, dan kam abin kunya ne wannan ai, sai kuma ya ji wani sashe kadan na son sannin ita kuma ina ta tafi sarkin sakarcin rukunkume mutanen?

Hajia sai tambayoyi take masa lafiyarsa? Ya ci abinci? Ya yi kaza? Ya yi kaza? Har dai abun ya ishe shi ya kafeta da ido ya ki bata amsa, hakan ya sakata yatsina fuska tana karkace kanta hadi da hararansa

Daria Mama Husaina kawai ta yi tana fadin" Son me yake damunka? Nima yau na ga Rashin fara'ar ta yi yawa menene?"

A hankali ya kalli Mama H??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????usainar, sai kuma ya samu kansa da sakar mata dan murmushi yana girgiza kansa a hankali

Mama ta sauke ajiyar zuciya ta fuskance shi sosai ta ce" Son dama ina ta so mu yi magana a kan wannan azalumin mutumen, shin haka za'a barshi kennan ya yi irin zalincin nan? Gaba daya na kasa jin zan iya yafewa wannan mutumen, Hajia ta nuna Nuriya na iya jin ba dadi, ni kam ba zan iya kyaleshi ba!"

Hajia ta ce " Ai kam maganar kyaleshi bata taso ba Husaina, sai dai abinda bana so kar ku tozarta shi ko dan y'arsa, ku sani haihuwarta ya yi, kuma y'ar halak ce"

Hasana ta yi murmushi tana girgiza kanta ta dubi Hajia sannan ta dubi Kan GIWA kafin ta kamo hannun y'ar uwarta ta ce" Ni kam da ni za'a bi, sai a kyale shi, ai ko a yanzu mu muke da riba a kansa, du yadda ya so ya wulakantamu Allah bai bashi dama ba gamu Allah ya sake hadamu da rai da lafiya da ci gaban rayuwa, To wai mema za'a yiwa Lawali a rama cutar da ya yi? Ai wannan launin azabar da ta dace da shi sai wanda ya halice shi, ni fa da zaki ji wani abu da na fada maki Maman Auta , sai nake ji kamar na yi gangamin na yafe masa, ko dan nima Allah ya yafe min wani laifin nawa,...... A yanzun bani da haushinsa sai tabo, wannan kuwa ya riga ya min shi zan je kiyama da shi"

Kan GIWA ya cire dubansa a kan HASANA ya maiwa kan agogon hannunsa bai ce masu komai ba hakan ya saka Hajia sake kureshi da kallon kar ka yi hali a gaban bakuwa mana,
Dan Murmushi ya sakar mata ya ki cewa komai din

Sake maka masa harara ta yi tana fadin" Yauwa dayar maganar kuma , Takwara na nemarwa y'ar uwarta dama a ba saurayinta dama ya fara zuwa zance ......"

Daga takwarar, har Mamanta sai da suka kalli bakin hajia a tsorace
A tsorace Murjanatu ta ce" Kai, Hajia?" A daidai lokacin da ya sauke idannuwansa a kan MURJANATUN yanai mata kallon da ya taba mata a lokacin da ya kashe fuskarta da mari

A hankali ta ja ta koma jikin mamanta ta lafe tana sake sada kanta, shi kuma wani tukuki da ya tare masa wuya ya kafeta da ido da kyar ya iya fadin" Saurayi kika yi Auta?"

Da karfi ta girgiza kanta tana fadin" Ni kuma? Ba nice ba fa, Nuriyah ce ta yi saurayin wannan yayan na Mami kawata"

A hankali ya ringa auna maganar a saman lebensa har ya gama gane fasararta a yarensa kafin ya kuma kafe matan kaf dinsu da ido

Kansa ya girgiza yana gyara zamansa ya ce" Kina jina, idan na kuma jin magana makamanciyar wannan shirmen sai na zane maku jiki daga ke har ita Nuriyar a gidan nan, bana son shiririta da shirmen banza, kin fahimta?"

Da sauri take gyada kanta dan amsa shi, sai dai bata gama ba Hajia ta katse hakan ta hanyar fadin" Ban gane me kake nufi ba MAI GIDA? Ban gane kar ka kuma jin maganar ba? Wani irin shiririta ?"

Kallonta ya yi yana tunanin so dai take sai ya yi fadan a gaban bakuwar fuskar ko? Dan haka ya dubeta da kyau ya ce" Dukansu nawa suke da za'a fara masu maganar wani zance salon su saka shirme a ransu su daina abinda zai fishe su?"

Da mamaki Hajia ta ce" Shekara ashirin da daya ne kake yiwa kallon nawa mace take? Kai Mu'azam a me ka dauki duniya da mutanen dake cikinta? In ba dan lamari naku da kuke gannin wayewa ba yanzun ai takwara da sa'aninta sun kai ace sun ajiye y'aya kamar hudu hudu, Husaina shigar min maganar nan?"

Da sauri ya mike yana kallon Hajia da fuskarsa da ta karra daukan ja ya ce" Yaran da shekarunsu kwata kwata ashirin da watani ne za'a wani basu damar fara shagaltar da rayuwarsu? Na san da zasu yi aure aman idan suka kai shekarun iya zaman auren ba a haka ba zan dauka na mikawa wani dan rainin wayon da zai wulakanta min ba!"
Ya juya kan Auta da ta sake boyewa jikin mamanta ya ce" Idan haka ne ku tatara ku koma bangarena daga ita har ke, ba zan lamunc shirme ba! Baku tafasa bama bale ku kone, ban yarda da maganar samari tun yanzu ba!"

Tsakaninsa da Allah fada ne yake yi da gaskiyarsa, sai dai bai ganne cewa a fadan nasa ya haura sama sosai ba ya wuce ka'idar da ya dace ace ya tsaya, watau bacin ran da abin ya hadasa masa ya haura misali, wani irin tukuki da yake ji na ci masa a kirjinsa da jin haushinsu baki dayansu da mamakinsu na gannin sun zauna sunna kallon yara kanana na kawo masu maganar raini irin wannan ya maida dubansa kan Mamansa da kuma abokiyar tagwaitakarta ya ga kuri shi take kallo itama ya cije lebensa ya rage ihun muryarsa yana fadin" Lawali kuwa ba zamu tozarta shi ba, sai dai rayuwar talaucin da yake gudarwa ita zamu kwatanta masa sannan mu barshi da mutanen dake zagaye da shi da nufin sunne masoyansa mu gani"

Yana gama fada ya juya yana jin kansa na son fara sara masa ,

Hajia ta daga murya tana fadin" Ka ji ubanmu, nace ka ji ubanmu ya yanke hukunci a kanmu, to bari ka ji Mu'azam walahi sai na aurar da jikokina ko ubanka ya tsaya maka! In ba bakin ciki ba so kake sai na mutu a mika su wa mazajensu? Kai ba auren ne ka yi ba kake rayuwa da matan? Ke Husaina ki rabani da d'anki na rantse da Allah ko ranki ya bace ! Yau ga bakon iskamci!"

Da sauri ya juyo ya dawo wajen da suke , hakan ya sa suka yo tsuru tsuru sunna kallonsa dan gannin me zai yi?

Yana zuwa ya kamo hannun Baby ya janyota daga jikin mamanta ya nuna mata hanyar bangaren Hajia fuskarsa a hade sosai

Da gudu ta nufi ciki tana waiwaye sannan ya juyo wajen HUSAINA ya hade hannayensa ya sanyayar da muryarsa sosai ya ce" Kin gani ko Mama? Ina zamana take son halaka ni ko? Ta barni na ji da rigingimun dake gabana mana zata ce yaren nan kananu zasu fara kula mazan nan na zamani da basu da kunya da tsoron Allah, shi din dan ubanshi meye hadinsa da su yara kanana zai ce yana so? Me yake so? Da take cewa wai ta mika su wa mazajensu ai sai ta saka su fara saka wasu abubuwan a ransu ko? To walahi ki mata magana in tsufa ne ya zo sosai ta je ta rungumi carbinta ta shafa min lafiya!"

Yana gama fada ya sake juyawa ko kallon Bangaren hajiar bai yi ba domin gaba daya ta gama shaka masa abin haushi , wai shi zata duba da wannan maganar? Bayan ta san tsarinsa? Lalema!

Da ido suka raka shi domin daya ta rasa kalmar bakinta har sai da ya warci motarsa ya bar wajen kafin Hasana ta saki daria tana sada kanta dan walahi fadan nasa gaba daya daria ya bata, wai irin kar a kawo masa rainin nan ko?

Husaina ta ringa tafa hannu tana salalami tana sake kallon hanyar ta juyo wajen hajia ta ce" A mana hakuri Hajia, in sha Allahu zan ganshi idan ya sauko zan lalaba shi "

Hajia ta yi murmushinta na dataku ta ce" Yanzun kin ga abinda na fada maki ranar nan?"

Da mamaki ta kure fuskar hajia kafin ta ce"



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
4?? 9??


Da mamaki ta kure fyskar Hajia kafin ta ce" Mama, hakan zai bani mamaki matuka, tabas hakan zai bani mamaki, kina gannin indiya da bayarabar da shi ya gani abinsama yaya zaman yake bale yar baby innocent din nan?"

Hajia ta gyada kanta tana wani murmushin ta ce" Shine bambancin da zan gwada masa a aikace, da ke a tunaninki irin zan dauka in bashi yana basarwa da cika da batsewa yana nunan dan na isa da shine zai min biyaya? Zai gane ta yaro kyau take bata karko zai kuma gane du cikar nan tasa bashi da nauyi a gaban rigimar da nake shirin bala masa"

Tana gama fada ta mike ta yi cen wajen tsuntsayenta zuciyarta fesss da farin cikin abunda ya fara nunawa a idannuwanta, ya riga ya yi sake a yanzun kam sai dai tace da shi sorry

Ajiyar zuciya Husaina ta sauke tana sake kallon y'ar uwarta ta ce" Wai me kike yiwa dariya ke kuwa ?"

Yannayin da ta yin ya tuna mata zamanin yanmatancinsu, hakan ya sa Hasanar sake yin yar dariya tana kallonta ta ce" Wai har yanzu kina fada ne? Bama wannan ba, ina matukar jin dadin irin yadda yayan mai gidanki ke mutunta ki, duba ki ga kan safe zuwa yanzu kiran da wanda ke kasar waje ya maki ya kai uku, ga wannan da na jima ina jin sunnansa a bakin mai gidana ina tunanin bai san kalmar dariya ko sakin fuska ba aman sai na ga a kanki yana da sanyi sosai, uwa uba Auta"

Husaina ta yi murmushi itama tana kallonta a sanyaye ta ce" Hasana, idan nace zan kwatanta maki kaunar da nake masu a furucin bakina zan iya yi maki karya, kin ga na sha shiga mamakin du irin yadda na kasance mai kiyaye gagawar kamuwa da kaunar mutun dan Adam y'ayan nan sun siye duka kaf space din zuciyata, ina jinsu tamkar ni na haife su a cikina, kin ga baby tunda aka nuna mata ni a matsayin uwa ta rungumeni ta doran kanta a kirjina na ji bugun zuciyata ya cenza, na ji dumin jikinta na ratsa nawa duda suturar dake jikina, na ji ina jinta a zuciyata kamar ni na haifeta, shima Rislan da wuri ya saba da ni, dan rigimar nawa ne sai a hankali da ya gane cewar bana tare da mahaifinsa dan dukiya sannan bana zaune da kannensa dan na birge mahaifinsa sai da zuciya daya ya sauko har yake kirana Mama, duda ban bashi shekarun haihuwa ba haka zan ce abu ya kuma yi, ko na hanna ya hannu , tabas mutun ne mai wani irin halin da muke fatan gannin ya cenza wasu a ciki kamar mu'amalarsa da iyalinsa, wanda Hajia ta saka wani dll din da nake gannin anya kuwa? anya hakan zai taba kasancewa kuwa? Domin zamani ne ya zo da sabon salon dake rikita tunanin bawa, a yanzu mata sun karyar da farashinsu ta yadda farashin maza ya hauhawa sosai, wasu mazan ba zasu taba gannin darajar mace ba domin an nuna masu sunne masu daranar su su kadai bayansu kowama a bayansu yake"

Hasana ta sauke ajiyar zuciya tana mamakin dama yana da mata? To yaya aka yi bata ga ko daya ba tun zuwanta jiya har yanzu? Sai dai bata furta ba ta yi adu'ar samun nasara domin ta san ko menene alkhairi Hajiar zata nema a wajen mai duka

"Tll me, kanwata fada min wace irrin rayuwa kike yi da shi? Yaya kike yin rayuwar aure da shi? Zama ne irin na wulaakanci da karfi da yaji , munafukin zama ne irin na lawali? Ko zama kuke yi mai anfani ?" Husaina ta fada tana sake tsatsare hasanarta da ido

Murmushi ta yi tana cire kanta a hankali ta ce" Nice yayarki fa............"
Sai kuma ta sake fuskantarta ta dan buda hannayenta tanaa fadin" Mutun ne mai tsauri, mai rigima, mai matukar rigima da rashin hakuri.......sai dai dukkan fitintinnunsa nada sauki aa wajena, Husaina kin san idan aka yi wata rayuwar wani lamarin sai a hankali, a tare da shi ban rasa ci, sha, ko sutura ba, ban rasa zama mu yi hira irin na miji da matarsa ba, munna raha yawancin lokuta, haka kuma idan rigimarsa ta hado shi da wani zaki ga an zo da gudu an kirawoni domin idan na zo wajen koda bai daina ba maganarsa zata yi laushi, da bakinsa ya fadan cewa yana jin kunya idan na ga tijararsa......kuma a haka muke rayuwarmu, ba karyace karyace, ban dora masa abinda ya fi karfinsa ba, shi kuma tunda ya gama aminta da ni sai ya zame min uba, dan uwa, aboki, kuma miji"

Sunna hirarsu a wajen nan aka karaso da mijinta dauke da akwatin kaya

Sosai suka gaisa yau da Husaina domin a jiya basu ko gaisa din ba

A saukake Husainar ta dube shi ta ce" Yaya, nace ba, dan Allah ka yi tunani sosai a kan maganar Aban Auta, idan ka ki hakan ba zai ji dadi ba sam, sai yaga kamar ko baka yarda da an zama daya ba"

Murmushi ya yi yana amsata har ta mike ta tafi sannan ya fuskanci Hasana yana dage mata girarakinsa ya ce" Harda ke a ciki ko?"

Yar dariya ta yi tana fadin" Nifa jiyama sai da nace da kai ka tsaya mu tafi, wai yanzun da gaske ka zo da kayanka da nawa nan kuma kaki ka amshi gidan ? To aman me yasa?"

Shima dariyar ya yi yana sake aauna abin, ya sani abin wani iri, ya zo gidan tawainar matarsa, sai dai ba zasu gane ba, a yanzu ba zai iya rayuwa mai tsayi nesa da ita ba, haka kuma ba zai iya amsar gidan da aka ce za'a bashi ba, yaya daga haduwa sai kawai dan shine sarkin hadama sai ya tashi ya amshi wannan gida? Zai so ya ciyar da hasana da guminsa , zai so ta yi ta kallonsa a jaruminsa har ya koma ga ubangijinsa, dan haka ya sake matse mata waje kadan yana fadin( kar ku manta fa, shi din ya gabatar da rayuwar eh yane ne, dan ya matse mata waje da kyauma, wasu dabi'un ko an tuba sukan zama jiki, ballema ai ba haramun bane kawai dai a wajen da hakan ke faruwa ne da kunya)" Hasanata, ki yi hakuri kin ji? Tuni na fadawa Elhaji dauda zan saki gidan nan ya sama min wanda ya fi shi dama sosai, ya kuma yarda dan ya san bana masa wasa da kudin haya, kin ga in sha Allahu ko cefanenmu zai cenza, zan kara kokari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login