Showing 66001 words to 69000 words out of 124070 words

Chapter 23 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

361

a wajen nan, bari ka ji bana kunyar marar kunya ko waye shi! Yadda baka ji kunyar cin amana ba, ba zan kunyar kunyataka ba ko waye kai!, Yadda ka iya mikawa matarka ragamar rayuwar Mama Hasana kai zaka bi ta inda ka hau a yau a nunan kushewarta ko ita a raye! Idan ba haka ba in ban shake wuyanka har ka daina motsi ba ubana goma, Hau malan mu je Hau!"

Babur din nan Hamza ya ciciba Lawali da ya kasa hawa ya dora shi a sama dar sannan yaa juya da gudu shima ya haye baya inda sojojin suka cika kamar zasu je kamen yan fashi fadi yake" Ku doka ranjess dinku a kasa, ku wasa hannayenku zamu daki mai laifi zamu kamo makasa ne! "









=??=??=??=??=?? Ku da muka ce a 40 zu tsaya?=? ?=? ?=? ?=? ?=? ?



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
4?? 1??


Jikinta na rawa sosai ta idasa saukowa kusa da shi kadan, harma ta bemi ta duka kasa jamar yadda take son mayarwa da dabi'arta a gabansa sakamakon tsoronsa da take ji da shayinsa a zuciyarta

Idannuwansa ya rintse lokacin da kanshin turarenta ya gama cike masa hanci, yana budewa ya yi gagawar cire kansa, domin dukawar da ta yi sai ta bada wata kala mai kyan gaske , wace zata kasance abin sha'awa ga idannuwan da zai kalla, domin gantsarewar da kugunta ya bada a lokacin idon da ya gani ne zai iya fasarawa dala dala

A dake ya furta" TASHI"

Tashin ta yi da sauri tana saka hannunta ta rike karfen matatakalar tana sake sada kanta kasa

Hannun nata wannan karron ya bi da kallo kafin ya sake zuba mata ido
A dake ya ce" Dabi'ar zir kuma zaki yafa a kanki dan cin wace riba?"

Wannan karron har ga Allah abin ya so ya bata mamaki, mutumen da aka ce idan yana waje ta tabata sai ta saka damamun kaya kafin ta bashi abinci da kyar Hajia ta hanna hakan, mutumen da aka ce dokar gidansa saka dan dingilin sket ko dogon wando ana watayawa ana shawagi tamkar tsuntsu hankaki kwonce a sake kamar ba musulmi ba? Shine a dazu ya mata maganar rashin Hijab, a yanzu kuwa ya dubeta harda dan kwali a yafe a kanta ya ce mata ZIR?
Yawun bakinta ta hadiye a hankali ta juya ta yi hawa daya biyu ta dajata sakamakon jin muryarsa ya sake fadin" INA ZAKI JE?"

A sanyaye ta furta" Zan dauko Hijab dina ne a daki, dama Hajia ce ta ce na zo a haka "

Irin yadda ta fada a sanyayen tana kuma kallonsa ya saka shi jin kamar ya takura mata , haka kawai sai ya ji yana jin kamar ya ce da ita ki yi hakuri ki zo mu je

Dan tsaki ya yi na jin haushin rauninsa a kan yarinyar, ko dan ya ji labaranta a lokacin da bata so fada masa shi ba? Dan takawa ya fara yi yana fadin" lets go"

A hankali ta lumshe idannuwanta a kan fafadan bayansa a lokacin da ya bada baya ya shige cen wajen Falon

Idannuwanta ta bude ta kurawa hannunta ido, a hankali ta furta" Yanzun Mutumen dake amsa sunnan mahaifina ne a falo, wanda ya min korar kare? Wanda ake kyautata zaton ya san inda mahaifiyata take? Idan har haka ne zai iya fada mana inda take? Ana nufin idan na fita a wajen cen na yi yannayi na wace take kamar matarsa zai yi anfani da damar dan ya samu maganar dake iya nuni cewa mahaifiyata na raye ko a mace?"

Wani gwauron numfashi mai zafi ta sauke a hankali ta idasa saukowa

Ta bayan kujerun ta bi ta karasa wajen baban table din da ake jera abinci da su kayan sha
A nanma sai da ta ba kanta kwarin gwuiwa ta ci gaba da ambatar cewa mahaifiyarta, mahaifiyarta, sannan ba yau ta saba zuba masa abu ta yi serving dinsa ba, juste na yau yana da bukatar ta dan sake matse masa waje kadan like hr wife

Wani kofi na glass ta dauka mai dan fadi, a hankali ta dauki wani pate ta dauko lemun tsamin dake ajiye kato wa'inda aka ajiye su ne dan cin gasashen kifin da aka yi
A nutse ta matse shi saman plate din sosai hakan ya sa ya matsu sosai da ruwansa
Siga ta zuba a wani plate din mai dan yawa sannan ta kawo saman kofin nan ta kifa shi a saman ruwan lemun tsamin nan ta jika bakin sosai sannan tana cirowa ta kifa shi saman sigan nan ta dan jujuya shi sosai a saman sigan sannan ta dauke ta ajiye shi ya dan sha iska, hakan ya sa Bakin glas din kofin ya yi wani abu tamkar an masa ado ne cen asali

Wajen jus din ta karasa ta dauko na lemun tsamin da na'a na'a ta dawo wajen kofin nan ta zuba a hankali ta yadda ba zai bara kwaliyar kofin ba sannan ta yadda ba zai isa har cen kusan kwaliyar kofin ba sannan ta mayar ta dawo ta saka kankara yan gutataki a ciki ta kuma yanka wani lemun tsamin gida uku, ta dauki na tsakiyar ta dan yanka shi zuwa tsakiya kadan sannan ta makala shi daga gefe ta dan karkata shi kadan
Ta kuma komawa ta dauko sucette watau abin nan dogo da ake zirawa ana sha da shi ta zira daya mai ruwan bayan lemun tsami watau kore

A hankali ta juyo ta dawo falon tana dukkan adu'ar da ta zo zuciyarta

Muryarta cen ciki sosai ta yi salama tana cire takalman kafafuwanta mararsa tudu ta barsu baya ta dora kafarta saman lalausan cafet din wace yau ko safar baby tsabar sun rikitata hakan ya sa ake iya gannin kafar a bayane

A hankali ta dago dubanta ta sake gannin inda KAN GIWAN ke zaune, kafarsa daya kan daya ya zuba mata ido , aman bai furta komai ba, sam bata kalli gefen da mahaifinta ke zaune ba, hasalima bata san a takamaiman inda yake zaunen ba, dan zaman kurmancin da suke yi ya sa bata san a ina yake ba, ita dai ta san cewa yana falon ne domin gaba daya yannayin da takan shiga idan yana waje na tsoro ya gama kamata ya mamayeta

A lokacin da ta tsaya gabansa kadan sai ta sauke Idannuwanta a kan Jus din tana sake rike shi da kyau kar ta maka masa ta jazawa kanta balakinsa

A lokacin shima hannun nata ya zubawa ido yana ta aauna abinda hakan yake nufi

Oh irin ta kawowa mijinta ruwan nan?
Da gangan sai ya saki dan murmushin yake yana sake dubanta da wannan fitinanen kanshi da ta fesa wanda a gaba zai ja mata kashedinsa

Dan muzgutawa ya yi ya matsa kadan yana furta " Zauna mana Madame"

Da sauri ta sauke dara daran idannuwanta a saman fuskarsa na yan sekwani, sai kuma ta core da gagawa domin tarr ita yake kallo

Wajen da ya nuna matan a tarihin zamanta a gidansu zata ce ko matansa bata taba ganni sun yi zaman matsewar waje irin wannan ba, yana nufin a saman kujera daya ita da shi su yi zama na daf da daf?

Idannuwanta ta yiwa luuuu a lokacin da ita kanta bata san ta aikata haka ba ta koma daga barin da ya fi karkata dan a nan ne hannun kujerat mai kauri yake ta yi kundunbala da tashin hankalinta ta ari jarumta ta dan yi dadage ta dosana makeken rabin duwawunta a kai sannan ta sake damke abin jus din nan da take ji a jikinta kadan ya masa saura ya fashe

Hannunsa ya kai a hankali ya amshe jus din yana mai kokarin saita kansa a kan su yi su gama lafiya sannan ya dan sake juyowa inda take ya zuba mata ido

A hankali ya saka hannunsa kusa da habarta ya ringa kusanta hannun nasa kafin ya idasa dora lalausan hannunsa a saman habarta ya dan talabe kadan sannan ya dago fuskarta wanda ta dago a hankalin tana sauke Idannuwanta a saman fuskarsa lokaci daya kuma hawayen da take ta yakin rikewa ya shiga bin kumatunta

Idannuwansa ya lumshe a saman fuskar tata da ta ringa daukan ja da hawayen da suka shiga balewa sai lebensa da ta dantse kadan dan karta kurma ihun kuka yana kallon fuskar

Da kyar ya iya tuno abinda zai fada a hankali ya furta" Me yasa kike kuka?"

Lawali karra wara ido ya yi a kansu, a ransa yana furta' Kan uba, lalle maza sai mata, ashe shima yana magana haka? Ga dukkan alamu wannan mai shige da yayan indiyawan matarsa ce , haba ko shi ya san kyau ai gashi ya rikice daga gannin tsaleliyar y'a a gabansa , Allah mai iko'

Idannuwanta ta cire a cikin nasa, lokaci daya tana kuma cire kanta a kansa a hankali ta sake hayewa saman abin kujerar ta rankwafo ta dora kanta a saman hannunsa na hagu dake ajiye yana mike saman abin kujerar ta fashe da kuka irin na cikin nan mai dan karamin sauti tana goga masa fuskar tata a saman hannun nasa tun daga gashin idannuwanta har zuwa habarta tana yi kamar zata sike

Hajia dake tsaye daga sama ce ta harde hannayenta tana sakin murmushi ta juya wajen Aba da ya yi mutsuwar tsaye shima yana kallon yadda Kan Giwa keta hade girarakinsa yana sake muzguta zamansa wanda kana ganni zaka fahimci yana so ya ji dadin zaman nasa ne ga dukkan alamu a haka baya jin dadin yannayin

Kan Giwa ya ringa sauke ajiyar Zuciya a ransa yana ayana ' wannan balakin fa, yarinyar nan me yasa take kin haka ne? Daga cewa ta yi abu kamar matata shikenan sai ta min kuka a jiki? ' (malan jikinka muka hau yo?=?D?)

A hankali ya dago hannunsa na daama dake kara rike masa ya jimke shi sosai sannan ya bude ya kawo shi wajen kanta, sai kuma ya dan kaishi kasa kadan a hankali ya dan yi taping din bayanta sanann ya gyara muryarsa ya ce" Ya isa hakanan Ma.....Ma.................." Idannuwansa ya sake lumshewa a hankali ya saci kallon Lawali ya ga kallon da yake masu harfa na kurulah
Dan haka ya cvi gaba da fadin" Ya isa kukan mana, ki yi hakuri haka ya isa, ke dai kulun kukanki mama mama mama? Dago fuskarki ki kalleni, plzz dago"

Sai da ta ja wani numfashi sannan ta dago fuskar nata a hankali ta saka Idannuwanta a cikin nasa
Hannayensa biyu ya saka ya talabe fuskarta yana sake jin abinda ke bin jikinsa na neman fin karfinsa ya ce" A kanki, babu abinda ba zan iya aikatawa, a kan kukanki zan iya harbe ko waye NURIYAH, a kan na samo maki farin cikin rayuwa koda na second daya ne, zan iya dokuwa ko da waye.........kin ga, bude idannuwanki da kyau ki kalli cen, na je yau na dauko Wanda aka tabatar min shi ya auri Maman Hasana ya rayu da ita har ta haife ki, ki kalle shi ki gani NURIYAH a yau idan bai fada min inda take ba ya shigo kennan zan kuma yi anfani da karfin ikona na masa kisan da ko kare ba za'a yiwa ba kuma na zubar a cikin tafkin kifayena!, Kin ga kukan nan naki na gaza NURIYAH na gaza dube shi ki tambayeshi da kanki, domin idan ni na tambayeshi ban san yaya zamu kare ba!"

A lokacin da ya nuna mata wajen da zata duba din a kusan tare suka juya daga ita din, har shi din, har Lawalin kansa dake zaune ya juya dan gannin mutumen da ake fadi, domin a kusa kusa bai kawowa ransa cewa shi din nan talaka Lawali bawan Allah shine ya ja ruwa ruwa ya ja shi har haka ba

Gannin ba kowa a bayansa haka kuma a gefe da gefensa ya saka shi juyowa a hankali a kuma tsarge da kansa

Idannuwansa ya zuba a saman kansu gannin shi din nan Lawali shi suka zubawa ido
Sai da ya kifta ido kamar sau biyar a sekwanin da basu gaza uku ba kafin ya sake zubawa yarinyar da ya ji sunnan kamar ya taba jinsa a duniya, sai dai wace uwarta ta bata sunnan nan ba wai ace sa'ar rayuwa ba ko meye ba zai taba malaka mata KAN GIWA ba
Dan haka ya ringa kokarin daidaita firgicin da ya hau fuskarsa, sai dai kafin yake idasa daidaitawa ya ji muryarta tana kallon idannuwansa sak ta ce" zan so na kireka da Aba, domin ko ba komai uba shine mutun, shine silar zuwan bawa duniya, sai dai da bakinka kace min iidan naa yarda na kuma shiga gidanka na hada maka gurmi da matarka ko na ganka a waje na kireka Aba sai ka tsine min, Lawali kake a gareni kai ba ubana bane...... "
Ta karashe tana son hanna kanta kuka ta dora da fadin" Dan Allah ka taimaka ka fada min a yau inda ka kai min mahaifiyatya mana? Dan Allah ka taimaki rayuwata ka fada min inda take mana? Idan ta mutu ne a wani makwontai ka birneta kuma su wanene shaida? Dsan Allah ka ........"

Da sauri ya mike tsaye jikinsa na daukan rawa yana sake zarro dara daran idannuwansa ya ce" Ke ke, ni a ina na sanki? Ni a ina na tabaa ganninki? Ke kin sanni ne da zaki ringa wata magana daban salon ace na cuta maki......""

"LAWALI!" ya aambata a kausashen da ya saka daga shi har NURIYAH kallonsa da sauri

Da idannuwansa ya masa alamun ya zauna
Sai dai ina, Lawalin sai ya ki zaman, asalima da sauri ya ringa kale kale ya sake dora idannuwansa a kansu ya ce"



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
4?? 3??



Tabas rana ke tarda mutun ba mutun ne yake tarda rana ba, da ace shine zai tarda wannan rana irin ta yau da kafafuwansa da ya rantse da wanda ya busa masa numfashi da kafafuwansa zai gudar mata

Sai gashi a yau dan ya wulakanta kansa ya fado a wulakance a arha kacak mijin y'arsa ta cikinsa ne ya doro shi a bayan mashin mai tsayin sama yake gudun fafalaki da shi , gaba daya babar rigar nan tasa sai da ta bahe iska ke dauka, hular kansa kuwa shi da kansa ba zai fadi ga lokacin da ta sauka daga samaan kansa ba, ya ga abu ya ga rana ya ga ikon Allah

Tunda aka shigo anguwarsa yan uba suka mike suka zuba masu ido, bai tabata da bayansa ake son gani ba sai da ya ga masu rakiyarsu na biyo baya

Da kyar ya iya saukowa domin dorkowa d'an nan ya yi kasa ya barshi a saman babur din nan mai dagogo dagogo, da kyar ya iya danna kafarsa da dandar kasa ya samu kafarsa ta sauka

Jikinsa kam ya gama rinewa da rawa , a yanzun ba rawa yake yi ba sai dai wani kaikayi da yake masa kamar rabonsa da wanka an yi wata goma

kan Giwa na gabam sauran sojojin yana masu bayanin a nan zasu tsaya su zasu shiga da Hamza da shi ya juyo kennan jin HAMZA na maimaita abinda Lawali ya fada da karfi kamar haka " Ka ce gidan matan aure ne mu dakata ka fara shiga? Gaskiya kana Ruwa malan....." Kafin ya karaso sai gani ya yi Hamza ya fali keyar Lawali fala irin ta tanda ya iza shi cikin gidan

Har ga Allah sai da ya ji wani tsam marar dadi, sannan ya sake rokon Allah kan ya rufa masa asiri duniya da kiyama ya mutu da mutuncinsa, idan tashin hankali da cin zarafi irin na saka kai a uku da son abin duniya ba, me zai kawo hannun Hamza dan cikinsa ya tali keyarsa? Ya subahannalah, sai dai babu abinda zai iya yi a kan haka dan Lawali na da dangantaka da matar mahaifinsa, ba zai yiwu ya hanna yaren nan aikinsu ba, domin Lawali fa mai laifi ne, dukkan wasu abubuwan rashin gaskiya sun bayana tare da shi , idan aka masa sanya tabas za'a ga ba dadi


Da ihu Lawali ya idasa shigewa gidansa yana tangal tangal da kyar ya iya rike kansa ya juyo yana kallon Hamza da ya idasa shiga shima


Mai gadinsa ne ya taso da sauri yana fadin" Kai wannan wani marar mutunci ne ya biyo Elhaji?"

Da karfi Lawali ya ce" Kar ka isa kar ka isa soja ne alkur'an kar ka isa, yau na ga rana na hadu da tashin hankalin duniya da kiyama, wannan balaki da me ya yi kama "

Da karfi Hamza ya ce" Kai yi mana shiru daina hadamu da balakin kiyama ka fara tsayuwa a na duniyar, mu kuwa ba'a haduwa da mu sai an taka doka, kai kuwa lange lange da wata rigarka kamar buhu karaso mana na tabata ko menene laifin uban gidanka tare kuke shukawa!"

Jikin mai gadi ne ya fara rawa ya kai dubansa kan uban gidan nasa jiki a mace ya ce" Yau dubu ta cika an kama kwayoyin ne Alhaji?"

Wani irin zarro ido da Lawali ya yi kai kace idannuwan waje zasu faso su fito yana kallon mai gadin ya ce" Uban waye ke siyar da kwaya, kai dai an yi wawa mahaukaci walahi"

Hamza ya ringa gyada kai ya juya wajen da Kan Giwa ya gama sauraronsu ya tura shima ya shigo gidan ya ja ya tsaya ya harde hannayensa yana kallonsu ya ce" S??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ir kennan diler ne?"

Kan GIWA ya watsa hannayensa irin bai sani din nan ba

Budurwar da ta fito da wani damamen wando a jikinta ga dukkan alamu daga barci ta farka tana wara idannuwanta dan gannin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login