Showing 114001 words to 117000 words out of 124070 words

Chapter 39 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

335

maganar yafe kwanakinki?"

Daga hajia har Kan Giwa da matansa kallon NURIYAH suke, du sai ta daburce ta sake maida kanta kasa muryarta har tana rawa tace" Du abinda aka yanke Mama........"

"Ke da abinda aka yanke din ashatarki y'ar nan!"
Hajia ta fada da karfi har tana karkacewa

"Fada mata!" Muryar Kan Giwa ta biyo baya yana sauke mata harare da gefen idannuwansa wanda kowa ya gani

Hajia ta sake tabe baki ta ce" Shirmen banza , ke Hudaina tashi je ki huta na kula yanzun bakya jin rigimar, ni kuwa ras nake bani da abinda zai hanani a yi, ke Nadia kike ko wa? Saura kwana biyar cir ya dawo bangarenku, ka ji ashata kiri kiri yo Allah na tuba ni an nuna min rigima ne? Ke in ba dan ba ni na haifi dan nan ba da na rubuta maki takardar saki,yome ake tsinta a ke din, ke bama mace bace mai yiwa miji sallar dare bale ace sallar fa? Ke sin nan haka kike lange lange kamar ki karye, shima ban san jarabar da ta kaishi ganoki ba, ta yiwu idannuwan da kwasheshen leben!" Fada take yi kamar zata ari baki, du kallonta ake yi har ta dasa aya
Lokaci daya Nadiya ta sake fashewa da wani kukan tana fadin ba zata yarda ba, ta yaya za'a aurawa mijinta mace uar aikinsa kuma ace sai ya mata sati daya cir? Ita ba zata yarda ba

Djamilarrt ta yi murmushi tana gyara zamanta ta ce" Da nace maki wannan duwawu sunne daidai me kika ce? Yarinya mai kyau walahi, ni da aka mini ke me nace? Ke sai da kika yi wata da shi a garinku kuka dawo ki bar yarinya ta yi zaman dadi da mijinta" ta idasa tana yar dariya ta wulakanci wace ta sake hargitsa Nadiya, lokacin ne kuma Aba ya mike tsam ya nufi ciki ya bi hanyarsu ya tafi bangarensu, dan ya kula hannun da yaronsa yake jimkewa ba na dadi bane, ba za'a yi da dadi ba,
Yana shiga wayarsa ya dauka ya yi kiran numbersa
Yana dagawa a hade ya ce" Idan zaka samu pilote ka dauketa ku tafi wani wajen dan rigimar ta yi sanyi itama ta samu sakewa"

A hankali ya amsawa mahaifinsa fuskarsa na washewa da wani farin cikin mamaki

Yana kashewa sai da ya gyara zamansa ya ce" Aba ya ce mu tafi wani garin ta huta"...............



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
6?? 1??



Nanauyan barci ta yi wanda da kyar ta iya farkawa ta shiga wanka ta fito tana jin cikinta tamkar an mata sata
Shadar dake ajiye ta dauka ta warware ninkin tana wara idannuwanta, domin dinkin da kalar shadar gaba daya sun tafi da ita
Murmushi ta yi gannin harda sarka da dan kunne
Sallolin da suke kanta ta gabatar tana mamakin lallema ta fara zama raguwa, tafia a jirgi ba a kafaba ta kama barcin nan?
Da gagawa ta shiga saka kayanta bayan ta gama domin Mama ta yi kiranta cewa ta taho dining ana jiranta
Turare ta dauka ta yiwa kanta wankansa kamar yadda ta saba tana ji a cen kasan zuciyarta tana missing dinsa sosai

A hankali take saukowa bayan ta kashe daurinta sasauka da slifas din yawo a cikin falon a kafarta ta sauko daidai chef ta kicin ta zo wucewa
Irin gaisuwar da take mata ta sakata yin murmushi kawai tana kallonta ta ce" Aunty zan shigo da kaina"
Itama murmushi a wadace a fuskarta take amsata sannan ta bata waje ta wuce

Tunda ta tunkaro makeken table din idannuwansu suka sarku da junna
Kallonta yake yi tun daga kasa har sama sannan ya sakar mata lalausan murmushi, sai dai ga mamakinsa bata mayar masa da murmushinsa ba, hasalima kanta ta cire a kansa ta shiga gaishe da Mama da Hajia sannan ta nemi nufar wajen Murjanatu dake mata hira da yar dariya da nufin zama

"A nan zaki zauna fa" ya fada a sanyaye ainun a lokacin da ya mike ya ja mata kujerar gefensa ta barin damarsa
Kujerar ta kalla zuciyarta na tsintsinkewa, ta maida dubanta kan arniyar dake zaune a gefensa na hagu, barinsa kuwa Djamilarttt ce tuni ta shiga cin abincinta hankali kwonce
Numfashi ta ja ta sake kallon yannayin zaman, suturar dake jikinsa kanta sutura ce da ta dace ace tasu ce su matayensa, ama shine wannan katuwar mai faratunnan zaki ke mane kusa da shi, irin su sakashi tsakiyan nan ko?
Sai dai mutanen dake wajen ba zata taba iya kin zuwa ta zauna a wajen da yake nuna matan ba, jiki a mace ta karasa ta zauna tana jan kujerar da kanta

Komawa ya yi ya zauna yana sake kallonta, shi fa du hankalinsa ya gaza kwonciya, ba haka suka rayu da ita na sati biyun nan ba, ya rayu da ita kamar dadin zama da ita zai kaishi kiyama, sai yanzu ta ringa hade masa fuska?

Kasa kasa sosai ya budi bakinsa a lokacin da baby ke zuba abincin da mamanta ta umarceta kan ta zubawa kowa ya ce" Wai me yake damunki ne?" Yana fada ne yana kokarin kama hannunta

A hankali ta janye hannun nata ta sake lumshe idannuwanta tana daidaita nutsuwarta
Baby na gama zubawa ta zauna, daidai lokacin ne wa'inda basu fara ci ba suka fara domin Djamilarttt dai har ta gama, ciki banda mutun biyu, Kan Giwa da ya zubawa NURIYAH ido yana son karantarta, sai ita dake rike da cokalin cin abincin tana dokashi a cikin plate din yana bada wani irin sautin da ita sam bata ji domin ta afka a dogon tunani

Kusan kowa kallonta yake yi, ama ita batama san ana yi ba
Hajia kuwa idannuwanta kamar zasu fado kirjin NURIYAH ta fi kurawa ido, abinda take son sani daya ne tak shin ta saka breziyar nan ta yan matan zamani mai ciko ko kuwa kirjinta ne ya karra girma fiye da da? Ta san yannayin yarinyar ne dan tana zama a kusa da ita ba hijab, ko yaya iyaye kan kula da irin haka , bata da kirji sosai a yanzu kuwa ya wani irin tumbatsa, ita sam yanzun wannan shine a gabanta

Da sauri ya dake maida hannunsa wajen hannunta da karfi ya dora hannun nasa dan kar ta janye din yana kallonta da dan karfi ya ce" Hey Bab stop it, whts hppn hey"
Da dan karfi ta so janye hannunta ya rike ta ja ya rike, lokaci daya mama ta mike da abincinta tana kallon baby wace ta gane yarenta ta mike ta bita, hakama Hajia ta tabe baki ta zabgawa Elizabeth harara ta mike ta yi gaba ya rage su uku kawai

A hankali NURIYAH ta ja kujerarta baya ta mike tsayinta tana kallonsa kasa kasa ta ce" Zan tafi ka cikani pkz SIR"

Gabansa sai da ya yanke ya fadi, tsakani da Allah kiransa da Sir da ta yi sai da ya sakashi jin hankalinsa na tashi, sai dai lamarin yan gayu idan ya maka riko sai a hankali,
Hannun nata ya saki yana kallonta ta wuce da sauri ta nufi dakin Baby ba tare da ta waigo ta dube shi ba

Mikewa ya yi ya bi bayanta ya je da dan sauri kadan ya kama abin budewar ya murda , sai dai jin a rufe bam ya saka shi sake dora kansa kadan jikin kofar, abinda ya fi komai daga masa hankali ganewar da ya yi fushi ne take yi, kuma da shi, aman bai san dalilin fushin ba, gashi ko abincin bata ci ba haka babu wanda ya wani ci sai Djamilarttt, domin Elizabeth ta fi kowa shiga tashin hankali gannin bakon lamari, yau Kan Giwa ne ya mike ya bi mace dan ta ki cin abinci ta tafi? Ita fa tun dazu ta gane yarinyar cen wai kishi ne take nunawa a kanta? To ita bata san ko Nadia hakura ta yi da tsakaninsu da Kan giwa ta bar masu soyayarsu ba? Inma ba rigima irin ta fitsararun yaren zamani ba ina ita ina manyan kaya ne?

A hankali ya ce" In wani abin na maki, ki yi kokari ki fada min kin ji?"

Ganewar da ya yi ba zata ji shi ba ya baro wajen ya dawo falo inda suke zazaune ya zauna yannayinsa a birkice ya ce" Na kasa gane kanta, lafiya muka shigo palace din nan da ita, Hajia har da zan fito daga mota mun ajiye zan kaita da kaina wajenku na ja maki rai....shine zata ringa wasu abubuwa daban? Ko nan din ne bata so in maidata cen?"

Ba Hajia ba, Baby kanta sai da ta kusa kwarewa tana kallonsa, mamakinta mai girman gaske ne, wai a sati biyun nan ne yayanta ya karra haukacewa haka? Bata taba tunanin zata ga ranar da fushin mace ya sakashi a damuwa ba sai yau

Hajia ta fuskanceshi dan ta fara anfani da damarta ta ce" MU'AZAM, yaya ba zata yi fushi ba? Yaya hankalinta ba zai tashi ba?, Ai idan bata yi fushi ba sai na damu, bari ka ji idan ta nuna maka ba komai bane itama sai na damu na fara nemo maka wata matar, kai ka san matar arziki kuwa? Tana son mijinta ne domin Allah, dukkan hanyar da zata kaishi ga halaka zata yaketa da dukkannin karfinta, yaya kake tunanin ita Nuriyah mai sonka domin Allah ta saki rai ta zauna kusa da kai a lokacin da kake zaune kusa da wancen matar? Ita wancen din me dinka ce? Babu wanda bai san abinda kuke aikatawa da ita ba ciki kuwa harda NURIYAH, da ta yi hakuri ta amsheka a haka dan tana sonka ne, ama da wahala ta yi hakuri ta iya ci gaba da zama da kai a haka, kai wasu matan ko waya ba'a masu da matan waje a gabansu, wasu matan koda matarka ce idan ba ranar kwananta ba baka da dukunin kulata, kai ni din nan ba zan taba gannin mijina ya rungumi wata a gabana da ba muharamarsa ba mu ba rainon larabawa ba dan tsohon islanci na kuma kallonsa, kai na karkare maka ni a gaban jama'ar tasa zan zubar da hauka tunda ai lamarin dace ne, ama ta iya janyo kanta ta zo gabanmu, ta yi mana salamar musulunci, har hankalina ya tashi da ba dan na ji kukanta a jikin kafadun mamanta ba!, Yanzu fada min cikon rigar mama ce a jikinta ko nata ne?"
'innalilahi' Baby ta ayana a zuciyarta, so ta yi ta zauna ta ji kul uwar daka ta ji yaya zasu karashe zancen shikenan wannan hajiar tana maganar arziki ta wani shiga abinda ba'a tambayeta ba, to ita batama ga dalilin da zai saka a wani kamo maganar nan dan Allah, kai lahaula wala kuwata wannan ai ba dadi sam walahi!, Da sauri ta bar wajen a lokacin da yake fadin" Yanzu dama saboda wannan dan abin ne har zata wani daga hankalinta? Ama ai ba yau ba nake tare da eli, bayan wannan ni yanzun tsakanina da Elizabeth mutunci ne kawai, na fada mata ba zan iya aurenta ba, dama bamu hadu dan na aureta ba, kuma na fada mata na bar wancen rayuwar fa ko?"

Hajia ta sake kallonsa ta ce" Kai nace abin cikon nan ta saka a rigarta ne?"

Da haushi haushi ya dafe gaban goshinsa yana fadin" Ni sani na yi ne? Dan Allah je ki sa ta ci abinci mana , kar ta kwonta da fushi ta ki cin abinci, yanzu in ba yarinta ba a nan meye abin fushin? Kai mata kam sun ji dadinsu"

Hajia ta ringa gyada kanta ta cika ta batse tana kallo Elizabeth ta fice ama Djamilarttt bata tashi ba

Ya jima nan zaune ya juya ya kalli kofar ya juyo ya kalli Hajia har ya gane ba fa budewa zata yi ba ya mike jiki ba karfi ya koma wajen table din dan daukan wayoyinsa

A lokacin ne Djamilarttt tana masa murmushi ta ce" Ogana, nace yau ranar Elizabeth ne ko?"

Zuba mata ido ya yi da sauri yana kallonta, ranar Elizabeth?
Kansa ya cire ya dauke harda ky dinsa sai ya sake kallonta ya ce" Bakya so na zo ne?"

Daria ta yi tana dan mikewa hadi da juyawa kadan ta ce" Ba haka bane wo, na dai fi so kana ta molewa sosai sosai ne..........ni babu damuwa na ba amalya ko Elizabeth wo....."
A da idan ta fadi haka , irin ta nuna ta bara ma Nadia ko Elizabeth shi abin na dan damunsa kadan, ama sai ya yi tafiyarsa wajen Elizabeth din ta kwana tana kula da shi, ama a yanzu abu daya ya shigo masa kwakwaluwa shine zamansu da NURIYAH, da farko idan yana so su kusan raba dare sunna abu daya idan ya nufita yakan togewa yana yi mata kallon kasa kasa dake mata nuni da abinda yake da muradi, kafin a hankali ya tambayeta shin ya zo ne? Takan buda masa hannayenta tana yar dariya, tarin annurin dake kan fuskarta shi yake haukata zuciyarsa, har yake samun gamsuwa da ita sama sama ba tare da ya ratsata ba, ama a yanzu sai ya samu kansa da tunanin Djamilarttt bama matsalar rashin sha'awa ke damunta ba, harda matsalar rashin sannin ciwon kai da shegen son abin duniya da ta saka a gabanta, irin su Djamilarttt anya ko kaurace mata ya yi kwata kwata zata damu kuwa? Sai dai fa ya kona kansa in yana so ama ba dai ta wani kawo masa gyara a wani bari na lamarinsa ba
Ficewa ya yi bayan ya sake kallon kofar ya tafi

A daren nan ita din da kanta barcinta kadan ne, bayan sun sha hira da baby, sun sha da Hajia, mamanta ta yi kiranta ta mata nasiha da sanyayar mata da zuciya ta nuna mata kar ta tsananta fushinta, kuma hakanma da ta yi ba laifi ta nuna masa ta kyakyawar hanya bata masaa shirme ba, kuma abin ya shige shi, so idan ya sake ganewa ya nemi kusanci da ita ta bashi dama, ta cika cikinta ta kwontar da hakarkarinta sai dai barci ya gagareta, kwana ta yi tana cenza yannayin kwonciya da juye juye da rukunkume filo hadi da sauke ajiyar zuciya, karshema bayi ta shiga ta yi kukanta ta fito bayan ta daura alwallah, tana saman salaya aka yi kiran sallar asubahi, tana gabatar da sallarta ta cenza tufafinta ta sake neman barci domin a yanzun tana jinsa sosai
Ai kuwa barcin ya dauketa har sai kusab karfe goma sha daya na safiya ta tashi ta sake kimtsawa ta yi walaha sannan ta fito da hijab dinta
Mutanen da ta gani zaune ya sakata zarro ido hadi da karasawa da sauri tana ambaton sunnayensu farin ciki fal tare da fuskarta
Mahaifiyar yayanta ce wanda ya mata sanadiyar zuwa gidan nan, da shi yayan nata, da yar uwarsa suka kawo masu ziyara a yau

Kunya da nauyi ke dawainiya da ita baba din irin yadda aka amshe su a gidan nan, wai dama wannan aljanar duniyar gidan auren yarinyar nan ce da suka wulakanta?, Uwa uba ita din kanta irin yadda take cike da matsanancin farin cikin ganninsu ya basu mamaki, kofa yake dama sun jima da fahimtar du inda ta fito yar mutunci ce tun a lokacin fa take fita nemanta ta dawo su amshe bata daga kai ta kale su bale ta fadawa mai gidanta ya mata maganar hakan

"Yau dai ga babarki ta zo Balaraba har sunna haramar tashi , shigata biyu fa dakin kina ta barci , mijinkima zuwansa uku a kulle baya samun shiga " hajia ke fada wace ta fito bayanta ma'aikatan gidan ne dauke da kaya jina jina da ta yiwa mutanen da suka rike Nuriyah alkhairinsa,

Yar hira suka karra yi du ba a sake ba, yayanta nema shi a sake yake domin dama sunna zumunci aikinsa nema yake da yawa ya da sukan dan dauki lokaci badu hafu ba, sukan gaisa a wayar Baby dai , kuma da shi aka yi daurin aurenta da komai, bai dai san tafiyarta ba ama ya san dawowarsu shi yasa ya kawo mamansa da ta damu kan ya kawota ta gaishe da Nuriyar

Rakiya sukai masu har filin gidan, inda motarsa take
Mamansa ta shiga da kanwarsa ya dakata jin NURIYAH ta yi kiransa
Ambulop din da Hajia ta bata ta basu ce ta bashi, sai dai ya nuna ba zai karba ba, domin ko kayan cen Hajia ta fi karfin ya nuna ba zai karba bane ya saka ya karba
Fuskar mamaki ta yi tana fadin" Yaya a kan me ba zaka amsa ba? Yaya na dan ban isa na baka wani abin ba aman ai yar uwata na ba ba kai ba ko?"

Shima da kula ya ce" Aya, aya, kin fa san sarai dalilin da ya sa ba zan yarda mamanmu ta ji dadin zuwa wajenki ba, sam bana so kudin nan su shiga hannun mamana, kin san dalilina na yin hakan, ina fama ne ina kuma fadawa Allah kan ya dafa min lamarinta a samu sauki a ciki koda bata cenza gaba dayanta ba ya kasance an samu sauki a lamuranta....kar ki ga haka, ko zuwan nan sai da kyar na iya amincewa dan du gani nake yi a yanzu da kika zama wani abu mama ke son hulda da ke"

A hankali ta girgiza kanta ta langwabar da kanta ta ce" Aya yayanah, ka yi hakuri ka daidaita harshenka idan kana magana a kan mama, ka sani kowani bawa da kalar kalubalen rayuwarsa, alhamdulilah mama bata fita waje ta dauko maka magana a wajen makota ba, ka ga kuwa da sauki, la ci gaba da fadawa Allah in sha Allah watarana sai ka yi mamakin Mama, a hakama mataki ne na cenzawar domin idan wata ce cenzawar rayuwar tawa zata sake rufe mata ido har ta ji tana kunci a banza a wofi.........dan Allah ka amshi sakon nan ka ba Mama, nima zan je gidan da zarar hankalina ya sake kwontawa"

Ajiyar zuciya ya sauke ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login