Showing 72001 words to 75000 words out of 124070 words

Chapter 25 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

349

min, kai ka san wahalar da na sha domin kai ka taimaka min na fadi gaskiya, Oga wannan matar dake kawo min tuwo lokaci zuwa lokaci HASANA ce"

Ya saurara yana murmushi ya ce" haka na shekara biyu a gidan yari na fito na koma wajen Hasana....., Daga wannan lokacin na ringa zama da son sannin abinda ya faru da wannan baiwar Allah, na takaice maka sai da na tabatar da mijinta ya saketa ta bakin yayata sannan na sheda mata, na ci gaba da bincikar y'arta da matar dake rikonta, sau biyu muna magana da matar dake rikonta da hasana ta nuna idan har ta amsheta tabas wata rana matar mijinta zata san inda muke ta sake binmu, du soyaya irin ta uwa da y'aya haka ta hakura daga bayama muka neme su muka rasa , Oga dai yayata da mijinta azalumai ne walahi, wai ita yayata dan rashin kunya sai ta bushi kasa ta kirayeni ta jadada min na fa halakaa Hasana fa, dan bakin iskanci idan na halakata ko na zauna da wa?"

Kan GIWA ya ce" Kana nufin tana raye tare da kai? A kauyen?"

Yusuf ya yi murmushi yana fadin" Mu je ciki ka gani"

Binsa Kan GIWA ya yi yana jin muryar da ta amsa salama mai sanyi da fita a nutse

A hankali ta fito da wani niimtacen murmushi a shinfide saman fuskarta tana fadin" Yau da wuri aka shigo haka malan Allah ya sa ba yinwa ce ta koro min kai ba "

Sai kuma ta tsayar da maganar tana fadin" Au da baki kuke tafe? Bismillah Bismillah " ta juya ciki dan dauko tabarma

Bayansa ya jinginar da garu yana kallon Yusuf ya bi bayanta ya shiga furta "Alhamdulilah " a hankali yana kallon kofar

Sun jima a ciki dan a kalla sun dauki minti goma sha a ciki kafin suka fito
Fuskarta ce ke nuna ta ci kuka sosai, sai hijab din jikinta da ta cenza ta karaso a sanyaye tana kallonsa muryarta na rawa sai kuma murmushi hade da muryar kuka tana kallonsa ta ce" Wai haka? Wai Husaina na tare da kai? Da kuma NURIYAH ? Wai su Aba basu rasu ba? Da Malan ke ce min na yi hakuri in sha Allah Allah zai sharen kukana ashe haka din ne? Dan Allah zaka kaini kuwa? Zaka kaini wajensu?" Ajiyar zuciya ya sauke ya gyada mata kai ya fuskanci Yusuf yana fadin" Zan so ace sai duhu ya shiga ku shigo Palace, zan so na dawo da kaina na dauke ku bayan na fada an shirya zuwanku, dan ita maman Auta tana fama da laulayi kar abin ya daketa ya saka mata wani abin , na ji an ce mai ciki bata son emotion mai karfi?"

Hasana ta kalle shi a sanyaye ta ce" Ciki? Wayo Allahna, Allah abin godiya, wai da ni har na saka hijab ka gani"

Murmushi ya yi mata mai girman gaske yana jinta a ransa, a hankali ya samu kansa da rike hannunta tamkar mamansa ya ce" *MAMAH* zan dawo da an jima, a nan zan salaci magariba, na dauke ki da darajarki na sadaki da y'ar uwarki da kuma, um da kuma NURIYAH.....i kn wait to see irin smil din da zai wanzu a fuskokinsu"

Su din kansu sun fi gamsuwa da haka, a haka suka fice a gidan ya salami su Hamza suka wuce da Matar Lawali dake ihun ai ba ita kadai ce mai laifin ba, kuma Yusuf hala ya kashe masu y'ar uwa ne? Shi dai Yusuf da ido ya rakata , sam bai ji dadin haka ba, aman kuma bashi da ja gaskiya, bai ga me ta masu ba , saima sune suka yi mata a rayuwa, duda haka suke binta da bita da kulli ?

______________________________________

"Barcin la'asar kike yi ne an matana?" Mama ta sake fada a sanyaye tana kallon Nuriyah dake kwonce a saman cafet ta yi ruf da ciki, tun bayan tafiyar su Kan GIWA ta kasa katabus, duda ta ji Hajia na fadin ya dawo aman ita ta kasa wani motsin kirki

Mama ta yi murmushi tana cewa" Saman idannuwanki na motsi fa, kin kasa zama mu zanta , tashi na gani zo na rungumeki"

Wayo kunya, ita walahi abin sai yake bata wata matsananciyar kunya, katuwa da ita a ringa mata magana kamar wata baby? Koda suke irin haka da baby ita kulun mamakinsu take ji, shine yau abun zai hau kanta

Idannuwanta ta bude ta mike zaune tana dan murmushi hadi da sosa kanta ta ce" Mama barci fa nake yi"

Baba ta yi yar dariyar da rabonta da ita an jima tana dungure habarta ta ce" Lalalala, ba barci a nan, idannuwanki biyu, taso maza ki yi wanka ki cenza rigar nan mu je ki ci abinci baby har ta ci ta tafi wajen malan tace yau a barki ki huta wai kin yi kuka"

NURIYAH ta sake sada kanta tana sauke ajiyar zuciya jin magangannun matar na samun muhali a zuciyarta

A sanyaye Mama ta ce" Wai haka kin sha kuka? Aman me yasa kika sha kuka? Yarinyata ko fushi kike da ni? Ko fushi kike yi da mamanki? Kina ji kamar kin tsane mu ne?"

Da sauri Nuriyah ta kalleta tana kwalalo idannuwanta waje hadi da rufe bakinta da hannunta
Mama ta yi murmushi tana cewa" Kar ki ji tsoron fada min, ko me kike ji a ranki, nifa mamanki ne, nice nan mamanki nice umanki fa"

NURIYAH ta tsatsareta da ido sai kuma ta fara magana muryarta na sarkewa ta ce" Ban tsaneku ba, walahi ban tsane ku ba, ni na kasa ganewa ne mama ke yar gayu kece y'ar uwar mamana? Ni ina farin cikin ganninki kuma idan na ganku ke da mamana ko yanzu na mutu burina ya cika Mama, gaba daya komai ne ya girmame ni mama komai ya min girma sosai mama....."
Sai kuma ta dora kanta a hankali a gefen kafadar Maman tana ta sheshekar kuka, maman kuwa ta shiga dan bubuga mata bayanta a hankali tana dan shafa mata bayan a sanyaye ta ce" Haka yake ce maki ya tsane ki ko? Haka yake korarki ko NURIYAH?"

A hankali Nuriyah ta gyada kanta, a sanyaye ta ce" Cewa ya yi ba shine abana ba, bai haifeni ba wai na daina zuwa inda yake"

Idannuwanta ta lumshe a wani sanyayen ta ce" Ni ina sonki, kuma mamankima haka, abinda na sani ke ba shegiya bace, kuma kina da dangi NURIYAH, shi kuma ya yi ta yi dan kansa, yadda ya tsaneki ni na fi tsanarsa, tun asali bana sonsa ita ta nace!"

A hankali NURIYAH ta dago ta sauke Idannuwanta a kan fuskar Husaina, sai ta ga Hajia a tsaye cikin hijab dinta da carbinta tana ja tana kallonsu

Murmushi ta sakar mata tana fadin " Tashi ki je ki yi wanka ki sauka kasa da gagawa ki zubawa yayanku abincinsa yana saman table bai ci komai ba yinwa yake ji NURIYAH "

NURIYAH ta yi wani kasakai tana kallon Hajia ta ce" Ni kuma?"

Hajia ta ce" Eh ke mana"

NURIYAH ta sada kanta tana ta tunanin to du jama'ar gidan nan sai itace za'a ce ta je ta bashi abinci? Bayan wannanma matansa fa? Ta ga dai rabonta da wannan aikin tunda ya nuna baya so ko?

Sai dai gannin hajia ta karaso ta zauna fuska daure sai ta mike ta shiga wankan da gagawa

Hajia ta sauke ajiyar zuciya tana fuskantar Mama ta ce" Ki fa kiyayi karfin jinni Husaina, kar ki yi mamakin ita da aka fi cutawa ta yafewa mahaifinta, domin babanta ne"

Da mamaki Mama ta ce" Uma, yanzun Nuriyah sai ta yafewa Lawali ? Du irin abinda ya mata?"

Hajia ta gyada kanta tana fadin" Sosai abu mafi saukima kuwa, bara na cirowa Nuriyah kayan da zata saka ina zuwa tare fa nake da albishiri mai dadi"


Cen ta koma ta daukowa Nuriya wata riga da sket na tampa, dinkin da ya fito aka kuma yi karamin dinki da shi da dan kwalinsa kawai ta kawo

Tana zuwa ta fito ta mika mata hadi da ajiye jan baki da turare

Kayan ta saka ta dan fefesa turaren tana daura dan kwalin hadi da eaige waige dan neman hijab dinta Hajia na murmushi ta ciro jan bakin tana fadin" Gaskiya Husaina sai kin yi da gaske a kan y'ayanki, babu mai son kwaliya , mace kuwa ai y'ar kwaliya ce ko? Duba ki ga wani dauri ko ni albarka ta kinshime gashin a ciki ita ga ta ladan....." Ta karashe tana daria ta mayar mata da daurin dazu ta goga mata jan baki ta ce" Maza jeki, gamunan zuwa muma"

NURIYAH jikinta a mace ta ce" Hajia yanzuma zan yi abu kamar matar tasa ne ko? Aban ya ki ya fadi inda Uman nawa take ko?"

Hajia ta kalleta sai kuma ta yi murmushi tana nuna mata hanya ta ce" Je ki dawo sai mu yi maganar, maza kawaliya je ki dawo"

Jiki a mace ta mike ta tsaya ta kalli kanta a gaban madubi, har ga Allah sai da ta ji kunya ta rufeta, kugun nan nata sai a hankali kara fadi yake yi, uwa uba dinkin ya dameta dam bama kamar kirjinta hannayen kuwa an masu wasu tsagu har wahen tsintsiyar hannun, haka kuma aka gangaro kan daurin nan gashinta duka a baje a bayanta, kuma jan bakin nan ai fiysara ne tsakani da Allah

Sake waiga su ta yi ta ga sai hirarsu suke ta juya tana ta tunanin me haka kuma?

Tana tunanin nan har ta sauka ta nufi dining din ba tare da ta kalli wanda ke sama ba ko tunanin ko ba shi kadai bane, tana ta tunanin maganar zirr da yace dazun

A hankali ta dago jin kamar ita yake kallo ta zuba kwayar idannuwan nata cikin nasa

Da sauri ta so cirewa saboda kallon kin rainanin nan da ta gani yanai mata

Kwalkwalkwal ta yiwa idannuwanta ta karasa da dan sauri ta rike kujerar hawayenta na balewa ta sauke masa duban tashin hankali ta budi bakinta ta ce"










Sun yi niya su kahe hi da ransa=??=??=??=??=؃?=؃?=؃?



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
4?? 6??


Maganin baki bakin fuska wanda shafe shafen wani abun ya haifar ko cin wani abin dai da sauransu..........

*Da farko sai an yiwa fuskar siraci dan kofofin fatar su bude, da zarar kofofin sun bude ki dauko lemon tsami ki raba biyu ki matse cikin kofi , sai ki kawo kwai ki zuba farin ruwan banda yelow din , sai ki cakuda ki ringa shafawa a fuskarki du yamaci ....zaki sha mamaki aman ki jure daukan dan lokaci domin shi abu natural yana da dan tsaikon kamawa, sai dai idan ya kama din bashi da mugun sakamako sai kyakyawa in sha Allah*



Ido ta tsurawa numbar dake kiran, numbobi ne masu kamanceceniya da junna, gashi duhun magariba ya fara kawo kai sosai domin har an kunna dukan wata na'ura dake dauke da hasken kwai mai haska palace din gaba daya , haka kuma sanyin magariba ya sanyo kai sosai

Muryarta a sanyaye ta yi salama ma number domin ba sunna a jiki, sai dai jin Shirun da ya wakana ya fi komai yawa ya sakata sake maimaita salamarta a sanyayenta tana jin kirjinta na dokawa da mugun karfi haka kawai

Kittt aka datse kiran, wanda ya yi daidai da jin kamar an datse mata wani abu da take son ji da dukan muradin zuciyarta

Sake zubawa allon wayar ido ta yi sai ga wani kiran ya kuma shigowa, sai dai wannan karron da sunna a sama an rubuta BESTY M a jiki, hakan ya sakata gane Mamy ce ke kira yanzun, dan haka sai ta faga da dan murmushi hadi da sauke ajiyar zuciya tana fadin" Asalamu alaikum Mami bara na kai mata wayar"

"Amen wa alaiki salam......." Ya amsa da dan saurin da ya sakata ja ta tsaya kikam tana jin yadda yakr sasauke ajiyar zuciyar shima a bangarensa, sai kuma ya ce" Dan Allah kar ki kai mata wayar nan, ki riketa a hannunki ki sakata a kunnenki ki yi ta saurarona koda ba zaki bani amsa ba NURIYAH"

Wata zufa ta ji tana neman karyo mata, a hankali ta koma ta zauna ta kai hannunta saman gashin kanta ta shafa dan ta dan samu kwarin gwuiwa, sai a lokacin ta ji gashin kanta a waje yake bata da dan kwali a kanya, hakan ya sa ta kamo jelar tana zarro ido a bayane kasa kasa sosai ta furta" Ya salam dan kwalina"

"Na'am?" Ya fada dan bai ji da kyau abinda ta fada din ba

Nuriyah ta sauke ajiyar zuciya tana kawar da firgicinta a hankali ta ce" Ina yini yaya"

Murmushi ya yi ya mike ya bar dakin kanwarsa da ya ritsa kan yau sai fa ta hada shi waya da yarinyar nan domin shi ya kamu, yana sonta zai aureta ya yi ta biyu da ita, ba dan matarsa ta gaza masa komai ba, kawai shi sonta ne yake yi, kuma yana fata ta zamto daya daga cikin iyayen y'ayansa, ba ruwansa wai dan iyayenta basu da kudi ko me, ba ruwansa da komaima shi ita din yake so

A nutse ya shiga gabatar masa da kansa , sai da ya gaba ta yi dan murmushin da ya saka shi fara sarewa da fara tunanin anya zata karbi tayinsa a guje kamar yadfa yake hasashe? Duba da shi dai namiji ne har namiji, sannan aljihunsa da nauyi ba laifi, haka kuma ya tara nasaba a tare da shi

A hankaki ya ce" NURIYAH, ko dai zuciyarki ta yiwa wani waje yayanki bawan Allah ba zai samu gurbi ba sai dai a bar kokonsa ba nauyi?"

Nuriyah ta buda idannuwanta da ta lumshe a hankali tana aauna maganarsa, kafin ta ce" Me ka gani yayanku?"

Murmushi ya yi ya ce" gani na yi kamar baki gane manufata ba, bayan na share kusan sati ina faman a bani numberki dan na gabatar da kaina, a kaf tarihin rayuwatama zan iya ce maki gaskiya ko a da da baba ke bani kudin school bana yiwa yarinya naci haka, aman a yanzu sai nake ji na damu sosai, Nuriyah shin baki gane ina sonki bane?"..............

Ido ta zarro cike da jin kunyar furucinsa ta saka hannunta ta rufe idon nata murmushi na kubce mata domin bata zata zai fadi maganar kai tsaye haka ba, duda ta kula yayan nasu ba dai surutu ba ashe........

A sanyaye ta byde bakinka jin ya ci gaba da faman sai ta bashi amsa ta ce" Yayanmu, masalatai ana kiraye kirayen sallah, ka taimaka ka mike ka je ka yi sallah sai mu yi waya idan an jima "

Yar dariya ya yi yana fadin" Kennan dai kin karbeni?"

Itama yar dariyar ce ta yi kadan sanann ta kashe layin kiran tana kurawa wayar ido , sai kuma ta mike jin sosai kiran sallah ake yi ta ko'ina

Juyowar da zata yi ta ga Hajia tsaye hannayenta harde tana kallonta

Da farko har ta tsorata dan yanzun kam kakar nan tasu ta fara bata tsoro, sai kuma ta saki murmushi itama gannin hajiar ta sakar mata murmushi tana fadin" Watau zance kika labe yi da mijinmu a nan kika barni ina walagigin nemanki a cen ko?, Taso zo nan yarinyata"

NURIYAH ta karasa wajenta cike da jin kunya da nauyi ta mika mata hannu kamar yadda ta bukata, a sanyaye Hajia ta ce" Zo mu je falo Baki fa kika yi"

Gaban Nuriyah ya yanke ya fadi jin wata magana kuma bakuwa , baki? Kuma hajia ta zo nemanta? Wasu irin bakima tukunnan? Ita dai bata taba yin baki ba a gidan nan, wanda ya kawota kan zagayowa ya ganya su sha hira ya sake tabatar da bata da damuwa ya komawarsa domin Shima aikinsa mai matukar girma ne akoy daukan lokaci, aman kuma baki? Hakan na nufin mutun sama da daya, sannan irin yadda ta ga jikin hajiar a mace duda dariar da take dorawa fuskarta ya so ya dan dameta

Aman dole ta bi bayan hajiar tana ta son tambayarta abinda zata rufe kanta, aman wani tunanin ya sha gaban wani

Tunda suka shigo falon ta ji kafafuwanta na son neman gagarar daukanta sakamakon muryar kukan dake dan hauhawar mata kanta
Jan da ta yi ta tsaya ya saka Hajia juyowa tana kallonta sanann ta sake riko hannunta ta janyota tana fadin" Mu je mana"

Maganar hajiar ya ankarar da dukan jama'ar dake falon, wa'inda matan ne kawai domin mazan sun wuce masalaci su hudu , watau Kaka, da Baba, da Kan Giwa, sai mijin Mamanta

A hankali Maman ke kallonta , gabanta na sake faduwa zuciyarta na tsintsinkewa
Y'ar uwarta dake zaune a jikinta a saman cafet su dukansu biyun itama ta zubawa NURIYAR ido tana son gannin r?action dinta a gannin mahaifiyarta a ba zatan nan, Murja autama dake sharar hawaye cike da tausayawa yan uwa biyun sai ya samu kanta da labe fuskarta tana toshe bakinta dan kar ta barke da wani kukan kallon kallon da Y'A da Uwa ke yiwa junnansu tamkar basu sheda junna ba

A hankali Maman NURIYAH ta ce" Husainata........ Yalabai da ya daukoni yace NURIYAHma a wajenki take........, To aman wannan y'ar kamar y'ar indiyawa ai ba ita bace ko?, Duda a lokacin da na ba Baba ita na kula kalar gashinta ba baki bane har daga baya ita tunanin ta yiwu wani ciwo ne, mai yiwuwa ko ta rasu da ciwon?"

Husainar ta karra rintse idannuwanta tana tunanin mai rabata da Lawali kam sai Allah, walahi walahi na zata barshi haka ba, ba zata taba barinsa ya ci bulus ba, ko haushinta Nuriyar zata ji sai dai ta ji!

Hajia ta sake janyo hannun NURIYAH, sai dai wannan karron ta ja ta tsaya a waje guda ta ki nuna alamun zata motsa , hakan ya saka Hajia sake kureta da ido ta ambaci sunnanta da kulawa

Kamar a firgice ta kalli Hajiar, sai kuma ta sake kallon wajensu, muryarta a shake sosai ta ce" Hajia, kalli kamarsu daya ko?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login