Showing 45001 words to 48000 words out of 124070 words

Chapter 16 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

336

bulbula a jikinsa

Ta madubin ya saci kallon Rislan din da ya tabata shine ya fitar da abincin nan da ya kwana a nan sannan kasa kasa sosai ya amsa masa gaisuwar da yake yi masa

Rislan ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" Yaya fita zaka yi?"

Kan Giwa ya sake kallonsa kadan cen cikin makoshi ya ce" Oummmm"

Rislan ya dan daburce dan sai ya ji ya samu wani irin shaku na maganar da ya kunso a bakinsa, sai dai ba zai iya ba idanma dukansa zai yi sai dai ya doke shi, dan haka ya rintse ido yana fadin" Yaya"

Kan Giwa ya sake dakatawa da kokarin bala boturan rigarsa na cen sama yana kallonsa da kulla , dan ya kulla akoy abinda ke damunsa

Rislan ya kikifta idannuwansa hawayen dake cikin zuciyarsa suka farra samun gurbin zuba ya hade hannayensa ya shiga fadin" Yaya, wannan rayuwar na damuna, wannan rayuwar na sakani a tunani, yaya Matayenka sunne ya dace ace a gidan nan sunne iyaye, sunne bangon du wani wanda yake cikin gidan nan domin Kaine baban yayau, kaine babanmu, kai muke kawowa kukanmu, tunda muka rasa mahaifiyarmu ka rikemu bamu nemi komai mun rasa a duniya ba daga mu har iyayenmu, Yaya sai dai wa'inda ke tare da kai da suke wasu iyayen namu sam mun kasa samun nutsuwar da ta dace da su, basu da lokacinnka bale su fuskanci rayuwarsu su daidaita abinda ke damunsu, yaya yanzu ace kai da girmanka da darajarka aman baka da lafiya har ta kaika haka? Why ba zaka daidaita masu tunaninsu ka sauko su su fuskanci rayuwa ba? Yayanmu ba haka ake rayuwar aure ba, ba haka ake zama da mace mai daraja ba, yayanmu ina kwadaita maka zama da mace mai mutunci mai daraja wace ta san ciwon kanka, yayanmu................." Tsitt ya yi sai hawayen da yake zubarwa a idannuwansa yana kallon yayansu da ya zuba masa manyan idannuwansa yana kallonsa shima

Dan murmushi ya yi hadi da juyar da kansa a hankali ya ce" Rislan ka san karfe goma sha daya zaka tashi ko?"

Rislan ya sada kansa kasa bai iya bashi amsa ba, saima kukan da yake hanna kansa yi ne da ya kwace masa wanda ya saka Mu'azam wara idannuwansa a kansa kafin ya saki murmushi mai sauti ya matso a hankali ya kama hannunsa ya zaunar da shi bakin bed yana kallonsa a hankali ya ce" Kuka kuma? Sai kace yar budurwa?"

Rislan ya ringa cije lebensa yana ta son goge hawayensa,
Kan giwa ya rike hannunsa yana kallonsa ya ce" ka yi kukanka Dan uwana, ka min kuka ka ji? Ka min kuka sosai, domin nima a jiya na yi kuka....Rislan na yi kuka cikin shiru harma na so ilata kaina, babu irin tunanin da ban yi ba, haka kuma na yarda cewa ashe zama lafiya da mace mai nagarta shine farin cikin rayuwa ba neman kudi na, ka ga ni na fi ba kudi mahinmanci sama da komai, shi yasa na je na zabo masu tsada na aura sannan.......Rislan sannan na rike Izabel a gaban kowa a idon kowa nake mu'amalantarta tamkar iyalina hankalina kwonce.............."

Ya dafe gaban goshinsa ya ce" Rislan ta yiwu dan na maida zinna ado ne Allah ke kamani ta nan, ko kuma gaba dayane ban iya shinfida rayuwar iyalina bane har na fuskanci haka? Rislan mata ne sai na nemo su du takamar tawa? Kuma idan na nemo sun ba zan taba samun nutsuwar zuciya ba?, Saima na yi wani fahimta da matan nan guda biyu jiya zuwa yau da suka ga barazana ta ina iya duban watansu a matsayin raya sunna ba watsewa ba suka haukace suke neman hanyar daga min hankali ta kowace fuska, sannan ka san abin takaicin.....?"

Rislan ya girgiza kansa da sauri cike da tarin takaicin matan nan , yayansa ya dan yi shiru yana tunanin shin ya fada masa a duk goce gocensu dan nuna yana da bukatarsu da ya yi ne aka sake daukaka bacin ransa ko bai dace kanninsa ya san irin haka ba?

Ajiyar zuciya ya sauke yana fadin" Miko min abincin na ci sai mu tafi A?roport na raka ka"

Rislan ya mike ya dauko abincin ya matso masa da shi a ransa yana ayana' babu inda zani walahi sai na hannawa matan nan zaman lafiya tunda mahaukata ne su!, Sai na koyar da su iya rike miji a matsayina na namiji, dan kuwa akoy mata a duniya su din ba sunne kadai karshen da suka rage ba da har zasu wulakanta aure haka ba!

Kwonkwasawar da ake yi ne ya saka Rislan bada damar shigowa yana budewa yayansa abincin yana saka spoon

Da sauri ta karaso da salama a bakinta fuskarta na nuni da ta ci kuka ne ko menene? Fuskar dai a kumbure domin sai dazu ne Nuriyah ke fada mata dukkan abinda ya faru cewar yayanta bashi da lafiya, shine ta haikace ta fashe da kuka da kyar Nuriyar ta lalasheta ta janyota ta rakota su gaishe shi domin ita yanzun matansa sun sa du ta tsani lamarin gidan

"Yaya me ya same ka? Me ya same ka? Yah Rislan ni ban san bashi da lafiya ba, jiya dare muka yi muna yin dambun naman nan, cikin dare ne Nuriyah tace zata zo ta kwashe komai dan ya tsane mansa , ni kuma barci ya hanna min fitowa da na san bashi da lafiya, ko da Mama ta ce ya ci abinci na ce mata eh ya ci, ashe bashi da lafiya, NURIYAH ta ce hannunsa ya kumbura ta ce jikinsa zafi, ta bashi ruwa kuma ta kirawoka Yayanahhhhhhh wayo Allahna....." Ta karashe maganar tana riko hannun yayanta da ya kurawa fuskarta ido tunda ta farra kayaniyar nan
Abinda ya iya tsinta wanda ya dawo masa da tunanin aljanar da ya gani tsakiyar dare ko mafarkin da ya yi a jiya cikin idannuwansa daidai Nuriyar ta shigo tana rabewa ta duka daga cen nesa da wannan zumbulelen hijab din nata tana mai bude muryarta mai sanyi da alamun tsoro wace ta yi masa magana da ita a jiya da farko kafin ta kula da hannunsa ta rikice ta rikeshi a lokacin da bata shiryawa hakan ba

A hankali ya lumshe idannuwansa ya sake budewa ya zuba mata ido , a saman lebensa ya bude bakinsa cen kasa kasa sosia ya furta" NORIYAHHHHHHHHHHHHHHHHHHHHHHHHHHHHHHHHHHHHH?"








=??=??=??=??=??=??=??=??=??=??






*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
3?? 3??

*I'm sorry yau kadan ne, ina matukar son gama shi kafin azuminma abin na neman min cikasssss, in dai ba so kuke mu ce fatiha an daura , bayan shekara goma sha biyar sun aurar da yarsu =??>?#? @&?=؃? wollah na aika*



A saman lebensa ya ambaci sunnantaa lokacin da Auta ke ta maimaita sunnan a cikin bayananta, sai aka taki sa'a ita dinma ta dago a hankali ta saka Idannuwanta a cikin nasa, lokaci daya sai lokacin da ta talabo shi ta kafa masa ruwa a bakinsa tana ambatar masa ya sha ya fado masa a ransa

Da sauri suka dauke idannuwansu a kan junna a tare, wanda hakan a kan idannuwan RISLAN ya faru
Mikewa ya yi daga zaunen da yake ya juya ya dauki karamar wayarsa dan ya tabata kakus tana cen ta rikice masu rabonta da shi tun jiya da sasafe basu yi wayar sasafen bama ta gado

Kannensa ya sake kallo da suke shinfide da yannayi na damuwa da damuwarsa ya sakar masu Murmushin da bakinsa saman lebensa ya juya yana fadin" Idan kun gama ku rufo dakin ina zuwa"

Baki sake Murjanatu ke kallon kofar da ya fice ta juyo tana fadin" Yah Rislan ina yaya zai tafi kuma? Ba shine ba lafiya ba? Kalli hannunsa fa ima zai tafi ne?"

Yar dariya ya yi shima yana fadin" Ni kam hakan ya min daidai ya manta shi yace yanzu zai kaini a?roport, a hakan da ya manta ta fi gyarani ta fadi gidan sauki Walahi "

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon Nuriyah ta ce" Nuriy sai ki tashi dodon naki ya tafi fa"

Nuriyah ta sake dagowa tana mikewa jikinta tamkar an cire mata lakka ta juya itama tana fadin" Bara na koma na hada kayan wankinmu Auta bana son wankin naj na inji sake kashe min jiki yake yi, na fi so na darj..............." Dif ta dauke wuta sakamakon goshinta da ya hade da kirjinsa a lokacin da ya dawo ya bude ya shigo

Shima idannuwansa ya sake dorawa a kanta yana binta da kallo irin tsoratar da ta yi ta yi baya tana wara manyan idannuwanta a saman kansa lokaci daya kuma ta nemi sake rikicewa irin na jiya da ta yi , watau ta daburce tana ta neman bashi hakuri da dukkan gaskiyarta

Haka kawai ya ringa ji a zuciyarsa tamkar ya riko hannunta ya bata hakuri kan doke mata goshi da ya yi, sosai ya ringa jin bakinsa zai bude ya nufeta ya rike ya ga goshinta ko ya ji mata rauni ne? Sai ya ringa ji yana so ya ce mata ta daina bashi hakuri bata yi masa komai ba
Aman sai ya kasa aikata hakan yama juya wajen Rislan yana fadin" Ka yi ka fito a kaika a?roport Likita"

Ya kuma juya wajen Murja yana fadin" Baby me ya hanna malaminki na islamiya zuwa kwana biyu?"

Auta ta ce" Yaya rasuwa aka yi masa ne, sunna zaman makoki ai Hajiama ta je ta yi gaisuwa"

Sake juyawa ya yi bai ce komai ba, da sauri Auta ta sake daga kafarta ta bi bayansa tana fadin" Yaya, dama , dama dan Allah ina so yau mu je shan ice cream"

Dan sake juyowa ya yi yana kallonta daidai Djamilart ta fito yauma cikin shiga ta atampa dakakiya mai kyan gaske ta kashe daurin nan nata tamkar gamo tana murmushi ta shiga gaishe shi da dan rage tsayinta tana hade hannayenta irin yadda suke yi din nan sannan ta bi hannunsa da kallo da kula ta ce " Hubby me ya samu hannunka ne?"

KAN GIWA ya bi hannun nasa da kallo ba tare da ya amsa gaisuwar tata ba a hade sosai ya furta mata kalmar "Nothing" sannan ya sake kallon Murjanatu yana duba agogonsa ya ce" Ku je karfe biyar na yama , ku dawo karfe shida da rabu har tafiya da dawowa, kar magariba ta maku a cen"

Cike da farin ciki take amsawa da in sha Allah sannan ya wuce ya tafi ya bar Djamilart da mamakin irin amsar da ta samu yau a wajensa ta halin ko in kula, kamar wata wace bai sani din nan ba bayan ita a sanninta bata aikata wani laifi ba, bayan wannanma ita fitane zata yi tana da bukatar kudi dan zata je ne ta yi wasu siyaya da ta gani an zuba sababin atampopi yan kasa da kasa

Kallon Murjanatu ta yi tana fadin" Me yake damunsa ne? Me ya samu hannunsa a nade haka?"

Murjanatu ta girgiza kanta itama a hade ta furta kalmar " I don't know" ta wuce wajen su Rislan dake tsaye shi da NURIYAH

NURIYAH ta yi yar dariya tana fadin" Wai tsaya yayanah, wai shi karatun dama wahala ne da shi kake jajen ba zaka koma ba baka son tafiya? Wani mawaki ke fadin tafiya mabudin ilimi ko dan ka tafi ka yi gane gane ka ilimantu ai zaka kwadaitu da son komawa"

Murmushi ya yi yana kallon Murjanatu da ta karaso tana fadin" Sis Nuriyah, ai shi Broth ya fi so ya yi zamansa a kasarsa, kuma shi ya ce sai ya yi karatun professor, daga bana nefa ya gama aman kin ga ya kiya sai da aka hado shi da baban yaya yanzun"

Yana makala abin wayarsa ya ce" Ba zaku gane bane yan matan Hajia, idan kana nesa da yaya komai a duhu ake baka, idan kana kusa ciki kake dumu dumu gaba da baya haja ce bashasha, a wannan karronma na so na zauna ne dan na daidaita rikicin cikin gidan nan, aman yaya ya ki koda amsani a kan maganar "

Nuriyah ta yi dan Murmushi tana juyawa tare da kama hanuar dakinsu dan ta kula zasu shiga maganar cikin gidansu tana fadin " A sauka lafiya, Allah ya bada sa'ar karatu, idan ka je ka cewa wannan dan film din nan musulmin nan wannan wanda Auta ke nunan wakokinsa a wayarta ina gaishe shi"

Murjanatu ta yi daria tana cewa" Oh sharukhan?, Ai kam kin san inda yake da family dinsa daga dlgu sai an shiga kwale kwale ya tsalakaka , Idan ya tsalakaka ko wa ya tambaya gidan Khan Sharu za'a nuna maka sai dai tsaron ne ba kowa ke iya shiga anguwar ba sai da katin gayata"

Shima dariyar ya yi yana kallonta har ta shige dakinsu sannan ya fuskanci Murjanatu ya riko hannunta yana fadin" Me kika fuskanta da bakuwarki kuma kawarki?"

Murjanatu ta dan ja tana kallonsa ta ce" Yaya kana tune dai dai da yadda kuka yi kafin ka yi tafiyar nan ko? Dan Allah ka barta ta yanke ta ga abinda ya dace da rayuwarta yaya"

Sai da ya tsatsareta da idannuwansa kafin ya yi murmushi ya ce" Ina tsoron ta samu yankewar shawarar da bata taba jira ko tsamani ba Auta, domin ni zan iya ce maki na yi dana sannin gagawar maganar da na yi a kanta, da na sani da na yi jira na ga wani abin daban.......sai dai ko a haka zan iya ce maki zan iya sadaukar da zuciyar dake bugawa a kirjina saboda wanda ya cencenta ya samu bale soyaya, gaskiya zan iya bada raina wa wannan bawa dan shima zai min sama da haka!"


Gaba daya ya sakata a cikin hali na tunanin abinda maganarsa ke nufi, a hankali ta ce" Yaya ban fahimci inda maganar nan ta dosa ba fa"

Bakinsa ya tabe yana yin gaba hadi da fadin" Zaki fahimta na tafi"

Da sauri ta bi bayansa dan ta masa rakiya

Sunna fitowa suka ga wani shirmen a wajen Djamilarth dake kwasar rigima da sojan dake kula da harkar shige da ficen mutan bangaren
Rai bace ta ce" Kai wai ka gane ni kuwa? Nice amaryar KAN GIWA a kan me zaka ce ba zan fita ba? Ka bani katin fita na fada maka"

Fuskarsa a daure yana tsaye kikam dinsa ya ce" Ki yi hakuri madame umarni ne daga oga , babu inda zaki je"

Daga haka ya maida bakin gilas dinsa da ya cire dan girmamawa a gareta ya juya ya ci gaba da aikinsa ba tare da ya sake koda yi mata kallo daya ba

Rai bace ta ringa magangannu da yarenta da su ashar kala daban daban ta juya ta koma tana fadin" Bara na kireshi shi sai ya baka damar barina fita, yaishe yake hannamu fita? Ko saudiya zan je daga nan ai zai barni na tafi ne"

Da ido suka bita har ta shige kafin Rislan ya sake zubawa makeken tsakiyar gidan ido yana fadin" Walahi idan suka kasance a nutsen nan sai ki rantse sai tsuntsaye a Palace KAN GIWA"

Yar dariya ta yi kadan tana fadin" kowa yana cen yana aikinsa, basu san idan akoy mutun mai sauki bayan yayanmu ne, shi fa wasu abubuwan da suke yi baima san dalilin da ya sa suke yi ba, shi kawai bai dame shi bane ya tsaya ya bincika din , idan ka ga yana fada kuwa to fa a fannin abinci ne, baya so ko da wasa a yi masa wasa da tsaftar abincinsa da wajen cin abincin da komai da komai da ya shafi abincin, shi yasa suke tsaye kan kafafuwansu basa ji basa gani basa wasa da girkinsa ko kadan

_______________________________________


Tafiyar da suka yi nata dauki lokaci ba domin ko minti arba'in basu dauka sunna tafiyar ba suka karaso dan kauyen da yayi niyar zuwa yai din

Tunda motocin suka tsaya ya zubawa koren shukokin dake kadawa a hankali alfarmar albarkar damina sun yi shar da su sai iska mai sanyi suke badawa kadan kadan sunna rausayawa

A hankali ya sake juyo hannunsa yana duba hannun nasa mai bandejin nan ya gwada jimke shi a hankali sannan ya sake kallon madubin motar da sojan dake tsaye mai farar fata nasara wanda gashin kansa ke dan kadawa sakamakon iskar dake kadawa mai sanyi da kanshin damina

A saman lebensa ya furta" *She takes care of me after all she s afraid of me* "........................ ......................... ............................... ...................................................................................Hannun nasa ya sake dubawa yana mikar da shi kadan irin yadda yakke girke sosai ya sauke dan murmushin da ya fito a saman lebensa a hankali ya sake furta" NOURIYAHHHH, who are u?......>.....juste ina son sannin daga ina laushinki ya samu? Yaya aka yi kika iya pretending like kina da tsoro kamar wata yar lalausar fulawa mai laushi ??????????????? Ko haka suke matan a kannanun shekaru irin naki ne?????????? Sai sun fara girma sai kuma su dawo kamar mahaukata ??????"











Aa fa........rashin sa'a aka ci oga kake tare da yan eyane=??=??=??=??






*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
3?? 4??




A wajen da suka yi ne zasu hadu da mai garin garin da kuma yan kauyen da suka kawo tallar kwaririkansu mutun har goma sha daya suka hade

Tunda ya karaso bayan bodyguard dinsa sun gama gyare gyaren wajen ya zauna ya ringa amsar hannayen jama'ar garin sunna gaisawa cike da mutuntawa du kuwa da irin duban da ya kula sunna binsa da shi wanda ya rasa fasararsa, kamar sun ga bakon halitar nan

A nutse ya fuskanci mai gari dake fadin" Alhamdulilah, Elhaji kamar yadda ka bukaci sannin a kan wani dalili mutanen kauyen nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login