Showing 84001 words to 87000 words out of 124070 words

Chapter 29 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

348

a kan wanda nake yi, wannan saide saidenma kar su Abanki su ce na sakaki saide saide su rabamu"

Da mamaki take kallonsa bayan ta dan katsa kadan dan sun kunacewa junna waje tace" Ban gane kar yace ka sakani saide saide ba ya rabamu, ban gane zaka saki gidanmu ka kama wani ba? Samunka ya ninku ne a rabuwarmu jiya zuwa yau?"

Kansa ya girgiza yana fadin" Alhmdulilah, ba maganar ninkuwa bane, aman a da na dauka ne ke din Y'ar masu kudo ce aman ban yi tunanin yawansa ya kai irin haka ba"

Da wani matsanancin mamakin ta ce" Sai aka yi yaya yayana?"

Cike da jin nauyi ya ce" Sai ya dace ki cenza salon rayuwarki da komai , anguwar nan bata dace da ke ba"

Yanzun kam har sai da ta rufe bakinta, kafin ta gyada kanta ta ce" Uhum, kana tunanin wannan duniyar ta mahaifina ce?inace ka ji gidan D'AN mijin y'ar uwata ne nan, sannan bama wannan ba, yanzun yaya du zaman da muka yi da kai ashe zaka iya yi min gurgiwar fahimta har haka? To da kake cewa ka cenzan rayuwa so kake mu koma rayuwar da ta fi karfinmu har na sakaka a matsala ko me? Da me ka rageni? A haka din da nake rayuwar a hakan me ya cenza a jikina ko a tufafina? Ko taro ake yi a anguwa fadi ake yi sabon kala sai matarka, na fi matan wasu masu kudin mararsa zuciyar yi, haka kuma kwonciyar hankalina ta fi ta wata matar bilonian, na taba kwatanta maka cewar a takure nake ne yayana? Kuma da kace wai abanmu ya rabamu dan ina sana'a, sana'a fa kace ba sata ba, shima mahaifin nawa dan kasuwar ne fa, me yasa zaka yi irin haka yaya?"

Ta karashe tana cika fuskarta, hakan ya bashi dariya dan gannin fushi ne ta yi , shi kuma a nasa tunanin gani ya yi gaskiya yanzun ta wuce da ajin gidan cen da suke, shikenan sai a yi fushi daga haka?

Ajiyar zuciya ya sauke yana godewa Allah da ya bashi mace irin haka, dama idan ka ga mai kudi da fadin rai shigar kudin ne aka yi daga sama kuma da burin wulakanta talauci, sai ka ga dan ana hawa yar mota ana neman keta wulakanci wa kowa, aman idan abin ka buda ido ka gani a gidanku koda kun dawo baku da komai na kadarar rayuwa mu'amalarka da kowa irin na Noble prsn ne, ya yi niya zai ninka sakin aljihunsa ya sake faranta mata, koda basu saki gida ba sai ta sake sakewa ta bararaje wa dadin duniya in dai yana raye........, Shi yanzun mijin yayarsa yake so su hada hanya.....kai yana da haushin mutumen bale da ya ga abinda ya yi a jiya, bai san cikin zanewa, da karya wuya wane zai mishi ba gaskiya

Karra matse mata wajen ya yi yana fadin" Haba budurwata, fushi kika yi hala na ga kumatun aun yi wani bulbul masha Allah"

Bata san lokacin da ta saka yar dariya tana matsawa sosai ta ce" Kai ko, gaskiya tashi ka komawarka gida in dai haka zakana yi a gaban mutane ni wollah yaya kunya nake ji, ka ga da y'arka ta fito ta ga haka fa? Yayana ka ga fa y'arka yadda ta girma kamar ba shekarunta ba*

Da ido ya tsatsareta a hankali ya ce" Hasanata, zata ce min Aba kuwa? Nima zan amsa sunnan Aba kuwa bayan laifukan da na tafka a rayuwata?"

Fara'ar fuskarta ta rage kadan tana kallonsa sai kuma ta sake sakar masa wani murmushin a hankali ta ce" na sha fada maka kaima ka haifa, Aba kake, zata ce maka Aba, yayana wai ka san su Aba sai gobe da yama koda zasu samu isowa? Garin nan da nisa......" Ta basar da zancen dan kar ya nemi saka damuwa a ransa dalilin hakan..........
Da wannan suka shantake abinsu sunna shan hirarsu

Washe gari da safe kusan karfe tara da rabi

Gaba daya gidan a hargitse yake, du iyayen sun kasa zaune sun kasa tsaye yau su da kansu ne a kicin sunna girke girke wa iyayensu da zasu sauka da yama a kasar

A falo kuwa su Hajia ne zaune tana sake jadada masu abinda zasu je boutique din yayan Mami su siyo mata wanda ta jadada cewa cen take so su je su siyo mata siyayar da suka rasa me zata yi da ita, domin a abinda ta zanna din basu ga abinda zata yi anfani da shi a yanzu baa gaskiya

Nuriyah ta sake rintse idannuwanta domin turaren da Hajia ta fesa mata ba kadan bane, gashi ita ba sabawa ta yi da kamarin turaren bama sai a gidan nan, yana da sanyin kanshi, damuwar ji take du inda ta gifta sai an ji kanshinsa

Hijabinta da ta zumbula ya saka Hajia binta da kallon takaici kafin ta dago dan kwalin abayarta tana nunaa mata ta ce" Ke kuwa wannan y'a dan kwalin rigar wani ya kashe maki a dangi da kika tsaneshi zaki saka wannan hijab din da ko ni ya min yawa?"

Nuriyah ta kalli Hijabinta ta dago ta kalli Hajia ta mika hannu tana amsar dan kwalin domin ita bata san abinda Hajiar ke shiryawa ba, ita dai takan yi mamakin wasu abubuwan da take yi kafin jiya zuwa yau

Jiki a sanyaye ta yafa mayafin tana jinta wani iri, bata sama ba ko daya, bata saba fita har waje a haka ba, duda a mota suke aman gaba daya sia take jin wani iri

Da murmushi ta raka su ta koma ta zauna da kyau tana sake daukan carbinta ta kishingida ta shiga jan astagfari hankali kwonce tana jin motsin sarakuwarta da y'ar uwarta a gefe hankakinta kwonce

Murmushin da Murja ta yi bayan sun gama waya da natacenta ta juyo a hankali tana zuba idannuwanta a saman fuskar NURIYAH
Wani Murmushin ta kuma yi tana fadin" NURIYAH walahi ki daina kwaliya idan zaki fito domin sai ki haukata maza"

NURIYAH ta sauke ajiyar zuciya tana fadin" Ke kawai sai an yi rigima dake in ana tare, Auta kalli fa Hajia ta hannani saka hijabina, kalli Boutique din nan yadda mutane suke, kuma kin wani yi kiransa kin ce masa zamu zo, fisabililahi ni yaya zan yi da raina?"

Auta ta tabe baki tana kwaikwayonta ta saka hannunta ta bude motar tana fadin" Ki kifa tsabar tsoro, ni da ni nake da gashinki ai da maza sun fadawa yan garinsu, tunda gashin suke so kamar me"

Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta fito ta shiga bin bayanta a hankali dan kar ta bace mata

Wajen abubuwan da Hajia ta zanna suka je suka loda mata sannan suka bi ta wajen kayan kwaliya suka tsintsinci abinda ya masu , suka sake bi ta wajen kwalam da makulashe da ba'a raba yan mata da shi suka jidi dangin chocolate sannan suka tafi wajen biya

A nan suka same shi zaune saman kujera yana jiransu
Da nacinsa da komai ya ja Nuriyah gefe guda ya shiga yadda manufarsa, wace kunya ta hannata katabus sai aukin murmushi da sada kanta kasa dan bata taba tsayuwa haka da namiji ba, haka kuma ba karya ta ji ya mata harma ya zarce yi mata domin shi din namiji ne har namiji

Da kyar ya barsu suka juya bayan ya shake masu kayn da basu san yaya zasu yi da shi ba wajen shiga falo a irin lokacin nan, haka kuma siyayar tasu ko kwondala aka ki karba su kam sun san sai sun tarar da abinda hankalinsu zai tashi a gida

Sun jima zazaune a motar sunna kallon bangaren na Hajia

Nuriyah ta ce " sai ki nemo mai shigar maki da kayan nan, kin ga tafiyata"

Murjanatu ta fito itama tana fadin" Zaki yi bayani ne , ai shagon saurayinki aka je malama"

Murmushi kawai ta mata ta shiga hawa matatakalar nan uku kafin a hau dan filin dake zagaye a shige falon Hajia

Gabanta sai da ya kwonci kwonci ya ruguzo kasa a lokacin da idannuwanta suka shiga cikin nasa da matarsa dake cikin adi na fitar hankali tana masa hira

A hankali ta saka hannunta ta rike karfen wajen, ta sada dubbanta sannan ta sanyayar da muryarta da yannayinta ta ce" Barka da warhaka Sir, barka da warhaka Madame"
Tana gama fada ta daga kafarta da nufin tafia ciki domin irin kallon da matarsa ke yi mata ya sakata kara sauri dan bata san me ta kashe mata ba take mata kallon kyankyami

" NURIYAH Zo nan" ya fada cen kasan makoshinsa lokaci daya kuma yana kallon matarsa da mamaki ya sakata fadin" Hero sunnan y'ar aiki ka kama kai tsaye ?"

Duban da ya mata yaa sakata gyara zamanta da sauri tana sake dora Idannuwanta a kan Nuriyah da ta dawo itama jiki a mace ta duka daidai lokacin da Murja ta karaso da kwali chocolate din da take gannin darajarsa ya fi gaban mai aiki ya kwaso shi

Da sauri ta rabe itama, yannayi na rashin gaskiya da tsoro suka bayana a tatare da ita fa muryarta a lokacin da take fadin" Yayayayayayana kaine a nan warhaka?"

Da ido ya raka masu aikin da suka jido kaya da kampanin dake jikin manyan ledojin da ake ta shiga da su kafin ya maido dubansa ya zuba Saman NURIYAH da gaba daya ta sarewa duniya kanta a kasa taa yi lakwas kamar wace ta ci dukan tsiya, sai kuma ya sake juyawa wajen baby da ta bude bakinta ta barke da kukan da bai san ko na meye ba, hasalima bai san kampanin waye ba, shi dai yana son sannin inda suka fita ba da sanninsa ba, aman wannan kuka na baby ya saka shi jin zuciyarsa na bugawa da mugun gudu harda tsoron jin abinda ke bakin Auta

A hankali ya sake maida dubansa kan NURIYAH ya ce"



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
5?? 0??





Ya Allah muna rokonka da sunnayenka tsarkaka , Allah ka sa mu cika da kyau da imani, ka sa mu rayu cikin mutunci mu mutu a mutunce, ya ubangiji ka yi mana sutura ka rufa mana asiri duniya da kiyama, Allah ka jikan magabatanmu, ka bamu lafiya mai inganci





A hankali yana kallon NURIYAH ya ce" Daga ina kuke?" Watau ya cenza akalar tambayar tasa, domin da farko ya so ne ya tambayi me yasa suka fita a gidan bashi da labari haka daga su sai direba bayan wani abin na iya faruwa da su a cikin gari ?

Dara daran idannuwanta da suka cika da kwalah hadi da kwalin da ya sake sakasu zama uniq ta dago ta zuba a saman fuskarsa hadi da saka idannuwanta cikin nasa
A hankali take bude bakinta lebunnanta na rawa kadan kadan hakan ya sa ta yi wani irin lamarin da ta yi ne dan ta samu kwarin gwuiwar bashi amsa inda ya bi bakin nata da kallo a lokacin da ta saka gefen lebenta na kasa ta dantse a hankali ta dan dago kirjinta kadan ta ja numfashi sannan ta maida ta ajiye tana raraba idannuwanta sannan ta saki a hankali ta budi baki zata bada amsa still Auta ta kuma budar bakinta ta ce" Yayanmu walahi Hajia ce ta aikemu kuma tace mu je boutique dinsa, kuma na rantse da Allahn da ya busa min numfashi babu irin gwagwarmayar da bamu sha ba sabado ya amshi kudin ya kiya yace Allah kiyaye masa da ya amshi kudin siyayar gidansu, wai ai da kunya"

Sai yanzu ya fahimci dalilin kukan na baby, a hankali ya cire idannuwansa daga fuskar NURIYAH wace ta sada kanta tana sake jimkar rigar dake jikinta wace ke nuni da hankalinta in ya yi dubu a tashe yake, ita dai bata da saurin kukan aman sanyin halin du sai ya dabaibayeta
Duban da ya yiwa baby ya sakata sake zubewa harda jan hanci tana sake rantsuwar basu je takanas ba, kuma basu je dan soyaya ba

"Soyaya" shine abinda lebensa ya maimaita a hankali yana mai karra dubanta da mamaki, wai baby ce ra iya furta kalmar nan a bakinta? Ta san me take nufi ko kuma kawai dai wannan hargitsatsiyar yarinyar ke son bata masa kanwa? Wai yanzu ace shi da girmansa da mutuncinsa ya saka doka Hajia ta take

Bai ce masu komai ba sai mikewar da ya yi ya shige ciki a daidai lokacin da Hajia ta yi wani bayanin da ya matukar saka Hasana a cikin jin kunya, mijinta kuwa cike da wani farin ciki ya kafe Kan GIWA da kallo yana sakin murmushi da auna abubuwa kala daban daban, bama kamar yadda Hajiar ta nuna y'ar tasa ce, burinta idan ta samu ta ga abinda take so a bayane ba a rufe ba , domin ita ta yi wayewar da bata ciki da game gamen nan na iyaye, haka kawai su hada wannan da wannan a bar yarinya ko yaron da zaman hakuri dan bashi da yadda zai yi, yawancin lokuta mace na hakuri da iya shegen wani namijin ne idan tana sonsa, haka shima namijin yawamcin lokutan zai kyautatawa mace ne dan yana son abinsa, koda yan magana kan cewa da an yi aure ina soyaya? Akoy soyaya kai, domin da kiyaya ta fi tasiri kan soyayar da an rabu

Murmushi ya yi ya sake duban Mahaifin Kan Giwa, wanda sai a yau a yanzu ya sake yarda da gaske mahaifiyarsa take, wanda ya nuna da du duniya sai ya fi kowa farin ciki idan ya wayi gari ya ga lalle d'ansa na tsaftatacen zaman aure ba shirme ba

Kansa tsaye ya karasa wajen da Hajia kw zaune da mahaifinsa gefenta ya zauna kusa da mijinta watau ya fuskanci su hajiar fuskar nan tasa a hade sosai ya ce" Hajia, yanzu fisabililahi me kika yi kennan?"

Hajia ta yi kamar bata san abinda ta yin ba ta kalle shi tana fadin" kai me na yi kuma ni? A ina?"

Kan GIWA ya juya wajen takwaransa ya ce" Yanzu Elhaji ya dace ace ni da girmana da darajata na dora doka jiya jiyan nan matarka ta saka kafa ta shure? Me ta yi kennan?"

Kasancewar shi ya fi kowa sannin shirin matarsa sai yau ya nemi goyawa Hajiar baya domin shima a ransa damuwar wannan mata da ake kira matan auren jikan nasa na damunsa, hakan ya sa ya ce" To me matata ta maka kai kuma"

Sai da ya zarro ido yana kallonsa ya ki waigawa wajen da mahaifinsa yake dan ya san in ya juya din zai masa komai a kan turke masa iyaye da ya shigo yi, a hankali ya ce" Magana ce a kan su Baby fa Elhaji, jiya ta min wata maganar da bata min ba, na nuna mata na soke maganar, shine yau na ga yaren nan na shigowa da wasu ledoji wai cen ta aike su?"

Elhaji ya gyara zamansa shima da fuskarsa ta tsufa ya yi dan Murmushi yana fadin" Kar dai ka ce min hanna manemin auren balaraba ka yi ya fara zuwa? To aman me yasa?"

Sai da ya kureshi da ido daidai sun shigo sunna gaishe da jama'ar falon a gagauce suka shiga haurawa, hakan ya sa ya rakasu da ido kafin ya juyo ransa na sake baci ya ce" Ba balaraba bane sunnanta "

Elhaji ya tabe baki ya karkace kai ya ce" kai bata maka shige da y'ayan larabawa irin masu kyau din nan na gidan sarautar saudiya?"

Yau kam ya fara yarda daga kakansa har kakarsa sun shirufce ko kuma sun fara shirufcewar, dan haka sai ya sasauta muryarsa dan ya tino masa komai dala dala, a hankali ya rike hannunsa da kyau ya ce" Takwarana nine takwaranka, baban jikanka kuma abokin shawararka, da bakina da naka muka yanke shawarar sai baby ta yi kwari zata fara kula saurayi, shima daya tak ya fito ya aureta su tafi su yi zaman farin ciki, kana tune da wannan ranar?"

Dariar dake cin mama Husaina ce take neman fitowa dan haka ta mike da dan sauri ta bar wajen a lokacin da sirikinta ke cewa d'an nata" eh ina tune da lokacin, to aman saurayi ta yi ne Autar?"

Kansa ya girgiza ya ce" Aa, NURIYAH ce wai ko wane yake sonta"

"To ai ta kai takwarana"
Kaka ya fada a sanyayensa yana sake kallon Kan GIWA

Kan GIWA ya kikifta ido yana kallonsa ya ce" Yarinyar nan karama ta kai ina? Sa'ar baby ce fa, babu inda ta kai dan haka na soke wannan maganar ka jawa matarka kunne"




























To>?#?



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
5?? 1??



Kaka ya tabe baki yana riko hannunsa ya dawo da shi yace" ka ga in magana kake da a bakinka dangane da Murjanatu gaka ga ita nan, ni ba zaka sakani yi mata fada ba ranta ya bace, bayanma wannan ai wannan karron Murjanatu nada gaskiya a kan fadanku, ita takwarar tata Allah na tuba sai ta tsufa zaka aurar da ita ne? Ai ta isa kuma itama ta fitar da miji mana , dayar maganar kuwa ai zan iya ce maka kawai ka saka a kawo gadaje domin ni dai na yanke hukuncin ya fito in da gaske yake a daura masu aure su je au yi zamansu"

Ido ya sake zuba masa a kausashe yace" Lalema, to in ba abinka ba ai ba kai bane babanta ko Elhaji?"

Shima ya masa irin kallon yace" Ai kaima zan tuna maka yayansu kake ba ubansu ba kuma ga uban Balaraba nan zaune yace eh hakan ya masa, hakama uban murja ka je ka tisa naka suma su haifo sai ka ga irin ikon da zan yi da su in ina raye, dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login