Showing 120001 words to 123000 words out of 124070 words

Chapter 41 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

353

to ni dukama sau sau................. .................. ...................."
Mikewar da ta yi ta zurra da gudu ya saka shi zabura ya tsaya hakama Hajia ta mike tsaye tana zarro ido da karfi ta ce" Innalilahi wa inna ilaihi rajune ke Balaraba kada fa kada fa"

Da sauri ya bi bayanta , Murjanatu kuwa ta kama dariya dan walahi dariya suka bata gaba dayansu, kuma ta tabata abinda yayanta ya so fada ne ya daka Nuriyah zabgawa da gudun nan, farin cikin dake zuciyarsu Allah kadai ya san irin girmanshi

A ranar hankali bai kwonta ba sai da ya ji daga bakin likita, da irin shawarwarin da aka bada, aka kuma jadada masa cewa ta isa daukan ciki sannan hankalinsa ya kwonta, mahaifinsa kansa kasa zama ya yi sai da ya je ya mata sannu da jiki kamar wace ke jinya, kakansa kuwa ba'a magana sadaka yake yi da godiyar Allaj, bale shi uban tafiyar.... ba'a maganarsa, du zumudinsa na ya kwana yana zikiri sai ya takaita domin likita ya kwatanta wani lokacin idan ciki bai gama zama bane yake samun barazana daga babansa, idan har baban nasa mai nacin abin ne, shi yasa ya dan taba ama kadan

A hankali ta shiga renon cikinta, cikin sam bashi da wani wahala baya bata wahala kam ko dan da dan yarinta kadan kuma ita din ba wata mai son jiki bace, wani sa'in takan ji tsokale tsokale irin na mai ciki aman sam bata kawo komai a kai bale ta langwabe

A bangaren Kan Giwa a yanzu du idan ya gama mata kwana biyunta damuwarsa biyu ce kawai, irin yadda take hanna shi sake dawowa gareta ta nuna kwanan watanta ce bayan watan tata sam baya gabanta, sai irin damuwar irin zamansa da Djamilarrt dake damunsa, sam baya gabanta, a duniya baiwar Allahn nan idan ba kudi ba bai ga abinda zai daga mata hankali ko ya sakata nutsuwa ta yi sauraro da biyaya ba, da ace bashi da komai ya tabata ba zata zauna da shi ba, nema take yi kamar wace za'ai mata likafani da su a kaita kiyama, nema take yi kamar ba zata mutu ba, a kulun kuma kari take so

Nadia kuwa ya tatara tarikitanta ya watsar a shara ya rufe babinta, idan har Nadia ta yarda ta saki kafarta inda yake ta tabatar ta zo da wanda yake jin kunya idan ba haka ba sai ya gama kakarya mata gaban jikinta kafin ya saketa, yanama kyautata zaton ta yiwu zata aikata aikin da wasu matan ke yi idan sun gama zama da namiji , watau basa zama su amshi takardar sakinsuma su suke sakin kansu su yi tafiyarsu su yi wani auren ko su yi zamansu ba auren ama kuma ba tare da mijinsu ba, koma me ta zabarwa kanta Allah yana gani ba shi ya bata izini ba, kuma ba zai saketa ba shi da it shege ka fasa! Ba'a aure ya aurota? Ita ta isa ta shiga tsakaninsa da uwar ya'yansa? A kan shan maganin tsarin iyali wace nasiha ce bai mata ba? Wani fada ne bai mata ba? Ashe sai ta je aka saka mata na mara, ita ta rantse yarinya ce ba ztaa haihu yanzu ba, ta nunawa Nuriy yarinta ne?


Shawarar da ya yankewa kansa, har ya tuntubi mahaifinsa ya zauna ya masa dala dalar abindaa yake faruwa ne yake zaune a falo yana kallon jus din da Djamilarrt ta ajiye masa sai karadi take irin na dan gida da uban gida

Yana kallonta ya yi murmushi ya ce" Djamilarrt, ina so na tambayeki ni kuwa, ko zaki fuskanceni mu yi maganar fahimta?"


Duka hankalinta ta bashi, domin abu daya ya zo kanta shine wata hanyar shigowar kudin ce zata samu

Kan Giwa ya sauke ajiyar zuciya ya ce"







Mun kusa>?#?>?#?>?#?>?#?>?#?>?#?>?#?>?#?>?#?>?#?>?#?



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
6?? 3?? 3?? 3?? 3?? 3?? 3?? 3?? 3?? 3?? 3?? 3?? 3?? 3?? 3?? 3?? 3?? 3?? 3?? 3?? 3?? 3?? 3??






Alhamdulilah





A nutse ya furta" Anya kina sha'awar zaman aure kuwa?"

Sake gyara zamanta ta yi ta ce" Zaman aure Oga? Ban gane ba sosai?"

Kan Giwa ya gyara zamansa ya fuskanceta sosai ya ce" ina nufin ke da na nemeki da kar na neme ki du bai shafeki ba, ke zaki iya rayuwama ba tare da an taba ki ba? Idanma inada wasu yan matan a waje ba zai dameki ba ko?"

Zamanta ta karra gyarawa ita dinma tana kallonsa ta ce" Oga wo, oga, to ni ai bana iyawa wannan abun naka oga, kuma na ni bani da matsala fa kana iya yin yan matan sosai sosai oga ai girmanka ne ogana"

Ikon Allah, ya ayana a zuciyarsa, a fili ya ce" ama kin san yin yan matan a waje ba kyau, haramun ne aikata zina, idan na mutu a cikin aikata zina wuta zan je, shine anfanin aurenki, da ke da sauran dan na kauracewa zina, kin san ba kyau ko?"

Murmushi take yi ta ce" To Oga ba sai ka tuba ba kafin ka mutun?"

Lalle ya yarda yau kam ya kuma idasa yarda wannan din ba matar a zauna da ita bace, macen da zata ce eh ka je ka yi zinar kafin ka mutu sai ka tuba? Kamar itace ke rike da lokacin mutuwarka!

Murmushi ya yi ya fara ciro takardar kudin da ya rubuta mata ya mika mata
Tunda ta karanta kudin ta ga yawansa ta nemi rikicewa, daga zaune sai da ta mike sau biyar tana komawa ta zauna, a haukace ta dake dubansa a gabansa zufa na neman karyo mata, wannan kudi, wannan kudi, wannan kudi bata san ina zata shiga dan ajiyarsu ba, godiya take yi masa kamar zata kifa goshinta kasa duka yana kallonta har sai da ta gama sannan ya yi murmushi ya ce" Ba komai, sannan ki yafe min idan na taba cuta maki a zamana da ke, ni kam na yafe maki, ba dan kin min wani laifin ba, idan har na ci gaba da zama da ke akoy cutarwa , na tabata zan iya kona kaina ......wannan din ki ja jari da shi, na yanke igiyar aurena da ke saki daya"

Tabas hankalinta ya tashi, sakin mace koda mugun zama ne sai ta ji a zuciyarta sai dai ta ki nunawa, bale ba laifin zamanta da shi komai tana samu, shi din bama mai damuwar sakawa mace ido komai zata yi yace sai ya mata kididiga ba, shi yasa zama da shi yake da dadi, irin yancin da ya basu a rayuwa kuwa ko gidan iyayensu suke zaune ba zasu samu haka ba, sosai ta ji jikinta ya yi sanyi, du ta inda ta bilo sai ya tareta da maganar da bata isa ta ja ba, a karshe dole a hakura ama ta nemi alfarmar zumunci da shi da danginsa, kuma shi din da kansa ya bata damar ta gama kwashe kayanta a nutse ba zai azalzaleta ba, kayan da bata zo da komai ba ya bata damar kwashe komai, wannan shine karshen zamansa da Djamilarrt a matsayin matarsa, wanda ba kowa ya dan da hakan ba ko a cikin gidan, sai a hankali suka fahimta , NURIYAH kuwa tun a daren da abin ya faru ya sanar mata shi a lokacin da suke kwonce cikin dare, sosai ta ji ba dadi, har ta so nuna masa, sai dai ya ci karfinta ya nuna mata hakan shine alkhairinsu baki daya, a dole ta yi shiru ta ci gaba da addu'ar Allah ya sake dora mijinta a kan hanya mafaidaiciya, wace zata zamto alkhairi a gareshi da du baki daya


A hankali take rainon cikinta, a hankali take samun kula yadda ya kamata, da farko farko ne ta ringa shan wahala a duk lokacin da ta samu bakuncin mijinta, daga baya da cikin ya zauna sosai sai ya zamto zuwan nasa abin nema ne a wajenta, har shi yake rike kansa dan a yanzu fatar cikinta ta fara ja ta fara cika ta fara nuna lalle akoy ajiya a cikinta, a lokacin da suka je awo na wata shida a daidai lokacin aka rike Mama Husaina a asibiti, domin nata cikin yanzu da ya kawo gangara gaba daya sai yake neman kifata da kasa, wahala yake bata sosai abinka da shekaru sun ja gashi bata taba samu ba, likita ke bata kyakyawar kulawa , kasancewar ta shiga satin haihuwarta dole aka riketa dan koda ta kwana domin sosai cikin na wahalar da ita
A wannan lokacin hankalin Kan giwa ya so tashi, shi ya kasa fahimtar lamarin ciki da yarintar ya fi zuwa ya wuce tamkar ba'a sha wahalarsa ba, gani yake yi Mama ma tana neman kasawa bale Nuriy? Gaba daya ya nemi ficewa a hayacinsa domin Allah yana gani idan har yana tunanin haka har kame kamen tunanin da bashi da anfani yake yi , abubuwa kala daban kan shigo masa cikin kwakwaluwarsa fuda ya san Allah baya barin wani dan wani ya ji dadi, sosai Hajia ta sake zaunar da shi ta yi masa karatun fari fari ta yadda ya dan kwontar da hankalinsa har aka yi bikin kanninsa da Mama ta samu da shi cikin nutsuwarsa

Watanin haihuwar Nuriyah na gabatowa Nadia ta dawo gidan

Wannan zuwan da Nadia ta yi du wani mai hankali ya dan da tarin rashin mutunci ta zo gidan, ta kuma taki Sa'a a lokacin ya yi tafiya har ta tsayin sati uku wace ta kama masa dole ya tafi a kan harkar aikinsa

A yau Nuriyah ta fito daga bangaren su Hajia karamar wayarta kange a kunnenta tana amsa wayar da ta zama ta rigima ba dare ba rana sunna kange da waya a kunne sunna karyace karyace in ji Hajia
Cikinta ya tura gaba masha Allah tamkar wace ta cike lokacin haihuwarta, koda yake ta kai wata takwas da kwana biyu

Tafiyarta take yi a hankali cikin rufafiyar shiga har fuskarta , tana yar daria tana ta takawa sunna waya cikin jin dadi da nishadi, kwarai take jin yannayin garin na ratsa jinni da jikinta , sanyin yamar na ratsata sosai

A hankali ta ce" Ka ki ka fada min maganar Abana Sir"

Dan shiru ne ya biyo baya kadan, bai san me zai ce mata ba, da ta san sanadiyarta irin dagawa wannan mutumen kafar da ya yi da sai mamaki ya kusan halakata, shi da kansa da Hajia ke masa nasihar ya kula fa, du irin wulakancin da mutumen nan ya yiwa yarsa ya kiyaye kar yace zai rama mata, karfin jinni daban ne, yar halak ce, kar daga baya ya rasa inda zai saka kansa dan kunya abin ya ringa bashi mamaki, sai dai a wata daya kacal da aka rabashi da dukkan wani abu d aya malaka a duniya ta hanyar yin biyayn shiri aka zo masa. Matsayin yan daba aka kwamushe dukkan wani abin da ya malaka sai ya dawo daga shi sai gidan da yake ciki, ko labule ba'a bar masa ba, a cikin yan kwanakin ya ga ikon Allah gannin idannuwansa, matar da ya kashe kansa da son zuciyarsa a kanta karara ta nuna masa a raba gidan a siyar a ja jari, da ya kiya taa kwashe takardun ta siyarwa wanda Kan giwa ya saka aikata aikin, bata san cewa kudin banza aka bata ba sai da ta je ta bude jakar arziki a banki dan zuba kudi da aka duba kudi aka ga na banza ne aka kamata, domin banki ai ba da wanda ya sayi gidanta suka zanta ba, yanzu haka tana hannu ba dan ba'a san gaskiya ba sai barinta da ya yi ta dana ukubar cel

Y'arsa da ya daga duniya ta sani ya yanka mata rago , yake yi mata soyaya daya tak da ba hadi ido da ido ta kwashi y nata y nata ta ce da shi gaskiya ba zata iya zaman geto ba ba ci ba sha, ita kam ta tafi Neman na kanta ta kowace hanya, yanzu haka dai mahaifinta na faskare ne da kyar da dako, wa'inda bai saba ba , gaba daya nema yake ya kunce dan rashi, shi kadai yake tafe yana sakin magangannu, a watanin nan kalilan yana neman zaucewa , ya saka mutane a ukubar shekara da shekaru, kai Lawali? Da ba dan Allah kan fitar da na kirki a cikin na banza ba da ya shiga uku a garin nan

A hankali ya ce" Yana nan, lafiyarsa kalau babyna, yanzu ki fada min yauma ya yi ta neman babansa ko? "

Shi yake yin maganar, ita kuwa tana sake wara idannuwanta tana kallon abinda ke nufota

A hankali ta ringa dan neman kaucewa, lokaci daya ta ambaci sunnanta sai kuma ta saki wani tartsatsin ihun da ya haukata duk wanda ya ji shi

A wajen ta fadi warwas jini ya yanke mata , daidai lokacin da sojawan dake shawagi suka cinmasu

Magangannun da yake tsinta sama sama, icen da kunnensa ya ji ana fadi da yaren turanci, sunnayen wa'inda ake ambata, da wace ake nufin a kamata koda matar oga ce, da wace ake fadin a yi gagawar kiran ambulance kar aje ta rasu ne ua saka shi neman zubewa a tsayen da ya mike

Ihu yake yana kiraye kirayen sunnaye babu mai amsa shi domin wayar ta yi gefenta ne ita kuma ta kifa a kas sumamiya sanadiyar icen da Nadia ta muka mata a barin ciki har jinni ya yanke mata

Rana ce da ba zai samu jirgin daukoshi zuwa garinsa ba, rana ce da ya yi dana sannin yin nesa da gida da kuma saka kaki a jikinsa
Rawar da jikinsa yake yi da irin tunani mai karfin da ya daki zuciyarsa ya saka shi zubewa a wajen a summe, abokanan aikinsa ne suka kawo masa talafi suka yi asibitinsu da shi


Bayan awani tara da yan mintunna

A hankali take bude idannuwanta, dishi dishin dake sake mayar mata idannuwan ya rufe ya saka ta fara lalube hadi da ambaton sunnan Allah

Da sauri ya rike hannunta ya kai gefen fuskarsa mai dauke da nutsatsen saje ya shiga shafawa a hankali a hankali yana yin kasa da hannun nasa muryarsa cen ciki gudun kar ya mata magana da ihu kamar yadda likita ya hanna ya ringa ambaton sunnanta a hankali yana mai bayana mata cewa shine , yana sake rike hannunya sosai yana shafa gefen fuskarta

Da matsananciyar wahalar da take ji da kuma yadda take jin jikinta tamkar ba nata ba take ta yakin bude ido da fadawa Allah har ta damu da kyar idannuwan nata suka bude ta ringa kallon fuskarsa da danshi danshin dake digar mata a saman nata fuskar

A hankali ta so yin magana, sai dai ta kasa domin bakinta ya mata mugun nauyi
Goshinsa ya hade da nata still yana rike da hannunta a hankali yana fadin" kar ki ji tsoro kin ji? Babu komai gani nan na dawo, ina nan, ina tare da ke kin ji?"

Wata irin nutsuwa da kwonciyar hankali ta ringa ji na ratsata, a hankali ta iya lalubar cikinta dake sukanta kuma bata jinsa a jikinta
Jin tudun cikin babu ua sakata bude idannuwanta da karfi tana kallonsa , kirjinta ya shiga wani irin sama da kasa da kyar ta iya fuzgo magana kamar haka" Ina cikin? Ina cikin yake ina cikina? Ina ina?"

"Shuiiiiit, gatacen tana cikin dakin jarirai, an maki aiki an cirota gatacen tana barci yanzu na fito daga wajenta, kin sama min baby girl kin ganta? Baba mai irin bakinki, tana ta muimuimui ance wai milk dina yanzu nata ne shi take so ta sha...."
Ya fafa kasa kasa sosai yana kwabe baki
Du zafin ciwo na aikin tiyatar da akai mata ba tare da ta san inda kanta yake ba sai da ta ji sanyi da nutsuwa harma da zumudi a zuciyarta, a hankali barcin ya sake dibarta ta koma domin dama allurar kashe gaba daya jiki da dauke hankali akai mata kafin a shiga da ita tiyata, Allah ya taimaka yarinyar bata samu rauni ba domin bata fadi a saman cikin ba, dukan kuwa uwar ya saukarwa bai daki abin cikin ba domin yarinyar kowa ya yi mamakin lafiyarta, uwar dai ce likita ya ja warning a kan kula da ita sosai domin gaskiya ita kam an daketa kuma ta raunata sosai, sai dai abinda ya kwontar masa da hankali murmushin da ta sakar masa bayan ta ji yarta na lafiya , lalle ya yarda da girman soyayar uwa da Wa, du irin halin da take ciki yar ta nema ana fada mata lafiyanta kalau ta samu nutsuwar da ta bayana a fuskarta


Alhamdulilah jinya ta shata, a kalla ta dauki sati uku a asibiti karkashin kulawar likitoci, ko zanen sunnan yarinyarta an yi shi ne a masalaci sai yanka da aka yi aka yi ta rabo sadaka yarinya ta ci baban sunna wato Fadimatu Zahra tana hannun Hajia Murjanatu dake zaune a asibitin bata zuwa gida ita da baby, sai su mama ke zuwa su dawo domin ko su din zuwan dai ne dan su taya hajia zama, dan harta da wanke baki majinyatan asibitin ke zuwa daga lokacin hakan ya yi a kula da hakan, ga KAN GIWA dake baza kayan kunya ba ji ba gani, idan ya fita dan ya je abinda ya zama dole ne sai aiki, shi kadai ke shiga wajenta har ta saku daga allurar nan likitan ya yarda da zata iya daukan hayaniya kafin ake barin dangi shiga wajen nata, ta sake haske ta yi fayau abin jinya ta rame ama kuma ba muguwar rama ba domin basa wasa da cikinta gaskiya

Bayan an sako su daga asibiti burinsa ya wuce da ita, sai dai sam iyayen suka kiya, mahaifinsa da kansa ya nuna cewa aa sai ta warware, a dole ya hakura ya ci gaba da aikinsa shima gefe daya kuma yana kula da ita

Kwonci tashi yau suke yin kwana arba'in, daga ita har baby Zahra sun yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login