Showing 54001 words to 57000 words out of 124070 words

Chapter 19 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

338

yadda kowa ba zai cutu ba? Haka fita ta gagaresu kiri kiri daga bangaren Kan Giwa, ya saka dokar ba su ba fita ko dan zuwa bangaren su Hajia, idannuwansu har sun fara daukan launin cikin gida sak sai kace matan kuble? Wayar ce bar ta fara isarsu gaba daya, TV ce yanzun bata gabansu kwata kwata , abubuwa na neman damunsu fiye da kima, shin yaya zasu yi ne?

Yau gaba dayansu da farin ciki marar misaltuwa suka tashi
Sun kuma dauki wanka daidai misali kowace ta saka abinda yake daidai da ita

Hakoran Murjanatu sun ki rufuwa hakama na NURIYAH
Sun hade kayansu tsaf sun daure kunnayensu kuwa na sauraron dukkan wani hayaniya na waje sunna jira su ji saukar jirgin da ya tashi da kaka mai gadon karfe

NURIYAH da ta gama saka turaren wuta a dakin ta kallo Murjanatu tana murmushi ta ce" Idan Hajia ta sauka da turanci zan gaisheta yau Baby"

Murjanatu ta sheke da daria tana fadin" So kike ta mana galala tana harararmu daga dawowarta ne?"

NURIYAH ta ce" Kin san Allah, ji nake kamar mu je cen mu yi jiran saukowarsu, na kagu"

Murjanatu ta ce" Nima irin kaguwar da na yi ba zaki gane NURIYAH, kin san Allah yau sai na yiwa mamana kuka ta wani je ta biyewa tsohuwar nan sati kusan hudu ta barmu a nan ba uwa sai gararamba muke a titi"

Nuriya ta yi dariya tana cire hijab golding yelow da ta saka tana ajiyewa gefe ta janyo mai ruwan marron zata saka Murjanatu ta ce" Me yasa zaki cenza shi ?"

Nuriyah ta kalle shi ta kalli Murjanatu ta ce" Ya yi min haske da yawa a jikina , bana jin dadinsa ne"

Murjanatu ta yi murmushi tana kallonta a lokacin da ta saka marron din a ranta tana ayana ' da kin san wannan din ya fi maki kyau shima da kin cire' a bayane kuwa sai ta kama akwatinta ta fara ja tana fadin" Kin ga janyo akwatinki kema mu kai dakinmu, idan ya so da sun dawo ba sai mun dawo nan ba mun kwashe komanmu"

Murmushi ta yi itama tana janyowar suka fito gaba dayansu sunna yar hira suka rufo kofar sunna janye da akwatunnansu masu kalar ruwan kasa suka karaso baban falon mai busa sansanyan kanshin AC da dadadan kanshi mai shiga zuciya

Turus suka yi gaba dayansu sanadiyar mutanen dake falon
Larabawa ne su uku, Maza biyu mace daya, cikin shiga irin tasu ta larabawa wace kuma da ka ganni ka san ba kananun mutane bane
Macen na magana ne da yaren larabci ziryan, dayan na fasarewa da turanci bugage , dayan kuwa yana rike da wata computer

Gefe daya kuma KAN GIWA ne yana zaune cikin shiga ta kananun kaya, yauma wando ne na jins a jikinsa blu sai bak'ar riga da ta rike kirjinsa da damatsunnan hannunsa
A yau haskawar da yake yi ta fi ta kullun, duda fuskarsa ba dariya yake yi ba aman kuma ba a daure take ba, a dan sake take yana fuskantar mai masa bayani da turancin, hannunsa daya ajiye yake jikin hannun kujerar dayan kuwa yana mike da shi ne kusa da hancinsa yana dan yawo da yatsarsa manuniya a kusa da hancin nasa yana kuma kallon su daya bayan daya

A hankali ya dauko dubansa kamar yadda sauran suka yi sunna kallon su Murjanatu ya sauke idannuwansa masu kaifi a saman fuskarta dake zagaye da marron din hijab din mai roba wajen wuya wanda ta daure shi ruf ta rufe gashin kanta sosai da shi

A hankali yake yawo da idannuwan nasa a saman fuskarta har zuwa daidai dan jan bakin da ta shafa marar yawa aman ana gane ta shafa dan ana ganninsa a fuskarta,

Idannuwansa ya cire a kanga ya hauda yatsar tasa wajen goshinsa ya shiga dan murzawa a hankali, lokaci daya kuma kunnensa na jiyo masa hakurin da Auta ke badawa da turanci tana fadin basu san da Mutane a falon ba, da sauri kuma ta ja hannunta suka juya da niyar ficewa a falon gaba daya

A hankali ya sake dago idannuwansa dan sauke a kan mutanen falon, sai ya ga daga mazan biyu har macen nan balarabiya mai larabci sak sun raka su da kallo

A hankali shima ya bi wajen da suke kallon wanda shi a nan idannuwansa suka sauka

Idannuwansa ya rintse da karfi yana dantse lebensa kafin a dan kausashe ya gyara zamansa ya ce"



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
3?? 7??



Idannuwansa ya rintse da karfi sakamakon wani abu marar dadi da ya ji daban aa ransa , a hankali ya dantse lebensa a dan kausashe ya gyara zamansa yana mai furta gyaran murya mai hade da maganaa magana domin a dole ya sa suka juyo gareshi gaba dayansu

Ido dayan ya zarro yana dan dafe bakinsa da alamu ma ya ji kunya da aikata abin nan da yaren turanci yana hadawa da jefi jefin larabcin da Kan giwar na tsinta kadan kadan ya ce" Subahannalah, kar dai aje matanka ne? Subahannalah sir yau nima na aikata aikin da ba nawa ba, dama ace dan uwana ne shine ya kware a aikata aiki irin wannan, ka ga yau nima na bi sahunsa dan Allah ka yi hakuri"

Sai da ya masa kallon baka da hankali na yan sekwani kafin ya cire kansa da kyar ya iya fadin" Ba matana bane, kanaina ne"

A bayane ya fuskanci sukuni a fuskokin samarin nan da suka zo dan hada hannun jari a harkar kasuwancin kwanoni da shi, su din mutane ne manya masu zuciyar nema da jajurcewa, ko a garinsu su din ana reapecting dinsu domin manya ne daidai misali sannan mai zuciyar nema ana bashi darajarsa sosai a ko'ina

Murmushi dan uwan nasa ya yi yana girgiza kansa ya ce" Mu a kasarmu matan basu da yannayin jiki irin wannan, dan kyau sunna da kyau sosai da sosai sai dai a tsaye suke sungulun, ya salam wannan budurwa dama a bani ita da zan dauka ko nawa ne zan iya biyan sadakinta sannan na kaita gidana na riritata tamkar kwai"

Matar ce t amshe itama da yannayi na mamaki ta ce" Tunda muka zo nake gannin matan garin nan masha Allah, aman wannanma gaskiya tana da kyau sosai dubi fa da hijab a jikinta aman kuma ji yadda jikinta ya nuna Masha Allah, gaskiya a da bana son abubuwan nan aman a garin nan na ga sunna da kyau sosai a jikinsu kuma basa hanna su motsawa "

Shi kam ikon Allah yake kallo, irin yadda suka dage suka masa magangannun da yake daukaa kamar wani sabo Allah ya tuba shi bai taba irin wannan tunanin ba, yaren gaba dayansuma nawa suke da har za'ace ana so za'a aura? Salon a aura din a je a halaka ko? A hada yaro da rashin lafiya ga rigimar namiji? No no no, shi yasa ya fi yarda da mace idan ta kai shekara wata talatin haka sai a yi mata aure, zuwa lokacin ta san ciwon kanta, tana aikinta da yan kudadenta a banki, tana iya zama da namiji a halin da ya zo mata, uwa uba idan ciki ta samu tana iya haihuwarsa ba wata matsala, aman a yanzun fisabililahi han jariran nan ko me yasa ake masu irin kallon nan

Agogon hannunsa ya duba ya dube su cikin dan tsare gida dan su fahimci baya son maganar yana so su ajiye maganar ya ce da su" Iyayena sun kusa sauka, idan suka sauka kuwa bani da time din zama da ku a yau, dole sai kun kara kwana a garin"

Da sauri Matar ta nemi da ya yi hakurin shagaltar da suka yi sannan ta ci gaba da yin bayaninta ana bashi fasara daidai yadda zai fahimta har suka gama suka tafi

Ya dan jima zaune har aka sheda masa cewar sun shigo cikin kasar sannan ya mike yana sauke ajiyar zuciya bai tsaya bi ta kan kowace ba ya fice yana sake duba agogon hannunsa da tunanin yanzu sa sauka su kuma karaso palace din

A nutse yake takawa har ya kusa wajen, nan ya ringa gannin alamu na farin ciki a tatare da jama'ar gidan, duda ba ihu suke yi sunna tsale da kakaba daria ba, aman du irin yannayin da ake gaishe shi da dan fara'ar fuska zai iya nuna maka cewa ana cikin hali ne na farin ciki

A hankali yake karasawa wajen da suke tsaye, yana tafia ne a hankali mutanen dake jejefe a gefe da gefensa da bayansa sunna take masa baya sunna bashi tsaro

Sake zuba idannuwansa ya yi a kansu, su uku ne a yanzun
Daya daga cikin ma'aikatansa ne wanda ya gane haka ta kakin dake jikinsa, yana magana da fara'a kwonce saman fuskarsa, uwa uba su yan matan dake dubansa sun fishi fara'ar a saman fuskokinsu

Idannuwansa ya sake dorawa a irin abinda take yi da hijab din jikinta, wanda take yawan dan jansa a jikinta sai ta kuma maidoshi ta gabanta, hakan ya sa yake ta lafe mata a jiki, haka kuma irin yadda suke magana zaka fahimci magana ce ta farin ciki, domin har daya ke hanna daya magana sunna gagawar magana

Dan ja ya yi yana waigawa bayansa kadan ya ga yadda ma'aikatan suka fara layi cen nesa kadan kamar zasu je tarban shugaban kasa

Bakinsa ya tabe yana tunanin yauma so suke ne sai ya kore su ko so suke su nuna masa zasu damu kakarsa daga dawowarta?

Yana wannan tunani nasa mau mahinmanci a wajensa ya ga karyowar kwanar Nadia

Ta sha shiga ne a yau irin nata na gargajiya watau sahari ne ta nada mai ruwan ja da blu ta kame gashin kanta a bayan keyarta ta saka wannan jan abu na gaban goshinta ta saka kwalin da ko daga nesa kana iya gannin tsarin idannuwanta tana tafe tana kyalkyalin saharin bodyguard biyu na take mata baya tana tafe sai raudawa take yi tamkar wace zata karye gida biyu

Idannuwansa ya cire a kanta yana jin lokacin da ake fadin cewa sun sauka kasa sunna tahowa a saman hanyar jurgin

A nutse ya sake juyawa wajen da ya hangi kanwarsa da bakinta , sai ya ga a yanzun sai su biyu ne suke tsaitsaye sun zubawa wajen da Jirgin zai bilo har daidai wajen da za'a dakatar da shi , da dukkan abinda za'a yi masa daga nesa, domin ba'a bari kowa ya karasa sai sun gama budewa an gama sauka tukunnan

Hannunta da ta sako cikin nasa ya saka shi dan saurarawa da kallon wajen nasu, lokaci daya kuma ya sake maida dubansa kansu ya yi tamkar bai san da wanzuwarta a wajen ba, domin ko hannunsa da take dan murzawa cikin nata salon na jan raayinsa bai nuna ya san da tana yi ba

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon wajen da yake kallo da muryarta ta shiga fadin" Yau auta farin cikinta ya ki boyuwa kakarta zata dawo da mamanta"

Yana jinta , aman tamkar kurma haka ya zame mata domin ko motsin da zai nuna mata ya jita bai yi ba

Idannuwanta ta sauke a kan yarinyar, a lokacin da Nuriyar ke sake maimaitawa Auta kalaman da zata yiwa kaka yau da yaren turanci, irin ta bada dukkan wani hankalinta da kulawarta ga murmushin saman fuskarta tana fadi Murjanatu kuwa na sauraro ta shirya tafa mata
Idannuwansa ya lumshe ya sake budewa a kansu, lokacin da Nadia ta sake kallonsa ta kuma kallon wajen da yake kallo

Haka kawai ta ji ta tsargu da kallon da yake yi din, dan haka ta sake duban damtsen hannunsa dake sheki yana halaka dukkan nutsuwarta , ta sake waigawa wajen da Nuriyar take ta ce" ita kuma me ya kawota wajen tarban mutanen cikin gida tamkar wata mai matsayi a cikin gidan?"

Ya kai minti daya da jin furucinta, har jirgin ya karaso da kukansa a hankali yana daidaita tsayuwarsa yana kallon yadda yan matan ke ta neman didira a tsayen nan na farin ciki

Dan murmushi ya subuce masa a hankali ya juyo wajen da muryar Djamilart ta sauka a kunnensa tana kokarin rike dayan hannun nasa itama a nutse ya ce" Ai Y'ar gida ce itama"

A tare suka dago sunna kallonsa, shima ya sada dubansa ya yiwa kowace kallo daya tak sannan ya janye hannunsa daga cikin nasu a nutse ya shiga takawa ya nufi wajen da aka idasa tsayar da jirgin har aka bude kofar

Da kallo suka raka shi su biyun dake tsaye su dukansu, Murjanatu ta daga kafarta da sauri ta bi bayansa , Nuriyah kuwa sai ta saki murmushi tana kallonsu har suka kusa karasawa sai kuma ta ga yayan nasu ya ja ya tsaya ya juyo wajen Murjanatun dake binsa da sauri tana ta washe baki

Ido ya tsura mata da kakausan kallon da ya sakata jin darr a cikin zuciyarta, a hankali ta ce" Yayanmu baka huce ba da muka fito ? Walahi bamu san cewa da baki bane yaya"

Bai ce mata komai ba, hakan ya sa ta farra tsurewa a tsaye da take tana ta kame kame tana neman fashe masa fa kuka

"Bawan Allah ni kamar y'ata ce a gaban baban yaya Allah dai ya sa ba laifi auta ta yi ba?" Muryar Mama ta shige kunnensa hakan ya sa ya cirw kakausan kallon da yake?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? mata ya juya wajen da muryar ta shiga kunnensa

Murmushi ya saki yana kallonsu, Maman tana dan talabe da Hajia dake fadin ita a saketa, ita kuma ta kiya tace sai ta saukota da kyau daga matakalar jirgin nan mai dagogo dagogo sannan zata saketa

Hajia ta ce" Kan giwa hala zalin takwarar tawa ne ake ci?"

Da sauri Murja ta zagayesshi ta nufe su da dna gudunta ta makalkale Mama tana ta murnar dawowarta yadda ka san wata yar jaririya

Hajia ta kara matsawa tana fadin" Gaskiya wannan lamari naku sam ba tsari, y'a gote gote kun laka mata auta, idan kika haihu sai na ga autanci"

Dif mama ta dauke wuta hakama Auta da Kan Giwa

Da sauri Auta ta ce" Hajia haihuwa? Mamana zata haihu? Dan Allah hajia mamana zata haihu?"

Kan giwarma ya juya wajen hajiar dan har ga Allah idan hakan ne gaba dayansu sai sun yi farin cikin hakan fiye da misali, sunna matukar son a samu y'aya a gidan nasu sosai, bale maman nasu da bata taba haihuwa ba , idan da gaske ciki ne da ita ai su za'a yiwa murna

Maman kuwa yadda ka sam zata nutse haka ta ji, da matsanancin mamakin yadda aka yi hajiar ta san da cikin da bai fi wata biyu a jikinta ba, wanda ita dinma bata san da shi ba sai a karshen watan nan da ta ga watan shiru ta yi gwajinta a bayi, da ta gani ta jima tana hawaye sannan ta yi shiru bata fadawa kowa ba dan ba zata saka bakinta a gaba ba kuma abin ya zo ba dadi shi yasa ta yi shiru take fadawa Allah kan ya bara masu

Da sauri ta shiga kame kame tana juyawa dan gannin Allah ya sa Aba baya nan

Ai kam shima a kafen yake ya kuma kura mata ido,

Wata irin ajiyar zuciya ta sauke ta shiga murje murjen goshi tana neman abinda zai rage mata jin kunyar nan mai tsananin gaske

Murmushi datako Elhaj ibrahim ya yi yana fadin" Allah ya raba lafiya, ke matar ni ba zaki zo ki min oyoyo din ba?"

Wata irin ajiyar zuciya ta sauke na jin ya kubutar da ita da doguwar maganar, lokaci daya kuma idannuwanta suka sauka a kan NURIYAH dake tsaye rungume da hannayenta a saman kirjinta

Irin tsayuwar da yarinyar ta yi a lokacin da ta dan karra matsowa kadan , fuskarta ta innocent girl ta bayana karara, yannayinta mai sanyi da karkatar da kanta da ta yi a saman kafadarta ta dama, yalwatacen murmushin da kamar zara baka duniya da farin cikin dake tare da shi ua saka zuciyar mama bada wani irin sautin duka mai karfi

Da sauri ta saki hannun Hajia fa ta sake rikowa ta sake zubawa NURIYAH ido, dan karra matsowar da Nuriyar ta yi ta kuma ja ta tsaya ta yi tsayuwa mai dan wara kafa kadan ta sake sakin murmushin da duka kaf kumatunta suka lotsa ne ya sakata sauri dafe gaban kirjinta sanadiyar neman fasowa ya fado daga kirjinta da ya yi

A hankali take ji dukkan wani farashi na kuzarinta na ragewa, jikinta na yin nauyi

A hankali ta kai hannunta wajen lebenta tana kallon Nuriyar muryarta cen ciki sai dai ana iya ji ta furta" *HUSAINAH*......."

So ta yi ta daga kafarta, da karfi Hajia ta ce" MUHAMADU KAMA MIN YARINYAR NAN bata cikin hayacinta!"

Da sauri KAN GIWA da ya san da shi take ya juya wajen da Mama ta yi taku daya biyu, sai dai bata karasa na ukun ba ta rasa dukkan wani kuzari nata da nutsuwarta ta tafi da niyar kifawa kan dan tayin da yanzu ya saka mutanen wajen farin ciki fiye da misali

Da karfi Aba ya ambaci sunnanta, abin ya zo a jejere kowa na ambatar sunnanta da abinda ya zo bakinsa wanda yake kiranta da shi

Da sauri NURIYAH dake tsayawa tana tsoron karasawa ta samu kanta da balowa da wani irin gudu sakamakon jin da ta yi tamkar an daki zuciyarta a lokacin da ta ga maman Murjanatu ta sume a hannun kan Giwa ya tareta dan kar ta kai kasa, sarakuwarta da Baby sun karasa sun kama masa, mijinta ya karaso ya talabata gaba daya jikinsa na rawa kowane na ambatarta da irin sunnan da ya zo bakinsa ta karasa itama ta manta cewa iyayen gidanta ne a wajen ta shige cikinsu ta nemi damkar hannun matar da basu yi zaman ko na awa daya da junna ba sai irin hafuwar shuuuuu a wuce din nan , aman ji take tamkar wani aman ke janta a jikin matar, har tana ji kamar zata wuce gona da iri a lokacin da wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login