Showing 48001 words to 51000 words out of 124070 words

Chapter 17 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

346

mai albarka suke son saka albarkar dake tare da su a kasuwa , harma ka ce kowa ya zo da dalilin nasa a bayane ka gani kafin a yi maganar gasunnan da kansu da kuma dalilansu, zan iya cewa a cikin nan mutun biyar magana ce ta gado, gasu da yan uwansu wanda ya zama wajibi a raba dukiyar mamaci bayan rasuwarsa wa shakikansa, yawansu ya sa ba zai yiwu su iya yiwa kwaririkansu kwaya takwas rabiya ta daidaitu ba, gashi kawunna a rabe sosai kowa da ina yake zaune da iyalinsa bale a yi aiki tare a raba ladan aikin, sai wa'inda harkar jarin kasuwarsu da suke yi a birni ne ya karye suke son dora wani jarin dan dogaro da kai ta kowani fanni idan dai mutun zai iya tsare kansa da fadawa halaka saboda datin duniya to fa alkhairi ne, dan samun kadarar da zaka juya dinma Alkhairi ne, sunne gasunnan su su hudu, sai Balan Sabo da zai aurar da y'arsa auta kuma babar y'arsa domin ita daya tal Allah ya bashi kuma har karatun boko ta yi da kake ganninta a nan, yanzun Allah ya fitar mata da miji dan Birni domin kuwa ma'aikacin gidan wuta nema, shi yasa ya sameni da tasa bukatar kan shima yana so a saka nasa a kasuwar dan yana son yiwa Auta bajinta , ka dai san kayanmu na aure na nan kauye da naku ba daya ba......to wannan shine dalilansu , gasu kuma da kansu a zazaune"

Shi Kan Giwa gaba daya a bayanan yarinyar da aka nuna aka ce za'a yiwa aure ne abin ya fi bashi mamaki da kuma damunsa
Dan haka bai yi kasa da gwuiwa ba wajen duban mai gari da kulawa sosai ya ce" Aman wannan yarinyar karama za'a aurar?"

Mai garinma ya dubi budurwar da Kan Giwa ke maganar yarinya karama za'a aurar, to ai su a garinsu wannan din gaskiya tama zama babar kanta ba'ai mata aure ba, domin mahaifinta mutun ne mau bin y'aya, ko dan ita daya ya malaka a duniya bafa mai takurawa y'ar baba, shi yasa ta yi karatunta har ta gama secondary school sannan zai aurar da ita, in ba Kan Giwa ba sa'aninta ai sun tara y'aya sosai wasun har sun zuba uku ai, yanzu haka kannan bayanta ne zasu mata gorance ai, a nutse shima ya bashi amsar kwarai kuwa ita

Kan Giwa mamaki ya sake neman kashe shi a zaunen da yake yana kiyasta shekarun yarinyar da tunanin anya ta kai shekara goma sha takwasma kuwa?
Sai dai bai kuma tofa wata magana a kan abinda ya shafi yarinyar ba ya fuskance su a nutse ya ce" A cikin masu son siyar da Kwarinsu na ware masu rabiyar gado, su sunna iya komawa gefe idan aj gama a yi bayanin abinda suka yanke sai a shelanta wa mutanen kauyen idan da mai so ya siya, in babu mai so sai a siyarwa wani, "

Du gefen suka koma sannan ya dora da magana bayan ya fuskanci sauran ya shiga fadin" A cikin yan kasuwar nan da suka rage, zan so na sake jinjinar bukatarku, ita wannan da kuke ganni kwari ce mai kawo kayan itatuwa da su lambu, ku kun fini sannin cewa rufin asiri ce wa kasuwancinku harma da iyalinku kansu, waje ne da zaku shuka , shukar ta firo ta yi yabanya, a ciki dole zaku siyar, ku ci, ku yi kyauta, ku yi sadaka......, Idan har abin juyawar hannayenku akoy kwari ne bashi da shi muna iya dubawa a karra maku hannun jari, idan kuma kun riga kun yanke hukuncin siyarwa ne, koda kun barta ba zaku kuma iya ci gaba da kulawa da ita yadda ya dace ba, a nemi mai so a fansa masa ya kula da ita yadda ya dace domin mu abin alfahari ne a wajenmu"

Dan kuskus ne yake wakana a tsakaninsu bayan shirun Kan Giwa, dan haka ya juya shima wajen mai garin da ya nemi talafinsa a matsayinsa na aboki, kuma Soja wanda ya tabata idan ya shiga lamarin ya yiwa mutan kauyen gwari gwari zasu iya daidaita tunaninsu a kan yinkuron siyar da alkhairan kauyen, dan kuwa ya maimaita maganarsu ne da suka ce anfanin kadara ai siyarwa ne dan su yarda da shi ba yana son hanna su bane dan wata manufa, aman idan kace kadarar dake ajiye a matsayin taka da zarar ka hadu da wani dan tashin hankali zaka kawar ka siyar ai da ba'a ajiye komai ba a duniya, balema su biyar din nan da suka rage yan kasuwar da Baba , a gaskiya bukatocinsu bai kai na su rabu da abu mai mahinmanci ba, shi ko dan yana dan karkarar ne shima? A duniya abun nan hudu baya son rabuwa da su da dadin rai, watau GONA, GARKA, ABIN KIWO, TSIRO, yana rike nasa da mahinmancin gaske, domin da su yake bajinta iya bajinta, ga darajar kauyen kanta ai sunne, su yan birnin da suke takamar birni birni birni idan babu Noma , ba kayayakin garka ai sun shiga ukunsu, shi kam baya son siyarwar gaskiya, sai dai kuma maganar karin jarin da Kan GIWA ya yi ne ya saka shi a tunanin tabas siyarwar zasu yi, domun mutumesn kauye ya ki jinnin ka ce zaka yi wani tunanin samun kudi da shi kai tsaye kawai, domin gurguwar fahimta zasu yiwa abin

Wanda ya fi wayewar aka saka ya yi tambayar yana ta firifiritu da ido ya ce" Elhaji, mun ji bayanin nan sosai, sai dai wani hanzari ba gudu ba, shi karin jarin biyansa da zamu ringa yi du shekara shekara ne? A shekarar nawa zamu ringa zubawa? Idan muka ji sai kowa ya je ya duba yannayin samunsa in zai iya sai ya amsa, idan ba zai iya ba kuwa sai ya siyar da Garkarsa domin ka san yannayin samun, yannayin kasuwar wani lokacin yadda ka kula ka je haka zaka lodo ka dawo har sai makocinka ya maka alfarmar kudin mauta bashi, wannan shine matsalarmu kuma abinda muke son ji"..........


Maimakun abin ya bata masa rai a yau sai ya samu kansa da jin wani farin cikin reaction din mutanen, ashe dai dan sunna cikin riga irin wannan sunna tafe kamar basu san ciwon kansu ba sunna da nasu tunanin summa? Dan haka ya gyara zamnsa yana Murmushi ya ce" Masha Allah, Masha Allah, in sha Allah shi talafin jarin za'a baku ne fisabililahi, nima mutun ne mai zuciyar nema, na horu da *NEMAN NA KAINA* tunda kannanun shekaruna, shi yasa nake ba mai nema daraja nake kuma talafa masa da dukkan abinda Allah ya sa zan iya bashi talafi dan gannin ya samu ci gaba a duniyar nemansa"

Baba dake zaunensa tun dazun yana yan muzuransa ya karkato da kyau da shegen mamaki ya ce" Kanga yaro, ka tabata da maganarka kuwa? Kana nufin za'a basu kudi kyauta haka salin alin su tafi ba wani bita da kulin da zai biyo baya? Ka ga fa maman Y'ar baba kan fadin yan birni akoy iya bita da kuli, dan nan aka kawo talabijin aka kafa aake kunnata da zafin ranar garin nan dan wani tsohon wulakanci da sata irin ta yan birni sai ka biya kulin zaka kalla, ni ai bai fi sai bakwai da na je na kalla ba, tunda na ga wata karya karara naa daina kallo kar a taba min imanina ina zaman zamana"

Murmushi ne ya subucew Kan Giwa gannin tsakaninsa da Allah yake maganarsa ya ce" Eh Baba, za'a yi takafi ne domin Allah, ba su kadai ba kowama in sha Allah"
Wani mamakin ya sake kama baba ya dan sake matsowa yana kallon kan Giwa ya ce" Yaro kana nufin talafin harda ni?"

Kan Giwa ya fuskanceshi sosai dan kuwa ya kula tsohon nan idan ba amsa ya bashi yadda ya dace ba tabas yana iya rikita tunanin kowa a nan din , ga yarsa sai son hanna shi take aman yana rike da hannunta yana fadin ta barshi ya yi magana mana kar a cuci su Muntaka a banza , ko ba komai ai shine ababa a nan din

Kan Giwa a nutsensa ya ce" In sha Allah Baba, har kaima za'a yiwa Auta kayan dakinta ba sai kaa siyar da Garkarka ba, tunda ka ga ai Garkar tana kawo anfani sosai ko?"

Dif wajen ya yi na yan sekwani kafin Baba ya sake wara idannuwansa ya rage muryarsa sosai yana fadin" Yaro, da Maman yar baba ta je birni da kawarta aka tambayo gado mai runfa irin na yan birni cewa suka suka yi sai a makudan kudin da suka kai rabin millian zasu mana har kujerunsa, ka ga kuwa wannan ai dole na sigar da garkarnan tunda kudin ai da yawa"

Yanzun kam murmushinsa sai da ya jima a saman lebensa ya fuskanci abokinsa da ya gama cika da farin ciki da sannin cewa yau fa mutan kauyensa sun taki sa'a mai girma da ya yarda ya zo da kansa, ya kuma san cewa a yau farin ciki sai ya shinfidu a waje da yawa, domin kuwa ya san waye Kan Giwa, tunda mahaifinsa ya rasu aka nada shi sarkin garin ya ajiye aiki ya dawo dole dan kula da kauyensu yake missing din aiki a karkashin kan Giwa, wanda ya zamto aboki a gareshi mai matukar mahinmanci

Mai gari ya ce" Eh baba, ai tunda Allah ya sa ya ce zai yi , zai yin ne in sha Allahu duka komai da komai"

Nan fa tsoho ya so rikice masu , zane yake yana fadin kudin kaza ne fa? Ana sake tabatar masa, karshe dai ya yi shiru da bakinsa kafin ya ce" to ko dai kannen shugaban kasa ne shi din?, Dan Allah a inaa kuke samun kudi haka ne yaro? Ko da aka ce yan birni sun ci gana har shuka kudi suke haka ne?"

Kan Giwa ya yi yar dariya yana fadin" Baba, ba'a shuka kudi, NEMAN SU ake yi, sai dai NEMAN nasu kansa kala daban daban ne wannan din da izinin Allah zaku ci halal, sai dai kar kudin kowama ya rudeku, domun Wani NEMAN NA KAN da Kai ake yinsa baba........"

Ai kam da wannan ya samu ya kakashe dukkan rigimar da ya dace sannan suka shiga yawatawa a cikin kwaririka sunna shan sansanyar iskar garin sunna dan zantawa gwanin ban sha'awa, a wannan kauyen ya yi sallar azahar, da la'asar, har sai da yama ta yi sosai suka kama hanyar gida yana waya da Su hajia dake ta tambayar jikinsa a rikice domin auta ta sanar mata bashi da lafiya shi kuma sai tarota yake yana sake fadin ba fa wani abu bane rikicin Auta ne har suka karaso bangaren Hajiar da yake so ya leka yau ya ga yaya suke kula da tsaftar wajen, domin koda basa nan bai rufe wajen ba ya bari a hannun amintatunsa ana kula da wajen sosai tamkar sunna nan


"Tsaya tsaya ki ga yadda take yi ita hajiar, bara ki gani sake riken jakar ke dai Auta" Nuriyah ta fada tana sake daka fuska da wanu kwasheshen gilas baki a fuskarta ta karkace daurin nan kwali ta turo shi sosai gaban goshinta tana harare harare da lebenta jajaye ta murza yar agogon hannunta tana fadin" Ke yarinya a kudin ayabar na cire ashirin ashirin idan zaki siyar ki siyar, idan ba zaki siyarba ki karra gaba warin rana kike kar ki goga min a jikina!"

A tare suka bushe da dariya Nuriyah ta juyo tana cire bakin gilasss din zara dora da surutun dake samunta idan suka kasance daga ita sai Murjanatu tamkar aku idannuwanta suka sauka a cikin nasa yana tsaye dan nesa da su kadan aman daga bayansu yana kallonsu gaba dayansu da kallon da bata san asalin wajenda ya dace ta ajiye shi ba, harara ne na sun cika masa waje da kayan shirme sunna kuma iface iface ko me?

Da sauri ta rike t???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?able din da suka cike da Ice cream dan kar ta kifa hakan ya sa dan kwalin da ta yi daurin irin hajiyoyin dake yaga su a bakin danja idan sunna tallah sunna shan dariya ita da Murjanatu ya kunce ya fadi kasa , hakan ya bayanar da lalausan gashin kanta mai saka bawa a kokonta asalinta domin idan ya haye da farar fatarta tamkar ba tamu ba mu mu din nan

Idannuwansa ya cire a hankali a kanta, lokaci daya kuma tamkar magnet ya sake maido au ya zuba mata a kanta tun daga kan rigar dake jikinta doguwa har kasa wace zai iya kiranta tamkar buhu ta mata domin rigar kamar abaya ce budadiya sosai da sosai, sam bata lafe mata a jikinta ko kadan ba kuma dogayen hannuwa ne da ita suma a buden sai wajen tsintsiyar ne ya daure a daidai nan kawai

Gashin kanta ne ya zubo gaba a lokacin da ta duke kasa gaba dayantaa tana ta son gaishe shi, wanda hakan ya sa Murjanatu juyawa ta gane shine tana murmushi itama ta mike ya tarboshi da yi masa oyoyo tana duban hannunsa da tambayar jikinsa

Idannuwansa a saman fuskarta sosai kasa kasa ya ce" Me yasa take saka atach ne ita kuma kalar wannan?"

Sai da Murjanatu ta juya ne ta gane da wace yake, da dan mamaki da kuma dariya dariya ta ce"










>?p?>?p?>?p?>?p?>?p? A sha ruwa lafiya sisters>?p?>?p?>?p?>?p?>?p?>?p?



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
3?? 5??



Sai da Murjanatu ta juya ne ta gane da wace yake magana, da dan mamakin gannin yayansu ne ya shiga harkar da bata shafe shi ba da kuma murmushi a saman fuskarta ta ce" Yaya ba gashin aro bane, gashin kanta ne, kuma bata shafa masa komai dan ya dauki kalar nan haka Allah ya haliceta da shi"

Dan shiru ya yi yana kallon fuskar Murjanatun, so yake ya tambayeta ita kuma a ina ta san duka haka da har take fadi da dukkan yardarta da kuma gaskiyarta ne? , Sai dai wani abin ya ankarar da shi wannan din ba huruminsa bane dan haka ya shiga takawa yana karasawa wajen table din nasu

Da sauri Nuriyah ta mike kanta a sade hannayenta a hadenta , watau ta kame waje daya dan ba mai girma girmansa da kuma kiyaye bata masa kamar yadda babu mai son aikata hakan a gidan baki daya, domin a dazu da ya fitan ana ta dan kai kawo aman a yanzu da ya dawo ta kula harta manyan sojojin kowane ya kama kansa , baka yin wani abin da ba a kan aikinka ba bale ita Nuriyah yar gidan baba tsohuwa Allah jikan rai?

Robobin Ice cream din yake kallo shake saman table dim kala daban daban wasun har sun narke wasun kuwa basu rigai sun narke ba, haka gefe cikin dan kwondon zuba abin shara an jejefa roba ta kai biyar a ciki ga ledojin chocolate da mememe, kai dai dukkan abu na yarinta da rashin sannin ciwon kai a tatare da wajen zaman da mutanen dake zaune a wajen

Murjanatu ya sake dagowa ya kalla wace du ta rikice dan ta san baya so tana kwasar zaki haka sake ba daidaitawa wai cutukan zamani wata cutar bakama san kana fama da ita ba sai ta tashi aikata tsiya ta bayana lokaci daya tai maka ilar da idan ta barka da rankama ba lalle ka anfani kanka yadda ya dace ba, watau dai zata gurbata jin dadin rayuwarka da motsinka a gidan duniyar baki daya
Kafin ya sake maida kansa kan yarinyar nan itama ya yi mata kallo na yan sekwani
Kasa kasa sosai da furucinsa ya furta" Who old are you?"

Ita dai a tsayen da take bata san me bawan Allahn nan ya fada ba, ita da nan hanyar da zata bara masu wajen nema take domin har ta gama yanke shawarar dauke kwondon sharar nan ta kai inda ake kaiwa ana tara sharar kafin a fitar duda ba aikinta bane hakan
Murjanatu kuwa ta san cewa a duniya idan akoy wanda ya san kwanakin haihuwarta bayanta bayan mamanta to fa shine, domin ya fi kowa saukon wishing dinta hppy birthday a duniya baki daya, dan haka ta san ba shekarunta yake son sani ba, hakan ya sa tana murmushinta ta bashi amsa hankali kwonce dan ta kula bai gane niyarsu na zama a nan a yau ba sun zauna ne dan su sha ice cream har sai sun kusa yin amai kafin su hakura, shi ya sa ta kwaso kaloli daban daban dan Nuriyah bata san kalar da ta fi birgeta ba, hasalima yau din ta fara sha

Da mamaki yake kallon Baby, da kula ya ce" Baby ita an cire mata harshe ne da dukkan tambayar da zan mata ke kike bani amsa ko wani salon raini ne?"

Da sauri Baby ta kalli NURIYAH, sai Kuma ta kalli yayanta cike da tausayawa itama da yaren turancin gangariyarsa ta ce" ka yi hakuri yayanah, ba raini bane ba, bata san me ka ce ba , batama san da ita kake ba dan bata iya turanci ba"


Manyan idannuwansa ya wara a kan Baby da mamaki sannan ya sake juyawa ya kalli Nuriyah na wasu yan sekwani kafin ya cire kansa a kanta ya juya da nufin tafia, sai kuma ya dakata ya dawo ya dauki babar ledar ciye ciyen nasu dake kasa ajiye ya budeta yana leka iyayen chocolate da biscuit din dake ciki
Kansa ya dan girgiza ya shiga kwashe ice cream din daya bayan daya yana maidawa cikin ledar har ya gama sannan ya sake kallon baby da ta yi wani iri da fuskarta tamkar yar jaririya , watau tana daf da fashewa da kuka dan rigima irin nata bayan ta san bata da gaskiya ko daya
Murmushi ya yi mata ya juya wajen Nuriyah da har yake mamakin bata gaji da sada kan bane?
" Ki daina shan sanyi da zaki da yawa, ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login