Showing 3001 words to 6000 words out of 124070 words

Chapter 2 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

322

suka tafi da ita, daga nan Bata kuma sannin inda kanta yake ba, sai bude idannuwanta tayi ta ganta a saman gadon asibiti, hannunta jone da karin ruwa

likita ne ya turo ya shigo da wani saurayi ? bayansa na biye da shi, sai ? wannan lokacin ta dago da idannuwanta ta sauke kan wata tsohuwar mata mai cike da kamala wace sai ? sannan ta ganta,

tunaninta ne ya katse lokacin da likita ke cewa " bata dauke da ciwon kanjamau, abinda ke damunta ? jikinta rashin isashen hutu, rashin kwonciyar hankali da kuma cutar cizon sabro, wa'innan abubuwan ne suka hadu suka bada gudumunwar shinfidar da ita, aman yanzu wannan hutun da ta samu na koma da ta shiga har kwana shida ya dan rage wasu abubuwan fannin damuwar domin idan idannuwanta ? bude ne kirjinta yake yawan bugawa,


katse musu magana tayi lokacin da ta gama fahimtar yanzufa ba innarta, to kodai mafarki ne tayi, domin kuwa innarta ai Bata kai wajen kwana shida da rasuwa ba, aman abin mamakin shine su kuwa wa'innan su waye su ? Mai suke nema a nan ? Cikin muryar marar lafiya tace " *Ina Innata*? Ku kuwa su wanene ku ?

? tare suka juyo suna kalonta, inda naga wannan tsohuwa ta dan matsa nesa kadan da gadon tana kalonta ba tare da ta furta komai ba,


? hankali wannan dan saurayin ya matsa kusa da gadon da take kwonce ya ce" kin farka ?

Nuriyah ta kasa magana sannan baci ya kuma daukanta ? hankali,


likitan ya gama yi musu bayani ya juya ya fita,

yana fita wannan tsohuwa tace " kai Mubarack karka kuskara ka matsa kusan yarinyar nan, kaji fa ance ga abinda ya kashe kakarta, ni Sam ban yarda da wannan likitan ba da gani macuci ne ya saka mu mu kwashi masifa mu kai gidan mu, ai indai taimako ne mun taimaka mata iya gwargwadon iyawar mu dan haka kawai ka mayar da ni gida kaima ka koma bakin aikinka karta jaza maka ? koreka domin kasan da aikin nan naka muka dogara gaba dayan mu

Mubarack ya danyi kasakai Yana sauraron maganar maman sa, can ya nisa yace " to baba ki cire mata wannan abin na fuskarta KO tayi nunfashi da kyau kinga dai ni namiji ne ba muharaminta ba, aman ke macece ba komai, wly ba abinda zaki goga ai kinji abinda docter yace


ta watsa masa harara ta ce" sanu sarkin ilimi, Wanda yafi uban kowa ilimin adinni, wannan iya yin naka irin na mahaifin ka bazai saka na biye maku ku kaini ku baroni ba, dan haka umarni nake baka ka fice min mu tafin tun kafin nayi mumunan furuci ? kanka Mubarack


Jin haka ya sakashi juyawa hankalinsa gaba daya ? kan Nuriyah ya bi bayan mahaifiyarsa dan cika umarninta......



*>?&? @&>?&? @&>?&? @& NEMAN NA KAINA>?&? @&>?&? @&>?&? @&*


Marubuciya: *SAJIDA*


*P+


*(4)*


Bayan tafiyar Mubarack da mahaifiyarsa Nuriyah ta kai wajen wata awa tana bacin wahala domin alurar baci docter ya saka mata ? karin ruwan dan ta samu isashen hutun zuciyarta

? hankali ta fara bude idannuwanta da suke shanye, daman ga magana ga abin baci sai suka bada kalar idannuwan mashaya, ? hankali ta kara gyara nikaf din da ban taba ganin inda ta cire shi ba, a hankali idanuwanta ke zubar da hawaye, cikin dakusashiyar murya ta furta inalilahi wa'ina ilaihi raj'une, Allah ya sa bakin wahalarki kenan innata, Allah ya jikanki da rahama, Allah ya sa can ta fiye miki nan, tabas mutuwa bata shawara bata fadin cewar tana hanya, kawai dauka take, sannan ba ruwanta da yaro KO baba, KO maraya KO mai iyaye, ba ruwanta da talaka KO mai kudi, ta lumshe idanuwanta ta bude kuma can ta ce " astaghfrullah, Allah n'a tuba ya Allah,

? hankali ta sauko daga saman bed din asibitin tana dan dingisa kafa ta bude, tana yiwa daular dakin asibitin bankwana,

Sai ? wannan lokacin ta Tina fa KO naira biyar babu a hannunta KO kudin ruwa bata da shi, taso ta nufi gidansu haka kawai taji bata mararin hakan, ta juya a hankali ta dauki hanyar yan hula

Tana isa ta samu an jibge hulunan, Dan nesa kadan da shi ta tsuguna ta gaishe shi

wannan Karin fuskarsa ba fara'a domin ya fara tunanin yarinyar nan ko wata mayaudariya ce, Hakan ya Sa ya amsa mata ba yabo ba falasa

Can ya dago yana kalonta yace" baiwar Allah lafiya? Naga kin zo munyi magana kuma kika dauke kafa, injin dai lafiya?

Nuriyah ta Kara dukar da kanta cikin alamar kuka tace " kayi hakuri, rasuwa ne aka yi min, kakata ce ta rasu kuma daman ita kadai tayi min saura shi yasa na zauna har yau

Wani irin tausayinta ne ya dirar masa, hakan ya saka bai Kara furta komai ba ya hada mata tarin huluna da uban sokilin da sabulu da komai, Haka ta tatara ta koma gefe tayi bismillah ta cire safar dake hanunta, hanayenta wani irin fari ne da su sai nayi tunanin yanayin zapin safar dake hannunta dare da Rana, hankalinta ta maida sosai ta shiga wanki hulunan nan

Ba ita ta Mike ba sai karfe daya da minti ashirin ta tashi ta Jere su wajen da ake shanya masa huluna

waje ta samu ta Dan rabe tana raba ido domin bata je ta ce masa ya biyata ta gama ba,

Suna haramar Shiga masalaci ya Lura da ita, cikin tausayawa ya irga hula hamsin daidai ta wanke ya irgo 7500 ya mika mata, har rawa hannunta yake ya karba tayi ta zuba godiya ta juya ta tafi

Tunda ta shigo layinsu ake Binta da ido da kalon tausayi wasu kuwa kyankyami,

gabanta ne ya yanke ya fadi lokacin da ta hango ana zubda yar sauran katangar gidansu ita da innarta,

Dafe Kirji tayi ta kwalalo ido ta nufi wajen da gudu tana tambayar kai Malan lafiya??????



Ya salam shin ina Nuriyah zata nufa? >?&? @&>?&? @&>?&? @&>?&? @&>?&? @&>?&? @&>?&? @&>?&? @&>?&? @&>?&? @&
*>?&? @&>?&? @&>?&? @& NEMAN NA KAINA>?&? @&>?&? @&>?&? @&*


Marubuciya: *SAJIDA*


*P+


*(5)*



Tambaya take kai Malan lafiya ? Mai kakeyi haka ? Wa ya sakaka zubar da gidan nan ?


Masu aikin suka dan dakata sunai mata kalon tausayi da kuma tsoro domin Wanda ya saka su aikin ya fada musu mutuwar kakarta ya haukatata sannan cutar kanjamau ce ta halakata dan haka yake son ya zubar da ginin nan yayi wani ? wajen ita kuwa ya maida ita kauye

Tambaya take aman ba Wanda ya bata amsa,

Wani yaro da yazo ficewa ne yake ce mata" ke yar gidan tsohuwa mai neman na kanta, kinga wannan datijon mai mota ja ne ya Zo tare da masu aikin nan aka shige rushe ginnin, yace wai kin haukace tunda tsohuwa ta mutu

Da sauri ta rintse idannuwanta sai ga hawaye sharr suna bin kumatunta, ta juya tana taka kafarta da kyar ta nufi wajen masalacin anguwar inda tayi canji a kudin aikinta na yau ta nemi waje ta zauna duk inda yara zasu fice sai ta kiraye su ta mika musu tana fadin ku tayani da adu'a, Allah ya jikan tsohuwa, sannan ya jikaina ya dafa min, sai kuwa yaran su artaya da murnan su suna fadin Allah ya saka maki da alkhairi



wata murya ce ta tsinto tana fadin" sadaka maganin musiba, sadaka falala mai yawa, Allah ya bamu ikon bayar da sadaka da zuciya guda,

saurin dago da kanta tayi tayi arba da wannan datijon arziki, Wanda ? tsahon rayuwarta shine mutun na biyu bayan inaRta wa'inda suka taimaki rayuwarta domin Allah

cikin yanayin farin cikin ganninsa ta kara dukawa daga zaunen da take tana gaishe shi

ansawa yake hankali kwonce Yana kara karantar nutsuwar yarinyar

can yace " ya Akayi kika gudu daga asibitin ? Abdul wahid yazo yake ce min ya koma bai sameki ba, kinsan shine Baban yarona yayi ta nemanki, shine yanzu da na fito daga masalaci na nufi gidan naku sai na tarar da mumunan labarin wai wani mai jar mota yace ? rushe ginnin

Y'ata, ina son ki fada min takamaimain labarinki domin sosai nake jin tausayinki a cikin raina, shin mainene ainahin labariki ?



Nuriyah tayi Jim can tace "

? yanda innata take bani labari, kakana na wajen mahaifiyata sunansa Elhaj Abubakar mai wazobiya, ya kasance cikaken musulmi mai sauke baki ? gidansa, wato idan dai taimako sai mai wazobiya, haka ne takensa

Elhaj abubakar matarsa daya wace Allah ya azurtata da haihuwar Yaya mata har hudu domin biyu tagwayu ne sai kuma biyun na baya, A?cha, Farida, sai hasana da hussaina,

sosai Elhaj abubakar yake cikin hatsari duba da irin sana'arsa wato siyar da gwal, hakan ya saka yake taka tsantsan da rayuwar iyalansa, ? koda yaushe suka tashi koda fita da wani saurayi daya ya yarda dari bisa dari shine yake tuka iyalan Elhaj Abubakar wato lawali mai kyau

lawali mai kyau dan unguwar ka taka ne dake ? cikin kano, gidan su lawali mai kyau talauci har ya fito ya shaida kansa aman shi lawali akoy shi da gwali hakan ya saka baya kwana ? gidansu Sam sai dai yaje gidansu abokansa ya kwana abinsa, sosai Allah ya bashi halitar kyau ? jikinsa duba da yanayin tsarin halitarsa Tun daga kansa har kafarsa

sosai yan matan anguwar ke sonsa domin ya iya gayu da suturar abokansa ga kyau hakan ya sa aka yi masa lakabi da lawali mai kyau

lawali akoy biyaya ga masu kudi, ya jima Yana yiwa Elhaj abubakar yan aikace aikace ? shago, harda su shara da komai, sannan KO sau daya Elhaj abubacar bai taba kama lawali da wani mugun abin ba, hakan ya saka ya kara yarda da shi harma ya biya masa ya samu takarda ta shaidar tukin mota,

Zo ka ga gwali wajen lawali domin saima ya daina yiwa gajaje magana har fadi yake ai yanzu kuma ya fi karfin ajinsu

Tafiya tayi tafiya inda Elhaj abubacar ya kara yarda da lawali dari bisa dari har ya yarje masa sannin gidansa ya bashi mukamin tuka matarsa Hajiya Halima da kuma yayansu mata

Shakuwa ta musaman ta shiga tsakanin Ousseina da lawali domin kuwa wani irin sonsa take da zuciya daya, Ouseina ta kasance kunu huce in shaka ce, ita bata san wannan kalma ba wai rigima, tunda lawali ya nuna cewar yana sonta sai kawai taji ta yarda da shi dari bisa dari


Tafiya tayi tafiya har soyayar ouseina da lawali ta fito fili inda Hajiya Halima cikin gurbataciyar hausarta ta samu mijinta take shaida masa wannan labari

Sosai Elhaj abubacar yayi murna da hakan domin kuwa shi fa ya yarda da shi ba dan kadan ba, nan da nan ya same shi yayi masa maganar kawai ya turo magabatansa ayi maganar aure


budar bakin lawali sai ya fashe da kuka Yana fadin " Aba ni maraya ne, banida uwa banida uba, dangina ban san inda suke ba, yanzu haka haya nake ? dan dakina ni daya, shi yasa nake ta faduwar gaban ranar da dan nemi Aure, ya kuma fashewa da wani kukan

Elhaj abubacar ya mugun tausaya masa yace" kayi hakuri lawali, kayi hakuri, haka Allah ya so, ni zan aura maka ouseina sannan na baku gidan zama, abinda nake SO da kai shine ka rike amana lawali ka rike amana, ka sani du Wanda ya riki amana to fa Allah zai biyashi, idan kuwa kaci amana Allah ba zai barka ba

tamkar lawali ya kwonta haka yake godiya Yana washe hakura,

Yana komawa anguwarsu ya je gidan su budurwarsa Saratu inda ya kwashe karya da gaskiya yake fada mata zancen auren ya kara da fadin " my Sarah, ke kinsan ina sonki, sannan wannan Aure da zanyi auren jari ne dan nima ba samu na kaina, ina samu zan baleta ta tafi gidan ubanta muci gaba da rayuwarmu da yayanmu

Saratu tayi na'am da shawarar lawali domin ? yanda take ji da kanta tana SO itama yau ace kaf cikin layinsu itace ta farkon da ta fara shiga gaban motar mijinta, dan haka ta yarjewa shawarar sa

KO wata ba'a saka ba inda elhaj abubacar ya yiwa lawali gata, ya aura masa Ouseina ya basu gida mai kyan gaske ya zuba musu kayan alatu sannan ya malaka masa mota ya bashi jari

tirkashi dagin kai sai ya karu inda kwata kwata ma ya dauke kafarsa daga anguwarsu mahaifansa daman kunya yake ace wai sune mahaifansa domin talauci ya saka har sukayi kamar sun wani masakance domin kuwa basuda hakuri, kuma Allah ya basu yaro maran Jin kai

Watanin farko daga wata daya har zuwa wata hudu Ouseina ta sha lele wajen lawali inda take zaune lafiya da mijinta da kuma mai aikinta inan sudan matar da take yiwa mahaifiyarta aiki da aka yi mata Aure sai aka hadata da ita dan ta kula da lamarinta

Sosai Inna ta karanci halayar lawali abinka da tsofafin da da basa baci Alan Aman Sai tayi shiru da bakinta domin furta wani abin ? nan ba huruminta bane, ita dai tana iya yinta dan ganin Ouseina ? cikin farin ciki


wata rana Ouseina na zaune da magariba kawai sai Jin dirar motoci tayi da guda ana shigowa gidanta,, ba Wanda yayi mata magana aka bude dakin dake kusa da na mijinta hannun dama aka shiga da matar

Cirko cirko suka yi suna kalon ikon Allah bayan fitar masu kawo amaryar nan, sai ga lawali ya shigo da babar rigarsa Yana washe hakori

Dan matsawa tayi cikin sanyin muryarta tana fadin " mai gida ,Aure ba ka kara ?

Lawali ya zuba mata ido Yana shirya karyar da zai mata, ya lemun kuwa sai cewa yayi" kai Ouseina da abin dariya kike, abokina ne yayi Aure shine fa na taimaka na basu dakin nan kafin Allah ya bashi ya ginawa matarsa gidan ya sakata

Sai ? lokacin ta sauke ajiyar zuciya, sannan wani amai ya Zo mata inda tayi bayinta da gudu tana kwararawa Inna nayi mata sannu domin ciki ne da ita har na wata uku da yan kwanaki

Baiwar Allah Ouseina ta yarda da maganar mijinta, domin kulun tare suke kwonci sai tsakar dare ya lalaba ya fada dakin saratu su ci karansu ba babaka ya dawo dakinta ya zube mata daudar

Kwonci tashi Ba wuya wajen Allah ? yan watanin nan Elhaj abubacar ya fuskanci matsaloli da yawa ? harkarsa domin barayi sun dauki abinda suka dauka

Magana yake da gadara inda yace" kai nawa na biyaku ? Na fada muku idan suka kawo muku gardama gaba dayansu ku kashe min yan iska ku kwaso min kudaden nan domin na jima Ina jiran irin wannan rana, dan haka na baku yau zuwa gobe ku tabatar da kun kwaso min arzikin Elhaj abubacar kun halaka shi da iyalan sa dan na samu na kaura gidan nan nasa da iyalaina

Ido na zaro daidai lokacin da wannan mutumin ya fada motarsa ya cire hular kansa domin lawali ne, haka ya harba motarsa bakin titi Yana tunanin daga an kashe iyalan Elhaj abubacar da shi din kansa shi kenan shi ya gama zama mai kudi, da ba dan ba da har Ouseina zai kashe aman ina Yana Jin dadin kasancewa da ita ga kyau ga biyaya, ga tsarin halita, dan haka ita bazai kasheta ba (ya rab>?&? @&)

Zaune Elhaj abubacar yake inda wayarsa ta dauki ruri, wannan Kira na tara kenan ana yi masa dan haka ya yanke shawarar dagawa yayi salama

Ba'a amsa salamarsa ba sai cewa akayi" ka taba taimakona nima zan taimAkeka, ta tabatar ka tatara iyalanka Kun bar Nigeria, domin ? yau karfe uku na dare zamu Zo da zumar kasheku mu kwashe dukiyar ku da takardun kadarorinku, dan haka kanada damar tsira awa biyar ta rage maku ku
Dif aka kashe,

Wata irin zufa ce ke karyo masa ? zaunen da yake inda cikin sauri ya shiga wuleliyar motarsa ya nufi gidansa, Yana zuwa ya samu iyalansa, cikin Siri ya sanar da su nan da nan suka tatara du wani abin bukata ? cikin daren nan suka fada wuleliyar motarsa suka kama hanyar barin kano

Hasana sai kuka take na yar uwarta inda mahaifiyarsu take rarashinta, cikin nutsuwa tace" mama, Ouseina, kar aje mutanen nan su cin mata idan suka rasa mu

Elhaj abubacar yace " hasana, Allah Yana tare da ita, ki sani, kinga Aure take, harda ciki idan muka rabata da mijinta ai mun Shiga hakinsa, na yarda da lawali nasan bazai Bari wani abin ya samu Ouseina ba sai inda karfinsa ya kare, dan haka insha Allahu idan wannan rigimar ta lafa zamu dawo mu daukesu da mijin nata muy tafiyar mu

Hakan kuwa akayi suka tafi suna kewar yarsu da kuma garin da suka zauna

Sam bai rintsa ba Yana jiran Jin dadadan labari , wayarsa na daukan kuka ya warta ya daga ya kara
Abinda ya ji ne ya mugun daga masa hankali, wai basa nan sannan kayansu ma basa nan,

Wata dunkulaliyar ashar ce ya dana inda ya mike ya fada dakin Ouseina Yana tambayar ta gidan ubanwa ubanta ya shiga

Tamkar mutun mutuni ta zama ? zaune da cikinta na wata bakwai tana kalonsa, tun daga ranar baiwar Allah ta zamo abin tausayi domin ta gane saratu fa matar lawali ce kuma iyayenta basa kasar, takan zauna taci kuka iya kuka ba mai rarashinta domin ya kori Inna ta samu wani datijo ta aura mai kanjan Mota ne Suna zamansu lafiya


Nakuda ce ta tasowa Ouseina tun wajen karfe bakwai na dare inda a ranar taci dukan lawali wai ya Kamata da kwarto ya jibgeta da tsohon cikinta har ya la'anci abin cikin cikin ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login