Showing 9001 words to 12000 words out of 124070 words

Chapter 4 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

320

saka da alkhairi

? hankali ta juya ta fada dakin nasu, tana shiga yauma ta tarar an warwatsa kayanta tamkar ana neman wani abun a ciki, cikin nutsuwa ta tatare kayanta ta ninke ta mayar cikin Jakarta sannan ta fada wanka hade da dauro alwallah sannan ta wanke doguwar rigarta ta shanya kuma ta saka wa'inda ta wanke ? jiya domin ta boye bakar rigar ba yanzu zata saka ba

koda dare yayi bayan sallar magariba Habiba ta shigo tace " ke tashi malan na kiranki

Nuriyah ta Mike da sauri ta fito cikin nutsuwa, tana karasowa ta duka dan nesa ta ce" Aba ina yini,

Malan isyak ya amsa mata Yana dan murmushi, can yace " ina fatan kin wuni lafiya, kin huta da ranki, kin cire yawan tunani, sannan kin ci abinci ?

carab Habiba ta cire zancen tace " hm malan ai ni yau nayi mamakin yar nan, da ta kama baci sai wajen sallar la'asar ta farka, tana farkawa ta fito tace ina abincin ta, hanu baka hanu kwarya har sai da na tausaya mata domin tana gama ci tace ina lemo, nace da ita ai sai dai ruwan tulu aman na yanyanka mata ayabar nan da ka siyo ta Ci sosai da sosai, kuma ta koma daki ta ci gaba da bacinta, nayi ta dariya ina cewa Farida ai fa ta samu yar uwa wajen baci


da Malan isyak da ita Nuriyah da Farida kanta sun zubawa Habiba ido Suna kalo,

Malan ya dan sauke ajiyar zuciya ya juyo kadan yace" Eyah ai kin san gajiya, sai ? hankali zata barta, sannan ai tsarabar nan ita ta sayo maku ita jiya har ina mamakin irin hankalin yarinyar

Habiba wani haushi da kunya suka turniketa haka Farida da ta tuna yanda ta Ringa gadara da ayabar da abarbar nan Sai taji wani iri,

haka Nuriyah ta dan jima ? tsugune daga bisani ta Mike tayi salama ta tafi , yau ma kamar jiya ta nemi waje ta dan rakube tayi kwonciyarta


kwonci tashi nuriyah tayi sati uku ? gidan Malan isyak, fanin zamanta da su sai hamdallah domin ? kulun cikin ikon Allah Ayukanta na gida karuwa suke, sannan ? turata neman na kanta, tana dawowa ? karbe ? raba masu da Farida sannan da Malan isyak ya dawo za'a kitsa abinda ba na alkhairi ba ace tayi, Inda Allah ya taimaketa bai taba kulawa da irin zancecekun tayi tayi din ba domin sarai ya san halayar matarsa, fanin sutura alhamdulilah domin ? yanzu hijabanta biyar haka ma kayan jiki masha Allah domin Malan isyak ya kara mata har kala hudu, inda Farida ta karbe biyun ta Bata tsofafin nata wa'inda ta gaji da Mora,duda haka murna take domin atanfofi ne ta wanke su ta goge abinta da dutsin guga da ta roka ta adanna suturunta

yau kam kasuwa alhamdulilah, domin yau mai huluna bai fito ba sunyi tafiya, cikin faduwar gaba ta nufi wajen yan fruits da kyar ta samu suka Bata dan yanzu kowa tsoronta yake, tana fitowa ta nufi titi sai dai kash du irin gudun da tayi da tallar da tayi cinikin naira dari biyar kawai tayi, har la'asar ta shige, ta kamo hanya da yar naira darinta ta nufo gida hankalinta ? tashe domin yau ta san fa Allah kawai zai kwaceta ? hannun Habiba

tana shiga ta tarar tana tsakar gida ta duka tana gaisheta, sannan hannunta na rawa ta miko mata naira darin tana cewa " yau mai hular baya nan shi yasa banyi ciniki ba sai ? wajen yan fruits na samu naira dari, dan Allah kiyi hakuri mama

idannuwan Habiba tamkar su fado kasa domin kuwa yau Malan ya dawo gida da wuri sanadiyar wajen gaisuwa da suka tafi da Mubarack,


du abinda ya faru ? kan kunuwansu, ya sauke ajiyar zuciya ? hankali yace " mahakurci mawadaci

mubarack ya dubi yanayin mahaifin nasa cikin yannayin damuwa, tabas ya san abansa yana son taimaka yarinyar nan, ? gaskiya rayuwar yarinyar ne abin ? tausaya mata, ya ja nunfashi ya sauke, cikin nutsuwa yace " Aban mu

Malan isyak ya kale shi da alamun ya amsa Kiran da yayi masa

yace " Aban mu ni kuwa inada shawara ? lamarin rayuwar Nuriyah, wace idan ka lamunce min zamu samu mafita ? yannayin rayuwar kunci da take ciki tun kafin Umanmu ta kona kanta

Malan isyak ya ce" ina sauraronka Mubarack wace shawara ce wannan ?





shin wace shawara ce Mubarack zai gabatar wa mahaifin sa ????????????? """""""""?????????????????
*>?&? @&>?&? @&>?&? @& NEMAN NA KAINA>?&? @&>?&? @&>?&? @&*


Marubuciya: *SAJIDA*


*P+


*(9)*



Yayi Jim ya ce" Aba , nasan baka ra'ayin barin y'a mace *Neman na kanta*, nasan ? duniya idan akoy abinda ka ki jini shine y'a mace ta ringa bin layi layi wai da sunnan tana sana'a, kace y'a mace abin ? kilace ce, Aba zan fada maka gaskiyar lamari, tunda yarinyar nan ta dawo gidan nan daidai yake da tana titin, aikin gidan nan gaba daya ita ke yinsa domin KO haki Farida bata daukewa, sannan tana gamawa KO wanka ba'a barinta tayi za'a turata *Neman na kanta*, Aba dan ma yarinyar nan mai tsoron Allah ce, ai da tuni ta kauce hanya, Kuma gagarumin abinda nake tsoro shine Aba ka dauko yarinyar nan dan ka taimaki rayuwarta kar aje ka fada halaka sanadiyar hakan, domin kuwa ? cikin kangin rayuwa take kuma bazaka taba Jin maganarta ba

Malan isyak ya gyada kai ya ce" to Mubarack ai baka fada min shawarar taka ba

Mubarack ya kuma nisawa Yana tsoron fasarar da Abansa zai yiwa shawarar tasa, ya ce" Aba, wajen da nake tsaron kofa, bangaran kakanin mai gidan ne, idan Allah ya taimakeni an kusan daukan ma'aikata a kara a gidan kowani bangare, da yake Hajiya mutun ce mai mutunci mai daraja talaka sai naje na nemi alfarmar ? taimaka min ? dauketa fanin ban ruwan fulawowi KO taya Hajiya zama dan miko min KO kaimin wancen, sai kaga idan Allah ya taimake mu an dauketa , dan kuwa idan bakada takardar shaidar ka gama secondry basa yarda su dauki mutun aiki, aman da adu'a sai kaga Hajiyar ta dauketa

Malan isyak Yana sauraronsa Yana dan gyada kai, can yace " Aman Mubarack, wannan gida naku mai hadari ? Gidan da ba'a jimawa sai an kai maku hari ? Gidan da du yawancin mutanen ciki suka dauki talaka tamkar bawa ? Gidan da idan aka kamaka da laifi baza'a saurara maka ba sai gidan yari,? Gidan da idan ka shiga ba kai ba zuwa ganin iyayenka sai wata wata ? to ya maganar Aure idan ta shige gidan nan ? ? ina zata samu miji tayi Aure ? Gidan da du rashin yarda yake sakawa koda da aurenki kika je aiki suturar da zaki saka KO dan sket da Riga KO dogon wando da Riga, masu Aure kadai keda ikon rufa dan hijabi ? tsokani adinni wa'inda basuda Aure kuwa sai dai dan gyale dan karami KO yar hula ? kansu ? Shin idan na dauki y'ata na kai nayiwa kaina adalci, KO na nemi yardar Allah ? tare da ni ?

Mubarack ya kara gyara zamansa yace " Abanmu, ni nayi maka alkawarin ? gidan nan namiji baya shiga hurumin macen da ba maharamarsa ba, da ace gefen samarin gidan ne ni kaina bazan yarda ba domin akoy marasa ji, aman aba gefen su Hajiya, kakar mai gidan mu, gefen Hajiya masu shiga wajenta daidaiku ne, kuma irin yanda take nuna min kauna ne zan je na nem alfarmar ta dauki Nuriyah ? bangaranta DAn nasan zata sota domin Allah kuma ta kula da lamarinta, zancen mijin Aure kuwa ni nan da idannuwana naga yan matan da Hajiya ta aurar da kanta ? gabanta domin kana samun miji cikin ikon Allah zata yi maka komai ta wanke ka ? kaika gidan mijinka, Aba wly gidan nan gidan mutunci ne, kuma dalilin da yasa kake ganin mata masu aiki da irin shigar nan dan saboda baza'a zubu ? yarda da masu irin shigar hijabai ba, domin irin yanda yayi suna, du duniya ta sanshi, mukamin da yake rike da shi ? harkar aikinsa na soja, irin cudanyan da yake da manya da irin yanda zai kaucewa muradin du wani mugu sannan ya tsaya tsayin daka dan ganin ya hana barna yake kawo masa makiya masu neman ransa da na iyalansa, Aba sai yayi wata biyar ? daji shi da kansa yake fita, hakan ya sa koda yaushe mu gidan mu da tsaro, Dan Allah Aba kayi tunani ? kai, hakan yafi irin yanda take yawon *Neman na kanta* Ba'a san da mai zata hadu ba, yau duniya taki dadi idan har aka lura da ita mutane sunki gaskiya suna iya yi mata wani mugun abin, Aba idan kuwa tana zaune ? gidan nan kasan dole ne Umanmu ta zata turata neman na kanta, ni fa ? tunanina gwara ta kasance ? can din don kuwa ba Wanda zai fitar da ita daga gidan nan sai dalili, aman ? nan fa Aba sai yanda Allah yayi

Malan isyak yace" ? KO'inan ma Mubarack sai yanda Allah yayi, ni dai zanyi shawara , zanyi dogon tunani sannan zan roki Allah, nan da sati zan baka abinda na yanke insha Allah


Haka Mubarack ya fito yayiwa mahaifiyarsa salama wace tunda ta galawa Nuriyah hararar maganar da tayi tayi dan tsai tana tunani hankalinta a dan tashe tana ta tunanin yanda zasu kwashe da shi

? hankali ta Mike ta shiga dakin inda ta duka ta gaishe da Malan isyak ta nufi cikin dakinsu inda tana shiga ta tarar Farida tana bincika mata kayanta......
*>?&? @&>?&? @&>?&? @& NEMAN NA KAINA>?&? @&>?&? @&>?&? @&*


Marubuciya: *SAJIDA*


*P+


*(10)*


Farida na ganninta ta shiga irin basarwar nan, can kuma ta ce" ke wai ina kike ajiyar sauran kudin da idan kin Zo umanmu ke rabawa ta baki ?

Nuriyah ta dan lumshe idanuwanta alamar gajiya ? tatare da ita ta ce" eyah, Aunty Farida ai bana ajiye su a gida ne


Farida ta ce" eh ai daman shi karuwa yafi uban kowa sannin zafin kudi, domin KO kudin haya wayar bayansa yake ji, shi yasa aka likewa aban mu, aka likewa gidan mu, sai yawo da nikaf wai ke ta Allah, zan fadawa umana ne yau ta karbe kudin duka ta bani yar rainin hankali,

Tana gama fada ta fice buguzum buguzum inda bata lura da mahaifinta Wanda ya labe Yana sauraron gaba daya rashin mutuncin y'arsa,

? hankali ya sauke ajiyar zuciya sannan ya kudiri niyar zai dan lafe dan yaga shin da gaske Mubarack yake, gaba daya abin nan Habiba na iya aikatawa dan mutun tamkar daba dan son zuciya irin nata ?


Haka yauma ta gama du abinda ta san aikinta ne, ta tatare tayi dan kwonciyarta zuciyarta FAL da fargabar idan malan ya fita
Sam Nuriyah bata san irin rayuwar nan ba, tabas zuna cikin talauci har talauci aman fa innarta bata taba daga mata murya ba, bale har ? kai ga duka, ? kulun innarta na bin ta da adu'a da nasiyah, Bata taba aibata ta KO ta shigo irin ranta a jagule dan tsokanar yara sai tayi yanda tayi ta mantar da ita damuwarta, tana sakar zuci har baci yayi awon gaba da ita,

Tunda asuba ta farka kamar kulun ta shiga aikace aikacenta, kan kace meye har ta gama, tana tsaka da kwashe sharar da tayi Farida ta fito da kulin kayan dauda ta mika mata tana cewa " ke marar gata, kama nan, jiya bayan kinyi bacin naki na hutu Kawata ta tawo kayanta da nace mata ana wankau ? gidan mu, dan kinga ai ? jiya baki kawo min kudina ba to a yau sai ki wanke ni kuwa na saka data da kudin

Tana gama fadin haka ta juya tayi tafiyarta inda ita kuwa ta hau wankinta, nan da nan ta gama ta fada dakin Nuriyah ta dauko su nikaf dinta da saura su ta saka abinta ta fito kenan tana sanda Habiba ta kirayi sunanta, tana isowa ta wanka mata mari,

da sauri Nuriyah ta kai kasa tana dafe kuncinta,

Habiba ta ce" ke yar gidan mai kanjamau dan ubanki SO kike ki rabani da mijina ? Idan ba bakin ciki kike yi min ba nima ya sake ni na tafi yawon gantalin irin naki mu saje karuwai biyu ? titi da tsufana kike fata ba dan mai zaki wani Zo Yana zaune ki miko min wata tsinaniyar naira dari ? Sannan ma gidan ubanwa kika kai kudin nan ? Fada min ?

Nuriyah jikinta dake kyarma tace " kiyi hakuri Umah, wly ban san aba Yana gidan nan ba, kuma jiya ban Sami wankin hulunan ba, aman kiyi hakuri

Habiba ta ce" haka fa sa? salo irin na yan iska, kinga ki tashi kawai kiyi maza ki tafi *Neman na kanki*, kuma sauran yauma aje malan ya dawo da wuri ki kuma bani kudin ? gabansa KO ki Zo min da zancen banzar baki SAMU aiki ba, idan kuma kostoman naki na da har sun gaji da morar ganga ne sun yar da ita ai sai ki nemi wasu dan ni dai kawai kudi na sani, kin saka Farida jiya bata ji labarin saurayinta na kasar waje ba, bace min da gani karki saka ina haikar baki har na tashe ta daga baci ranta ya baci

da sauri Nuriyah ta mike tana share hawaye ta nufi hanya inda ta fice malan isyak labe bayan kyauran kofar gidan Wanda komai ya wakana ? gabansa

Tafe take tana dan layi dan kuwa kanta tamkar ya tarwatse haka take ji, shi kuwa Yana dan biye da ita ? hankali suna tafiya ? ransa Yana aiyana tabas idan har ana irin haka maganar Mubarack zata tabata wata rana,

Yana zaune nesa Yana kalon irin yanda take wankin hulunan nan domin ? yau an Sami aiki, ya ja ajiyar zuciya ya sauke,, shi dai bai ga inda ta karya ba, haka kuma bai ga inda ta sayi abinci ba, sannan iya kalo ta karbi sadaka aman tana kule ? leda bata ci ba, KO ruwa ? waje baiga ta sha ba, ya farakara Jin haushin Habiba ? ransa, yace " tabas Mubarack yayi gajiya ? haka sai dai mu kone daga ni har Habiba da Farida, domin ni na dauko nauyi ? kaina, su kuwa suna shiga haki ba dare ba rana, sannan tabas wata ranar ana iya kaucewa hanya duba da irin furucin Habiba cewar ita dai kudi ta sani ba kamar da ba, domin da ran innarta ta samo bata samo ba to fa da murnarta zata shiga gidan su dan ta san ana jiranta da fara'a, ? yanzu kuwa ya Dan Girgiza kai Yana kalon lokacin da take dan shanshanya su

Wasu samari ne su biyu suka Zo ficewa dayan yace "Baba, ina gaya maka wannan babyn fa mai zafi ce, kawai mu SAMU wata rana mu afka mata

Wanda aka kiraya Da Baba ya ce" kai oga kaifa baka da kyau, yanzu ? nan har ka hAngo Hutu ?

Dayan yayi dariya ya ce" kai na rabaka da eh yane, karka yi mamakin Jin ka fada ? kogi tanjam sannan kaji an rike maka wuta, kai Allah baba mu shirya mata dan da gani babyn nan zata rike wuta

? daidai nan malan isyak ya juyo ya barsu suka ci gaba da tsara yanda zasu cima Nuriyah

Sauri saurasauri Ya rigayeta karasowa gida inda Yana shiga ya nemi dan guri ya labe Yana jiran gannin karshen ranar nan


Tana shigowa ta karasa ta duka tana gaishe su, ba Wanda ya amsa mata Habiba ta mika hanu ta karbe kudin ta irge yau har dubu takwass, ta ce" yau KO kwondala bazan baki ba, dan kuwa harda na jiya, dan haka bace min da gani kin wani yi tsuguno kamar ta Allah

Da saurinta ta mike ta fada daki, inda malan yaji Dan Danshi danshi ? fuskarsa, Yana lalubawa yaji hawaye ne, yayi saurin gogewa



Haka malan yaci gaba da labewa ? kulun ta Allah Yana kalon irin yanda nuriyah ke gannin taskun rayuwa ? gidan sa, wani abin tausayin ma sai irin yanda zata je har wajen gidansu inda ake tada gini tayi ta share hawaye sannan ta biyo ta wajen makabarta tayi ta adu'a har tana dan lekawa kamar tana son ganin wani, sannan ta karkato ta koma gida ta tarar da taskun Habiba da Farida, kuma masu biyar bayanta Basu daina ba, suma suna hakon ranar da zasu kai gareta ? kulun cikin taretsare Tsare suke


? yau dai Mubarack ya dawo gida da fara'ar sa, domin ya samu tsohuwa tace ya kawo kanwar tasa idan tanada nutsuwa zata dauketa ? bangarenta, zuwa wannan lokacin damuwarsa aba ne kawai ina rokon Allah, Allah ya sa ya yarjewaYarjewa kudirinsa,

Zaune malan isyak yake bayan ya dawo daga masalaci salar isha'i, Yana kalon kwanon abincin da aka zuba masa aman ya kasa ci,

Mubarack yayi salama ya duka yana gaishe da shi

Bayan ya gama ansawa yayi dan jim

Malan isyak yace " daman ina nemanka, bisa shawarar da nace maka zanyi, toh na yanke shawarar.............




=?K? @&=?K? @&=?K? @&=?K? @&=?K? @&=?K? @&=?K? @&=?K? @&=?K? @&
*>?&? @&>?&? @&>?&? @& NEMAN NA KAINA>?&? @&>?&? @&>?&? @&*


Marubuciya: *SAJIDA*


*P+


*(11)*


*Basa comment=??*



Malan isyak ya ce" daman ina nemanka, bisa shawarar da nace maka zanyi, to na yanke shawarar bayan dogon nazari, eh lale fa yarinyar nan ? sama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login