Showing 87001 words to 90000 words out of 124070 words

Chapter 30 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

332

walahi karya kake kace sai y'aya sun tsufa za'a aurar da su, idan mijin me bai samu ba ba dakuwa, aman ace ga miji ya samu ni zan yi gangancin tauye kuruciyarsu? me zasu kennan na dadin zaman auren idan shekarunsu ya haura talatin din da kake so? Kai ka fadan gaskiya da ka yi hakan zayano min dadin auren da kake sha, kawai takwara mu yi shiru mu dukanmu tunda iyayensu sun ce aure zasu musu ka ga bamu da karfi fa a maganar nan tunda ba mu muka haifa ba ehe!"

"Muhamadu rasululahi sallalahu alaihi wa salam yanzun ni ka ciwa mutunci Elhaji?" Kan Giwa ya fada a lokacin da ya mike yana kallon takwaransa da kyau yana gane cewar babu wata maganar shiftaka a tatare da shi

Elhaj ya tabe baki yana kallon Hajia dake kyakyata dariarta son ranta
Kan GIWA ya sake fadin" A gabanta ka yakan rigar mutunci harda su gori ko? To walahi ba za'a yi ba, kowama ya shafa musu lafiya su girma, barama na tarda su kayan cen sai an maida masa tunda ba matsiyaci bane ni!"

Sai a lokacin mahaifinsa da kyar ya dane tasa dariar ya mike yana kwala masa kira domin tuni ya shiga haurawa

Hajia na daria tana sake rike hijabin dake jikinta aa hankali take kiran danta kan ya dawo

Dawowa ya yi yana murmushi hadi da girgiza kansa cike da mamakin wai dama zai ga rikici irin wanda mutumen dake cikin mahaukaciyar soyaya kan iya nunawa aman muraiai ya take a kan KAN GIWA ? ya ce" Mama kar ya je ya dake su fa?"

Hajia ta yi yar dariya tana fadin" da yana iya dukansu da tun a waje zai daka, mu ya raina yake yiwa ihu aman ba zai iya aikata mata komai ba, da yana dukan yarinyar nan da ya jima da fara dukanta tun a lokacin da ta zuba masa ruwa a falon nan a jikinsa, kai dai zauna kuma tatare kafafuwanka ta yiwu tarban sirikanka yau banda dan gaban gishinsu za'a je"

Yadda ka san zai tashi sama haka yake haurawa har ya idasa kofar dakin ya saka hannunsa da karfi ya bude yana fadin" Auta, jiya da na yi magana ba a gabanki na yita ba? Shine yau da wuri haka kika taka dokata? To wannan shine last warning da zan yi a kanku dangane da maza, idan na kuma................"
Dif maganarsa ta dauke idannuwansa suka sauka a kan NURIYAH da ta yi mutuwar tsaye gannin yana fada ne yana son zare belt, hakan ya sa jikonta na kerma da tsoron bulalar da take yo a rayuwarta sakamakon a dukkan wahakar da ta sha ta gidan duniya bata sha ta duka ba, kwata kwata bata san duka ba, ta san wahala ta san zafin rana , ta san zafin nema aman fa bata san zafin bulala ba dan babu mai dukanta a gida ko a waje ya sa shaf ta manta wandon roba ne wanda ya dara gwuiwarta kadan a jikinta wanda take sakawa kulun idan zata dora kaya a sama, sun gama jajen bata masa ran da suka yi ne, sun kuma daukarwa kansu cewar ba zasu kuma ba , ta mike tana cire kayanta dan ta watsa ruwa ya banki dakin, watau ta cire abayar sauran riba yar karama mai siririn hannu wace bata zarce ramin cibiyarta ba da wandon da ya hate har saman cibiyarta ya rike taf mararta ya kuma sauka ya hau kan abaje din dake baje a bayanta ya dame kasan daidai kwaurinta yana rawa dan kansa domin irin na robar nan ne masu kyau, gashin kanta kuwa a kunce a baje a bayanta dan ta cire ribom din dake jiki ta rintse ido da karfi jikinta na daukan rawa ta bude da karfi jin ya sake bude muryarsa wannan karron a shake ya kuma fadin" Daga yau, Daga yau.........................i....i.........." A hankali ya fitar da halshensa ya lashi lebensa na kasa dan ya jika leben nasa da ya ji ya bushe masa kau ko zai iya karasa maganar yana sake kallonta da duban da shi kansa ya rasa wani irin duba ne haka na kauyencu yake yi kamar wanda bashi da ilimi?

Da sauri ta fara tako kafarta dan ta fito da kyau ta duka ta bashi hakuri, bakinta na rawa tana fadin" Daga yau ba zamu kuma fita zuwa shagonsa ba, koda hajia ta aike mu zamu je wani shagon dan Allah ka........"

"Kar ki fado min!" Ya fada da dan karfi yana daga kafarsa ya yi baya yana sake zarro idannuwansa yana kallonta, domin gaba daya a tunaninsa rufto masa ne zata yi

Tsorata ta yi da jin dan ihun nasa, gaba daya ta rintse ido ta shiga neman kai hannun nasa inda ya kai dan son kince belt ya tsoratar da su sosai, domin ya kula daga baby din har ita matsoratan bulala ne
Ido ya sake firfitowa ya saka hannayensa biyu ya tareta ya riketa kyam a gabansa yana ta sauke ajiyar zuciya a kai a kai yana kallon yadda take kuka tun karfinta , sai dai kukan gaba daya kamar na shagwababiyar yarinya marar jin magana ne, bama irin lebenta yadda take tabe shi, uwa uba idannuwanta yanna take shanye su
Baby kam yanzu ta yi saranda ta san yau zata kuma daukan dukan yayanta a karro na biyu a rayuwa, ta san idan ta rikice tana tonawa kanta asiri aman gwara ita da NURIYAH, NURIYAH idan ta rikice ko ta tsorata afkawa abinda ya rikitata ko yaa tsoratata take yi , ko hakuri zata bada fa sai ta lange maka a jiki yau gata zata riko hantsar wandon yayansu=?-?? Dole yau ya masu dukkan mutuwa ba zasu tsira ba sam

Ajiyar zuciya mai radadi ta sauke itama tana kukan da bashi hakuri tana rantsuwar ba zasu kuma ba

Dukkan wata lakka dake jikinsa ke neman barin jikinsa
Kukanta da na baby hauhawa yake yo har cen???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? cikin kwakwaluwarsa yana hadasa masa da yannayin da yake ji kamar ya rungumo su baki daya ya basu hakuri da masu alkawarin ba zai kuma bari su yi kuka ba

Wata zuciyar ta tunasar da shi cewa idan bai tsaya a kan kafarsa ba tabas za'a taka dokarsa, dan haka a hankali ya saketa yana hankalce da ita dan kar ta rukunkume shi ta halaka shi ya koma bakin gadon ya zauna yana dafe kansa da hannayensa bibiyu

Itama wajen babyn ta je da sauri ta tsuguna tana lalubar hannunta ta rike dan ta samu kwarin gwuiwar amsar dukan

A hankali ya dago ya masu kallo daya ya cire kansa a kausashe ya ce" Ya isa haka kukan ku min shiru"

Tamkar kadangaru suke gyada kai kowace na share hawayenta
Sai kuma NURIYAH ta sake kallon Baby muryarta a shake ta ce" Dan Allah ki karra bashi hakuri, walahi bana son duka"

Baby ta gyada mata kai tana jimke hannunta dan ta yi Shiru kar su hasala shi

Duka abinda suka yi yana kallonsu, hakan ya saka shi lumshe idannuwansa yana jin wani iri a ransa

A hankali ya ce" Idan kuka fara kula harkar samari, ba zaku iya dainawa ba, ni kuma ba zan iya barinku ku dauki shekaru kunna kula samari ba, kun fahimta?"

Ita dai Nuriyah ba wani fahimtar ta yi ba, baby ce kawai ta fahimta, dan haka suka amsa masa da eh

Ya sake fadin" Duka abinda ya baku za'a kai a auna a masa transfer, kar ku kuma cin abin hannun saurayi,ba kowane zai baku da zuciya daya ba"

Yanzuma amsawar suka yi, shi kuma ya ci gabada naganarsa da dukkan gaskiyarsa ya ce" bayan wannan sam bai mini ba yaron nan, zan fi so idan lokacin hakan ya yi ku samu mai mutunci kun fahimta?"

Amsar eh din dai ce, dan haka ya mike da kyar dan ji yake kamar an masa duka ya kama hanyar fita yana fadin" Baby bani wayoyinku"

Baby ta tashi da sauri gabanta na dukan casa'in casa'in cike da tsoro ta dauko wayar ta mikawa yayanta

Yana kallonta ya ce" Ina dayar wayar?"

Baby ta ce" Ita bata da waya, bata fara anfani da ita ba"

Idannuwansa ya sake dagawa ya sauke a kanta gannin ta dauko hijab ga dukkan alama yanzu da ta ga ba dukanta zai yi ba hankalinta ya dawo jikinta har ta tuna ya dace ta lulube jikin nan nata mai kayan haushi, haka kawai ya samu kansa da tunanin yanzun kowama idan zai daketa ko ya bata Tsoro sai ta auka masa ta rukunkume shi kennan? Subahannalah wannan ai ba Dabi'a bace gaskiya, kwata kwata ba dabi'a bace wannan

A hankali ya furta sunnanta, wanda hakan sai da ya sakata rintse Idannuwanta sakamakon jin yadda gabanta ya fadi

A hankali ta karaso tana sada kanta kasa

Sai da ya yi wani lamari da idannuwansa, watau ya sake tausasa dubansa a kanta dan kat ya tsoratata, dan haka kawia yake ji a ransa a yanzu baya so yana tsoratata, sam baya son hakan, tunda ba kyau, sai dai kashe sun da ya yi suka bada kala na kwaraton namiji(=??>??? @&?), yama dubanta a hankali ya sake ambaton sunnanta, a wani irin sanyayen da ya saka harta Murjanatu sai da ta kureshi da kallon mamaki, gaba daya ya yi jajajir kamar wanda ya sha wahakar balaki, idannuwan nan nasa da ya halake ta hanyar kashewa sai sahibinta ya fado mata a rai, da sauri ta yi astgfari ta kori shedan dan ya fara sako mata tunani irin na haramun a zuciyarta, to haramun mana, sai ta ga yayanta kamar yana yin duba irin na wanda soyaya ta yiwa mugun kamu, bayan hakan ba zai taba yiwuwa ba, to yayansu da baya kallon matama sai orin wa'inda suka matsa masa fisabililahi?


A hankali ya sake kiran sunnanta gannin da ta dago ta kalle shi sake maida idannuwanta ta yi kasa tana kallon kasa dan ba zata juri kallonsa a haka ba

Wannan karron da ta dago hancinsa ta kurawa idon tana jin wani iri dangane da hancin, bama kamar leben mutumen nan, lebensa kamar na jariri haka yake, har mamaki take idan fada na fita daga bakinsa, irin Tsoron da ake masa a gidan nan na bata mamaki sosai, ita ta gama.karantar in ba sabgarsa ka shiga ba bakwa zaman wukakanci fa, baya maka fada

A hankali ya ce" Idan kika ji kina tsoron mutun ko abin wani abun ki daina fadawa mutun kin ji? Dan kar ki je kan mugu ya cutar da ke aje abinda kike tsoron a hannunsa ya ji maki rauni kin ji?"

Bata taba kawo cewa maganar nan zai mata ba, hakan ya sa dagowarta da zuba idannuwanta cikin nasa ya zamto ba da gangan ko da tsoro ba, sai dan ta sake dubansa da duban da takan yiwa mutane masu darajar da suke nuna mata wani lamari lokaci zuwa lokaci, yau ta masa kallo karro na uku irin na rashin tsoro da mamakinsa,
A hankali bakinta ya yawalta da dan alamu dake nuna farin ciki har hakoranta masu haske suka bayanar da kansu ta sakar masa kyakyawan murmushin da shi kadai ta malaka wanda zata iya bashi matsayin kyauta

Murmushin nata yake kallo girarakinsa na saki alamun daurewa na barinsa, a hankali ya saki hannun koffar ya juya ya bar dakin yana tafia da wani irin sanyin da bai san yana tare da jikinsa ba

Tafiyar yake yi har ya sauko kasa bai san da jama'ar da suka rage su uku a falon shi suka zubawa ido ba, watau Hajia, da Elhaji, da mahaifinsa

"Dukansu ka yi ne? Mugun fada?" Ya ji maganar sama sama a kansa hakan ya sa ya dan firgice ya dubesu gaba dayansu
Sai ya samu kansa da tambayar Duka kuma? Fada kuma? To me suka yi da zafi haka da za'a dake su ko a masu fada?
Baki ya tabe yana tunanin matar nan so take ta masa abinda ba shikenan ba, dan haka sai ya dage girarsa yana duban agogon bango dan gannin ko lokacin saukar sirikan mahaifinsa ya yi ya ce" NASIHA na mata, waima ina ruwanki?".......








Ah to tambayar mana ita wai ina ruwanta dan Allah ?=? ?=? ?=? ?=? ?>?#?>?#?>?#?>?#?=??=??=??=??=?B?=?B?=?B?=?B?=?B?=?B?=?B?=?B?>?z?>?z?>?z?>?z?>?z?>?z?>?z?>?z?



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
5?? 2??



"Nasiha kuma? Yanzun du yadda suka bata maka rai sai ka masu nasiha ka kyale su? Lafiyarka kalau kuwa? Gaskiya ba zai yiwu ba je ka zane min su" ta fada tana tsatsareshi da ido

Shima kallon nata ya kuma yi, sai kuma ya tabe bakinsa ya juya yana fadin" Abana ku mu tafi a?roport din sun kusa sauka fa"
Yana fada ya wuce gaba daya ya nufi bangarensa dan ya watsa ruwa kadan , domin ji yake jikinsa ya masa nauyi

A gagauce ya gama ya fito, a lokacin har an gama shiryawa kowa ya kama wajensa a cikin mota ya zauna

Dan tsayawa ya yi yana gannin motoci har biyar, sai kuma ya karasa da dan sauri wace ya san direbansa ne ke jansa da ita ya bude gaba ya shiga da waya a hannunsa yana amsa kiran baban sojojin garin mali da zasu hada wani taro nasu na kansu a kan maganar jiragen yaki masu kilometer dari hudu a awa daya da kasashen ke son siya, gasu da tsadar tsiya domin magana ce ta bilioniyoyin kudade ba kadan ba

A haka suka karaso Aeroport din suka kai cen wajen parking din motoci suka tsaitsaya, hakan ya sa kowa fitowa daga motar ciki harda matansa da suke cikin motarsa aman kuma shi bai fito ba dan yana kira

Gefe guda wanda ya zamto gefen barin da yake zaune dan nesa da shi kadan Hajia ce da jikokinta su biyu a tsaye sun zubawa matansa ido sakamakon maganar da hajia ta fadi a kan matan nasa ya saka Nuriyah da Murjanatu fashewa da dariar da basu shirya ba, itama hajiar me zata yi banda dariar ta ce" Takwara dan Allah ke baki ga haka a tatare da ita wancen bayarabar ba?"

Baby ta yi inga girgza kai tana rufe bakinta ta ce" Hajia ke bakinki ya fi karfin duka a yanzun ko a wajen Elhaji ne , mu kuwa sai a dakamu mu din da kanmu ba wai iya bakinmu ba, dan Allah ki rufa mana asiri da rigimar yaya"

NURIYAH kam abin ba karamin dariya ya bata ba, ta sake juyawa tana kallonsu sosai dan ita dayan abin da ya fi bata mamaki shine irin shigarsu ko a yanzu da aka fito gaba daya, babu mai mayafin kirki aman ita yana ce mata kar ta kuma fita tsirara saboda kanwarsa?

Dan murmushi ne ya subuce masa a bakinsa yana gannin irin yadda Murmushi ya wadaci fuskarta da yannayinta, ya fuskanci ko me suke fadi a kan matansa ne dan cen suke kallo su dukansu basa ko irin juyawar nan, sai ya sake yin murmushi yana kallon sarkin rigimar wace ya tabata ko me ya basu daria itace sila

Hello? Hello? Din da ake ta yi masa ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya afka

Ajiyar zuciya ya sauke ya maida hankalinsa suka gana maganar sannan ya byde motar da kansa ya fito dan direbansama ya bashi waje ya gama wayar , motar sojawan da ta masu rakiya kuwa sun barbazu a a?roport din sunna zagaye

Wajen da ake zama dan jiran baki ko dan rakiyar baki suka karasa gaba dayansu suka zazauna, hakan ya sa a yanzu dole zaman a waje daya aka yi shi gaba daya family din, sai dai wasu kusa da wasu ne, inda Hajia ke kusa da Kan Giwa sosai tana ta nazarinsa da tunanin abinda ya dace ta yi, bale da ta kula jifa jifa sai ya kalli wajen da Nuriyaj ke zaune daure da jar lafayarta da bak'ar rigarta a ciki mai dogon hannu da daurinta irin na mata masu daraja

Dan murmushi ta yi ta buda jakarta ta ciro dubu guda ta dubi Nuriyar ta ce" Balaraba zo ku je cen wajen filin jirgin nan ku taka sosai a kafafuwanku ku samo min goro na hangi wasu masu tebura a cen bakin hanya na samu na kantsawa na bar gorona a gida gashi ya fara kamani"

Irin yadda ta fadi kamanin kamar na mashayin da idan ya fara sakuwa zaka ga yana neman rikicewa in babu abin kwalewa a kusan nan, koda yake goronma ai aikinsa kennan maciyinsa baya zama babu shi a kusa dan yanzu kasala, ciwon kai, barci zai nemi damunsa

Dubu gudan ya raka da kallo a lokacin da ta mika ta gaban idannuwansa
A hankali Nuriyah ta karasa ta saka hannayenta bibiyu ta rage tsayinta kadan zata amshi kuWin, domin har ta dora hannunta a kan kudin daga gefe kadan ta gabanshi
Lalausan hannunsa ya dora saman hannunta ta kasa ya riki gefen kudin yana shirin yi mata kallon da zai saka ta koma wajenta ta zauna Hajia ta dauko hannunta na dama ta dora saman nasa dake saman na Nuriyah wace nata kuma ke rike da kudin hajia ta kasa ta yi raf da hannun ta sake rikewa sosai dan kar Nuriyah ta janye nata hannun ta juyo barinsa tana hade fuska ta ce" Malan yaya dai? Kudina ne ai?"

Da kyar ya iya sauke numfashin da ya tsaye masa a kirjinsa sanadiyar hade hannunsa da na Nuriyah da Hajia ta yi da karfi wanda ya hadasa masa jin wani irin yarrrrrrr tun daga kansa har tafin kafafuwansa ya zuba idannuwansa a kan hannayen sai kuma ya dauko dubansa a hankali ya saka a cikin idannuwan Nuriyah wace itama du ta nemi daburcewa yana hangen kiris ya rage ta aikata aikin da ta iya watau afkowa mutun idan ta tsorata, hakan ya sa ya sake tsatsareta da ido a hankali saman lebensa ya furta" Ba na hannaki tsorata ba?"

Nuriyah ta lumshe idannuwanta ta sake budewa a kan fuskar tasa, a lokacin da ya sake furta mata" Menene abin tsoron? Nine fa, da Hajia kakarki.....kar ki yi abin cen kin ji a nan".............. Ya idasa yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login