Showing 117001 words to 120000 words out of 124070 words

Chapter 40 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

327

saka hannunsa biyu ya amsa ya shiga yi mata godiyar da ta sakata dariya hadi da girgiza kanta, dan ya bata kunya ainun, ita bata gode mada a rayuwa ba shine zai gode mata?

Juyowa suka yi suka dawo wajen motar ya bude ya shiga suka yi masu salama
Maimakun su taho tare gaba daya sai hajia tace bara ta fan yawata kafafuwanta, kuma ta ki Nuriyah ta bita, domin a lokacin da suke tsaye Mu'azam ya leko daga saman Elhaji, ya jima a tsaye yana kallonsu bama kamar da suka matsa gefe din nan
Nuriyah ta nufi gidan tana tunanin shiga kicin wajen ma'aikatan gidan su yi aiki ita kam bata son zama waje daya, Hajia kuwa ta shiga rawatawar a filin gidan a zuciyarta tana ayana' Zamu ga idan halitar kishi shirme ne na mata ko mazanma sunna da shi, in ba mijin ba abinda aljannah ta haramta ga namijin da baya kishin iyalinsa sai su ce zasu yi koyi da koyarwar nasara mai sakarwa mace mara ta yi fitsari, irin ta wataya ta ji dadin rayuwarta tana da yancin yin dukkan abinda ta yi niya ba haramun bane a gareta a ganninsu

Tana shigowa Falon kanshin turarensa ne ya sheda mata cewa yana wajen

A hankali ta ringa satar kallon waje waje har idannuwansu suka sarku da junna
Kallon yan sekwani ta yi masa a hankali ta cire dubanta a kansa ta nemi shigewa ciki

"Shi yana da damar gannin dariyarki da doguwar hirarki ama ni kin ki ko hannunki na taba? Wannan shine tsohon saurayin naki?" Ya fada a kausashe yana duban agogon hannunsa hadi da bale shi ya cire shi a hannun nasa

Sosai maganar ta daketa, sai dai ta yi iya yinta ta hadiye, bayan ta saurare shi dan ta jadada darajarsa a idannuwanta sai kuma ta juya ta kara daga kafarta daya zata fice
Da sauri ya dago yana kallonta ransa na neman dugunzuma ya ce" Idan kika yarda kika bar falon nan NURIYAH ban san irin hukuncin da zai iya hawa kanki ba, ki fahimci yannayina ki dawo ki amsa tambayoyina, ina kololuwar bacin ran da ba zan so na mike da nufin tarda ke dakin cen ba!"

Ko a yadda ya yi magana ta gane iya gaskiyarsa ya fada, dan haka sai ta juyo din ta dawo falon ta nemi waje ta zauna kanta a kasa
Cike da wani bacin ran ya shiga fada, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, idannuwansa sun rikide sun masa jajajir, yayanta ya kwashi rabonsa har kamar sababin kalamai a nan ya rawaito su, ya yi ya yi ya gama kanta a kasa hawayenta na kwarara, har sai da ya gaji ya kuma dubeta da wani bacin ran ya ce" Ga shashasha ko? Na zauna ina maki magana kin min shiru ko? To bari ki ji walahi in dai har da wani abu a zuciyarki dangane da mutumen nan ki shirya takabarsa, ke ba shi ba har danginsa sai na auna awonsu a gabana!"

Da sauri ta dago idannuwanta ta sauke masa nanauyan kallon dake zuciyarta, muryarta kasa da tashi sosai ta shiga fadin" idan ka aikata masa wani abu ko ka yanke neman abincinsa saboda hasashe da kake yi ni zan dubi haramun dina ka shiga hakinsa, domin a karkashinka yake samun abinda zai ciyar da danginsa harma ya yi taimako, wannan din shine wanda ya taimaka min harma ya kawo ni nan na damu aikin yi dan na dogara da kaina, ko a da babu wannan maganar a tsakanina da shi domin shi din adali ne , koda ya so hakan hango min wahala ya daka shi janyewa baima nuna ba"
Ta ajiye a hankali tana saka hijab dinta ta share hawayenta ta kuma dubansa a hankali ta ce" Sir, kana tunanin nima an bani damar kula wani bayanka ne da nufin soyaya? Ko kai da aka ba wannan dama an ce da kai ka aura, ba ace ka tsaya kulawa a waje ba....domin wannan aikin ba aikin mutanen kirki bane, baban sabo ne mai zubar da mutunci da kima, mai maida dukiya baya, mai bibiya tamkar tsohon bashi, mai ajiye tabo irin na kunnar wuta....mai bakin sakamako a gobe kiyama, ni kuma mace an haramta min kula wani da nufin soyaya bayan nawa mijin, kuma in sha Allah ba zan yi gangancin duban wani ba da wannan fuskar sai dai idan babu igiyar aurenka a wuyana....."

Tana ajiye maganar ta sake maida kanta kasa a hankali ta fashe da kuka tana biye fuskarta dan walahi ji take kamar ta je ta shaki wuyan Elizabeth din cen ta rike makogwaronta har sai ta aikata kiyama!

Jikinsa ne ya ringa mutuwa, dukkan gabobobin jikinsa na yin nauyi, kukanta na hawa kansa kamar wanda yake ji zai fasa ihun shima

A hankali ya dawo gefenta ya dago fuskarta yana kallon baby face din da take kukan da ita kamar zata summe , a hankali yake fadi " Hey bab, please ya isa hakanan, menene? Wai menene? Ki tuna fa irin rayuwar da muka yi mai dadi, me yasa zaki nemi cenza min ne? Duba ki gani ko magana kike min kina kuka, ama shine zaki masa dariya ki raka shi? Me kuka ce ? Me yace maki? Kalli zuciyata ciwo take min, ina jin ciwo a kaina da komai na jikina, tun jiya rabona da rintsa ido, ban san wannan pain din ba, ban sanshi ba me yasa kike son rikitani ne? Menene dan Allah ki fada min"

"Jikinka fa ta rike, bai isheta ba ta kwonta a lalausan fafadan bayanka, du bai isheta ba ta kama albarkar da nake kishi.....bai isheta ba ta yi maka rada a wajen da nake yi maka....du baka tsinka mata mari ba ka saurareta.........................yaya zaka bari kazamin hannunta ya ribanceka ne? Me kake so na yi maka? Yaya kake so a yi shi? A ina kake so mu yi shi? Kwana kake son yi kana yi? Menene anfanina? Tell me menene take yi maka dake birgeka? A gabana kake waya da ita, yaya zara hadu da ahalina ta ci abinci? Ni din iyalinka ce, ita fa? Idan aurota zaka yi ka aurota mana, yaya kake son bata mana tsatsonmu ne? Yaya kake so gobe kiyama namanka ya samu azaba? Godiyar ALLAHn kennan a tarin niimar da ya yi maka? Me ka rasa? Mu uku bamu wadaceka ba? Ta musulunta ka cike ta hudu da ita sai ka samu gamshashen gamsuwa..... Ama ta yaya kake tunanin gannin fuskata bayan kana kokowa da kwonciyar hankalinka? Just tll me menene take da shi da bamu da shi? We love u so much , i.....i ....love u so much da zan iya hakurin gannin hakan....dan Allah dan Allah kar ka halaka min innocence dina, kar ka sa na zama wata iri manhhhhhjh, ka tausayawa shekarunah i bg.............. ..... .......
Hadiye sauran kalaman ta yi , ko nace a cikin bakinsa take idasa su, a lokacin fa ya idasa saukowa kasa da ita ya shiga zazafarta da daidai misalin gudun jinnin da ta karawa jinnin jikinsa da zuciyarsa

A cen kasan makoshinsa yake furya" Im sorry wife, I'm sorry, i lv y, i lv u will allll ma hrt, hey kalleni, kalleni please.....dama da gaske shine damuwarki? Eli ce damuwarki? Dubeni, dama itace damuwarki har na gaza gannin murmushinki? , Nuriy idan kika ce minma a daina dainawa fa za'a yi?"

Idannuwanta ta dan kankance ta ce" Oh really?"

"Oh yeah" ya fada yana sake janyota jikinsa yana dafa wuyanta da mamakin zafin jikinta dake karuwa

A hankali ta ce" to a daina"

Sai da ya mana mata kiss a goshinta ya ce" An daina, ba zaki kuma ganninta ba in sha Allah "

"Kuma kaima ka gujewa ganninta" ta fada tana dago dubanta tana kallonsa

Sai da ya mata murmushi cike da mamakin dama wai wannan dan abin kan iya taba zuciyar mace? Me yasa Nadia ta nuna ita kawai aurowar ce kar ya yi, ita kuma wannan ta nuna ko aurowar zaya yi ba wani hakan zai birgeta ba ama da ya bi a waje gwara ya kawo?
A hankali ya ringa kallonta, she is beautiful, nd pure.....................

"Nuriyah?" Ya fada kasa sosai
Amsashi ta yi tana kallonsa

Ya ce" kika ce na yi har safe? Haka a jirgi kika ce na shiga? Zaki iya kuwa? Kin manta suma kika yi ranar nan?"

Ajiyar zuciya ta sauke ta maida kanta ta lafe a hankali ta ce"



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
6?? 2??


Cen kasan makoshinta ta furta " Tana gidan fa har yanzu"

A hankalin shima ya tambayeta cewar wa fa?

Idannuwanta ta dago tana kallonsa , sai kuma ta turo bakinta ta ce" Ni nama manta sunnanta "

Samun kansa ya yi da sakin murmushi ya sake riko bakinta a hankali ya bashi kyakyawar kulawa kafin ya mike da ita ya zaunar da ita saman kujera ya nufi dakin da ya shiga jiya ya dauko ky din bangarenta ya dawo ya bata a hankali ya ce" Ki koma gidanmu dan Allah, kafin na dawo kin ji?"

Hannunsa ta riko da sauri tana kallonsa a hankali ta ce" Ina zaka je ne mijina?"

Bakin mai fadin mijina din yake ta kallo, kai ua shiga uku, da soyayar a nan gida take yake hauka wayo shi wayo kansa da a kusa soyayar take a tare da y'ar hausawa yake cen yana lalube da hango soyaya a wani wajen?, Ya shiga ukunsa kar dai fita ta gagareshi shi jikan mutun hudu, wollah kamar yar jaririya idan ta shagwagwabe fuskar, sam tsoro yake kar ta fashe da kuka
Sai da ya sake komawa da wani rarashin dake sakata dariya a zuciyarta dan ta kula kaf duniya baya gannin yarintar kowa irin tata ya ringa rarashinta kafin ya fice

Mikewa ta yi ta je kicin ta yo hafin da ta ji yana biya kata a ranta ta dawo falon ta zauna ta shiga lasa da yatsarta tamkar zata cire hannu, hadin ba komai bane face mai da yaji da mayonaise, wannan hadin da idan lafiyarka kalau ko da bilala ba zaka sha bane ta zauna take tanda tana jin zata iya shansa duka kaf rayuwarta ba tare da ya gundureta ba
Ta dauki lokaci tana tandar abin nan ga ruwa mai sanyin gaske gefe tana kwonkwada
Salamar su baby ne ya dakata dago kai ita da mamanta hannayensu rike da ledoji niki niki, bayansu kuwa Hajia ce fuskarta kamar gonar auduga haka take washe bakinta tamkar an mata albishiri da gidan aljannah

Zamansu kowace abinda yake gaban Nuriyah yake kallo stll sunna amsa gaisuwar da take yi masu da tambayar inda suke je sai da ta farka ta ga basa nan

Hajia ta ce" Ke y'ar nan bari tambayar inda suka je albishirinki, yau na ga jaraba gannin idona, Hisaina na fada maki yarinyar nan sai ta ci mutuncin taurin kai da tsagerancin yaron cen, kai ama banasariya bata iya kuka ba sam ba dadin kallo , ama Mijin ya iya abinda ba shikenan ba yana tsaye tana ihun magana yana kallonta har ta gama ta shige motar ta tafi"

Nuriyah ta sada kanta dan abinda take ji din nema yake ya sakata sakin murmushi a gaban Hajia

Hajia ta sake kallon abinda ke cikin plat din ta dubi Nuriyah da kyau ta ce" Wai yarinyar nan kardai wannan abin ne kika saka a gaba kike sha? Yinwa kike ji ne ko menene?"

Nuriyah ta kalli abin, ta kalli hajia, a hankali ta girgiza kanta ta ce" Hajia ba yinwa bace kawai ji na yi ina sha'awarsa ne"

Hajia ta kalli Mama a zabure wace ta sake kurawa Nuriyar ido itama tana kallonta sai kuma ta kawar da kanta a lokacin da ta ga irin kallon da Hajia ke yi mata

Hajia ta ce" Na ga Annabi idan na yi hali na gari, ke yanzu fulako zai sa ki cuceni Husaina du zamana da ke a gidan nan? Na tambayeki nonon yar nan nata ne ko ciko ta saka kika yi shiru, na tambaye shi shima ya ce ya sani ne? Ke Balaraba a kirjinki da rigar nono ko babu?"

Daga ita har Murjanatu a zabure suka kalli kirjin nata, sai ta rasa ta inda zata fara, shin da gudu zata zura a gaban tsohuwar nan ko ta kwonta ta yi ta burgima tana kuka ne? Ina hadin Hajia da nononta? Tsakani da Allah ina hadin Hajia da nononta?

Salamar Kan Giwa tafe da jaka a hannunsa baka ya sakata sake sine kanta tana fatan maganar ta katse kar ta yi nisa
Tunda ya zauna baby ta mike dan kawo masa ruwa shima idannuwansa suka sauka a saman plate din , duda ta cire hannunta tuni ama kasancewarsa a gabanta ya sa ya gane nata ne
Yana shirin tambayar menene Hajia ta sake yin tambayar da ta saka duka aka kuma juyowa ana kallonta, a wajen kowane samun kansa ya yi da jin wani irin nauyi, shi kan Giwa hakan ya faru ne sakamakon Mama dake wajen, ko da yana kunyar Mama fa, dan walahi a gabanta baya yin du abinda ya ga dama bale yanzu, Baby kam ita ta fi kowa shiga uku da Hajia, anma in sha Allah yau sai ta mata kashedi a daki, Mama din kanta rasa me zata ce ta yi ta sada kai, domin ita ta gama gane abinda ke tare da Nuriyar, badai zata fada bane kai tsaye tunda ba aunawa aka yi ba, ta kasa hane dalilin da ya hanna hajia ganewa kai tsaye, ko dan an jima ana nema ne????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
ya sa yanzunma take kokonta?
Nuriyah kuwa gani take yi kaf ba wanda aka sak uku irinta, fisabililahi Hajia ta daina irin magana haka a gaban jama'a wai menene damuwarta da wajen nan? Ita yanzun nauyinsuma take ji bata san me yasa suka karra girma ba kuma kansu yake damunta da kaikayi ga wani tsini da yake dan yi ba kamar da da yake shafe ba

"Yaya ina magana du kun min shiru, nace wai a rigar y'ar nan da cikon nan na zamani ko........"

"Babu" ya ji bakinsa mai aikata aikin da bai saka shi fada, walahi a zuciyarsa ya so ya fada, a cen kasan zuciyarsa ya ayana , sai kawai ya ji amon maganar, innalilahi Hajia Hajia Hajia!

Mama ta sake sada kanta har zufa take ji tana neman fara damunta da lamarin Hajia
Da takaici ya dubeta ya ce" Kin huta ko? Babu sai me kuma?" To a ganninsa ai aikin gama ya gama ta sakashi fadin matarsa bata saka breziya ba a gaban mamanta ai shikenan ta samu abinda take nema

Hajia ta maka masa harara ta kawar da kanta barin da Nuriyah take tana fadin"Sai ubanka, ke Balaraba yaushe rabonki da gannin al'adarki ne bayan aurenki kin gani ko kafin aurenki? Sannan bayan rashin lafiyar da kika yi bayan tarewarki kin gani ko baki gani ba? A cen garin naku da kuka je shin Mijin ya.........."

A sanyaye Mama ta katse maganar tana sake sada kanta ta ce" MAMA abinda kike zargi ne , sai fatan Allah ya raba lafiya" domin kunnayenta na daf da dodewa idan ta bar Hajia na cenke cenken nan, bata san abinda zai iya zuwa bayan fusrucinta ba

Sai da Hajia ta zarro ido ta sake duban Mama har tana karkatowa ta ce" Husaina kina nufin ciki ne da ita?"

Yanzun kam gaba dayansu suka kalli Mama a zabure , bama kamar Kan GIWA

Mama ta gyada kai tana cire dubanta a kansu

Salalamin da Hajia ta dauka ta mike tana yawo a falon kamar kazar da ake son kamawa tana tsere da zagaye lokaci daya ga kuka tana yi ya saka Mama mikewa ta bita domin sauran Baby ta saka ihun da ya girgiza kunnen mutanen falon ta rukunkume Nuriyah, Lan Giwa kuwa ya yi mutuwar zaune ya zuba mata ido cike da abubuwan da ba kowa zai iya fahimta a cen cikin kwakwaluwarsa ba

Mama ta rike Hajia da kyar tana fadin" Mama ki daina kukan mana dan Allah ki dawo mu zauna kafarki fa kina taketa da karfi bayan likita ya hanna tafia da karfima bale taketa a haka"

Mama ta ce" Barni y'ar nan, barni na yi kuka, barni na zubar da hawaye, barni na godewa Allah, wani abin sai kulan, wayo Allahna dadi ko yau na mutu Alhamdulilahi, ashe shima ba juya bane yana da kwai a duniya kawai yan iska aka aura masa suka dakatar da haihuwar? Ashe shima za haihu a duniya ban sani ba? Allah mai hikima mai kyauta fa kari, Allah dama Mu'Azam zai samu dan dagwai dagwai ya kireshi da baba? Wayo duniya dadi in ji maki mutuwa, to ni idan ban yi kuka ba me zan yi? Yau ko Elhaji sai ya rusa kuka ni na fada maki, ke ko mijinki da baya magana yau sai kin ya saka ihu nice nan na fada maki domin son da yake ma yaron cen sai da na kwabe shi dan kar ya ringa nunawa a gaban yan uwansa ya daina, wayo Husaina ashe ku din kunne zaku bamu ya'yan da yawa? Kin ga ke uban iya Wan!"

'ikon Allah na shiga uku da hajia' mama ke fada a kasan zuciyarta

Da kyar ta dawo da ita kusan Kan giwa dake kallon Murjanatu na kukan itama hadi da daria , Nuriyahma tana tayata kukan da bata san ko na me take yi ba

Hajia ta dafa kafadarsa ta girgiza tana fadin" Kai, farka haba farka kaima ka summa a zaune ne ko? Ai abin daga Allah ne ciki ne da ita kaima zaka zama baba da gaske"

Idannuwansa ya ringa kikiftawa ya juyo barin Mama a harhade ya shuga fadin" Mama ciciki? Mama ta yaya zaki gane ciki ne da ita ba'a mata gwaji ba? Mama kuma bata yi karama da daukan ciki ba? Na ga katoto yake yi a jikin mutane yaya zata iya tafia da shi yarinya ce fa? Mama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login