Showing 42001 words to 45000 words out of 124070 words

Chapter 15 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

352

muryarta kuwa hankalina sai ya nemi gushewa, shin me ya faru da y'ar uwata ne? Tana raye ne ko bata raye? Ina Lawali ya koma ina ya kaimin ita? Cikin da muka barta da shi yana ina? Abanmu ya rigai ya kamu da ciwon da sai dai a lalaba kawai sakamakon tunaninta, ya Rab......" Ta idasa tana rufe bakinta da hannayenta bibiyu tana fashewa da kuka hadi da zama a bakin kujerar tana hanna kanta yin kukan tun karfi domin Hajia na yawan yi mata nasiha a kan hakan

Sake salama Hajia ta yi tana tsaye har sai da Aba ya ji ya juyo hankakinsa du a tashe ya amsa ya kamota suka idasa shiga dakin ya zaunar da ita saman kujera tana kallonsa shi da Mama a tausashe ta ce" Wannan karron sau uku kennan ina hankalce da dukkan nutsuwarki na barin gangar jikinki da zarar kin ga Nuriyah, me yake faruwa ne?"

Mama ta sauke ajiyar zuciya tana fadin" Mama ni da kaina ban sani ba, abin na fin karfina ne sosai, bayan ban ga mahadi ba.....aman wasu lamura kadan kadan dake fitowa a tare da yarinyar kam saka zuciyata dokawa da karfi, misali irin dagowar da ta yi dazu , y'ar uwata na yin haka idan abu ya taba mata zuciya, tafiyar yarinyar na karra dulmiyani a yannayi na tunani, muryarta ta yi sanyi sosai a kan tamu sai dai gura gurarta dake dan sake sakani a nazari, Mama a ina kuka samo yarinyar ne?"

Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Kina ji Ouseina, abinda nake so da ke shine ki saka hakuri da nutsuwa a cikin zuciyarki, ki dauka cewa idan tana raye zata bayana idanma ta rasu ne tabas zamu sani, kin ga daga ranar da kika fada min kema haifafiyar garina ce har kika fadan labarinki nake kwana ina tashi da abin a zuciyata, fada maki ne bana yi aman nima ina cikin masu neman yar uwarki, kin ga Nuriyah dai ban san iyayenta ba, aman yayanta ne ya kawo min ita, da zarar mun koma zan kirawo shi mu yi magana sai hankalinki ya kwonta in sha Allah "

Da wannan suka rarasheta, Hajia ta karra da nasiha sosai har ta dan samu nutsuwa a zuciyarta har ta iya sakewa ta ci gaba da yan shagulgulanta , aman cen kasan zuciyarta gaba daya hoton yarinyar ne a dankare a ciki ta rasa gane kan naci irin na idannuwanta a kan abu

__________________________________

"Auta.....Auta.....Auta? Ki tashi mana haka wai ni ki rakani na dauko a juye masa a rufe masa shi mana" ta sake fada tana dan dadaba Murjanatu dake ta juyi tana alamun ta kiya domin barcinta ya yi nisa sosai ba zata iya tashi ba

Sake dadabata ta yi zata sake cewa ta tashi Murjar ta buda idannuwanta da kyar tana fadin" Gaskiya Nuriyah ba zan je ba.... fisabililahi ke bakya gajiya da aiki ne ? Ni ba zan je ba"
Ta idasa tana turo baki hadi da sake juyawa ta ja bargo ta rufe kanta ruf dan gani take farmaki ne kawai Nuriyar ke son kawo mata tana zaman zamanta

Yar dariya ta yi a sanyaye ta sauko kafafuwanta tana mika da rigar barcin dake jikinta doguwa wace ta kai har kasa, sai dai mai santsin nan ce sosai domin gaba daya a jikinta take kuma bata da nauyi ko daya sannan siraren hannaye ne da ita, sai hula irin mai hudojin nan bak'a a jikin gashinta wanda ta kasa saka gashin gaba dayansa cikin hular dole sai saman gashin ta dora hular shi kuwa ta tufke shi ta barshi a bayanta hakanan

Hankali kwonce ta nufi hanyar fita, dan ta riga ta san dabi'ar mutanen gidan, sun kasance tamkar horon nasaru basa wuce lokacin kwonciyarsu , haka kuma idan ba lokacin su fito ya yi ba basa fitowa, shi yasa kai tsaye ta fitowarta ta yi hanyar kicin

A daidai zata yi kwanar kicin din da lalube ta laluba ta dadana abubuwan kunna fitilun falon tama dan yamutsa fuskarta domin gaba daya iskar falon sai ta ji bata jin dadinta a hancinta

Ita da zata wuce ta dauko dambun naman sai ta zagaya ta dauko kaskon da Murjanatu ta saka turaren wuta tunda sasafe ta yi kicin din da shi ta saka abin budewa ta bude da Bismillah ta shige da ayatul kursiyu da take yi a bakinta kasa kasa tana tafe tana dan lumshe idannuwanta da murmushin da bai barta ba wanda ta kwanta da shi tun albarkar da maman Murjanatu ta saka mata haka kawai take jin abin a cencen kasan zuciyarta

Wajen gawayin da kayan turaren wutar ta je ta ajiye kaskon ta shiga bubude kwalaben tana sinsinawa hadi da lumshe idannuwanta tana jin yadda kanshin ke ratsawa har zuwa cikin zuciyarta tana sake shinshinawa

Cike da rausayar da ba da gangan take yi ba da farin ciki ta kunna gawayin nan biyu ta dan ja baya tana kallon kwalaben turaren wutar ta ce"





I'm sorry >?p?>?p?>?p?>?p?>?p?>?p? ku mu bashi amsa mu ji???????>?p?>?p?>?p?>?p?>?p?>?p?>?p?>?p?>?p?






*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
3?? 2??



Cike da rausayar da ba da gangan take yi ba da farin ciki ta dan ja baya tana kallon kwalaben turaren wutar ta ce " Nama rasa wane ya fi dadi, bara a yi tsakani tsakani , tsakanin gizo da kogi in ba gizon ba gigogi kantana da awa da adam....nana nana, nana gwadamini gidan gaskiya wai ke ni ba gashinan ba......." Ta idasa da murmushi ta dauki kwalbar tana budewa ta dibo dan daidai misali ba da barna ba ta zuba tana sake fadin" bara kicin din ya fara yin kanshin sai na kai falon....., Koda yake bara na kai falon ya dauki kanshin sai na maido kicin d................................"

Dif ta yi shiru sakamakon muryar da ta ce da ita" Wacece ke?"

Jikinta ne ya dauki bari a tsayen da take, zuciyarta kuwa ta aniya neman fitowa daga cikin bakinta ta fado kasa,
Hankalinta ya dugunzuma ya tashi, kwakwaluwarta ta nemi hadewa ta sakata doke doke irin na wace bata da hankali

A tsayen da yake bibiyu yake ganninta, tun bayan kwonciyarsa a dakinsa ya kasa barcin domin jikinsa sake daukan zafi yake yi, haka kuma hannunsa sai ya idasa zundumewa tamkar ba nasa ba, wannan dalilin ya sa ya mike da kyar ya shiga neman wayoyinsa aman gaba daya ya rikice domin du a rikicen yake

Fitowar da ya yi da nufin ya je ya yi anfani da wayar falon ya kirayi Rislan ne dan shi ya zo masa da likita sai dai bai karasa wajen wayar ba ya zauna a falon yana rike da hannun nasa a hankali yana shafawa dan ya ji wajen da ya fi sukansan nan dan ya tabata Kwalbar nan ce a ciki ya tsigeta ko zai takaita masa sukar
Yana wannan halin ya ringa jin maganar mutun a kansa, bai ganta ba dan duhu har sai da ta kunna fitilun nan ta kuma juyo ita kadai sai hira take tana murmushi ta dauki abin turaren wuta ta nufi kicin din gidan
Wannan dalili ya saka shi kamewa a zaune da mamaki, domin wannan budurwar bai santa ba, bai san ko wacece ba, nan da nan ya shiga tunanin ko dai aljanna ce? Domin tsarin halitar yarinyar zai iya cewa a kurkusa idannuwansa basu hango masa irinta ba sam, irin yadda samanta ke dore a saman kugunta subahannalah tabas aljannah ce, ga kalar gashin kanta uwa uba yadda ta sake take sha'aninta a gidansa tamkar wace gidan nata ne

Da kyar ya ciciba dan ya karasa ya ga ko mecece ita, da wannan ya idasa kicin din ya tsaya yana gannin yadda ta ringa magana da murmushi ita daya har zuwa yar wakar tsakani tsakanin da ta yi dan daukan turaren wutar

Kwalar da ta cicika idannuwanta fuskarta ta dauki yannayin tsoron da ya saba ganninta da ita ba yannayi na farin ciki da sakewa da walwala ba ta juyo tashi daya ta sauke idannuwanta a saman fuskarsa kafin ta idasa sakin shagwababen bakinta , tabararen bakinta ta fashe da kuka tana sada kanta bakinta na rawa ta ce" IIIIna kwana , iina yini, dama dambun naman Yah Rislan ne na zo dan na juye a flas sai kuma, sai kuma nace tunda barci kuke bara na saka turaren wuta dan kar ku tashi dakin na kannin kayan yaji..... Innalilahi wa inna ilaihi raj'une.........." Ta idasa tana karasa sakin kukanta dan ita da kanta dake bada bayanin baya mata dadi a kunnenta yadda ya dace, kawai fadinsa take yi zuuuuuuu kamar wace ke sheka karya

A hankali, muryarsa na nuni da baya jin dadin jikinsa ya saka hannunsa ya talabe dayan ya sake fuskantarta ba alamun tsoronta a tare da shi duda kokonta na cewa aljannah ce dake cikin zuciyarsa ya ce" I sd who are you?"

Ido ta shiga kikiftawa tana kallonsa hakan ya saka shi girgiza kansa da dan daga murya kadan Wanda ya hadasa masa tari ya ce" na ce wacece ke?!" Sai kuma tari ya kama shi a hankali ya hade bayansa da jikin garun kicin din yana lumshe idannuwansa

A tsorace take bin yannayinsa da kallo, du irin rikicewar da take ciki ba zai hanna mata gane wannan bawan Allahn na cikin wani hali na rashin lafiya ba, dan haka take dan matsowa duda ta san kasada ce aikata hakan har ta idasa matsowa kusa da shi sosai a hankali take kallonsa har ya kare tarin yana sake lulumshe idannuwansa

Da sauri ta juya ta dauki kofi ta kunna ruwa ta darwaye sannan ta zubo ruwan pampon ta dawo wajen da ya durkushe yana dan bubuga kirjinsa dan tarin ya kwonta masa
Gaba daya ta samu kanta da dora hannayenta ta samu da kyar ta dago kansa da ya sada ta kawo kofin ta saka masa a bakinsa tana talabe da fuskarsa ta ce" Sha , idan ka sha ruwan zai bari kuma.ka daina sada kanka tarin ba zai tsaya ba, sannu "

Idannuwansa ke lumshe ya hade da bayan hannunta yana shan ruwan a hankali a hankali har ya ji sosai ruwan ya dira masa harma ya ji ya daina tarin sosai sannan ta cire ruwan t??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a ajiye a kusa da su tana sake hura masa fuska tamkar wani yaro karami, domin ita du ta rikice taimaka masa take yi , idan ka mata tambaya a lokacin tsabar rikicewa da wahala ra shaida maka da wa take tare

A hankali a hankali yake sauke ajiyar zuciya yana jin gaban goshinsa na sara masa

Muryarsa cen ciki ya kamo hannun nata a gefen fuskarsa ya ce" Call Rislan fr m pllz"

Fuskarsa ta kurawa ido tama son fasarce yarensa a cikin zuciyarta
Hannun nasa da ya yi kaba ta zubawa ido wanda hakan sai da ya sa tsigar jikinta tashi gaba daya
Da sauri ta janye hannunta ta mike ta yi falon jikinta na fawa ta karasa wajen wayar ta saka nmber bangaren Rislan din ta yi kira domin gaba daya na kowani bangare kake shanyewa idan kana ma'aikacin gidan

Ta jima tana ringin kafin ya daga muryarsa a shake da alamun barci yake yi shi dinma

Muryarta a sanyaye ta shaida masa cewar ya zo bangaren Kan giwa bashi da lafiya

Sai da gabansa ya fadi, da sauri ya wartsake yana wara idannuwansa ya saki wayar ya nufi hanyar wucewa da wani irin sauri kwata kwatama bai tsaya ya dauki komai ba

Itama tana nan tsayen jikinta bai daina bari ba tana sake leka hanyar da yake jingine idannuwansa lumshe har Aka shiga buga bangaren nasu

Da sauri ta je ta bude tana kaucewa Rislam ya shigo kai tsaye zai fara magana idannuwaansa suka sauka a kanta

Da sauri ya cire dubansa yana waige waigen falon dan son gannin mutanen bangaren da yayansu, sai dai ita daya ya gani a lokacin da ta juya ta nufi hanyar kicin din tana nuna masa tana kuma fadin" Yana cen Yah Rislan mu je ka gani"

Wani irin mamaki, da tunani ne ya darsu a cikin zuciyarsa a lokacin da ya ga suturar jikinta ya kuma tabata cewar itace kadai ke tare da yayansa, me ya sa daga ita sai shi a irin wannan lokacin? Me take yi da wannan shiga a haka bayan Nuriyar da ya sani ba zata iya fitowa a haka gaban wanin da ba muharaminta ba? Shima yana cikin wa'inda suka yi maganar a barta ta saka suturar da take so dan aiki a gidan nan

Yana tsakanda maganar zuci cak tunaninsa ya tsaya sakamakon damkar damtsen hannunsa da ta yi gannin ya ja ya tsaya a birkicen da take ta sake nuna masa hawaye na bin kumatunta ta ce" yana cen din fa, ka je dan Allah"

Sai a lokacin ya iya gane ko me yake tafe da Nuriya, tabas tana cikin hali na rikicewa wanda da yawan mutane idan suka rikice sukan rasa abin yi ne, saima daga baya ake iya fada masu ga abinda ya faru

Kamar wadda ya kunna haka ta shiga fadin" Ni ja fito ne dan na juye dambun namanka sai na shiga kunna turaren wuta sai kawai na ji maganarsa a bayana, sai da na juyo sai ya karaso sai ya........"

A hankali ya ce" NURIYAH, NURIYAH "

Ta yi dif tana kikifta ido a birkice

A hankali ya ce" Je ki kwonta kin ji? Tafi dakinki ki kwonta ki yi barci kin ji?"

Da sauri ta ringa gyada kanta ta juya ta yi dakin nasu gaba daya ba a cikin hayacinta ba
Sai da ta kulewa ganninsa sannan ya juya ya nufi wajen yayansa
Yana dora hannunsa a saman wuyansa ya ji zafin da ya kwasa ga kuma yadda hannunsa ya yi , dan haka da sauri ya fice ya kirawo masu tsaron lafiyarsa mutun biyu suka kama masa suka yi dakinsa da shi sannan ya saka aka je cen bangarensa aka kwaso masa baban kit dinsa na asibiti ya shiga ba yayansa talafin da ya dace cikin gagawa, domin ya gane wannan ciwuka na hannunsa da wasu kwalaben basu fita bane suka hadasa masa zafin zazabin nan mai fitar da mutun a hayacinsa

Sosai ya cire ya wanke sannan ya saka magani ya nade masa kuma ya jona masa karin ruwa mai hade da maganin zafin zazabin sannan ya zauna a gefensa ya zuba masa ido

Gaba daya a duniya bawa kan hadu da jarabawa kala daban daban, kuma kowani dan Adam tara yake bai cika goma ba, kamar yadda du jin dadin mutun ko kudinsa yakan hadu da wata tangarda ta rayuwa....to hakan ce a kan yayansu
KAN GIWA ya kasance mutun mai arziki, mai kuma mulki, sai dai gaba daya rayuwarsa a abinda ya shafi mace a hagunce ya zo masa
Shi yaro ne a kansa, aman zai iya fadin menene matsalar yayansa kuma menene maganinta
Tunda farko shi ya fara saka kansa a damuwa da ya dauka cewa idan ya yi duba da abinda ke wakana ta bakin yan bariki ne gaskiya, sai ya mike ya ce shi a duniya macenma ga daga bakin shekarun da zai iya dauka, ya je ya zabo din ya darje a tunaninsa yana neman wace zasu zauna su fahimci junna, sai ya samo sun aman kuma sai ya fara bata rawarsa da kansa ta hanyar yin sake wa tarbiyar ahalinsa, ba maganar shakuwa, ba maganar zaman aure a tatare da su, kuma shi dai ya dauki hakan a matsayin tsabagen samun waje da raini domin a cikinsu ko yare suke koda basu da alkibla daga gaban uwa da uba aka dauko su........a yanzu bai san ta yadda zai yi ya daidaita al'amarin nan ba, abinda ya sani shine a gaskiya ran kowa zai bace a gidan nan ta yadda yayansu KAN GIWA ne bashi da lafiya aman iyalinsa na kwonce sunna shagalinsu? Wannan ba zama na aure ake yi ba, ko zaman bariki ne zara yi maka biyaya ko dan kudaden aljihunka

Zuciyarsa ke hucin bacin rai , yakan saka hannunsa ya shafe hawayen da ya Tarun masa a idannuwansa da tunanin yanzun a gobe dole zai bar gidan nan ya tafi jami'ar indiya dan ya karasa karatunsa na zama baban professeurn likita? To yaya zai bar bayansa da irin wannan rikicin? Yayansa ba zai taba dubawa ba!

A nan a zaune sai barci barawo ne ya kwashe shi wanda ya yi mai nauyin da har bai san an yi kiran sallar asubah ba

Shima kasancewar ya samu barcin sai da hasken safiya ya fara dilowa ne ya fara bude idannuwansa a hankali yana dan maida su yana lumshewa

A hankali ya kuma budewa ya sauke dubansa a kan karin ruwan da ya karre Rislan ya kashe tun kafin barci ya kwashe shi sannan ya dago hannunsa mai daure da bandeji yana kallo

Idannuwansa ya lumshe a hankali ya ciciba da niyar tashi yana dan sauke numfashi kadan daga makogwaronsa,
Wannan motsi ya tayar da Rislan da sauri daga barcin da yake a karkace a saman kujera yana kallon yayansa

Da sauri ya mike yana saukowa hadi da fadin" Sannu yaya, yi a hankali bara na kama ka"

Barin ya yi ya taimaka mada ya mike kan kafafuwansa yana sake yamutsa fuska ya rike shi da kyau suka nufi bayi sannan ya barshi ya dawo yana tunanin koma meye ya same shi madubin bayin nan da ya yi ratsa ratsa ne ya shishige masa hannu domin ga digo digon jinni nan ga kuma madubin a zuzubde ko'ina

Shima wucewa ya yi ya koma bangarensa da gagawa ya samu ya yi wanka ya yi sallah sannan ya fito ya zaga baban kicin ya saka aka loda masa hanta ruwa ruwa da jus ya turo ya dawo yana duba lokaci karfe tara ce ta yi falon na kanshin turaren wuta ya wuce ciki

Gaban madubi ya same shi tsaye yana balla agogo a hannunsa mai ciwon a hankali, shi kuma yana cikin shiga ta dogon wando na yadi baki lalausa sai riga mai dogwayen hannu fara kal sai kanshi yake zubawa na turaren da ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login