Showing 102001 words to 105000 words out of 124070 words

Chapter 35 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

354

shigar alfarma a dakin Hajia saman gadonta kunnayenta na jiyo mata saukar da ake yi har nanauyen barci ya yi awon gaba da ita tana kara ji a wai ne zata amsa kiran mata a wajensa


___________________________________


*RANAR TA ZO*

A cikin lulubin bargon da take barcin da ta rasa ko na menene wanda da kyar aka iya tashinta ta yi sallah ta koma, wanda bata sani ba wani lipton ne da aka mata hadinsa ke dauke da sinadaren saka barci sosai, kasancewar kuma bata taba shan wani abin saka barci ba sai ya yi mata karfi har ya zamto yanzu kusan karfe daya na rana da Mazan gidan suka yi salama suka wuce baban masalacin da zasu gabatar da sallah bayan sallar a daura aurenta bata dan wainar da ake toyawa ba

Cikin barcin nata mai sansanyan dadi take ta jin susa a tafin hannayenta,
Zuwa yanzu barcin ya fara sakinta, hakan ya sa a hankali ta ringa dan janye hannayenta tana dan matsawa, sai dai jin abin ya ki ya bari ta bude nanauyan idannuwanta tana saukesu a kan Murjanatu da ta sha wani dan uban makup take walwali kamar zata je gasar sarauniyar kyau

Idannuwanta ta kikifta tana kallonta muryarta cen ciki da abin barci ta ce" Ina zaki je kikai kwaliya haka kawas?"

Murjanatu ta saki murmushi tana hadiye hawayenta na farin ciki da gannin tun kukan da Nuriyah ta yi na jiya bata kuma yin wani ba, ita dai ba'a ji ra'ayinta a kan KAN GIWA ba, aman kyma ba'a ji wata mumunar magana ko maganar dake iya daga hankali dangane da auren nata ba

Shigowar Mama Husaina ya sakata sake zubawa maman ido, itama tamkar a saceta a gudu, ta sha dan uban leshh wanda kyansa zai fada maka kudinsa, ba wani mai hatsaniya ba, ta nada lafaya mai ruwan blue din sararin samaniya da dauri irin na zarah buhari a ciki wanda ya wani irin hawa kanta ya mata dasss, sai dan uban kanshi take bazawa mai daraja da tsayawa a waje koda ta bar wajen

Idannuwanta bata ji zasu fado kasa ba sai da mahaifiyarta ta bayana, ashe haka matar ta hadu? Ashe haka mamanta keda tsararen kyau? Bata taba ganninta ba hijab ba sai yau, ta yi shiri irin na yar uwarta sak, harma ta so fin yar uwar tata kyau domin mama Husaina ta fara amsar cenje cenje na mai ciki wanda idan yana cenzaka Allah ya sa a saman kudi kake lilo sai ya bayanaka (=??)

A hankali ta ringa tunna makasudin kwaliyarsu kuma ina zasu tafi?

Da sauri ta juya barin agogo a lokacin da ta tunna kamar an tasheta ta salaci sallar asubahi, hakan na nufin safiyar daurin aurenta ce ta waye
Wani irin nauyi da wani irin abu ya ringa bin jikinta daidai Mama Husaina na yaye lulubin bargonta kanshin turaren da suka shafeta da shi ya daki hancinta tana fadin" Taso mu je ki yi wanka"

Jiki ba karfi ta zirro kaffafuwanta tana sake kallon Murjanatu, tana so ta mata tambayoyi sai dai idannuwan su mama ba zai bari ta yi hakan ba

A cikin wani katon baho aka yi mata nuni mai dauke da danyar madarar da aka shake da sinadarai irin na gyaran jiki aka bata umarnin ta tube ta shiga ciki

Baya mama Husaina ta bata dan haka ta tube da sauri ta shige ciki ita kuma ta juyo ta saka abin dibar madarar ta zuba mata ita sosai har gashinta da ya warware sannan ta dubeta a hankali ta ce" Zaki dauki minti talatin a cikin madarar nan daughter, kar ki fito har sai na dawo, gashi har magariba ke gabatowa domin an kusa kiran sallar magaribar, maza saki jikinki ya ratsa dukkan wajen da ya dace ace ya ratsa kin ji?"

Kai ta iya gyadawa sannan ta rakata da kallo jikinta na sake mutuwa.....a hankali ta ayana Magariba? A ranta, sai kuma ta sake sada dubanta tana ji gabanta na dan faduwa da tunanin idan har magariba ce ta kawo kai tana barci, idan har yau ne za'a daura mata auren kamar yadda aka fada jiya, hakan na nufin an daura mata aure kennan?

Wani iri jikinta ya ci gaba da yi mata, dan haka sai ta lumshe idannuwanta a bayin na Hajia ta ringa kore dukkan tunanin da zai iya jagula lisafinta tana kamo tunanin hirarakin da suke tataunawa da mahaifiyarta da zarar sun samu sarari

Mama Husaina na fita a dakin kiran Hajia ta amsa

A zaune take a gabanta kasa saman cafet hajiar kuwa na saman kujera ta mike kafafuwanta da suka gabi sosai dan yau ta yi kai kawo ya fi a irga, a tsaye take kan kafafuwanta ana sauka a bangaren da aka gyarawa NURIYAH wanda dalilin wannan sai da ta kashe wata rigimar ta matansa kwana uku da ya shige cewa a hada su waje daya mana, gudun kar su nuna ba'a masu adalci ba ta saka aka warewa kowace bangarenta, ama duka a baban filin gefen KAN GIWAR sai dai idan ba kai ka je wajen dan uwanka ba sai ku rayu ku gama baku hadu da junna ba, ga baki dake zuwa fatan alkhairi maza da mata, kun san fa biki na mai hannu da maiko, ba sai ya yi gaya ba

A nutse Hajia ta ce" Husaina, ke dai ganau ce ba jiyau ba dangane da halayar yaron nan na naci a kan abu da kuma tsayuwa a kan bakansa ko?"

Mama Husaina ta amsa Hajia tana dan murmushi

Hajia ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Allah shi kyauta, wannan lamari yake ta nukurkusata a lokacin da na tabata burinsa ta zama malakinsa ya raineta har ta cika shekara talatin koda zai amshi dakinta"
Hajia ta dan dakata domin maganar gaskiya mai nauyi ce, sai dai bata da yadda zata yi dole su yita

A nutse ta ce" Na san da nauyi, da kuma girma maganar nan, sai dai bani da yadda zan yi, kuma da ke din dai zan yita domin mahaifiyarta ta fi kowa kunya a gidan nan ba zata taba saurarena ba, Husaina kin ji ikirarin iyalinsa duda basu isa su yi komai na, ama sunna da gaskiya da suka karra jadadda cewa aure dai aka masaa ama babu abinda zai shiga tsakaninsa da matar har sai mun gaji mun raba auren, domin shi nas ra'ayin ya sha bambam d na kowa , ....ban sani ba Husaina ko yana tare da lamarin da yake gannin zai iya halaka yarinya mai shekara ashirin da biyu a duniya? Ko kawai nasa ra'ayin ne haka? Abinda na sani shine shekaru ja suke yi, a lokacin da yake tunanin amsar dakin yarinyar nan ta yiwu ya ba arba'in baya hati, watau a lokacin da tsufa zai riske shi idan yana da tsayin rai yana da rabon haihuwar yayansa sunna yawo dugwui dugwui da kafafuwansu , watau kananun da basu taka suka kai mizalin malakar hankalin kansu bama bale su taimaki iyayensu, gamu da rashin kwai da yawa, kin ga mijinki shi kadai Allah ya bani ban taba shan abin hanna haihuwa ba, shima ya samu uku sai wannan da nake fatan ganninsa , ama shi mijin matayen nasa sunna anfani da abin dakatar da haihuwar dan gayu....tunda na fuskanci haka kimar mutanen nan ta rage a raina, na ga wannan ai wauta ce da cutar kai"

Mama Husaina ta girgiza kanta ta ce" Ba'a kyauta ba kam Mama, Allah ya sanyaya lamarin nan"

Hajia ta ce" Amen, shi yasa na nemi number matar nan dake bada magungunna wace ake talace talacen magungunnanta a TV ta zo har gidan nan yau kwana hudu kennan muka gana na yi mata bayanin muradina, kin ga abinda ta bani tace idan dai wace zata yi anfani da shi t shafa kadan in sha Allahu bukata zata biya, domin komai taurin kan namiji da kansa zai salama "

Mama Husaina dai ba yarinya bace, kuma abinda Hajiar ta bata ta jima da siyansa ita da kanta, domin mijinta dai ba mutun bane da ya wani damu da abin nan sosai, ko dan shekaru sun fara ja? To fa du idan ita tana cikin hali na bukatuwar hakan abin nan take dan shafawa, to fa a ranar sai inda karfinsa ya kare bawan Allah, zai yi kokari iya kokari har sai ta gajiya kuma, domin dama lamari ne dai dake naturel dake iya bijirowa mutun mai lafiya, sannan a shekarunta bata yi wanda hakan zai zamto damuwa a gareta ba sai dai bukatuwa a gareta, sai a yanzu tunanin hakan ya darsu a zuciyarta itama, bama kamar maganar da Nadia ta fada din nan ta mata zafi sosai, wai ana takama an tara duwawu sai dai su anfana wajen yin kashi ba dai wajen miji ba, domin mijinta baya hawa karamin doki sai jimame, itama da kanta zata so ace yau NURIYAH ta amshi duty mai sunna duty, shima zata so ya zauna ya yiwa kansa fada da nasiha ya gane cewa ba wai daga haka bane abin

"Idan kuwa kin ga a barsu har a kwana biyu babu damuwa Husaina, ni dama dai nace zan baki, sai ku duba ku yabke shawarar abinda ya dace ku zartar .....ba zan so ya wuce yau ba a nawa ra'ayin" hajia ta sake fada a tausashe tana sake duban Mama Husaina

Mama ta sake sada kanta ta yi murmushi a nutse ta furta" In sha Allah ba zai wuce yau ba Mama,, " ta fada tana mikewa sau kuma ta juyo ta sake dukawa tana dafa jikin kujerar ta ce" Zan gama shiryata ne Mama, ni ba zan rakata ba dan yarona, mahaifiyarta kuwa ba zata taba rakata ba....."

Hajia ta yi yar daria tana jinjina kawaicinsu ta ce" Nice zan kaita dama, jira nake ku gama na mikata dakinta, barama na shige dakin Elhaji na yi sallah na shirya "

Amsata ta yi tana murmushin itama ta juya ta fice a dakin

Da wannan Mama Husaina na koma bayin nan ta sabe Nuriyah da wanka irin wanda ake yiwa amarya da kanta sannan ta fito da ita

A nutse ta gabatar mata da dukkan shirin da ya dace a yiwa amarya mai kunya, ta ciro zani da riga na atampa namu na hausa da aka yiwa dinkin kanence da zani ta bata danar sakawa, ko bra bata bata ba, ta sake dan shafa mata man lebe kadan sannan ta sakata tsuguna turaren wuta mai hade da maganin gyara ta gama, sannan ta kawo katon hijab dinta mai haske sosai ta rufashi a turaren wutar, sai da ya dauka sannan ta bude turaren nan na ruwa na wajen hajiya ta shiga shafa mata shi a hankali a bayan kunnayenta ne, wuyanta ne, kuncinta ne, goshinta ne, kai karshe gaba daya ta aniya zazage turaren nan a jikin tufafinta tana sake lumde mata ko'ina da shi har ta gama sannan ta zira mata hijabinta da kuma nikaf dinta da safar kafarta wa'inda ko kunshi ba'ai mata ba bale kitso duka kaf sai a gobe za'ai mata su

A bakin bed din ta zaunar da ita ta fitar da baby ta turo Hasana wajenta

Irin nasihar da mahaifiyarta ke yi mata mai hade da dan fada da hannunka mai sanda uwa uba da fada a kan kuka ya sakata sake tsurewa, nasiha take yi mata na zaman aure da nuna mahinmancin hakuri da jadada mata babu wace bata hakuri a gidanta ko y'ar waye, da sake sheda mata cewa kowa da irin tasa jarabawar zaman gidan miji, idan taka ta sameka ba haukacewa zaka yi ba, ba kum da garaje zaka taketa ba, sai da addu'a da hakuri da kuma biyaya
A dole daga karshe su dukansu suka yi kukan, kiraye kirayen sallar isha'i ya saka Mama Hasana umartarta yin sallah sannan ta nuna mata cewa ta yiwa mijinta biyaya , ta mike ta fice a dakin ta yi dakin da aka sauketa tana mai zubar da hawayen da kowace uwa ke yi yayin rabuwa da yarta

Ta jima saman salayar bayan ta gama sallar tana hawaye , zuciyarta ta karye sosai walahi, shikenan yanzun sunnanta matar aure? Shikenan yanzu matar KAN GIWA ce ita? Wayo Allah yaya zata yi da tsoronsa? Yaya zata yi ne da shi a matsayin miji? Miji fa? Miji?

"Nuriyah kuka kike yi?" Muryar Hajia ta sakata dagowa da sauri tana kallonta
Da sauri kuma sai ta girgiza kanta, hakan ya sa Hajia sakar mata murmushi tana fadin" Taso mu tafi"

NURIYAH ta ce" Hajia ins?"

Hajia ta ce" Dakinki Mana Balaraba taso maza taso bana sonki da wannan sakin jikin fa"

NURIYAH kam bata da ta cewa, a hankali take tafe a lokacin da suka sauka daga cikin galeliyar motar da ta kawosu daidai kofar part din da yake nata a yau

A hankali Murjanatu ke dan sake fefesa mata turaren da Hajia ta bata , Hajiar kuwa tana addu'a a bayane bayan ta umarceta da ta yi itama sannan suka tura kofar falon ta madubi suka shiga da salama a bakinsu

Turus Hajia ta yi ganninsa zaune saman kujerar ya yi wani freshhh da shi tare da bakon da ya yi sunna zantawa

Bakon ke yi masu marhaba, shi kuma ya kafe su da ido

Da murmushi hajia ta amsa gaisuwar bakon da yake aboki a wajensa mai mutunci magidanci shima da yake da ya'ya sosai da matansa biyu Aisha da Rukaya

Ciki suka wuce da ita , shi kuma ya rakasu da kallo har Murjanatu ta bacewa ganninsa ita dake baya aka rufo dakin sannan ya dan cire idannuwansa yana dan tunanin dama nan din zata dawo da zama tun yau? Shi ai a tunaninsa an gyara mata nan ne idan ta yi ra'ayin kwana ta zo ta kwana, idan bata so ta yi zamanta a bangaren Hajiar

Abokinsa kam tunda ya ga an shigo da amaryar ya mike yana masa salama, da fatan alkhairi da addu'ar zama lafiya, harda y'ar tsokanar da yakan masa lokaci zuwa lokaci ya masa rakiya har wajen motarsa ya tafi sannan ya juyo ya dawo baangaren hannunsa daya cikin aljihun wandon shadar da bai cire ba ya bude ya shigo

Yana shigowa Hajia ta mike tana sake riko hannun Baby dake magiyar a barta a nan ta fara turata tana kallonsa ta tabe baki ta ce" Zama ka nemeni ne dan nema"

Murmushi kawai yake yi yana kallonta har suka fice bai ce mata komai ba, tunda aka sanar masa za'a aura masa NURIYAH ne ba waninsa ba Hajia ke nemansa da fitina
Sunna tafia ya sake zubawa kofar ido
A hankali ya nufi hanyar dakin da dan murmushin dake saman lebensa ya kama hndl din ya tura kofar

Turus ya yi a lokacin da ya hangeta saman bed kanta a sade saman hannunta tanaa hawaye, watau tana kuka kasa kasa sosai
Mamaki ne ya kama shi yana sake kallonta, ba zai manta ba yakan ji a wahen maza cewa sun yi rarashin matarsu a darensu na farko tana kukan rabuwa da iyayenta, yakan yi murmushi kawai dan shi dai gani yake yi wani munafurci ne, meye na kukan a ciki! Matan da ya aura babu wace ta zo masa da kuka, da zumudi ake tarbo shi a masa barka da farin cikin samun cikar burin malakar junna, Nadiya sarkin romance itacema ta fara kissing dinsa a ranar , da abu ya girmama kuma ta nuna aa

A hankali ya karasa da niyar ya dagota ya hannata kukan, sannan ya fada mata idan tsoron zama da shi take ji ta kwontar da hankalinta, ba zai zauna da ita dan ya taba jikinta a yanzu ba, zai zauna da ita ya raineta, sai ya haukata zuciyar y'ar nan, irin yadda ta hanna masa sukuni itama sai ya hanna mata

A hankali ya daka hannayensa biyu yana hawa saman royal bed din dake girke kan kafafuwansa dan madaidaici ba wani rangameme ba tsarin kalar soyaya dai ya dagota gaba dayanta a hankali yana furta" Hi prncsss why are you crying? Hey Nuriy dubeni menene abin kuka ? Bakya so aka yi maki ko? Bakya so?"

A hankali yake kara matse mata waje da zuciy daya dan ya hanna mata kukan da take yi har ya zamto ta dago din ya cire nikaf dinta gaba daya a fuskarta ya zubawa fuskarta ido yana kallonta a hankali ya kai lebunnansa wajen goshinta ya mana mata sansanyan kisss, hakan ya sakashi lalubo kanshin dake wajen ya lumshe idannuwansa yana jin yadda zuciyarsa ke dan bugawa

A hankali ya ci gaba da sanyayar mata da zuciya, ta hanyar nuna mata menene na kuka? Ta daina kuka abinda a gida daya suke da su Hajiar? Ta daina kuka ta bude fuskarta su tafi dining su ci abinci ta dawo ta kwonta ta yi barcinta, barci take ji ko? Ta cire hijab din jikinta ta kwontar da hankalinta shi babu abinda zai yi mata ai bata manta maganar da ya fada mata ba ko? To yana kan bakansa shi babu abinda zai yi mata............
Da wannan ya sabule mata hijabin jikinta, ya sake sakata a jikinsa da dabi'a irin tasa ta consoling dinta, bai san ruwa ya balawa kansa ba har sai da ya fara ficewa a hayacinsa a hankali ya fara kai hancinsa wajen wuyanta yana sake shakar kanshin da wuyan nata yake yi
Sake ji ya yi a lokacin baban bukatarsa shine ya lashi dokin wuyanta, a hankali ya shiga sinsinarta yana ta so ya sake jadada mata cewa koda zai tabata sai nan da shekaru takwas ko tara in sha Allah, sai dai da zarar ya buda bakin nasa harshensa ke yawo a wuyanta a hankali a kuma sanyaye

Da sauri ta dago fuskarta jin yamyamtun ya mata yawa a wuyanta da kuma irin likuwa da yake sake yi da jikinta ta zubawa fuskarsa ido
Idannuwansa a lumshe suke gaba dayansu, fuskarsa ta fara yin jajajir bama kamar kumatunsa, makwaloton wuyansa kuwa sai sama da kasa yake yi da sauri da sauri kamar yana son hafiyar yawu ne ya kasa

A hankali ta so yin baya daga jikinsa, ya saka hannunsa da sauri ya janyota ya maneta da kirjinsa yana so ya bude idannuwansa tarr ya kaza sai ta kasa yake kallon fuskarta

A hankali ya riko bayan keyarta yana sake kallonta lafin yake hade bakinsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login