Showing 57001 words to 60000 words out of 124070 words

Chapter 20 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

341

irin kukan da ya fi karfin zuciyarta ya bale mata wanda ta rasa shi kuma na saka ukun menene? Shin na tausayin irin kukan da Baby ta fara ne, ko na tausayin baiwar Allahn nan ne? Ko kuma kawai shishigi ne irin nata yau zata yiwa kanta sanadiyar rasa aikinta, dan wani ganganci haihuwa da damina bata idasa sannin yau da ita da mahaukaciya mai doke doke marabinsu kalilan ne sai da ta matsewa mutumen da ko kakarsa zata masa magana take masa da rarashi waje ta aniya dora kanta a gefen damtsen hannunsa da bakinta mai jaye jaye mai saka bawa a uku ta bude bakinta ita NURIYAH jikar baba marigayiya ta kawo hannunta na hagu ta dora a saman kafarsa da yake talabe da baby ya juya zai ba baban sojan da ya karaso da gudu umarnin a yi ciki wajen likita da mamansu maganarsa ta fauke diffff ya juyo a birkice sakamakon shima dokawar da zuciyarsa ta yi a lokacin da dumin hawayenta suka sauka a damtsen hannunsa da muryarta mai duka a kunne tamkar ta zazafar mawakiya ta aniya saka kanta a uku ta ce" *Wayo mamanmu*"




Yanzu fisabililahi NURIYAH, a gaban matansa, a gaban iyayensa, a gabansa shi kansa, kuncewar kan naki ta ki samuwa sai yanzu, kika rukunkume dan mutane kika cewa mamansa mamanki? Iyi yanzu idan suka maki dukan mutuwa fa? Kai jama'a=??=??=??=??=??=?? abu idan zai sameka baya maka shawara>?#?



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
3?? 8??




A hankali ya sauke idannuwansa a saman haannayenta, zuwa saman kanta dake kife a damtsen nasa hannun

Kamar shi kadai take yiwa ihu a kunne, ko yace kamar wace take da wani abu a muryarta da ya saka shi a matsanancin tashin hankalin ihun kukanta ya saka shi saurin saka hannun ya dora saman nata da niyar warcewa ya hankadata ko zai ji saukin ihun da take masa a kunne , sai dai yana dorawar sai da ya kusan rabin minti a haka yaa jimke bayan hannun nata kafin yake saki ya dago yana kallon mutanen dake kansa yana ji gaba daya shi aka tararwa ana yiwa hayaniya bayan ba shune ya summa ba , Mama ce ta summa

Kowa nasa maganar yake yi, kuma gaba daya shi suke aikowa da tasu tambayoyin
Pilot fin da ya karaso da wata jaka yar sumulmula mai kyau ya ajiye cikin nutsuwa ya bude ya fitar da abin bukata ya karaso sosai kusansu a nutse ya ce" Ku dan bata iska haka kun matse mata waje sosai bayan mutun a irin conditions dinta yana da bukattar space ko yayane,..............."

Kamar jira yake ya yi magana , sai ya samu kansa da kallonsa a hankali ya ce" Kai din likita ne dama BASHIR?"

Pilot din ya yi murmushi yana fadin" Ba cen cen ba sir, aman du wani ma'aikacin jirgi akan basu formation na abubuwa masu mahinmanci..........."

Yana magana ne yana kallon yadda hajia ke bambare Murjanatu daga jikin uwar har abun ya isheta ta ce" Na ga annabi idan na yi hali na gari, ke Murjanatu ki saketa haka mana sai ta shige duniyar kusan mutuwa dan ubanki da jikana a cikinta? Saketa mana je kusan y'ar uwarki ku yi ta kukan, ni kam na ga sangartatu yan nema a wajen nan!"

Murmushi ya yi bayan ya ama hada maganin da zai mata anfani da shi a nutse ya kalli Aba da shine ya fi kowa zama a kasa sosai yana rike da ita a jikinsa, Kan giwa kuwa na tsugune ne a gefensa, Hajia na ta salati tana yawo uwa kazar da ta gama kyankyasa, kaka kuwa yana tsaye da carbinsa yana tofa adu'a a kanta , shi kam rikicewarsa idan ya yi sai kawai ya kama salati abinsa komai girmanta masha Allah, a nutse ya yi mata anfani da maganin bayan ya gama gane summa ce sannan ya dan saurara yana kallonta dan gannin idan ta motsa ya ce" Ana koya mana harda amsar haihuwa domin wata haihuwar na samuwa ne ana tsaka da tafia a sararin samaniya, ana koya mana abubuwa da yawa wa'inda a kalla mukan dauki shekara biyu ko sama muna karatun hakan, kuma akan bamu takardar shedar mu likitoci ne duda idan da likitan a waje bama aiwatar da aikin hakan, idan ya kasance ne daga mu sai mu to fa dole zamu ajiye aikin jirgi mu riki na likitan ,......"

Motsawar da ta yi lokaci daya hadi da jan wani gwauron numfashi ya saka shi da sauri matsawa a tausashe ya shiga fada mata magana kamar haka" Ma'am, ki yi a hankali, kar ki manta conditions dinki, halin summa ko baka dauke da komai ba'a so ka firgice da yawa, ki yi hakuri a kamaki a hankali mu karasa gida na auna hawan jinninki da komai, ki samu ki ci abinci ki huta kin ji?"

A hankali Aba ke shafa saman kanta, muryarsa a matukar raunane ya ce" Maman Auta, ki daina shashekar alamun kukan nan haka mana kin ji? Kin ga ai mun zo, ko menene yanzun ai zamu ji kin ji? Ki rufa mana asiri ki daina daga hankalinki haka mana"

Hajia ta zagayo bayan ta salami matan Kan Giwa ta raka su da hararan jin haushi dan sun karaso din aman an rasa wace zata karasa ta yi sannu ko tambayar kirki, asalima a tsayen da suke tambayar da suka yi shin wani abu ya sameta a cen ne? Kana ganninsu zaka fahimci sunna cikin hali ne na tsoro ba na jimami ba, shine ita kuma ta kasa hakuri ta ce su je bamgarensu su huta mutane za'a rarage idan sun huta sai su je su mata sannu

Ai kam suka wuce abinsu, dan a cikinsu babu wace bata tsoron matsawa kar aje matar baban mijin nasu mutuwa ce ta yi a tada su tsaye rungumar gawa, to ko wata rashin lafiya ce ta jajibo ta yaba masu sunna tatalin kuruciyarsu, shi yasa suka gabatar da aikin nan da ankarewa dan idan ta same su ko shi mijin nasu zai gaji ne da wahala ya kamo wasu


Tana zuwa ta kamawa Aba tana fadin" Ni kam abin nan yanzun da kaina zan shiga gari, kwararo kwararo, lungu lungu, sako sako na nemo yar uwar nan taki, haba Hasana wannan ai sai ki rikita mutun"

Shi kam Kan GIWA sai da suka gama mikewa ya sauke wata irin ajiyar zuciya ya sake bin hannun mahaifinsa da kallo, wanda ya ci gaba da dan shafa bayan matarsa hakan na nuni da yana matukar jin ciwonta a cen kadan zuciyarsa , yana jin ciwon sosai bashi da yadda zai yi ne yake bata kula ta hanyar dan taping din bayanta,
Irin yadda itama ta langwabe a jikinsa hakan na nufin bata da wajen da ta fi jin dadin kasancewa ko a hali na rashin lafiya sama da jikinsa ba

Iska mai dan zafi ya furzar a hankali ya dora hannunsa saman damtsen hannunsa na hagu da yake ji ya masa nauyi, sai kuma ya dauke yana harhade girarakinsa yana kai dubansa da kakausan kallo kan shashashun yaren nan da har yanzu basu gama dan kokensu na jin dadin duniya ba sun riki hannun Kaka sunna tafe sunna rangaji

Kai ya gyada yana dantse lebensa yana ayana' Tabas sai na yi maganinku, harda ke auta sai na yi maganinki, irin yadda kuka rikita mana waje da koke koke sai na yi maganinku, ku da mararsa nutsuwa ko? Mutun na summe ku kunna masa ihun wane tashi? Zaku yi bayani ne mu je mu rakata ku fito ku fada min waye yake kunkunce kusoshin kawunnanku ne kulun maimakun ya daure su!'

A falo ta ja tunga, a falo ta nuna tana so ta zauna
Du irin yadda Aba ya kiya abin ya gagara domin kuka ta aniya neman fashe masu da shi, wanda ya ba Su Murjanatu da Kan Giwa mamaki, harma suka shiga tunanin to ko cikin ke sakata haka ne?

Da sauri Nuriyah ta juya ta yi cen hanyar kicin dan ta tarbo su ta tabata an turo kayan saukarsu ta taya su rabawa

Da ido ta rakata sannan ta juyo wajen Hajia tana fadin" Uma, walahi walahi wannan din jinnin Husainata ce, harta tafiyarsu iri daya ce"

Hajia ta kama baki tana fadin" Yanzun ba zaki bari ki samu nutsuwa kafin a yi maganar nan ba y'ar nan?, Kuma da hijabinta ta yaya zaki gane tafiyar yar uwarki a tare da ita? Kin ce bata kama da yar uwarki aman kuma kina cewa jinninta ce"

Muryarta na dan rawa ta ce" Uma, kamanin LAWALI nake ganni a jikinta, motsinta kuma na Husainata ne, Uma na Usainata ne, kin ga bara na kirawota ta core hijab din ki ga tafiyar tata, kin ga yadda Husainata take tafia haka nake yi nima, muna bada karfin tafiyarmu a kan kafarmu ta dama kamar muna dan dingisawa bayan ba dingishi muke yi ba yannayin halitarmu ne ya haifar mana da haka , Uma jinni zai yi karya kuwa? Abinda nake ji a kanta idan hasashe ne to fa lalle yarinyar nan nada baiwa Uma"

Ajiyar zuciya Hajia ta sauke zata kuma yin magana Elhaji ya yi dan gyaran murya yana fadin" Tabas babu abinda ke kasara bawa irin tunani, tunani shine silar komai na koma bayan bawa, tunani har furfurar wuri yake haifarwa da tsufa da ciwace ciwace, kuma tunanin dan uwa baban tunani ne mai iya haifarwa da bawa tashin hankali, Murjana inaga a taimaka a bata nutsuwa a kan tunaninta a kan yarinyar, domin ta saka abin a ranta sosai"

KAN GIWA da murjanatu kallonau dai suke, shi Kan GIWA gaba daya ya rasa da wa ake maganar , ita kuma Murjanatu wace aka ce a tsaya ta dawo din ta fi tunanin ko wace, da kuma son gane me maganar take nufi

A sanyayenta ta dawo da salamarta kasa kasa sosai sannan cikin nutsuwa sannnan ta nemi wajen da zata ajiye baban abin turawar da aka shako da kayayakin aabinci

Turus ta yi sakamakon kiranta da hajia ta yi da wata murya mai sanyin da ta saka gabanta faduwa
Sai a lokaciana ta kuka gaba daya tamkar ita ake kallo, sai dai ta kawar da hakan a ranta ta karasa wajen Hajiar ta duka har kasa tana amsawa

A hankali Hajia ta ce" NURIYAH,, Jikata dan Allah zan maki wata tambaya mai matukar mahinmanci, ki yi kokari ki bani amsa gamsashiya sannan ki fada min gaskiya a cikin amsarki , ko zaki iya yi min haka?"

Gabanta ne ya yanke ya fadi, a hankali ta sake kai gwuiwoyinta kasa sosai tana ta ambaton Allah a kasan zuciyarta, tsoronta daya kar an fadawa Hajia wace ita dan kakarta ta rasu da ciwo da ake gudunta itama hajia gudun nata zata yi? A hankali ta kai dubanta kan Murjanatu tana mai yin yannayi na ta ceceta, sai dai irin kallon da ta ga Murjanatun na yi mata ya sake sanyayar mata da gwuiwa

A nutse Hajia ya saka hannunta tana juyo fuskarta ta ce" Da farko ki cirw hijab din nan ki yi tafia zuwa gaban mamanku ki dawo nan kin ji yarinyata?, Tashi mu gani"

Wani yawun ta sake hadiyewa jikinta na rawa hakama hannunta ta saka ta cire hijab din da shine rufin asirin rigar jikinta, domin rigar daga wajen hannuwa ne kawai ta saki wajen duwawunta ta mugun rikewa kuma ta roba ce, shi yasa suka sake zaunawa das a muhalinsu suke barbarbar na neman fitina

A hankali ta iya mikewa hakan ya sa dan ribom din dake daure da gashin kanta ya saku gaba daya gashin nata ya baje a gadon bayanta
A hankali ta juya ta shiga tafiyar da kusan kowa kafar tata da take ba karfi ya fi kurawa ido

A hankali Kan Giwa ya sake maida dubansa a kanta a lokacin da ta kusa karasawa gaban maman ta zube kasa tana kokarin rike kanta ta fashe da kukan tsoron dake zuciyarta tana fadin" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, walahi Hajia idan an kawo maki rahoton cutar HIV ce ta kashe kakata bata sameta ta hanyar banza ba, Kuma ta bani tarbiya daidai gwargwadon iyawarta, ta rikeni tamkar jinninta, ta bani soyaya fiye da tunanin bawa, du halin da muke ciki kuwa na nemi na kaina ne ta hanyar halal, Hajia a kulun Baba kan min nasiha cewa neman kudi ba hauka bane, na na da gumina, na saka riba komai kankantarta alkhairina ne, na je lungu lungu, sako sako har wankin hula na yi hajia, aman ban taba kauce hanya ba, har ta koma ga ubangijinta kuma a wajentama ban ga aiki na lalata ba, dan Allah kar a koreni"

"NURIYAH" Mama ta fada tana sake kureta da kallo
Sak rikicewa irin ta y'ar uwarta uwa uba a yau ga abu sak na yar uwarta a jikin yarinyar watau gashin kanta

A sanyaye ta ce" Ina Husaina ne NURIYAH?*

NURIYAH ta zubawa Mama ido da hali na rashin gane maganarta, hakan ya sa Mama kallon Murjanatu fake sake riketa tana son tausarta kar ta yi kuka a hankali ta ce" Autana, ki barni na ji dan Allah kin ji? Autana kin san a nan muka tafi muka barya, shikenan bamu sake samun labarinta ba, ba ita din ba LAWALIN, NURIYAH dan Allah ke din Y'ar wanene? Wanda ya kawo ki dan uwanki ne? Iyayenku daya ne? Ina mamanki take ne? Ina mahaifinki yake ne? Zo nan yarinyata, zo ki fada min mana kin ji? Zo ki sanyayar min da zuciyata ki saka min nutsuwar tunanina, zo kin ji?"

Hannun Nata NURIYAH ke kallo, da sauri ta juya wajen Hajia, ta waiga wajen Aba, da kaka , da wani saurin ta juya wajen da KAN GIWA ke zaune, a lokacin da ta saka Idannuwanta cikin nasa sai ta samu da idannuwan nata da nutsewa a cikin nasa har na yan sekwani, da wani karfin ikon Allahn ta cire idannuwanta ta sake sakasu a na Mama

Muryarta na rawa ta ce" Mama, kin san mutumen da aka ce shine mahaifina ne?, Ina nufin LAWALI?"

Sai da Mama ta dora hannunta a saman zuciyarta kafin ta fashe da kuka tama silalowa kasa , da rarafe ta karasa ta janyo NURIYAH da karfi ta sakata a jikinta , da muryar kukan take fadin" Uma kin gani ko? Wannan din jinina ce, ni ina ganninta na ji karfin kaunarta a zuciyata ta wuce ta tausayi ko shaawar tarbiyarta, ita din jinina ce Uma, Uma me ya kawo jinina aikatau? Me ya kawota aikatau? Shin jarin da Aba ya ba Lawali karewa ya yi kuka shiga halin rayuwar da har ta kai Husaina barinki da yarintarki kika shiga aikatau da neman na kai lungu lungu kwararo kwararo bayan mace kike? Shin Husainar bata da hankali ne da ta kasa hanna haka ko har yanzu tana nan da sanyin halin nan nata da kuma makauniyar kaunar wannan miji nata ne?"

NURIYAH da sai yanzu take ta dauko kan maganar gaba daya tsigar jikinta ta tashi, a hankali ta rike fuskar Hasana tana kallonta, muryarta a sanyaye cen cikin cikinta ta ce" Mamah, ke din Y'ar uwar mahaifiyata ce hala?"

Kai Maman ke gyadawa da sauri murmushi na son wanzuwa a saman fuskarta, sai dai lokaci daya ya dauke a lokacin da ta kuma cewa" To ita maman tawa kuma fa tana ina? Ko kunna tare ne?"

Muryarta na son birkicewa ta budi baki zata yi magana Hajia da ta ji tana jin tsoron abin ta ce" Hasana, me zai hanna ku huta haka? Idan ya so sai a yi maganar daga baya?"

Mama ta Kalli Hajia, ta sake kallon NURIYAH, bakinta na dan rawa ta ce" baki san inda take bane Maman naki?"

Itama a yanzun ta gama cire ran gannin mahaifiya jin tunanin da take yi cewa ko mamanta na tare da danginta ne ba haka ba, a sanyaye ta ce" Ni ai ban taba ganninta bama, banma santa ba, baba dai ta ce min rabonta da ita ta bata ni tace ta kular mata da ni amana, bayanshi zuwanta ya fi a irga shi Lawalin na korarta, karshema sai ta hakura domin ya saka polisai sun kamata sun mata duka kan barauniya ce, sai ta hakura take binta da adu'a, kumama nika na je gidan sau biyu matar da na samu dai gaskiya inaga ba ita bace domin zazagina ta yi ta sa shima ya zazageni suka koreni, kuma da na je ranar rasuwar Babama korata ya yi ni kuma nace na hakura da nemansa a duniya , nace ita kuma maman tawa ta yiwu tana wajen danginta, kuma baku san inda take ba ko ta rasun da gaske kamar yadda ya fada?"

Idannuwansa ya rintse da karfi sakamakon wani irin abu mai matukar girma da ya daki zuciyarsa na tausayin dan Adam da bai taba jin irinsa ba a duniya

A hankali ya bude idannuwansa da sukai masa jajajir yana ji muryayoyin mata hudun dake falon sunna masu fashewa da kuka, maza biyun kuwa sunna masu basu hakuri muryoyinsu na nuni da summa dan sunna maza ne suka kasa fashewa da kukan

Muryar mama cikin kuka ta sake talabo Nuriyah tana fadin"





>?p?>?p?>?p?=??=?? Ai na fada maku idan da comment zamu dan tafiya fa



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
3?? 9??

Muryar Mama cikin kuka ta sake talabo fuskar Nuriyah da ta yi jajajir tana fadin " Nuriyah, shi Lawalin ne ya zama azalumi marar tsoron Allah har haka? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une, tsoro nake ji a cen kasan zuciyata, a lokacin da aka yi kiran mahaifina aka ce masa maza mu bar gidanmu da dukiyarmu mu gudu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login