Showing 93001 words to 96000 words out of 124070 words

Chapter 32 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

329

yana dan cirata daga kasa yana kallonta da kyau ya ce" Ki kula da furucinki a cikin ahalina, Hausawa muke akoy kunya a dabi'unmu da furucinmi!, Sannan ki kiyayi titsiyeni dan ni ba yaronki bane! Nadia kin isama ki hannani SONTA? Babu wanda ya isa ya hannani sonta!, Da kine fadin abinda ta fi ki shi da kuwa ki auna ki gani da kanki! "

Daga nan ya jata da karfi har wajen motarsa da aka zo shima daukansa ya bude ya turata ciki ya basu damar su tafi domin ba zai iya shiga motar nan ya zauna ba , komai na iya faruwa! Ya kasa yarda cewa yau shine matarsa ta wulakanta haka! To ita in baa garaje ba bata kula ta ga shima baya yiwa lamarin yarinyar garaje ba? Lalle tana son saka shi take dokarsa da kansa, domin ba zai iya hadiye wani abin ba idan ya hadiye wanin! Ya kasa barin kanninsa a gari dan ya kula sunna doguwar hira da dariyama bale wani dan iska? (=?.?)


__________________________________

"Idan kuwa kika ce haka zaki yi, lalle kina tare da wahala domin shi din nan da kansa mutun ne mai yawan cusawa mace tashin hankali idan baki iya kwatar kanki ba yaya zaki zauna a tsakaninsu?" Hajia ta fada da zafi zafi tana gannin yadda Nuriya ta wani lange ita mai tsoron kar a daketa

Daga Nuriyar har Murjanatu kallonta suke sunna kuma kallon motar dan gannin ko su hudu ne a wajen ba su uku ba? Ma'ana da wata daban hajaju makatu ke magana?


Hajia ta sake kureta da kallo ta ce"










Asalamu alaikum jama'a



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
5?? 4??


Hajia ta sake kureta da kallo tana ta tunanin abinda zata fadawa yarinyar dan tana son gane wani abin a tatare da ita komai kankantarsa, dan haka ta dan kama baki da salon wayo irin na wanda ya rigayeka zuwa duniya koda da awa daya ne ta ce" Au na zata saurayinki ne shi din Mai gidan nawa?"

Sai da Nuriyah ta nemi sarkewa da yawun bakinta, lokaci daya ta dago ta yi firinke firinke da ita, a zabure ta ce" Ni kuma?"

Hajia ta sake kallonta ta ce" Yau na ga abubuwa da yawa, aa ni"

Nuriyah ta shiga yarfe hannayenta ta ce" Ba shi bane ba fa saurayin nawa ko baby? Baby fadawa Hajia dan Allah, Hajia matarsa ce take cewa wai na fita a hanyarsa sannan na fada mata me na fada masa ya min murmushi, itama wani tunanin take yi marar kyau walahi bayanshi babu komai, Hajia Allah na tuba wannan abin ai sam ba kyau"

Hajia ta kawar da kanta gannin kuri din da Auta ta yi mata tana ta son sai ta ganota ta yatsina bakinta ta ce" Ah ni ai na zatama saurayinki ne, to ku dai kuka jiyo share hawayen nan naki maza ki tarbi kakaninki ko ganninsu baki yi ba har sun shiga ciki, ki daina yiwa kowa kuka kinga wannan kara da zannin matar tasa? Idan ta kuma nuna maki yatsa kama ki cije yatsar ko ko sharara mata mari, tsoron mari ne da su walahi basa son abinda zai taba kyan fuskarsu, ko ki kwashi kafafuwan fitsarar ki yar a kas mu ga ta lalata kin ji balarabiyata?"

Irin yadda take maganar tana tayata share hawayen ya sakata sauke ajiyar zuciya da dauka cewa ai kawai tunanin hakan da hajiar take ne ya sakata fadin haka, aman yanzu da ta bayanar mata gaskiya ta bar maganar
Murjanatu kuwa gaba daya ta kasa cire abin a ranta, ta san wace kakarta ta kuma san waye yayanta, ta tabata idan har babu wani abin dake damun zuciyar dan uwanta a kan Nuriyah ba zai taba nuna ya san tana raye a duniya bama bale har ya ringa babakere a kan lamarinta, karara ta ringa gannin hakurinsa a kan wajen da baya hakuri ko kanta ne, sai ta rintse ido dan jin ihunsa a kan wajen da yake iya yin mahaukacin ihun fada sai ta ga yana rarashi, kai koda jikinta cike yake kunnaye ba zata aminta da wani zaurancen ba, a gidansu ake mata kallon yar baby aman ita ein kimemiyar malamar soyaya ce a makaranta

Nuriyah ta fara fita a motar, Murjanatu ta bi bayanta, sai hajia da ta sauko a hankali sanadiyar kafarta

Har sun dan fara takawa muryar Hajia ta saka su juyowa a tare a lokacin da Hajia ta ce" NURIYAH, kuma kin tabata bakya jin soyayarsa a ranki?"

Takwaf takwaf ta kuma yi da fuska da nufin zata sake wata rikicewar Hajia ta zarro mata ido ta ce" Malama ki koyi bada amsa da amsa ba wani kuka ba, dan walahi haukataki zasu yi idan suka gane shashasha ce ke ta wannan fannin!"

Tana gama fada ta karaso ta wuce su hankalinta kwonce da carbinta a hannunta ta nufi bangarenta

Murjanatu ta juyo tana kallon NURIYAH wace ta kurawa kasa ido

A hankali ta ce" Kina son shi?"

Nuriyah ta kalleta a firgice ta ce" Kema tambayar da zaki yi min Kennan? Me ya hadani da soyayar uban gidana? Mema ya kawoni ya kawo maganat nan ne? Yaya zaku ringa abubuwan da basu dace ba sam? Wani dalili kuka fuskanta ya sa kuke irin wannan gwaramar? Kun fuskanci wani rawar kai a tatare da ni da ya shafe shi wanda ya dara mutuntashi da kare dokokinsa ne da zan ringa fuskantar barazanar kwonciyar hankalina? Dan girman Allah ku rufa min asiri ku daina min irin haka, ban san wane zan duba ba, ban kuma san wane zan yiwa jayaya ba.........babu wannan maganar tsakanina da shi"

"Dan bai isa ki so shi ba? Ko dan baya birgeki? Wannan amsar kawai nake son ji idan kina yiwa girman Allah kar ki kawo min maganar fin karfi, maganar shi uban gidanki da waye waye, juste ki bani amsa a kan haka"

Dukkan da zuciyarta ke yi ya sakata jin inama bata fito rakiyar nan ba? Wani irin tsoron amsar dake bakinta take ji, a hankali ta sake kureta da ido, sai kuma ta ja numfashi ta juya ta nufi ciki jikinta tamkar babu lakkah, ta rasa amsar da zata ba Murjanatu, sam bata da amsa, maganar da take son furta mata karya ce ba gaskiya ba, shi yasa ta yi shiru da ta tafka karya ta samu zunubi gwara ta kama bakinta da mutuncinta

Murmushi Murjanatu ta yi tana rakaya da kallo a hankali tace" Allah ne gatanki, kuma shi ya saka mahaukacin sonki a zuciyar uban gidanki, fatana makahon so din nan ya zamto alkhairi a gareku da mu baki daya"


A lokacin d ta shiga falo, iyayenta sun gama kukan nasu sun dawo labarin bayan gamo

Salamarta ta saka suka yi shiru suka juyo dukkansu suka zuba mata ido
A hankali ta dan ja ta tsaya ta zubawa fuskokin tsofafi biyun da ba Hajia da Elhajin su Murnatu ido ba,
Namijin baki ne ba cen ba, macen kuwa fara ce cencen, daga inda take tsaye ta gane namijin bashi da lafiyama domin yannayinsa a bayane yake ba a boye ba

Idannuwan da suka zuba mata su dukkansu basu yi mata magana ba ya sakata sake jin dari dari a zuciyarta sannan ta nemi cire dubanta a kansu baki daya

A hankali Husai??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????na ta sake rike hannun mahaifinta kasa kasa sosai ta ce" Ita din da kanta da ya haifa bai barta ba, kamaninta da shi kar ya sa ku ka sa nuna mata soyayar da kuke yi mata a zuciyarku, ta rayu ne da neman mafaka, ta rayu da ciwonsa a zuciyarta, wace kuka hadasu dab ta kula da ita ta rasu aman ya koreta bai dubeta ya tausayawa maraici da kasancewarta mace ba, Allah ne ya kawota gidan ban a matsayin yar aiki har na zo na ganta......"

Da kyar yake yin magana, domin bakinsa da ya samu matsala sakamakon hawan jinni, shi yasa idan zai fadi abu yakan dan jima kafin ya ciro maganar daga bakinsa
A hankali ya iya furta" Aikatau?"

Kai ta gyada tana kallonsu, a hankali ta ringa gannin tausayi da tarin jinkai a fuskokinsu, ta sake rike hannayensu da kyau ta ce" Mama, bata san dadin iyaye ba, Lawali har yar da ya haifa ya wulakanta, kuma jinninmu ce, jikarku ce ta farko daya kwal da Allah ya nuna maku, kar ku hukuntata da laifin mahaifinta, please"

Mahaifiyarsu ta lumshe idannuwanta jawayen dake ciki suka samu damar fitowa a hankali ta ce" wai yanzu wannan din tamu ce? Kin tabata wannan fine lady din jikata ce? Ya Allah......" Sai kuma ta juyo tana dago hannayenta a hankali ta furta" zo gareni zo zo"

NURIYAH ta saki ajiyar zuciya a hankali ta ringa tahowa har ta karaso ta zuba gwuiwoyinta a kasa ta saka hannayenta cikin hannayen tsohuwar masu dauke da dumi tana kallon fuskarta sai kuma ta dora kanta a saman cinyarta a hankali tana lumshe idannuwanta

Itana shafa kanta take yi bayan ta cire mata dan kwalinta a hankali ta janyo hannun mijinta dake murmushi ta dora a saman kan Nuriyah kasa kasa sosai ta ce" Jikarmu ce, ka ga kishiyata kuwa? Ba'a taba yaba kishiya ba aman ni zan yaba, Masha Allahu lakuwata ila billah"

Murmushi ya wadaci fuskarsa, a lokacin ne Murjanatu ta karaso itama ta karasa kusa da su sosai da fara'ar da ta saba wanzuwa a fuskarta da ranta idan sau dubu zata gansu, ba zata taba yin kewa ta kakani ba in dai sunna cikin rayayu, su din sun mayar da ita itama tamkar jikarsu ta jinninsu, shi yasa da take kiran mamanta da Mama har bata so a tambayeta ita ta haifeta? Shi yasa take rayuwarta a cen tare da ita hankali kwonce domin ba'a zama da ita da aikata goshi ko dan a faranta ran mahaifinta, domin Allah aka amsheta a jikar kuma aka rike da hannu bibiyu
Yana murmushin da kyar ya iya furta" Masha Allah, Alhamdulilah......Allah ya yi maku albarka"

Sai a lokacin Mama Hasana ta samu wani boyayan sanyi ya ziyarceta a zuciyarta, hamdallah ta ringa yiwa ubangiji da iyayen nata suka yarda suka amshi yarta kwalin kwal a duniya, tana yiwa gidan nan karra har wace ta wuce kima, domin tunda ta shigo shi ta gane masu mutunci ne da suka san menene karar

Murjanatu na kallon Hajiar su Mamanta ta ce" Kuka kika yi ko?"

Hajiar ta girgiza kai da dan sauri tana turo baki, sai kuma ta gala mata harrara tana fadin" Ke an yi kukan"
Daria suka saka s hankali ta kama hannunta da take miko mata suka gaisa sunna kallon junna da kauna Murjanatu ta ce" i miss you"

Hajia dake dawowa daga sama domin du waje aka basu dan an kula sun ki taba komai ta kai zaune a hankali tana fadin" ba wani tunda ta zo ta samu Nuriyah bata yi maganarki ba, takwara ai yar cin amana ce"

Nanfa hira ta barke ta mutunci da zumunci da kuyaye harshe tsakanin sirikan, har sai da mazan suka shigo daga sallar magariba bayan suma sun gama tasu sallar kakan Nuriyah ya karaso da kyar da sandunnansa ya zauna a lokacin harda Kan Giwa wanda bai shigo gidan ba kwata kwata sai yanzun, a nan suka shiga nuna alamun zasu tafi

Da sauri Husaina ta kalli mahaifiyarta, wace ta sakar mata murmushi ta cire kanta a kanta, sai kuma ta kalli wajen Hajia da itama lokaci daya hirar da take yi a sake ta nemi bacewa

Jiki a sanyaye Hajia ta ce" Na zata wannan karron a nan zaku zauna? Me yasa bakwa son zama a nan ne? Na fada maku ni y'ata ce husaina ba wata sarakuwa, me zai hanna ku yi zamanku nan ga mutane zai fi maku nutsuwa ai?"

Murmushi kawai Mahaifin su Hasana ya yi, shi kam ba da shi ba tarewa a gidan siriki, ba zai taba iyawa ba, yayama zai iya rintsawa? Shi kam fulatu ba zai barshi wannan aiki ba sam,
Matarsa ce ta sasauta zamanta , ita kanta zata so daren nan su rabashi da yayanta a gefenta sunna zanta rayuwa, bata taba sannin da dan sauran kwarinta ba sai yau da ta daga kafarta da hanzari ta rungume yayanta a jikinta, zata so ace sun zauna harda Husaina sun zanta, sai dai aure mai daraja ba zai bada damar hakan ba, uwa uba nata mijin nada tarbiya irin ta mutanenmu na da, ba zai taba aminta da irin haka ba, ba zai yarda su kwana ba

A nutse tace" Hajia ai kin san halin baban biyu, ba zai taba aminta ba, ko haka fa kin ga ruwa kawai ya sha kunya ba zata barshi ya ci wani abin ba, tunda muna nan ai Alhamdulilah da wahalama idan zai yarda mu koma, ya fini kulafircin yayan nan baya iya nunawa ne a gaban mutane"

Yar dariya Elhaji ya yi yana kallon mahaifin sarakuwar tasa ya ce" Ai kam Ba dai fulako ba a wajen Elhaj mai dala, to yanzun harda Balarabar zaku kwashe mana duka kaf?"

Wayar da yake dannawa tun zamansa yana sauraron maganarsu bai tofa ko A ba sai yanzu ya ji kamar an saka masa pose yana dan sauraro dan son jin amsar da za'a bada, sai dai shiru ya dan biyo baya , sai kuma ya ji Hajia na fadin" Ni da kaina zan so ku je tare da su, dan ta karra jin dummin uwa, na kula Hasana sak halin mahaifinta ta biyo, ban taba gannin ta kebe da yar nan ba, sai dai na ringa gannin tana satar kallonta, Balarabiya ko ba zaki bi iyayenki da sabon angonki ba?" Ta karashe tana kallon barin da su Murjanatu suka nutsu tun shigowar Kan Giwa babu wace ta yi kwakwaran motsi har Murjanatun kuwa domin gani suke yi sun bata masa dazu"

Kasa kasa ya sauke dubansa a kan Hajia ya dan maida kanta a lokacin da ta budi wata muryarta kamar ta jaririya tana fadin du yadda aka yanke, sai kuma Hajia ta ringa gyada wani kanta da wani murmushin da bai san ko na meye ba tace to su je tare wanda hakan ya sakashi sake dubanta suka hada ido hudu ta cire kanta hankali kwonce

Yana zaune har mahaifinsa ya ba matarsa damar ta bi iyayenta, domin ya sani ne a yau zasu so kadaicewa da junna ko yayane, dan haka sau ya bata har kwana biyu cif kan ta je ta samu nutsuwa da iyayenta
Farin cikinsu kasa boyuwa ya yi, haka yana zaune kamar an dasa shi aka gama shiri aka juyo wajensa kan ya bada damar a kaisu

Ajiyar zuciya ya sauke ya mike yana tafe a hankali ya fice a falon, Hajia ta raka shi da kallo ta yi murmushi, ita da kanta zata yi missing din yan matan nata sosai, sai dai wata hikima ta sakata aikata haka

Sai da ta bari ya dawo da wa'inda zasu fitar da akwatinnan iyayen su Hasana da na NURIYAH ta shiga fadin" To hajia, ni dai ba dan na so ba, aman idan mijin namu ya zo zance zan rakashi da kaina"

Hajia ta juyo tana tambayar karin bayani,a lokacin ne sumui sumui Nuriyah ta wuce ta gabansa ta wuce, wai ita ga mai kunya
Ji ya yi kansa na neman tarwatsewa a lokacin da sabon zance ya bude aka shiga bada dogon labarin da yake gannin sam bashi da wani anfani

Juyawa ya yi ya sake ficewa a falon, sai a lokacin suka ankara da Murjanatu sanadiyar dariyar da ta fashe da shi

Korarta abanta ya ya zauna ya rafka tagumi yana kallon mahaifiyarsa da tunanin ba zata yi hakuri su tafiyarsu su huta ba? Idan har abinda take hasashen nan gaskiya ne da zasu falasa kansu da kansu?

"Gaba daya burina ace yau sun tona kansu , ba zna taba yarda aurensu ya dauki lokaci ba, ban san mahaifinta ko zai amince ba? Bana so ne a yi mata na dole ita dinma, haka kuma da yardar mahaifinta" Elhaji ya fada shima a nutse domin zama aka sake yi, dama mahaifin su Hasana bai tashi ba

Da yannayin maganarsa ta rashin lafiya ya budi bakinsa a hankali ya ce" Har wani uba gareta bayanmu? Menene na jiran amincewar tata? Zamanin jiran su zaba yake saka su zabo wanda zai halaka su, ba zan taba bari y'ata budurwa ko jikata ta zabi miji ba, dama sakin koyarwa muke yi mu bi zamani da soyayar ya'ya, hakan bai haifar min d'a da ido ba, zan so nima a yi shi auren nan kwana kusa domin zan na kasance cikin wa'inda zasu ga ranar da raina da lafiyata, wancen kuwa ko sunnansa na haramtawa kaina bale jikata, dama ai ba sonta yake yi ba, ni ina so, kuma na mata miji shine MU'AZAM!" da kyar ya idasa maganar domin a gajiye yake ainun, magana na wahalar da shi, ko yanzun yana yi matarsa da fadin wasu harufan d bai fada daidai ba, shi kam bai ga ranar auren Lawali ba kuma ba zai taba amincewa har a dauki lokaci da auren jikarsa da wannan yaro dan mutunci, idan sunna so in kai hadasu a gida daya su kashe junan kawai idan basa son junna



Tunda ya fito ya ja ya tsaya ya samu kansa da raraba ido dan neman abinda bai ajiye ba

Hangota da ya yi a gaban kejin dawosun da aka mayar dan sun fara kyankyasa yanzun sai ana maida su gidansu tana kallonsu ya saka shi kureta da ido, domin da hasken fitilun gidan ana ganin mutun rassss


A hankali ya karasa ya ja ya tsaya kafafuwansa a dan ware ya sok hannayensa cikin aljihun wandonsa ya zuba mata ido dan daf da ita

Inuwa inuwar da take ganni na mutun ya sakata juyowa da sauri, ganninsa a tsaye ya sakata jin gabanta ya yanke ya fadi sannan hankalinta na neman tashi

A hankali ta ringa karantar yannayinsa, sau jyma ta faraa jin nutsuwa na dan shigarta a hankali a hankali

Kallonta yake yi har ya gamsu cewa ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login