Showing 75001 words to 78000 words out of 124070 words

Chapter 26 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

359

Wamcen din wacece?"

Abinka da mata , basu da juriyar kuka , idan abin a yi kuka ya samu nan da nan waje zai rikice in dai mata ne a wajen sai kawai Hajia ta aniya neman fashewa da kukan itama tana kallon Nuriyah ta ce" Haba NURIYAH yaya zaki tsaya ki karasa mana sai ki ga ko wacece kin ji? Wuce mu je jikata"

A hankali NURIYAH ta janye hannunta tana noke kafadarta tamkar yarinyar goye, domin a lokacin ji take idan ta kara taka kafarta daya to fa lalle tana iya rasa ranta a irin dokawar da zuciyarta ke yi

Lalausan hannun da ya shiga cikin nata hannun ya rike mata shi da kyau sannan ya mata jan da nan take ta gane bambancin jan Hajia tsohuwa da nasa ya sakata dagowa a firgice ta bi mai hannun da ido lokaci daya kuma tana girgiza kanta dukan shika shikai na tashin hankali sun tabata a gareta ba boyayu ba bayananu , hakan ya saka shi tausasa dubansa domin ya sani ne wannan lokaci dole zai zo da shok wa bayin Allahn nan bale ita wannan da bai san me zata ji a ranta ba, yana ji a ransa shi da ya ga gawar tasa mahaifiyar yaya yake rayuwa da rashinta bale su da suka rayu da tunanin kila wa kala?
Hakan ya saka ya mata uzuri har ya mata duba mai taushi a hankali ya furta" Mu je"

Nuriyah dake kallon lebunnansa kamar tana son koyon yarensa a sanyaye ta ce" Tsoro nake ji, ina jin tsoron zuwa cen, kamaninsu ya yi yawa kana gani?"

Idannuwansa ya lumshe mata kafin a sanyaye ya ce" kina nufin baki gane mahaifiyarki ba du karfi irin na tsakanin uwa da d'a?"

Sensation din mai girma ce, gaba daya ji ta yi an zare lakar jikinta hakan ya sa ta nemi zubewa kasa kan kafafuwanta sakamakon kasa daukanta da kafafuwanta suka yi

A hankali ya rabata da jikinsa dan ya bata talafin da zai hanna mata faduwa kasa yana jin kukan matan ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?gaba daya kamar zasu hauda shi bori

Muryarta na rawa ta ce" Sir ni ai ban santa ba, ban taba ganninta ba maman nawa....dama bata rasu ba? Tana raye a cikin duniya?"

"Ya isa haka NURIYAHhhhhhhh, ki daina magana haka....." Ya fada mata a cikin kunnenta kasa kasa sosai dan tsakani da Allah bai taba gannin abinda ya bashi tausayi irin yarinyar nan ba

Ita kuma idannuwanta ta lumshe gaba daya tana jin yadfa yake tafia da ita har ta ji ya rage mata tsayi gaba daya kafin ta ji wani hannu mai dumi yana rawa ya karbeta a hannunsa

A hankali hancinta ya shaki kamshin turaren humura mai sanyi , da dukan sauran karfin da ya rage mata ta ja numfashinta dan kara samun nutsuwar da take ji a jikin wadda ta rungumeta, daga haka ta daina fahimtar komai

Mamanta dake rukunkume da ita da rikon da bata yi mata a hhaihuwarta ba sai a yanzun ta kasa koda fashewa da kukan ita kam ta rasa ta inda zata hfara kukan gaba daya ranar nan ta yau ta zo mata da manyan abubuwam da ko ruwan azumin dake bakinta ta kasa sha sai a tsaye ta dan kurba dan shan ruwa a kan lokaci

Bakinta take ta budewa da kyar ta iya ambaton hsunnan NURIYAH tana sake talabota duda uban nauyin da ta ji ta kara sakamakon sakewa da jikinta ya yi

HA hankali ta cirota a jikinta, Husaina ta kama mata dan ta kula ta mata nauyi suka zuba mata idoh

A birkice ta ringa shafa gaban goshinta , sai kuma ta dago a rikice ta ce" Husainata bata motsi, kuma kalli ta sake nauyi Husainata ta mutu ne?"
Itama rikicewar ta yi lokaci daya tana ambatar sunnan Nuriyarh, su Hajia da Auta suka rufun masu suka ririke Nuriyah da ta langwabe suka nemi sake rikita junnansu domin babu mai ba y'ar uwarta hakuri kowace na neman hargitsa wajen

A nutse Elhaji ya dubi Kan GIWA tabas dake tsaye kikam nesa kadan da shi ya zuba mas ido ba zaka gane halin da yake ciki ba domin cen dama bai cika yawan fara'a ba sai ta kama, ya bashi umarnin ya amsheta dan ya kula nema suke su birkita kansu maimakun a yi zaman jimami kankani sannan a yi na farin ciki mai yawa dan ko ba komai shi gani yake rana ce da ya dace a tsayar da hawayen hakanan, shi yama fi tausayin iyayen yaren, y tabata idan suka ji a yau a yau zasu kamo hanya ko a kafa ne......

Sai da ya gama auna abinda ya dace ya yi kafin ya koma wajen nasu a tausashen da bai san ya iya ba ya shiga son su bashi ita

A raunane mamanta ta dube shi bayan ya amsheta ta ce" Ka tabata bata mutuba yalabai?"

Kan GIWA ya sakar mata murmushin da iyakarsa lebenta duda dan ya sake kwontar mata da hankalali sannan ya gyada mata kai

Mamanta ta kuma fadin" Yanzun idan ta farfado zaka bari na kuma ganninta ko shikenan ba zan kuma ganninta ba??"

"Zaki ganta mana Hasana, zaki yi ta gannin abarki har karshen rayuwarki, kin ga kukan ne ya isa haka dan haka ku bari ya sadata da likita a dubata ku kuma ku ganna da junnanku, emotion ne ya sakata sumewa ba komai ba"

Kanta take gyadawa tana kallo har ya bacema ganninta ya haura sama da Nuriyah sannan ta koma ta zauna kusa da y'ar uwarta suka rike hannayen junnansu gam aman babu mai cewa komai, domin a yanzun ta daina gannne komai a hirarakin da s Hajia ke yi, gaba daya ta rasa nutsuwarta har dai Hajia ta fahimci hakan ta basu damar su je sama bangaren Husainar da zumar da zarar ta samu karfin jikinta zata turo masu ita da kanta sannan itama ta mike dan zuwa bangaren girki da kanta dan a kara karama bakin nasu

A hankali ya ajiyeta a saman bed din dakin AUTA, sai dai a baki baki ne ya ajiyetan sannan ta danne babar rigar dake jikinsa hakan ya sa da ya motsa da nufin ficewa ta nemi fadowa

Da sauri ya saka hannayensa wajen damtsenta ya tareta sannan ya saka wajen cinyarta ya sake haudata sosai saman bed din yana cije lebensa cike da jin wani makuki a ransa na abinda bai san ko menene ba

"Yayanah ga ruwa" Murjanatu dake ta sharbar hawaye da muryar kuka ta miko masa cofin da ta zubo ruwa a ciki

Fuskarta ya tsare da ido yana tunanin kuka baya yiwa auta kadan ko wahala tsabar sangarta irin tata sannan ya saka hannayensa ya amshi ruwan ya juya wajenta a sanyaye ya shafa mata kadan a fuskarta sannan suka zuba mata ido
Gannin kamar bata da alamun farkawa sau kawai ya zuba mai yawa a hannunsa duda ya san a baki ake gumtsawa a fesawa mutun aman sai ya fi gane a hannun, ya daga hannunsa zai watsa mata ta ja wani irin numfashi lokaci daya ta nemi mikewa a gigice irin na wanda ya suma a figicen nan

Da sauri ya saka hannunsa dan riketa domin shi ya fi kusa da ita, ko ba wannan ba baya tunanin idan baby zata iya riketa dan yankansu ba daya ba gaskiya
Ita kuwa abinda ya fi kusanci da ita ta kaiwa wawura watau shi din gaba daya , a haukace ta rukunkume shi da dukan karfin da Allah ya bata, hakan ya saka shi neman zubewa daga gurfanen da yake kadan , lokaci daya ya rintse idannuwansa jin dukan farashin karfi na jikinsa a matsayinsa na ingarman namiji mai amsa sunnan Kan giwa ba dan komai ba sai da ya zamto madugu uban tafia a dukan abinda ya sako a gaba
A hankali ya samu kansa da karbar Hailalalar da Auta ke yi tamkar yana shirin fitar rai, domin itama a tsorace tamkar itane ta aikata abin nan da ta kira zunubi mai kaurin gaske wanda bata san hukuncinsu ba daga ita har NURIYAR , hakan ya sa sama sama hannayenta saman kanta take hailala da dukan karfinta dan ta fargar da Nuriyar abinda ta aikata ,
Sai dai jin muryar yayanta cen ciki da wata irin jigataciyar murya tamkar wanda ya ci dukan mutuwa yana amsar hailalarta kamar haka sai ta kai tsugune ta hade hannayenta a raunane ta shiga fadin"



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
4?? 5??



Walahi ki gwada kuma ki jure zaki sha mamaki,maganin rage tumbi a sha kofi biyu da sasafe sannan a sha idan an zo kwonciya barci
*Gamgamba, Canelle, ki matse lemun tsami kamar biyu, sai ruwa shi na ba mai zafi ba shi ba mai sanyi ba ki hade su, sunne abin shan*

Barkarmu da sallah yan uwa, Allah ya amshi ibadunmu, ya maimaita mana Alfarmar fiyayen halita=?O?
Ta sauke masa duban tashin hankali ta budi baki ta a birkice ta ce" Bar.....bar....barka da yamaci Sir"

Idannuwan nata da ta tsaurara masa kallo da su a ganninsa su ya fi karra tsatsarewa da ido, kafin ya ga ta cire ta kuma kama hannayenta ta shiga murzawa a birkicen nan
Sakwani kalilan ta saki ta juyo da dan sauri ta koma bangaren da abincin yake hakan ya ba dukan wata gaba kai dauke da tsokar da aka ba damar motsawa idan ta motsa , motsawar da hima ba da wasa ba

Idannuwansa dake kanta bai dauke ba har yanzun ya Kuma dagowa ya sake yi mata kallon nan daya da aka bashi dama, wanda jikan malan ya kara bayani cewa idan ka yi daya tal baka dauke idannuwanka ba sunnansa daya (=??), watau bai ba kansa damar koda kifta idannuwan ba bale a kai ga sake wani kallon da zai wuce misali, duda a yanzu kallon da yake mata yanai mata kallo ne dan ya gane manufar abinda take yi a bayane, domin kwata kwata kansa ya shiga duhu, ya rasa me yasa a yanzu ita wannan y'ar yarinyar take som raina shi, fisabililahi dazu fa ya gama mata maganar ta ringa suturta jikinta, yana gannin ai kowa sheda ne, aman shine yanzun zata kuma fitowa a haka ? Wama ya sakara zuba masa abinci ne? Ina ma'aikatan gidan nan suke ne? (Ka manta ma'aikaciyar take itama ne Oga ?)

Wukar da ta dauka dan ta yanka gasashen naman da aka dotoshi tafkeke cikin katon kwano ne ta kubce ta fadi sakamakon yadda hannunta ke rawa kar kar kar tamkar zata fadin ita dinma da kanta

Da sauri ta sauke wata wawuyar ajiyar zuciya sannan ta gyara tsayuwarta ta duka gaba daya dan dauko wukar hakan ya sake bashi wani damar da ya saka shi sakin ajiyar zuciyar da bai shirya yi ba kwata kwata

Idannuwansa ya dauke wannan karron domin ya fara fahimtar yaren da aka hanna kure abu da kallo cewar ba kyau, ya farra yarda da maganar

Wani karkarkar din ya saka shi sake juyowa yana kallonta,

A hankali ya samu kansa da mikewa daga zaunen da yake ya shiga takawa har ya karasa daf da ita sosai, wanda kanshin turarensa da karfin innuwar mutun dan Adam ya sheda mata cewar ya mata matsewar wajen da dan Adam ba zai so wanda ba huruminsa ya masa haka ba

Gaba daya ta juyo dan gaskata abinda take ji a kanta da jikinta, hakan ya sa kirjinta hadewa da nasa sannan kanta ya daki gaban kirjinsa da kyau

A birkice ta dora hannayenta saman kirjin nasa tana mai fashewa da kuka ta shiga murzawa da gagawa tana fadin" Daga Allah muke, gareshi zamu koma, ya salam ya salam dan Allah ka yi hakuri walahi ban san ka taso daukan wani abu ba, na ji maka ciwo ko? Na maka rauni? Dan Allah ka yafe min"

Gaba daya wannan yarinya a yau ya yarda cewa aike ce wani mai neman ransa ya labe ya masa dan ta halaka shi
A yannayi na neman fita a hayaci yaa saka hannayensa biyu ya damki nata hannayen da take cakumar manyan kayan da ya saka dam zuwa ya dauko mahaifiyarta , domin ko ba komai ai ba zai koma masu da kananun kaya irin na dazu ba, bale a irin gannin da ya yiwa matar akoy adini, shine dan wani bakon balaki take masa cakumar yan maye?

Sai dai kash, kasantuwar lamari na farko, watau zuwa na farko da ya taba hannunta shi KAN GIWA sai ya ji kamar wani hannun jariri ya damka, a kan dole tun kafin ta nemi agajin ya sasauta mata rikon ya sasauta mata shi dan kar ya karya masu yarinya

Idannuwansa da suka yi jajajir ya cire a kan fuskarta da hawaye ya wanke lebunnanta ke hadewa sunna karkarkar , muryarsa a shake ya ce" Ki daina taba ni "

Kasamcewar dan kwalinta tuni ya bar saman kanta dan firgita hakan ya sa gashinta mai tsayi da cika da kalar ruwan na y'ayan turai du ya barbazu har gaban goshinta kadan, a hankali take gyada kanta dan amsa masa cewar ta daina taba shin, duda a yanzun nasa hannayen ne a saman nata, watau ba itace ta tabashin ba, shine ya yi raf da ita

Muryarta aa sanyaye ainun tana kallon sajen fuskarsa da wajen gemunsa kadan ta ce" Ka yafe min idan na bata maka dan Allah"

Idannuwansa ya lumshe jin wata irin murya mai amon sanyin da zai iya rantsewa bai taba jin wani dan Adam ya masa anfani da ita ba a duniya, sannan ya shiga budewa a hankali yana sake dawo da dubansa shima saman fuskar tata da yake gujewa yiwa kallon kurillah

Kaamar wani gaula , shi KAN GIWA ya samu kansa da rage amon muryarsa shima a sanyayen ya ce" Me yasa bakya jin magana ne? Ina ce dazu nace da ke ki daina yawo tsirara"

Kalmar tsiraran ta mata nauyi a cikin kwakwaluwarta, duda ta san yana nufin ba hijab, duda kuma ta san cewa domin kar kanwarsa ta dauki Dabi'ar nan yake mata fadan nan, du kuwa da mamaki kan kamata idan ta yi duba da duban jama'ar gidan na saka sutura ne yadda suka ga dama ciki kuwa harda matansa da yake aure aman nata kadai ke bata masa rai, sai ta samu kanta da sada dubanta ta dora saman hannayensu, inda ta kurawa tarin gashin hannayensa ido , muryarta a sanyaye ta ce" Ka yi hakuri, ni da kaina sai da na nemi dauko hijabin sai hajia tace na yi maza na zo ma zuba abincin, na dauka cewa Abana ne ya kuma zuwa ......" Ta idasa tama sake dago masa idannuwan nan nata ta sauke a cikin nasa

Ajiyar zuciya ya sauke ya kasa furta wata magana dangance da abinda suke tataunawar a kai
Jiki ba karfi ya mata umarnim taa tafi, sai dai ya ga ta ki tafiyar, hakan ya sa ya sake zuba mata ido dan ya ga me kuma take son ganni ne yarinyar nan?
A nan ya lura da hannayensu ta zubawa ido da duba irinna to ka sakeni mana

Da sauri ya saki hannayen nata ya ja baya sosai ya juya bayansa, hakan ya sa ta dan tatare sket dinta ta kwasa a guje ta nufi hanyar da ake masu karatu ba tare da tama san cen din take nufa ba

Hajia da Mama dake tsaye tun saukowarsu ne kusan tun lokacin da ya matso kusa da Nuriyar ne suka kalli junna
Nauyi da kunya da tunanin maganar hajiar ya saka mama sada kanta hadi da juyawa da sauri dan walahi kunya ta ji sosai yau ta d'an nata ta kamata

Hajia ta yu wani murmushin ta idasa shigowa hankalinta kwonce tana fadin" Mijin lafiya kake tsaye ka kalli arewa , wai baka ci abincin bama?"

Lebensa ya dantse yana sake daidaita yannayinsa da haushi haushin hajiar da yake ji yana tunanin ko menene itace ta janyo masa ya juyo yana muzurai ya zagayeta ya yi ficewarsa gaba daya ba tare da ya ce da ita ufan ba

Da wani murmushin ta sake raka shi a bayane kasa kasa tace" Mu zuba mu gani "

A bangaren NURIYAH kuwa a guje har tana cin tuntube sakamakon takalmin dake kafarta ta fice a falon gaba daya ta baya ta nufi bangaren da ake yi masu karatu

Allaj ya taimaka an gama malan ya tafi ya zamto saura Murja dake amsa wayar kawarta tana dariar wai yayanta ne ya matsa dan Allah ta sada shi da Nuriyah, hakan ya sa dole ta mike daga zaunen da take tana shan sansanyar iskar wajen da nufin zuwa dan ta ga ko Nuriyar ta farka a barcin da ta samu, daidai nan suka kusa cin gware, a dan tsorace ta dace kiran tama kamo hannun Nuriyah da ta tsaya gabanta jikinta na rawa tana kallonta

Hankalinta ta ju itama yana neman tashi, hakan ya sa a dan tsorace ta ce" Nuriyah lafiya? Menene?"

NURIYAH ta ringa sauke ajiyar zuciya tana jin irin yadfa zuciyarta ke bugawa kafin ta nemi neman zama a nan wajen
Gannin haka ya saka Murjanatu karasawa da ita wajen wata kujera ta zaunar da ita tana sake tambayarta abinda ya tsorata har ya sakata gudu haka , bayan ita din mutun ce mai wuyar shiga irin yannayin nan, bama kamar yadfa zuciyarta ke bugawa a bayane

NURIYAH ta dora goshinta a saman hannunta tana ambaton sunnayen Allah, sannu a hankali har ta ji nutsuwa na fara ziyartarta, kafin ta fara dawowa hayacinta harma ta rage hakin da take yi sosai sannan ta shiga tariyo komai daki daki

A hankali ta zubawa Murjanatu ido tana sake maida tambayar Murjanatun a ranta, haka kawai sai ta ji ta yaya zata cewa Murjanatu hannunta ne yau ya shiga cikin na Kan giwa sakamakon rashin jinta? Ta ina zata fara fada mata abinda ya faru cewar da hannayenta ne ta kama rigarsa ita kuwa bayan ta taka dokar da ya gindaya mata?
Jiki a sanyaye jin dole ta yiwa Murjanatun karya na farko a rayuwarta ta cire dubanta a kanta a sanyaye ta ce" Faduwa naje yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login