Showing 63001 words to 66000 words out of 124070 words

Chapter 22 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

331

san ta inda za'a fara ba"

Kan GIWA cike da takaici ya waiga wajen da Lawali yake ya sake juyowa ya rike dogon abin fitilar dake haskawa a kausashe ya ce" Aba ka saka a handsfree "

Mahaifinsa ya saka a handsfree din ya ajiye wayar a kusa da Hajia

A wani kausashen ya ce" Ki nutsu, ki farka ki cire koma meye tunanin dake kanki, walau tsoro ne ko ganganci ne? Ki mayar da shi gefe, tunda har na iya daukan abin kunyar rabawa kaina maganar shirmen auren karamar yarinya irinki da baki fita a fitsarinki ba dan na ga na cinma aikina a nutse ba tare da na karya wuyan wannan mutumen ba, ina so ki gane idan baki sauko daga dakin nan kin fito fuskarki a washe kin yi pretending like ur surprised da gannina da shi, sannan kika gwada shirme irin na mace da mijin nan har muka budi bakinsa ya min bayani, kafin na rataye shi ke zan fara ratayewa!"

Daga haka kittt ya kashe wayar ya sake yin gaba sosai yana ta controling din bacin ransa dan kar ya fara saukewa a yanzu da gagawa haka, ya fi so a zo gabar da ta dace, wajen da ya dace su fahimci junna , ya fi so a zo filin da ya dace ba ja da baya ba kallon baya kafin ya fitar da asalin fuskarsa wa wannan mutumen, ya fi so sai hankalin matar da take kukan rashin y'ar uwarta ya kwonta waje daya ta hanyar dangana kwata kwata idan bata duniyar ne ko kuma haduwarsu idan tana raye ne ya samu kafin ya hade wancen mutumen da bai san wani yare bane bama ya ninkashi biyu ya zuba a dustin kowa ya huta ba, dan lokaci ya basu dan ya san wancen yarinyar shirmenta ya fi hankalinta yawa


A cikin dakin kuwa ba Nuriyah kadai ba, harta Murja ta rikice ta kasa rarashin Nuriyar dake tsugune tana salalami tana fadin" idan na fito a matsayin matarsa summa zan yi Hajia dan Allah ki ce masa na fito a matsayin Y'ar aikinsa ko ko ko bakuwarsa ko....... Auta ki taimaka min ki fadawa Hajia mana ke zata fi gane yarenki"

Murjanatu ta ce" Kai ina, Hajia idan ta fita a matsayin matarsa daga baya zao zaunar da mu ne ya mana tatas da jan kashedin kar mu saki mu saka aure a rayukanmu yanzu sai mun cika shekaru talatin talatin koda zai mana, ko a shekaran jiya ina jin maganarsa da Rislan yana cewa mace idan ba haka ta kai ba ko an aureta shirme aka kwasa, ki taimaka kar yace kennan munna tunanin a mana aure ne ya sa ta amshi maganar ta fito a matsayin matarsa ita NURIYAH "

NURIYAH ta gyada kai tana share hawaye da fadin" Fada mata Auta fada masu dan Allah auta, ko ranar da Malan ke mana tarihin matar fiyayen halita da ya aura da kannanun shekaru ba sai da yace kuma ya raineta ba ya kuma ce mana kar ya ji muna dora wasu abubuwan a kanmu domin zamani ba daya ba, wasu abubuwan sun fi karfin tunaninmu ba?"

Hajia dake kallonsu da duba irin na nutsuwa ta dago idannuwanta dake mata dan zogi domin ta ci kuka kam yau ba laifi ta kalli Aba dake tsaye bawan Allah cike da damuwar halin da matarsa ke ciki, danma Elhaji ne ya zauna a wajenta a cen baban falon Hajia yana ta yi mata nasiha , sukai ido hudu ta ce" Shi din Mai gidan nawa ne ke cewa auren yarinya mai shekarunku shirme ne? Baku isa aure ba?"

A tare suka amsata da eh

Idannuwa ta zubawa NURIYAH na yan sekwani kafin ta ce" Tashi maza ki gyara daurin dan kwalin mana, ke takwara shafa mata jan baki, ni atampar nan ta matse ko dai ba dinkinta bane ba?"

Kallon kallon da suka yi gaba dayansu ya saka Hajia mikewa tana fadin" Ke bani dan kwalin nan ana maku maganar ku maida hankali kunna wasa ga dukkan alamu baku san waye yayanku ba ko dan ya sake maku dan bana nan ne oho, maza matso min nan ni , ke kuma bude jakar taku bani jan bakin da turare yi gagawa mana Takwara"

Ikon Allah shi suka tsaya kallo a lokacin da Hajia da kanta ta daurawa NURIYAH daurin dan kwali irin na ture ka ga tsiya, irin wanda mata masu ji da kansu na da ke kashewa a saman kai, sannan ta fitar da jan bakin ta mika ma Auta tana bata umarnin ta shafa mata, ita kuma ta shiha fesa mata turarukan da Autar ta dauko a cikin akwatinsu manyan turatuka masu tsadar gaske kala biyu wa'inda kudinsu yake kamar haka *AMOR AMOR DUBU SITTIN DA BAKWAI, LANCOME DUBU SITTIN DA TARA* (watau turarukan nan daidaiku ne a cikin turarukan da muke kawowa, ba zaki gane bane hajia sai kin fesa sau biyu kacal kin ji zazafa sansanya natacen kanshi mai sakawa mijinki ya zamto maki bita zaizai .............turare shine mace, idan bakya kanshi special kanshi ba wanda ya saba ji a jikin kowace eyane ba akoy matsala, nace akoy matsala hajiata)

Sai da ta gama fesa mata sannan ta dauko agogo bak'a sidik mai dan igiya kamfanin QUEEN STYL wace take dubu talatin da biyar ta daura mata ta kama hannunta ta rakota har kan kofar tana kallonta ta ce" Ki je Nuriyahna"

NURIYAH ta yi kwalkwalkwal da manyan idannuwanta muryarta a shake ta ce" Hajia, Auta ta rakani mana, sannan ki bani hijab dina , doguwar rigar lesh din nan ta kamani da yawa Hajia ta matseni"

Hajia ta lumshe idannuwanta tana mai astgrafi a cen kasam zuciyarta, duda ta san ta niyarta na aikata haka daban ce da ta sauran, aman kuma kyakyawar niya ce mai daraja sosai ta furta" Ki je na ce mana Nuriyah, me yasa zaki tsaya mu musanta yawu ne?"

Da sauri ta juya jin Hajia na son cewa zasu musanta yawu da junna ta shiga bin hanya tana mai rike gaban kirjinta inda ta dora hannun nata a saman mamanta na hagu ta damka tana ta fitar da numfashi ta bakinta dan kar ta summa ta ringa saukowa daga matatakalar tana adu'ar Allah ya hanneta summa a gaban Lawali!

Kansa ya dago ya zuba a saman hanyar da ake saukowa, domin tunda ya shigo da Lawalin ya nuna masa kujera ya zauna shi kuma ya zo wajen matatakalar yana jira ya ga ikon Allah shin za'a bi umarninsa ne ko sai ya hau ya masu hauka ta yadda zasu gane ba fa cenzawa ya yi ba, just bai samu abin raba hali bane? Sai ga takun saukowar da ya saka shi kafeta da ido yana kallonta

Jikinta na rawa sosai ta idasa saukowa kusa da shi kadan, harma ta nemi da ta duka kasa kamar yadda take son mayarwa da dabiarta a gabansa

Sai da ya rintse ido kafin ya saka hannunsa ya........








Ya yi me? Me zai yi? Na higa uku=?3?>?z? @&? @&? @&? @&?



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
4?? 2??





Da idannuwansa ya masa alamun ya zauna, sai dai ina, Lawalin sai ya ki zama, asalima da sauri yya ringa waige waige tamkar wanda yake neman abinda ya yar bai samu ba, ya sake dora idannuwansa a kansu ya ce" YALABAI wannan yarinyar ban santa ba, ban taba ganninta ba, tana neman kulla min shari ne kawai ni ban santa ba, wani irin mahaifiyarta? Wace mahaifiyar tata? Ni ban san a kan maganar da take yi ba"

Kan GIWA ya kai haannunsa wajen hancinsa a hankali yana dan shafawa kafin ya rintse idannuwansa ya zabura daga zaunen da yake a kiftawa da Bismillah ya yi taku biyu saura kiris ya cinma Lawali da niya ta ya je ya tataka tsageran ya ji wani irin abu mai dumi da santsi a jikinsa ta bayansa, wani irin rungumar da ba'a taba yi masa ba a duniya ce ta same shi, a yanzu a irin wannan lokacin
Bai taba haduwa da abinda ya sauke farashin bacin ransa tashi daya ba irin na wannan rana, da sauri ya kai hannunsa ya damki dogon abin flower na kwalba , sai dai abin bai riku da kyau ba ya kubce, ko nace karfin rikon da ya mas aya fi karfin da yake da shi a jikinsa, a dole ya kubce gaba dayansa ya yi baya, wanda Tsoron faduwarsa a kasa ya saka ta sake rukunkume shi ta baya jikinta na wani irin rawa a tunaninta mahaifin nata ne ya kaiwa duka, ga tarin takaicin kanta ma ji da ta yi ba zata iya bari tana kallo a daki mahaifinta ba, ko menene laifinsa ba, bata taba tunanin ko jansa ake a kasa zata ji zafi ba sai yau da ta ga da gaske Kan Giwa na iya zane mata uba hankalinta ya tashi har ta rukunkume shi ta baya, muryarta na fita da kyar ga tsoro ga tashin hankali tana girgiza kanta ta ce" Abana ne fa, kar ka dake shi a gabana dan Allah, ka barni na koma sama sai ka dake shin aman a gabana hankalina ba zai taba kwonciya ba"

Shima idannuwan nasa a rintsen suke, inda Lawali ya koma kan kujerar ya fada bayan ya saki uhu ya rukunkume jikinsa da kansa ya cusa cikin kafafuwansa yana jiran jin duka ta ko'ina hankalinsa tashe

A hankali Aba ya kalli rigarsa da hajia ta riko da duka hannayenta , kasa kasa sosai ya ce" Uma, kin san fa zai iya dukan mahaifinta a gabanta, ko me ya yi ai jinni ya fi gaban wasa kar daga baya yarinyar ta ringa kallonsa da abin, sakeni na masa magana kawai a je da mutumen nan gidan sojawan cen su saka ya fadi inda take"

Hajia ta yi dan murmushi ta ce" Na zai iya dukansa ba, ka ga ta hanna ya dake shin ai ba sai ka yi wani abu ba"

Juyawa ya yi da sauri ya zuba idannuwansa a kan Kan Giwa da gaba daya kanna kallonsa zaka san idan a me yake ciki to fa rikicinsa na da ya fi na yanzu girma

A sanyaye ya ce" Ka ji tace wai kar a dake ka, wai kai din mahaifinta ne kar a dake ka"

Da sauri Lawali ya dago kansa yana kallonsu

A zabure ya sauko kasa yana hade hannayensa ya ce" Eh walahi, nine nan mahaifinta ni na haifeta nine mahaifinta kuma sunnan nan nata NURIYAH mahaifiyarta ce ta saka mata da kanta, dan Allah kar ka dakeni, idan ka dibeni a nan me zai rage?"

Kan giwa ya kakausan kallonsa ya saka hannunsa yana bambare nata da yake ji kamar neman kasheshi take yi, bayan ya fasa dukan a kan me zata masa rikon nan ne wai?

Sai da ya banbare ya juyo yana kallonta ya ce" ki je ki zauna kar ki fadi"

Kai ta gyada ta juya ta koma kasa ta zauna ta hade kafafuwanta tana kallon Lawali da irin yadda yake binta da kallo
Kan Giwa kuwa sai da ya sake kallon kwalbar nan da ya fasa sannan ya daga kafarsa ya karasa kusa da Lawali, wanda ya kuma hade jikinsa yana barin jiki

Zama ya yi a saman kujerar, Lawalin kuwa na kasa zaune
A hankali sosai ya ce" A gaskiya ban san idan zan iya hakura ba ni, kana ganni kukan nan shine cinta, shanta barcinta da farkawarta, ka yiwa matata ila gaskiya, kace kai ba babanta bane, to menene gaskiyar lamarin? Kuma ina mahaifiyarta?"

A birkice ya ce" Yalabai zan fadi gaskiyar abinda ya faru, a lokacin da mahaifinta ya yi tafiyarsa da iyalinsa aka bara min ita, daga ni sai ita, sai na karra aure, to muna zamanmu lafiya da matata ta yanzu sai kawai ita din cikinta yaa tsufa, dama ta jima da kaurace min, kai ka san ciwon kauracewa namiji ai ko tunda dai kana da aure, to du sai nima na yi watsi da ita tunda ai inada wata, yalabi har ga Allah ina son Hasana kawai abinda ta min ne yake min ciwo, wai hasana da ciki na tardota da kato?"

Idannuwansa ya rintse saboda jin dacin maganar da girmanta a kunnensa, bai waiga wajen da NURIYAH take ba dan ya tabata ita ta fishi jin dacin hakan, duda ya kula kamar ta riga ta shanye dacin magangannun mahaifin nata a zuciyarta

Lawali ya dora da fadin". A ranar ne raina ya kiya na maidota dakin mai gadi da zama, a cen ne ta haihu matata ce da kanta ta sake fada min cewa ai y'ar ba tawa bace , kuma nima ai na gani, ni kuma tun daga wannan lokacin sai na janye hannuna a kan komai nata na zuba mata ido na barta da duniyar, ni kaina ban san inda ta nufa ba, na dai kori ita mai mata aiki da jaririyar tunda ita ta daure mata, daga nan ni kuma na goge babinta a rayuwata na manta da lamarinta, tunda ita din yar cin amana ce"

Shirun da yya wanzu na dan lokaci ya saka Lawali dagowa ya sauke idannuwansa a cikin na Kan GIWA

Da sauri ya sada kansa hankalinsa na sake tashi, Kan GIWA kuwa a dagowar tasa ya idasa tabatar da zargin da yake a zuciyyarsa cewa ta yiwu yana dan daga kwalba

A hankali ya ce" Kana dai so kace min idanma ta rasu kai baka birneta da hannunka ba?"

Da sauri ya girgiza kansa yana furta" Kai ina aa,, ban yi ba walahi"

Kaan Giwa ya sake cewa"a zamanin da ka cireta a duniyarka kai da wa da waye a gidan naka? A yanzu fa?"

Lawali ya ce" a lokacin ni da matata da ita, da mai gadi da mai aikinta ne, yanzu kuwa matata ta haifi Y'aya biyu sai ni sai mai gadin dai domin dan uwan matata ne"

Kan giwa ya ce" Ohk, mu je"

Kallonsa ya yi da sauri cikinsa na sake juyawa ya ce" Mu je? Ina zamu je?"

Kan Giwa ya kalle shi da kyau kafin ya dan sasabto zamansa ya ce" Tafia zamu yi mana ko a nan zaka zauna ne?"

Lawali ya ringa gyada kai sai kuma ya girgiza da sauri yana cewa" To ai niu je din ne ban gane ba, dan Allah kar ka tafi da ni, kar ka je ka saka a min dukan mutuwa, ka ga fa ni mahaifin matarka ne?"

Kan GIWA ya kalleshi da kyau, ya juya wajen Nuriyah ya ga su take kallo

A hankali ya ce" Yanzu fa ka gama cewa ba kai ka haifeta ba kuma"

A birkice ya ce" Walahi a da na zata haka ne, aman a yanzu da ta wanku sai na ga komai nawa ne ta yi yarinyar rankatakaf, yarinyar nan y'ata ce gaba da baya"

Kan giwa ya gyada kansa ya ce" Haka ne akoy kama, aman tashi zaka yi mu je gidanka mu tambaya inda mamanta ta tafi, ka ga ba zan iya kuma ganninta a haka ba, sai mu dawo ko?"

Lawali ya yi wani irin tsomomo da shi na lokaci mai tsayin gaske a kalla minti daya da sekwani yana tunani kafin ya mike jiki ba karfi ya juya hanyar fita yana waigen Nuriyah da ta sada kanta ta tsurawa waje daya ido gaba daya hankalinta tamkar ba a jikinta ba

Sai da ya foce kwata kwata sannan Kan Giwa ya mike shima hankalinsa a kanta

Da farko har ya tabe bakinsa zai wuce, sai kuma ya juyo a hankali ya zuba mata ido, gannin kamar kwata kwata bata cikin hayacinta ya saka shi dawowa ya yi tsaye a kanta

Ya dan jima haka aman bata motsa ba hakan ya saka shi a hankali ya rage tsayinsa yana kallonta ya yi gyaran murya

Shiru da gaske ta afka a tunani mai zurfin gaske, dan haka ya girgiza kansa ya ce" So kike ki kamu da wata cuta yarinya karama da ke?"

A zabure ta dago ta zuba masa ido, sai kuma ta bude bakinta a sanyaye ta ce" Kana tunanin gaskiya ya fada? Ni fa ce min ya yi ta mutu , hakama yan anguwa haka ya fada masu cewa ta rasu"

Kan GIWA ya kawar da idannuwansa a cikin nata ya furta" Idanma menene idan na fita da shi daga gabanki yanzun zai fadi ainahin gaskiyar,"

Shiru ne ya biyo baya ya sake tsareta da ido ya ce" Hey, me kika aikata da kika hada jikinki da nawa?"

Yanzun saura kiris ta hantsila a irin tsugunon da ta yi, da kanta da komai nata suka shiga tariyo mata inda aka yi haka, ita ta hada jikinta da nasa ita?

A kausashe ya ce" Ban san wani shirme ne haka ba, aman ki dauke shi shirmen....kuma bana son shirme, kar ki kuma maimaitawa kin fahimta?"

Da sauri take gyada kanta ta raka shi da ido har ya bacewa ganninta

Wannan karron murmushin hajia a bayane yake ta juya ta bayan ta fadi maganar da ta saka Aba a cikin tunanin maganarta a likacin da ta furta" yawancin kunnar hannu na samuwa ne daga ubangijiyar mai shi, bangon nan ya riga ya tsage, kadangare kuwa dole ya samu wajen shiga"


________________________________________


A lokacin da KAN GIWA ya fito ya gama tatare hannun rigar dake jikinsa har cen saman damtsensa

Lawali na tsaye bai ankkara ba ya ji an masa wata irin damka mai zafin gaske an fizge shi

Tafia yake yi da shi wace shi tafia yake yi shi kuma gudu gudu

Yana tafiar nan ya ce" Ai ido ake gudu, na kauda ido zan gwada sa'ata da tsagera ko wanene!"

Da karfi ya kuma fadin"HAMZA HAMZA"

Hamza dake cen gefe ya taho da wani irin sauri yana amsawa

Kan Giwa ya ce"Janyo min Apash din cen ku kuwa ku dauko mota mai baya bude ka zuba min maza mu je kwaso yan ta'ada!"

Da wani hargagin balakin ya juyo wajen Lawali dake shirin dukewa ya nuno shi da yatsa ya ce" Bilahilazi idan ka duka min ko ka min kukan marar imani sai na tatakaka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login