Showing 78001 words to 81000 words out of 124070 words

Chapter 27 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

345

sai wancen jimnan ya tsoratani"

Kasancewar ta santa da tsoron Jiminar sai ta sauke ajiyar zuciya kafin ta kalleta da kulawa ta ce" Nuriyah, ki rage tsoro da nuna tsoronki wa koma minene, kin ga duniyar nan ta lalace, wani baka kashe masa ba , baka birne masa ba yana iya anfani da damar da ya fuskanta a tatare da kai ta tsoron koma menene ya ilataka, kuma kin san sihiri gaskiya ne ko? Dan Allah ki ringa biye tsoron abu kin ji y'ar uwata?"

Nuriyah ta kure fuskarta da kallo itama, kalmar y'ar uwata da ta kurayeta da ita ita ta fi bata sha'awa, duda ta jima tana kiranta da hakan, aman na yau sai ya samu wajensa ya zauna radam a zuciyarta harma take jin eh ba karya ta yi ba ita din Y'ar uwarta ce?,

Murjanatu ta waiga wajen wayyarta ta saki murmushi ta janyo tana kallo sannan ta sake fuskantar Nuriyah ta ce" kin ga wannan bawan Allahn kam yau fa ya dage, bana tunanin in zai daga kafa , da gaske yake wannan karron bai zo da wasa ba, kina ganni wai shi kawai sai na baki kun yi magana"

Nuriyah ta yi tsuru still bata ce komai ba, Murjanatu sai ta dauki hakan a matsayin dan har yanzu a tsorace take ne, dan haka ta ci gaba da fadin" yayan Mami ne, Nuriyah me zai hanna ki saurareshi? Kin ga na tabata idan har da wasa ya zo ba zai yarda ya yada badalarsa a gidan nan ba, domin ya san wanene yaya, please ki saurareshi ya damu sosai"

Nuriyah da yannayin mamaki ta ce" Auta, kina nufin yayan Mamin nan kawarki? Wannan mutumen mai kampanin nan da ake haskowa a TV na shadoji, lesuka, da atampopi?"

Murja ta bata amsar cewa eh shi fa, duda bata san dalilinta na yin tambayar haka ba

NURIYAH ta yi murmushi marar karfi tana kallonta ta ce" Ke kuwa sai na ga ba a april muke ba bale ki min wasan nan na yan gayu, Auta me ya hada jirgi da babur?"

Da mamaki Murja ta ce"Ban gane hausarki ba"

Nuriyah ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Murjanatu a hankali ta ce" Auta ban san yaya zan fayace maki yarena ba, aman ina so ki farga ki gane wasu abubuwa kamar haka.....kin ga, saka ci gaban da na samu na rayuwa ba shi zai saka na fara daukan kaina kamar ke ba, Alhmdulilah a yanzu ina tsaka da yaki da jahilci bayan a da NEMAN NA KAINA kadai na iya, a yanzu na iya saka kaya harma na iya kwaliya, uwa uba ina kwana a waje mai kyau na tashi a waje mai kyau, sannan na ci abinci mai kyau da gina jiki har zuwa koshina....., Auta wata niimar ta ubangiji a yau na budi ido na ga mamanki y'ar uwar mamana ce, duka na gani na kuma tsinci farin ciki mai girma............., Sai dai hakan ba shi zai bani damar manta wacece ni ba, ba shi zai sakani shiga a ukun da ba zan iya fitar da kaina ba, Auta kin san yayana da ya kawo ni gidan nan ya nunan muradinsa na son aurena? Shima na dakatar da shi a lokacin dan na san ya fi karfina kuma mahaifiyarsa ba zata taba bari ya aureni ba bayan bata san usulina ba, bale wannan bawan Allah? Dan Allah auta ki yi gagawar katse hanzarinsa, domin ba zan taba daukan kaina na kai wajen da Allah bai kaini ba, dan na jima da sannin cewa kwadayi mabudin wahala ne, dogon buri kuwa shi ke kai bawa ya baro, bani da su, burina na samu daidai ni talaka mai sanyin hali mu zauna dan mi raya sunnar fiyayen halita"

Gaba daya magangannunta sun daki Murjanatu ta yadfa ta saki baki da hanci tana kallonta kafin ta shiga girgiza kai tana yannayi mai nuni da dariar takaici, sannan ta kuma kureta da dan duban da ya saka Nuriyar shan jinnin jikinta domin sai idannuwan mutumen da ta yamutsawa kirji suka bayana a fuskar kanwarsa har ta ji kamar zata kuma rikicewa irin ma dazu

Da haushi haushi ta ce" To kuwa lalle kin bani mamaki, kin kuma saka na fara tunanin irin nisan sanninki a matsayinki na mutun, ke ki ciren komai ki kawo lamarin wanda ya haliceki ya halici du wani mai takamar shi wanine, shin baki yarda da cewa Allah na iya saka soyayarki a zuciyar wanda bakya tunani bane? Ko kina so ki ce hakan ba zai taba yiwuwa ba dan haramun ne?"

Nuriyah ta girgiza kai tana kallonta

Murjanatu ta yatsina bakinta ta ci gaba da fadin" Sai kuma mu dawo kan zamani, da abinda yake a bayane ba a boye ba, nawa kika gani an dauko daga cikin wajen da ba zaki taba tunanin za'a iya kwakulota a ganota a aureta ba aman lamari na ubangiji ya zuba mata baiwar da mai tinkahon bata da shi kuma ya halita ana iya aurenta dan halinta, ko dan kyanta sai ki ga sarki ya auro talaka ta zama sarauniya, wannanma ba kyau?"..........
Kafinma Nuriyah ta bata amsa ta ci gaba da fadin" Bale shi din wanene a kasar? Ki gane mutane da yawa na mararin son mu'amala da ke sakamakon sun ji furucina y'ar uwata Nuriyah, Dp dina hotonmu mu biyu, bini bini na dora status da mu da ke , manyan da ba zaki taba kawowa ranki ba sun nunan hakan, aman ina duba takun mutun na auna nagartarsa, da kika ga na maki maganar wannan ki dauka cewa ya cencenta ne, ba dan yana yayan kawata ba sai dan sannin wacece mahaifiyarsa sannan yaya yake a zahiri duda ban san badininsa ba....... Nuriyah ga wayar nan yana ta kira ki daga sai ki bashi amsar da ta fi kwonta maki a ranki.....na gode"

Ta karashe tana mikewa gaba daya ta yi gaba da yannayin dake nuna cewa ranta ya baci da furucin NURIYAH yau a kanta, haba dole ranta ya bace ta rasa gane me yasa karfi da yaji Nuriyar ke baya baya da komai take nuna ita ba kowa bace, sai tana yin abubuwan da sam ba tsari a cikinsu,bata san me yasa take nuna wani ya fita ba bayan ita din mutun ce mai daraja da bata watsa kanta ba ta rike mutuncin kanta ta nemi na kanta ta hanyar halataciya bata yi aiki da kyanta ta janyo kudajen bariji a jikinta ba!

Jiki a sanyaye take kara rakata da ido har ta bacewa ganninta kafin ta samu kanta da sauke wata wawuyar ajiyar zuciya ta sake bin hanyar da Murja ta bi da ido ta yinkura a hankali da nufin bin bayanta wayar ta sake daukan ruri



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
4?? 7??



A raunane take fadin" Wayo Allahna yayanmu ba da gangan bane na tabata idan a cikin hayacinta take ba zata taba aikata haka ba, domin mutun ce mai matukar girmama manya yayanmu....halin dimuwa na gannin mahaifiyarta wace bata taba gani ba a rayuwarta ya makantar da ita aikata haka.........ka yafe mata yayanmu"

Idannuwansa dake lumshe yana ta son rike hannunta da kyar ya iya rikewar dan cakumarsa take kamar an aikota a hankali ya samu ya fincike jikinsa sannan ya mike tsaye gaba dayansa sai sake hafe gira yake ya juya ya tafiyarsa ba tare da ya tsaya yama kirayi likitan ba, ya shiga tafiya yana harhada sawunsa tsabar sauri

Yana barin dakin Murjanatu ta koma wajen da ya kifa NURIYAH ta dagota ta rungumeta a jikinta tana jin yadda jikinta ya fara daukan zafi sannan ta yi shiru sai damkar rigar Murjanatun take wace ta gama fahimtar NURIYAH ta koyawa kanta idan ta shiga halin rudu ta yi ta murzar hannunta ko dukkan abinda ke kusa da hannunta ne, dan haka sai ta bata dama a hankali tana kara dan shafa gashin kanta kuma tana matsar mata da shi daga gaban fuskarta dan kar ya dameta

A kadan sun dauki kusan minti goma a haka kafin Murjanatu ta fara ambatar sunnanta a hankali dan ta kula zafin jikin nata dada karuwa yake yi a hankali a hankali

Shiru ta mata a kira na farko, sai a na biyu ta dago idannuwanta ta sauke dubanta a saman fuskarta

Cike da kula Murjanatu ta ce" Menene haka wai? Tarbar da ya dace ki yi mata kennan?"

Da kyar NURIYAH ta samu muryarta ta fito a raunane ta budi bakinta tace" Auta, ashe tana raye? Ashe inada uwa na rayu tamkar marainiyar da bata da dangi? Ashe mamana na duniya? Me muka yiwa abana da zaf................." Sai kawai muryar tata ta sake shakewa ta fashe da kuka wannan karron ta dora kanta a saman cinyar Murjanatu, haka itama ta biyeta suke rera kukan tamkar sunna gwada zakin muryoyinsu ne har sai da Murjanatu ta ga abun ba na karau bane sannan ta ringa dadaba bayanta a hankali tana fadin" Ai kin ga fashin bakin karan maganar da ake fadin Allah shi ke raya maraya koda mai uba baya so ko?, Ki yi Shiru haka ki tashi da sauri ki yi wanka mu koma wajensu na san bakya sallah yau ko? Ki je ki ga Mama, ki nuna mata soyayar da baki nuna mata a shekarun da kika yi ba ita ba, ki rungumeta ki ji dumin jikinta, Aba kuwa ba zan ce komai a kansa ba, ko ba komai mahaifinki ne,, ina masa fatan shiriya, aman kin ga Mama? Ina gannin kina karra bata lokaci ne baki je da gudu kin rukunkumeta ba, NURIYAH kin ga nima ba wani sannin kirki na mata bafa mahaifiyata, nakan yi tunanin yaya take? Yaya mu'amalarta da kowa take? Ni kadai sai na yi hamdallah na gode Allah, tunda ya bani wata uwar mai kaunata wace in ba fadi aka yi ba babu wanda zai ce ba ita ta haifeni ba........ki mike ki bar shiririta y'ar uwata ki je na tabata itama bata cikin nutsuwar zuciya tunda ta ganki a summe"

Ai kam kwarin gwuiwar da ta rasa ne ta samu, da karfin jiki ta mike din ta shige bayin
Bata tsaya wani iya yi wajen wanka ba ta yi shi da gagawa shima dan ta cenja abinda ke jikinta ne
Tana fitowa t ajiye rigar da ta cire da sket a ciki sannan ta dauki abayar da Murjanatu ta ciro mata ta saka kafin ta shiga nufar wajen sif da dam sauri tana fadin bara na dauko hijabina

Da mamaki Murjanatu ta ce" Hijabi kuma? Ga dankwalinta nan fa rigar"

Dan kwalin ta bi da kallo, dan karami da shi kuma shara shara
A hankali ta girgiza kanta tana tuna maganar tsirara a ranta, bata son abinda zai sake mata kallon wace zata lalata tarbiyar kanwarsa, yana da gaskiya sun shaku da Murja sosai ta yadda daya ke kwaikwayar daidaikun dabi'un dayan, dukda Murjanatu ce mai dabi'ar saka kannanun kaya idan a ciki suke, aman sai ta kiyaye dan kar ta ja abinda zai saka da girmansa yana mata maganar da ta fi daya, hakan na iya zama rashin kunya a wajensa

Tabas soyaya irin ta uwa daban take, bata da algus, soyaya ce mai cike da abubuwan mamaki, soyaya ce da bata da misali
Sam hasana bata yi wani kumbuya kumbiya ba, ido take bin yarinyarta da ita , tambayoyi take mata tana ta faman shafa du inda hannunta ya kai dan ta karra tabatuwa da nutsuwa da kwonciyar hankakin y'arta kamar yadda idannuwanta ke kallo

Ta yi kuka mai zafi na rayuwar yarinyarta, duda ta san wani abu a ciki, wanu ne bakonta, aman haka ta ringa sauraro kamar yanzu ake zana mata komai a idannuwanta
Ba rayuwarta ta fi bata tausayi ba irin ta yarinyarta, haka kuma sau ta ji du duniya bata da makiyi sama da Lawali, dama soyaya da jin kai kan zama jikici?, Haka summa Nuriyar da Husaina rayuwar Hasanar ta fi basu tausayi fiye da komai,hita suke tamkar ba zasu daina ba, har sai da suka raba dare Hasana ta tuna da mijinta wanda tuni ya bar salahun a gaisheta zai koma, danma ya ki yarda ya kwana yace zai je ya kimtsa mata gidan da kayan sana'arta du a waje, aman kuma ya tafi cike da tsoron kar dai yanzu ya rasa Hasana, domin a yanzu da ya karra gannin gatan da matar tasa take da shi sai ya sarewa duniyar baki daya harma ya ga ganganci irin na yayarsa da mijinya, ashe abin nasu mai girma suka dauko haka? Shi kam ya tabata ta yayarsa ta kare domin yana gannin lokacin da ta so tsugunawa dan ta ba Kan GIWA hakuri inda ya cakumeta ya watsata a bayan motarsu ta sojoji, wa ya san inda za'a mikata, Allah ya taimakesu basu aikata kisan ba, da ya tabata a filin Allah hukuncin da musulunci ya zo da shi zai hau kansu, ya san waye Kan GIWA farin sani ba boyayen sani ba, kuma yana girmama irin yadda ya ga damuwar matarsa a idannuwansa da fuskarsa,

Da dan murmushi ta yi anfani da karamar wayar dake hannunta wace itace wayarta da mijinta ya siya mata ta yi kiran numbersa
Sosai suka taba hira cike da kula da junna,
A hankali take dariya a lokacin da ya nuna mata cewar yama Tsoron a raba aurensu dan ya gane cewa ta fi karfinsa rabon su zauna tare ne ya hada hanyarsu
Bata ce masa komai ba dangane da haka, dan ta san zai yi tunanin hakak, sai dai zata fi so ya gane cewa ita a yanzu ai komai na duniya ta gama samunsa tunda ta sake haduwa da ahalinta da y'arta ga kuma shi a gefe, kudin da yake gani a matsayin wani abun dake iya gitawa tsakaninsu dati ne a wajenta, ba zata taba manta giyar kudi ba a rayuwa, domin ta wujijiga dukan wani farin ciki nata, ta tsorata da kudi, da ba dan Allah ya nuna mata a cikin talakawanma akoy na arziki ba ta hanyar hadata da shi ya zamto farin cikinta, da bata san wani tunani zai zauna a ranta dangane da maganar nan da ake fada cewa akoy na kirki a cikin mutane






*Ta'aziya zuwa ga sisina, Allah ya jikan Hajia ya sa mutuwa hutu ce a gareta*



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
4?? 8??



*DANDONON KADAN DAGA CIKIN LABARINA DA ZAI ZO MAI TAKEN NI ZAN LADABIHHHHHH, WATAU PAID BOOK=?
?>?p?>?p?>?p?>?p? in sha Allah: Bata taba jin ana neman ciwa suturar dake jikinta mutunci ba sai yau, shikenan yanzun an kai matsayin da ta yannayin suturar jikinka an gane kai talakah ne sai a nemi wulakantaka? . Rai bace ta juya ta nufi wajen da ta tabata a ciki mai wajen yake, haka kuma biyu na biye da ita da sauri dan basu tana hanninta a tunzure haka ba . Da karfi ta bude wajen sanann ta kutsa kanta da salamar da ta zamto tarbiyar bakinta sannan ta shiga baza ido dan ta ga abinda ta shigo nema watau mai wajen , .A hankali ya dago lumsasun idannuwansa ya sauke saman kanta da yarenta,. Wayar da yake yi bai katse ba haka kuma bai daina kallonta ba. Da haushi haushi ta sake kureshi da kallon raini irin na y'ayan masu kudi sannan ta ce" Boy i want to talk to your father, the owner of this company " Kallon da yake mata da kuma dan waiwaiga hagu da damansa ya sakata bi itama da kallo, sai ta sake dubansa ta shiga tunanin ko kurma ne? Da wani bacin ran ta budi baki ta ce.......*




Da haka suka gama wayarsu sannan ta koma wajen yar uwarta da y'arta wace ta kasa daina kallonta, mamakinta wai ita ta haifi y'ar nan? Koda yake ai kyau kam Lawali yana da shi harda na tsoro, kyau ne da shi mahaukacin kyau, kamar shi ya zana kansa bawan Allahn, sai dai kuma babu hali, sam ba hali, bama kamar gashinta, gashinta na bata mamaki , uwa uba ta dauko kirar Husaina sai kuma ta dauko tafiyar Hasanar, tafia ta hankali irin kana tafe kamar ana zana maka inda zaka dora kafafuwanka jikinka na amsawa, sanyin idannuwanta wajen motsawa kadai abin kallo ne, tunda ta nanukun masu a tsakiyarsu ya zamto idan ta juya ta rungumi wannan tana rike da hijab din wannan a haka har barci ya dauketa tamkar yar baby da kyar suka iya yin shiru suka rintsa shima da kyar Hasana ta bar Husainar kwana a wajenta, sai da Hajia ta saka baki sannan ta barta a ganninta ga mijinta ta je bangarensu mana, akan firrr Husaina ta kiya
Da wannan yan uwan suka kwonta da kaunar junna cike da farin cikin da suka jima basu samu kansu a ciki ba

Bangaren Kan GIWA kuwa yana komawa bangarensa dakinsa ya wuce direct ya zauna bakin bed dinsa yana dora hannayensa a wajen kansa yana yamutsa gashin kansa

A hankali ya mika hannunsa ya lalubo wayarsa ya shiga wajen mesg dinsa yana duba irin kalaman da Elizabeth ke aiko masa tari tari
Gannin abubuwa dake cikin magangannunta na neman shagaltar da shi ya saka shi goge su ya wurgar da wayar sannan ya mike ya nufi ciki da nufinsa wanda ya barawa ransa shi shi kadai


___________________________________

Washe gari


Yau kam ba maganar kuka bace ce, sun hadu ne baki dayansu a filin gidan Hajia Murjanatu saman farar kasar wajen mai tsafta da tsari mai daukan ido saman shinfidar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login