Showing 96001 words to 99000 words out of 124070 words

Chapter 33 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

326

kuka zata fashe da shi ba, domin daurewar fuskar da ya fito da ita ya samu kansa da sasautawa a lokacin da ya ga fuskarsa ta kure da kallo dan ta afka a duniyar tsoronsa ko akasin hakan

Idannuwansa dake shanye ya sake lumshewa a hankali ya kara taku daya ya isa gabanta, itama sai ta yi guda ta yi baya da sauri ta hade jikinta da gidan dawisun nan

Sake kallonta yake yi ya sake matsawa , hakan ya sakata sada kanta kasa tana rungume hannayenta a jikin doguwar rigar dake jikinta ta dan rungume tana ta tinano maganganun hajia gabanta na faduwa

"Me yasa kike son fitowa jikinki ba a suturce ba?" Ya fada a sanyaye yana sake bin jikin nata da kallo

Idannuwanta ta dago da kyau ta kalle shi, ta kalli jikinta ta sake kallonsa, mamakinta ya kasa boyuwa hakama furucinta suka kasa rikuwa, da dan mamaki ta ce" Jikina a suturce yake fa"

Kansa ya girgiza ya ce" Aa, hakan ba suturcewa bane, ko hijabanki du wasu iri kamar ba hijaban adinin musulunci ba"

Ajiyar zuciya ta sauke tana cire dubanta a kansa ta ce" Ka yi hakuri sir, ba zan koya mata saka kannanun kaya ba, hasalima ni nike mata fadan hakan kuma bata sakawa ita din da kanta bata da ra'ayin sakawar...." Ta fad a mugun sanyaye dan ganni take yi kamar bata da wani galihu irin abinda yake nuna mata haka?

Shi kuma da mamaki da kuma mantuwar a lokacin da ya fada mata ya nuna mata baya so Murjanatu ta koya ne ya ce" Wace?"

Nuriyah ta juyo tana kallonsa, sai kuma ta ce" Baby"

Sai a lokacin ya tino, ya tabe bakinsa yana tatare naman goshinsa waje daya ya ce" An fada maki dan baby ya sa na fadi haka? "

Da mamaki take kallonsa, ta ce" Sir kai da kanka ka fada min"

Ya sake hade muryarsa kadan ya ce" Ba wannan ne dalili ba, bakya gannin kayan basa maki kyau? Manyan kaya sun fi yi maki kyau NURIYAH"

A hankali ta ringa jin kunya da mamakin furucinsa a kanta a yau, uwa uba yadda suka tsaya haka ita da shi suka yi magana mai tsayi kuma a hankali daga ita sai shi?

Gannin tana ta sada kanta alamun kunyar da take ji ya saka shi sakin dan murmushi , dan kunyarta na matukar kayatar da shi a rayuwa
Sai kuma ya daure fuskarsa kadan a hankali ya ambaci sunnanta da yannayi mai zafi

Dago idannuwanta ta yi ta zuba a cikin nasa,

Sai da ya sake matsawa ya zamto yanzun idan dai tace zata yi wani motsi sai dai a jikinsa dan kuwa harta da numfashinsa na samun goshinta, haka kuma ya gaje wajen da kirjinsa da hannayensa yana kallonta ya ce" NURIYAH kina son shi?"

Gabanta kam ta san a yau sai ya bar kirjinta, da karfi ta rintse idannuwanta zufa na keto mata ta sake budewa tana kallonsa a lokacin da ya kuma kure fuskarta da lebenta da kallo
Gabanta duka yake yi da karfin gaske, a lokacin da ya sake fadin" Tlll me nah? Do you love hm?"

Idannuwanta ta lumshe a hankali ta ji kaikayin zafin da damshin hawaye na cika su, t sake budewa tana kallonsa a hankali ta ce" Wa.....wa.....wane?"

"Nuriyah kin san ko wa nake magana, wanda yanzuma Hajia ke koranta shi kika fito dan ana maganar saurayinki ko?" Ya fada da tsatsare gida

Da sauri ta girgiza kanta tana fadin" Aa ba haka bane"

"Ba haka bane mene? Ba haka bane bakya sonsa ko ba haka bane kina sonshi?"

A hankali ta kawo hannunta zata dora wajen kirjinsa dan ganni take yi kamar zai fado mata tana ta sauke ajiyar zuciya kala daban daban

Janyewa ya yi baya kadan yana fuskantarta, gannin ta rasa bakin magana ya sakashi lumshe idannuwansa yana jin kansa na ta sara masa sosai

A hankali yaa kamo hannun nata da take ta murzawa ya dan jimke shi kadan a cikin nasa , sai kuma ya saki ya lalubi karamar wayarsa ta gida ya damka mata kasa kasa sosai ya furta" I will miss you, ki kula da kanki.............Nuriyah kaina da nan dina na ciwo sosai, zan je gida na kwonta" ya idasa fadi bayan ya nuna mata kirjinsa da kansa dake masa ciwo ya juya ya tafi ta cen hanyar


Da ido ta raka shi har ya bacewa ganninta, sai kuma ta zabura kamar an wankawa fuskarta mari ta shiga shesheka kamar ta yi gudun tsirar da rai

A haukace ta juya da kafarta tana takawa sai kuma ta ja ta tsaya ta dago yan yatsunta ta shiga magana da su a gabanta tana maimaita magangannunsa

Kafafuwanta ta ji sun gaza daukarta sai kawai ta kai kasa ta tsuguna a wajen ta dora kanta saman gwuiwoyinta tana ta jujuya ido, da kyar ta samu ta samu wasu hawaye masu dumi a kumatunta wa'inda ta gaza ba kanta amsarsu

*Manyan kaya sun fi miki kyau Nuriyah, zan ji kewarki sosai Nuriyah, ki kula da kanki Nuriyah, nan dina da kaina ke min ciwo Nuriyah* sunne abubuwan da suke son tarwatsa mata kwakwaluwa bale idan ta dago ta hangi iya hangenta idannuwanta suka kasa gannin karshen girman palace din KAN GIWA sai ta karra susucewa ta rikice ta yi tunanin gamo ta yi da mai kama da shi, aman idan ta kuma shafa wayar dake kirjinta mai santsi da sulbi yar karama fara kal sai ta fara tunanin ko gaskiya ne shine?

"Wayo wayo wayo Allahna na shiga uku, shine ko ba shi bane? Wayo na mutu shine ko ba shi bane?" Take maimaitawa a bayane sai dai kasa kasa sosai da amon muryarta, ga kuma kuka abincinta da ta fashe da shi.......


"SHINE WA?" aka jefo mata tambayar bayan an gama nazartarta da muryar da ba zata so ta kamata a wannan yannayi ba


Da sauri ta dago........









Yauwa ku tataro mu je kantin kwari mu fitar da anko>??? @&?>??? @&?>??? @&?>??? @&?>??? @&?>??? @&?>??? @&?>??? @&?>??? @&?>??? @&?>??? @&?>??? @&?>??? @&?>??? @&?>??? @&?>??? @&?>??? @&?>??? @&?>??? @&?>??? @&?>??? @&?=ض? @&?=ض? @&?=ض? @&?=ض? @&?=ض? @&?=ض? @&?=ض? @&?=ض? @&?=ض? @&?=ض? @&?=ض? @&?=ض? @&?=ض? @&?=ض? @&?=ض? @&?=ض? @&?=ض? @&?=ض? @&?=ض? @&?
Ni kam azdawn zan yi:&?:&?:&?:&?:&?:&?:&?:&?:&?=?C?=?C?=?C?=?C?=?C?=?C?=?C?=?C?=?C?



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
5?? 5??


Da sauri da kuma tsoro ta dago tana kallon Murjanatu, wace fuskarta ta wadatu da yalwatacen murmushin da ta kasa fasara ko na menene

A dan daburce ta ce" Ba, ba kowa ba"

Sai kuma ta mike tana tare rigarta dan kar wayar ta fado ta kama hannun Murjanatu tana fadin" Kun fito ne? Kema zaki je ko? Idan ba zaki tafi ba nima ba zan je ba fa"

Murjanatu ta yi murmushi bata bata amsa ba suka nufi motocin dake jiransu

Tunda suka je gidan nan dake dauke da falo pankameme daya sai dakunna barkatai, sannan ba mai bene bane, haka kuma mutanen cikinsa basu kai na palace yawa ba, ko rabin rabinsu basu kai ba ta fara fuskantar wani irin mu'amala ta tsakanin soyayar iyaye karara da kakani, duda a cen gaban Hajia Murjanatu ba rasa wannan ta yi ba, aman wannan din wata irin soyaya ce wace ko motsi ta yi sai wani ya dubeta da kulawa ya bukaci son sannin idan tana bukatar wani abin ne ko wani abin ne bai mata ba a zaunen da take

Da farko rashin shakuwa ya dan wahalar da ita, a hankali wayayiyar kakarta, da kuma iyayenta suka sakata sakin jikinta harma ta fahimci wanene kakanta, shiru shirunsa da kawar da kansa a gaban mutane fulako ke dawainiya da shi, idan ya zamto daga ita sai shi har tsokana irin ta kaka da jika yake yi mata, sai aukin son sannin rayuwarta ta baya wace ta kula idan tana fada masa karra rura tsanar mahaifinta take yi a zuciyarsa a bayane ba a boye ba, dan kuwa da ake cewa kar ka kure bafilatani bai iya fushi ba a nan take fahimtar yaren
Gefe daya ga aminiyarta, yar uwarta, ciwon kanta, wace ta zamto mata jini da tsokar jikinta, tana gefenta tana karra wayar da ita abubuwan da ya dace ace ta waye da su ba yau ba, a mutunce da cikaken gayu hakan ya sa take sake daukan abubuwa a bayane ba a boye ba,

Abu daya ya so ya dan dameta sosai a awanin da suka gabata kafin ta nemi waje cen kasan akwatin kayanta ta totsa wayar bayan ta kasheta da tunanin bai fadi kalaman nan da wata manufa ba ta watsar da dukan wani faduwar gaba da tsoro ta fuskanci kwonciyar hankalin da ta samu kanta fiye da da a ciki, dama abinda ka kwalafa rai yake wahalar da kai, bata saka maganarsa a ranta ba, sai ya zamto ta manta tasirinta a gareta

A dawowar kakaninta, baki basa xuwa domin basu sanarwa kowa zuwansu ba, sunna so sai komai ya tafi masu daidai kafin suke sanarwa jama'ar da aka ci gaba da rike zumunci cewar sun dawo sunna gari, duda kakanta ya yanke zai daura mata aure nan da sati biyu masu gabata, domin ba zai tsaya wani saka saka rana da wani abubuwa daban ba

Wani lamari da ta ringa karanta a kan mahaifiyarta shine, kaf masoyanta dake zagaye da ita babu wanda ya kaita sonta, sai dai hali irin na mahaifinta ke dawainiya da ita, ta sha ta juyo ta kamata tana satar kallonta, da zarar sun hada ido sai ta kawar da dubanta kamar ba ita ba, takan yi murmushi ta ci gaba da gabatar da dukkan abinda zai sanyaya ran maman nata dan gani take yi du wahalar da ta sha bata kai ta mahaifiyarta ba
A haka har wani lokaci Mama Husaina ta janyota dakin mahaifiyarta ta turata ta rufo dakin ta barsu daga ita sai ita
A lokacin ta ga soyaya gannin idannuwanta, harma ta kwana a cinyar mahaifiyar tata

Bayan kwana biyu Mama Husaina ta tatara ta koma gidanta kusa da mijinta mai adalci ta barsu a gidan tare da tsofafin da Murjanatu da mahaifiyarta

Sai dai a bangarenta ne lamari ke dada nitsata a cikin kogin farin cikin zama kusa da iyaye
A bangaren bawan Allahn ba haka lamarin yake ba
Ba wai zama yake yi ya kadaice kansa ya ringa lilo a jirgin da babu sauka ba, sai dai ya zamto ko me yake yi sai ya samu kansa tsundum a cikin tunanin da babu wani anfani

Yakan samu kansa a cikin tunanin me yasa wayar da ya bata bata shiga? Me yasa bata yi kiransa ba bayan ya nuna mata interst dinsa a kanta? ......a hankali a hankali kuzarinsa ya ringa ragewa, walwalar da yake da ita a gaban iyayensa ya ringa rasawa, domin ya fara saka damuwar yannayin matansa a ransa bilhaki, bayan a da yana zaune da su ne da zurra ido da tunanin idan sun gyara oho, idan basu gyara bama ohon masu, bama kamar yadda ya dawo da maganar su ringa dafa masa abinci, hakan ya girgiza su, ba wai abincin ne basu iya dafawa ba, kowace ta iya nata na garinsu, sabon da ya masu ya saka su sakin jiki da tunanin su da ta tukunya sai dai hange ya saka su rikicewa, babu wace ta san abinda ya fi kauna bale adadin da yake ci da lokutan da yake ci, a nan gidan nasa ya fara karra daukan haramar cakulewa domin ya nuna cewa duk wace ta yi girki zata kawo kanta turaka ne, wani sabon salo da bakon yannayi a garesu, a girki ukun da suka yi sai ya fara tunanin janyewa da kansa, domin girkin kansa ana yin mai sauki ne wanda idan da hali ya ci kawai idan ba hali ya bari, sannan da an zo wajen da ya dace a nuna masa bajinta sai gajiya ta lulube mace na dan girkin da ta girka a kicin dinta na yan mintina
Sai ya samu kansa da zama ya lalubi wayarsa ya rubuta numbersa dake cikin wayar da ya bata ya yi ta gwada kira, sai dai ba amsa, ga gajiyar neman na shinkafa ga rashin samun kulawa, dole tunani ya nemi damun magidanci

Da wannan yau da sanyin safiya ya shige bangaren hajia dake zaune da mahaifinsa ya zo gaisheta gaisuwar safe

Har kasa ya duka ya gaishe shi sannan ya koma gefenta ya zauna yana dan kishingida kadan yana gaisheta kasa kasa sosai

Baki ta tabe ta ce" Gaskiya mai gida ka raina ni, ni ba zaka duka ka gaishenin ba dan bakon iya shege?"

Dan satar kallonta ya yi ya maida kansa ya kwontar ya mata shiru bai ce komai ba, hakan ya sa ta juyo tana kallonsa, domin ba haka suka saba ba, idan ta yanko masa ashar komai kankantarsa sai ya mata jan kunne sun raba hali ko a gaban babansa ne dan ya san idan babansa ya yi fadanma ita zata tare masa, sai ta ga yau ya yi lakwas da shi yana sauke ajiyar zuciya

A dame ta ce" Me yake damunka ne Mijin?""

Yanzunma bai bata amsa ba sai shirun da ya sake daukan wajen

Dan tsaki ta saki tana kallon danta ta ce" Haka zaka yi ta kallonsa, ka tashi ka shige gaba ka daura masa aure da yan iska sunna neman kashe shi, wai ace mai mace biyu ne a haka? Sai tsamun rai da ya zame masa ado, du ya kode ya yi fari fat tsabar rashin jini, ba kwonciyar hankali ba ta lafiyar jiki kai kulun farin cikinka ragage ne bukatunka ba cikaku bane? Gaskiya ni kai ka cuceni da ka yarda ka aura masa bayaraba da ba'indiya , da su yan iska ne? Ka duba ka ga dan jikana yadda ya zama tunani ya masa yawa bashi da walwala ko kadan!"

Daga shi har baban nasa zuba mata ido suka yi, kai Hajia? Rikici ya fara saukowa, har ta manta itace da bakinta tace a aura masa wace yake so aljihunsa ne shi ya san zai iya ko ba zai iya ba a lokacin da ya nuna du yayanmu na hausawa basu masa ba sai ya je ketare? Kuma yau ita ke nuna an cuci jikanta
Shi kuma kallon da yake mata wai wani bukatunka ba a cike ba, shi kam bai san me yasa take masa shishigi ba walahi

Hakuri mahaifinsa ya ringa bata da addu'ar Allah ya kyauta

Hajia ta ce" Amen, Allah ya kyauta din, yaya maganar daurin auren Balarabar?"

Idanuwansa da ya mayar ya rintse ya samu kansa da budewa lokaci daya yana jin irin sarawar da kansa ya yi a lokacin da mahaifinsa ke fadin" Yadda ya yanke ne, yace baya so ko kadan abin ya dauki lokaci, a sati biyu ai an ci kwana hudu yau"

Hajia ta gyada kai ta ce" Allah nuna mana, baiwar Allah balaraba yarinya mai kyau mai kyan hali, na so ace zuri'ata ta samu y'ar nan"

Aba dai shiru ya sake yi kafin ya mike ya mata salama dan zuwa zai yi anguwa su gana da datijon malamin da ya saka a tayasu bawa Allah zabi a kan lamarin, domin aure auren yaron babu daya da aka yi a haka, kowane an gabatar da shine a tsarin nasara, ko lefe Husaina tace ba yanzu ba a bari a gama daurin aure ta tare, gashi itama Husainar zata fita ita da y'ar uwarta wace mahaifinta ya riketa a gidansa ya hannata komawa nata gidan, hakan na damun mijinta fiye da kima, shi kuwa mahaifinta ya zuba masu ido ne yana so ya idasa gamsuwa da koda masa mijin y'ar tasa da ake ta yi, ya fi so ya gamsu da kansa ba wai a yi ta yaba masa shi ba, domin shi duniya ta masa dukan da baya yarda da kyan dan maciji,


Bayan fitarsa shiru ne ya ratsa wajen, Hajia ta yi shiru tana taunar goron safiyarta, Inda KAN GIWA yake zaune yana ji juwa na yawo da shi kamar zai summa daga kwoncen

Cen ta sake juyowa ta ce" Wai lafiyarka kalau kuwa yaron nan?"

Kansa ya dago gaba daya ya maka mata harara yana mikewa ya ce" Ina ruwanki!"

Da ido da baki a bude ta raka shi, sai kuma ta saki murmushi tana furta" Anya kuwa wannan zai fadi abinda ke zuciyarsa? Gashi na yi rantsuwar sai ya nuna yana sonta, ga kakanta ya yanke lokacin aurenta ya hanna a yi taron komai....., To Allah gamu gareka"

Wanka ya dauka cikin shiga ta hausawa, dinkin samari da baya wuce kasan gwuiwarsu kadan sannan ya riko hular kayan a hannunsa bayan ya yiwa jikinsa wankan turaren da daga nesa zaka iya jiyo kanshinsa sannan idan ya bar wajenka zai bara maka kanshin

A nutse yake takawa cikin lafiyayen takalminsa ya ratsa falonsa ya fice a lokacin da karfe takwas ta gota kadan ya nufi balbalin gidansa ya tarda sojan dake jiransa wanda ya fitar da mota ya gyara mata tsayuwa

Tsayawa ya yi kadan yana tunanin shin zai tafi da shi ne ko kuwa? Wani tunanin da ya yi ya saka shi karasawa ya shiga bayan motar da ya bude masa, sojan ya rufe bayan ya sara masa sannan ya shiga ya zauna ya dakata ya ji inda suka nufa kafin ya shiga jansa

Tunda suka kama hanya ya samu kansa da lumshe idannuwansa
Zuciyarsa tafarfasa take yi fiye da kima, ransa baci yake yi, sai dai ya fi ganewa saurarawa dan baya so ya nuna har sai ya ji ba'asi

Tsayawar motar da bude get din ya saka shi sake zuba idannuwansa a farfajiyar gidan har ya tsayar da motar ya fito ya bude masa

A nutse ya dago hular ya daidaitata a saman kansa ya kafata , ya samu kansa da son sannin idan ta hau kan nasa da kyau a lokacin da ya fito sojan nasa ya kureshi da kallo a nutse ya dan rage nisan dake tsakaninsu ya furta" Ta hau hular?"

Sojan dake matukar yaba kyan da ogan nasa ya yi ya samu kansa da sakin murmushi yana amsa shi harda dogon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login