Showing 30001 words to 33000 words out of 124070 words

Chapter 11 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

351

ta tsargu da kanta ta kasa nutsuwa waje daya sai kakawar da kanta take yi

A nutse hajia ta ce" Takwara, ki kula kin ji ko? Kin ga yana matukar tsoron zuciyarki, zan iya ce maki gwarama ni na yi kuka da ki yi, ki matsa masa sosai ta yadda zai fara sannin mahinmancin rayuwa, ina so ya iya zama da iyalansa, ya koyi raha da su, takwara ki yi hakuri na san bakya son zama da su aman idan har kika jure kika kai zuciyarki nesa zaki yi taimako ne wa mutumen dake yi maki so daya tak da ba algus, ke kin san yayanki na iya tunkarar komai dan gannin kin samu ci gaban rayuwa da farin ciki, shin zaki iya yin hakan kuwa?"

Babar Muryar da ta sanar da karasowar Kan Giwa ne ya saka dukan mutanen daidaituwa a bakin hanyar kowa ya kama kansa bayan baima idasa tahowa ba an dai fadi cewar ya shigo get na farko ne kuma sai ya biya ya dauko Elhaj da baba kafin su karaso aman a haka du aka nutsu ana jiran karasowarsa

Hajia Murja ta kai dubanta wajen Chef ta kicin ta ce" Mariam, kamar yadda kika san ana kiyaye lokutan cin abincinsa, ana dafa masa abinda ba mai a ciki dan yannayin aikinsa, Mariam ki kula idan kuka dafa masa abu da mai ya bata maku bana kusa bale na hanna dan Allah kin ji? Kuma a karra kiyaye tsaftar bangarensa da na matayensa kafin su daidaita lamuransu, idan kuka yi sanya yana iya zubar da kowa ya zuba sababi kun san halinsa sarai gashi ni din bana kusa bale na tsawatar"

Da biyaya take amsawa, duda zuciyarta ita kanta a darare take da tsoron barinsu da za'a yi daga su sai uban gidan nasu, duda ya kasance mai yawan tafia aman basa tunanin zai yita bayan ba kowa duba da Baby na gari, hakan yake saka su a cikin hali na zulumi

Karasowar motar da suke ciko ne ta katse tunanin kara daukan lamarin Kan giwa serius da Nuriyah ke yi, sosai ta shiga wani rudanin itama da tashin hankali duda Hajia na fadin ga Baby tana iya hanna shi aikata wani abin, aman ba zata manta babyn kanta ya taba keta mata marin da ya kusan sati bai baje a fuskarta ba, gaba daya sai tsoro ya karra shigarta nasa a lokacin da ta dago da dubanta ta sauke a kansa ya bude ya fito ya zagaya ya bude bangaren kakansa da mahaifinsa ya fara fitowa kafin ya taimakawa mahaifinsa ya fitar da shi cikin motar cike da kula

Magana Kan Giwa yake yi kasa kasa wace hakan ya saka mahaifinsa dagowa ya maka masa harara, wada ta saka ya dan daga hannunsa yana nuna alamun ya sara masa

Hannun ta bi da kallo da fafadan kirjinsa , gaba daya kamar wanda yake box, watau fadan nan na kakafar mazan turawa da sauransu , abin dai ba'a yi a nan wajenmu y'ayan africa sai cen wazajen,
A hankali ta janye dubanta gannin sun juyo sunna tahowa bayan ta yiwa irin tafiyarsa kallo daya tak ta sada kanta irin na yan uwanta ta nutsu, domin itama ba kowa bace a wajen nan alfarmar baby take co wace ta tabata sangarta ce irin ta shagwababu duda Baby na nuna mata soyaya ta zumunci aman tana guje ranar da zata daina yayinta ko ta koma kasar wajen da ta fito sunnanta ya dawo matsayin yar aikin da yake da, ta tabata hakan zai haifar mata da matsala idan har ta ari yannayi na yar masu gida ta yafawa kanta

Hajia Murja ce a nutse ta ce" Nuriyah?"

Nuriyah ta dago kanta , haka ya sa sukai ido hudu da mama dake ta kallonta tana ta jin wani iri a kan yarinyar, duda muguwar gajiyar dake tare da ita na tafiyar jirgin da ta yi yau ta shigo dan tana so ta raka hajia gannin likita da kanta gashi kuma a yau zasu wuce dusa mijin nata ya ce ta bari ya tarda ita cen au wuce ta ga za'a wahalar da hajiar ita ta taho, hakan bai hanna mata kin zuwa ta zauna ba , tama fi sha'awar bin yarinyar da kallo,
Sanyin halinta,
Yannayin kallonta
Irin tafiyarta na kayar mata da gaba
Sai dai tasu an ce masu ta rasu
Tasu an ce masu bayan rasuwartamaa wuta ce ta ci namanta
Tasu ko kabarinta basu taba gani ba
Ta rasu da abinda yake cikinta aka ce masu
Aman me yasa kamanin, abubuwan suke kusa da junna duda Allah kan halici bayinsa da kusan kamaceceniyar kamani da dabi'u?

A sanyaye hajia Murja ta ce" Ki kiyaye dukan abinda zai hadasa fada da wani har Allah ya dawo da ji lafia kin ji?, Na san ke ba mai fitina bace, wa'inda ke tare da ke ne auka cika fitina, so ki kiyaye lamarin KAN Giwa har Allah ya dawo da mu kin ji?"

Kai ta gyada tana kokarin maida kwalar da ta ciko idannuwanta muryarsa ta saka ta kasa rikewa ta bar abinta gudu a saman fuskarta a lokacin da ya ce"





*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
2?? 7??




Muryarsa ta saka ta kasa rike kwalar dan ji ta yi kamar zai mareta tsabar ta saka tsoronsa ko mace shayinsa a ranta sakamakon irin yadda ake karra tsoratata da lamarinsa a lokacin da ya dan sake wara idannuwansa a kan mutanen wajen yana fadin" Me kuma kuke jira? Kowa ya kama gabansa!"
Dama da haushi haushin an saka shi kwana biyu da matansa a bangare daya wa'inda tunda suka dawo bangaren nasa zai iya cewa banda takura babu abinda ya tsina a wajensu, yanzun idoma ya kawo ya zuba masu dan ya ga irin nasu haukan, matan nan babu wace zata zo ta neme shi sai shine mai abu a hannu ko?, Uwa uba a yanzun da ya karaso ya baro Mahaifinsa na kokarin taimakawa kakansa fitowa a motar ya karaso wajen nan ne dan ya gazkata tunaninsa cewa basu zo wajen yiwa kakanninsa bankwana ba

Lebensa ya dan cije na kasa yana kallon yadda Mamansu ke bankwana da auta tana nuna mata maza ta tafi yayansu na tsaye , sannan ta juyo ta kamo hannun Nuriyah dake barin jiki suma suka bi layin yan barin wajen domin ga dukkan alamu ta tsorata sosai kamar wace aka kama sunnanta daban da sauran aka wanka mata mari

Da mamaki Hajia Murjanatu ke kallonsa irin yadda du ya korar mata mutanenta, sai kuma ta yi murmushi tana girgiza kanta a sanyaye ta ce" Dan Albarka, ta yiwu mu jima a tafiyar nan, ta yiwu kuma ba zamu jima ba zamu dawo, dan Allah dudai yadda hali ya kama ka riken yan amana da zuciya daya ka ji? Ka kular min da su, ina fatan mu??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????na zuwa likita yace ai da ta wayama yana iya rubutan magani mu dawo na tatali yan bayin Allahna bama kamar takwarata da kawarta sunne abin tausayi ka ji?"

Bakinsa ya dan tabe bai ce mata komai ba , watau kin yin maganar ne ya yi hakan ya sa ta shaka itama, dan ai Kan giwa ba mutun mai shiru shiru bane, yanada maganarsa daidai gwargwado

Har zata sake masa magana da hargagin da ya dace da shi mahaifinsa da tsoho mai ran karfe suka karaso sunna tafiya a hankali, ba dan komai ba sai dan jikin tsufa da ya dace a tatala a bi a hankali

Juyawa ya yi ya kama hannun tsohon ya nufi wajen jirgin da shi kasa kasa sosai yana fadin" Wai kai du inda ta yi sai ka bita baka tausaya min ne ka zauna kusa da ni mana ka barta yawo ne fa take so, baka ganninta tsaye kan kafafuwanta masha Allah!"

Murmushi ne ya fadada a saman fuskar tsohon da yi ya riko da adininsa ka'in da na'in hakan ya sa yake cikin hayacinsa sannan yake da kwari fiye da dubunnan masu shekaru irin nasa
A hankali ya sake rike shi da kyau yana dora kaffafuwansa har suka idasa hayewa suka shige ya kaishi wajen zamansa ya zaunar da shi ya daura masa belt ya daidaita sanyin saman kansa ya masa komai sannan Tsohon ya ce" Dama ina da rai ka hadu da irin tawa, dama tun ina raye na ganka a gaban macen da ta amsa sunnanta mace ? Macen dake gyara adinin mijinta, take gyara halayansa, take wasan kura da zuciyarsa, take tausayinsa fiye da kowa a duniya take tatalar arzikinsa? Ka san irin matan nan irin dadin zamman da sukeda kuwa? Takwara su fa yi masu biyaya yana zame mana wajibi ne, irin abu ne da idan baka yi ba zaka kasance a takure ne, dukantama nawa take da zan barta ta je gannin likita ita kadai? A wajena jaririyata ce koda ita ta haife duniya, nutsuwata ce, farin cikina ce, ka ga wannan matar da ubanka ya sanyo a kanta ina iya komawa filin yaki koda kuwa bani da karfin yakin"

Shima wajen ya zubawa ido Abansa ya kawota ya zaunar da ita saman kujerarta itama a nutse kusa da mijinta ya gyara mata komai

Idannuwansa ya sauke saman hannunta da ta saka cikin na tsohon mijinta kasa kasa ta ce" Kakan Kan giwa, ina fatan kana cikin koshin lafiya?"

Murmushi ya maida mata ya ce" Kakar Kan giwa tunda kin karaso komai ya daidaita In sha Allah"

Da mamaki yake karra kallonsu irin yadda du suka ba junna kulawa ta hanyar jifan junna da lalausan kalamai masu daraja sannan suka sake maida kansu kan d'ansu dake karra jadada kar su kunna AC su bar na cikin jirginma ya isa du sunna amsa shi, gefe daya kuma sarakuwarsu mai datakon alkhairi tana nata basu kulawar daidai misali

Murmushi ya yi yana kawar da mamakinsu da kulun baya barin zuciyarsa
To shi fisabililahi bai taba haduwa da rayuwa irin wannan ba
Shi dai matan nan saima da ya zabi wa'inda ko a TV akan yawan nuno su a matsayin wa'inda suka fi kowa iya soyaya, Ba'indiya ko a labarin samari da yan mata sukan so su samu kwatamkwacin indiyawa a yadda ake hasko mana su, mai kyau ce, siririya ce, ga gashi, ga manyan idannuwa, ga kyakyawan kugu, bai san me yasa cen din yake haka ba sam......., Sai kuma a zo kan bayarabiyarsa, ko a cikin yarabawan ita din wace take da daraja ce, ba zai manta da aka zo miko masa ita a matsayin mace ba gaba daya ta ruguje ta kai kwonce sai da aka ringa mata yayafi kafin ta mike, a ranar ya gama samun nutsuwar tunaninsa cewa ya gama dace, sai dai kashhh, ba'a je ko'ina ba ya ga haza, ya ga rubutu a rubuce, hakan ke bashi mamaki, shin kowama haka yake rayuwa da matan ne? Matan gaba dayansu haka suke ne? Yanzun da wannan kakansa ya rayu har yake ikirarin a yadda yake tankwasar nan zai je filin yaki saboda kakarsa? To shi yana gannin a bariki kadai yake yin daidaya ya amshi kaya daidai misali, a barikin kanta abin sama sama ne domin idan ya ce zai karra takan firgicewa ne karrara ta nuna mutuwa zata yi ya bata dama ta shiga ruwan zafi

Riko hannunsa da aka yi ya saka shi sado kansa yana kallonta

Fuskarta ta sake sanyayawa sosai a nutse ta ce" Rislan ya ce zai dawo cikin satin nan, idan Allah ya dawo da shi ka sake rarashinsa kan maganar karatun nan ,ya yi hakuri ya koma domin ba'a fushi ka ji dan albarka?"

Kallonta yake da fuskarta dake nuni da dukkan alamu na rarashi da take masa da dadin baki dan ya rarashi yaron da ya riga ya girma ya kai mizalin da yake tunanin shi fa yama isa aure?

Dan musmushin da sam bai gamsheta ba ya sakar mata hakan ya sa ta kalli mijinta dan ya tofa wani abu a maganar,
Sai dai shima bai ce komai ba, domin gaskiya ya fara tunanin dole sai ya bar Rislan da Kharibullah din dan su ganewa junna tsakaninsu dan haka nema ya kawar da kansa gefe yana fata kar Rislan ya yi shirme irin na yarinta ya yi tunanin ai Kharibullah din yayansa ne ya dan kwatanta gardama, dan bai san abinda zai faru ba

Baki ta dan turo ta sake duban Kan giwa ta kuma fadin " Ka kula da kanka, Dukan abinda zaka aikata ka ringa duba da matanka, da kanwarka da rayuwarka kanta wadda nan gaba burina na budi ido na ga yan dagwai dagwai sunna ja min gyale sunna min ihu a kunnena, wannan zai sa na mutu da nutsuwa a zuciyata MUHAMADU"

Murmushi ya sakar mata still da wani salo na neman fitina yana kin yi mata magana bayan ya san ta tsani hakan ya ja hannunsa da nufin tafiyarsa
sake rike hannun ta yi raf tana sake kallonsa da tatare girarta

Fuskarsa ya juyar ya sake juyowa ya ce" Ki sakeni mana madame wai hala a cen zaki shekare ne? To bari ki ji da kika saka mijinki a gaba zaku tafi tare idan niyarku jimawa ki yi ki tataro ki dawo, domin ni dai ba zan iya da yawan maganar mutanen gidan nan ba in ba haka ba na hada su dukansu na kaisu bariki a horasu gaskiya daidai laifinka daidai horonka"

Ido mai sunnansa ya zarro , wato takwaransa sai kuma ya saka dariya irin ta nutsuwar nan yana girgiza kansa ya saka hannunsa ya raba hannayen yana fadin" Jeka abinka in sha Allahu ko mun dawo zan mayar da abata gefe ta ci gaba da ibadarta dan na kula hayaniyar gidanka na sake hada mata ciwon kai, matanka su fito su fuskanci ragamar gidan Kan giwa, fatana Allah ya sadamu da alkhairi"

Murmushi ya yi ya juya ya karasa wajen mahaifinsa ya karra sada kansa sosai mahaifin nasa na yi masa adu'o'in tsari har ya gama cikin dakewa ya ce" Abinda zan sake jadada maka a kai shine, ka kiyaye harkar zinna babana, domin ita din bashi ce, Allah ya shirya min kai ya tsare"

A samaan lebensa ya amsa da amen sannan ya sake zuwa wajen Mamansu dake daura belt itama, murmushi ya mata sosai yana sada kansa a ladafce kamar yadda ta siyawa kanta mutunci a wajensu sakamakon zama da ciki daya da take yi da su a matsayinta na matar mahaifinsu ya yi mata fatan alkhairi, inda ta bishi da adu'a hankalinta kwonce ba wata damuwar ta bar yar autarta a nan, asalima ta sani ne soyayar da yake yiwa auta ta musaman ce, yar kanwarsa ce, autarsa ce, ririta abinsa yake yi son ransa dan a kan auta yana iya rufe ido ya ja masu ba daidai ba

Bai sauka ba sai da ya karasa wajen matuka jirgin su biyu dake zaune sunna dan taba hira dan sun gama duba komai a tsare yake shi suke jira ya fita su daga
Murmushi ya masu bayan sun yi musabaha a nutse ya ce" GENERALS Allah ya sauke ku lafiya"

Da wannan suka yi salama da junnansu ya fice ya yi nesa sosai yana tsaye hannayensa duka biyu cikin aljihunsa yana kallon yadda suka yi tafiya saman doguwar hanyar da ya yi ta bayan gidan nasa wajen jirgin da yake tafiya kafin ya cira har ya cira ya tafi sannan ya sauke ajiyar zuciya yana sake bin jirgin da kallo har ya bacewa ganninsa

Juyowa ya yi a nutse yana tafia
Shi tafiyarsa yake yi dan ya karasa bangarensa domin fita yake son yi duba da yamma ta sanyo kai yana da wajen da zai je, su kuma ma'aikatansa na faman dudukawa dan su gaishe da shi da sauransu, sam bai wani damu da hakan ba dan hankalinsa ba a kansu yake ba, shi baima taba lura da tarin tsoronsa da suke ji ba a rayuwa, yana rayuwarsa ne yadda ya dace ta zo masa, yana aiki yana kuma kasuwanci, yana mu'amala da mutane masu yawa da suke kasansa da kuma da yawa da suke daidai da shi, haka kuma da wa'inda suke sama da shi
A mu'amalarsa da wa'inda suke sama da shi kuma babu maganar tsoronsu ko yi masu biyaya dan dole, ana girmama junna a ilimance, shi ba mai zama bane ko daya, baya zama a gidan na lokaci mai tsayi, idan ya yi tafiyarsa sai ya dawo, idan ya dawo yana fita nema, mutanen dake tare da shi suka fi daukaka lamarinsa ta yadda idan ya zo wucewa akan duka har kasa a gaishe shi ko a yi gagawar nutsuwa da dukkan abinda ake yi dan a bashi girma

Hannun kofar bangarensa ya kama ya murda ya shige kansa tsaye yana dan dage hannunsa da cusawa cikin gashin kansa

Turus ya yi yana kallon tsaitsayen da aka yi tsakanin su hudu, tsayuwar da ta nuna matakin kowa a gidan, kama daga su da suke da shi da kanwarsa mai shi, sai kuma yar aiki zai kireta ko abar kaunar kakarsa dake gefe tana tsaye kamar wace ta aikata wani laifi domin tsayuwar tata wata iri ce kuma a gefe take sosai

Nadiya ce ta fara dubansa da rantsatsen turancinta ta ce" Ur excelency Murja ta ce Grandma tace a nan zata zauna, wai kuma sai tace harda wannan yarinyar....bayan muna da masu aiki sun wadacemu bama son karri?"

Da mamaki ya zuba masu ido yana yaba nasu sallon rainin wayon, watau basu san cewa ya yi mamakin rashin ganninsu a wajen yiwa kakanninsa salama da mahaifinsa ba harma ya kulace su kuma shine Nadiya zata kama sunnan kaka gatsau haka dan rashin kunya? Kai da ba dan sunnan tata kakar a cikin hinduma tsofafin sunnaye bane da idan wuka za'a dora masa a wuya a yanzu ba zai tuna yaya sunnan yake bama bale har ya kama kai tsaye da ya kwatanta, aman zai binciko ko dan ya kama ya sani sarai sai ta yi kamar zata kifa dan sunna girmama nasu sosai

Su kuwa matansa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login