Showing 69001 words to 72000 words out of 124070 words

Chapter 24 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

343

mai neman jarabar dake masu diban albarkar nan a gida ta sauke dubanta kan Hamza dake sanye da kakin sojoji sai kuma Kan Giwa dake tsaye yana kallonsu
Hannunta ta kai wajen habarta gannin irin zaman da mahaifinta ya yi a bakin hanyar hawa yar matatakalar dake sadaka da baban falonsu ta ce" Toh fa Aba yau me ya hadaka da soja kuma?"

Kan GIWA ya gyada kansa yana dai tsaye yana kallon Lokacin da Hamza ya karasa ya rage tsayinsa ya kamo kafar Lawali daya ya aniya janyo shi daga saman nan, kawar da kansa ya yi gefe, domin haka kawai sai ya tino furucinsa a sanyaye da ta ce" Mahaifina ne fa "

Ihu Lawali ke yi da dukan karfinsa, da gudu y'arsa ta yi ciki ta fada dakin mamansu dake waya da air puce a kunnenta bata jin hayaniyarsu bata san abinda ake yi ba ta shiga fada mata abinda yake faruwa bayan ta warce abin kunnen

Sai da ta zarro ido ta dirko ta fito itama a da wani irin sauri tana rike zanninta dake son kubcewa

Bata tsaya ko'ina ba sai kusa da Hamza, da tsageranci irin na y'ar layi wace ta shaku da iya shege ta aniya nuna shi da yatsa tana fadin" Kai, baka da hankali zaka tardo magidanci kamar Elhahji lawali ka ringa ja masa kafa? Uban me ya yi? Ai dan Adam nada yanci a kan me za'a wulakantamu? Ko me muka yi ai sai a bamu damar daukan Lauyyyyyyyyy"

Bai barta ta karasa ba ya lauya mata wani mahaukacin marin da ya sakata jan magar Yyyyyyya din kafin ta rike kumatunta ta fasa ihu tana kokarin dira

A kausashe Kan GIWA da ya juyo barin nasu ya furta" kara mata!"

Wani marin Hamza ya kuma tarota da shi yana kallon Kan Giwa da ya tsareshi da ido yana mai masa kallon iya gudunka kennan?
Wannan karron sai da ya dora ya dira mata wani marin da ta baje a kasa ta shiga burgima da ihun yau Lawali ya kawo mata jaraba har gida za'a kasheta
Belt din da Hamza ya kunce ya nade a hannunsa ya sakata zabura daga burgimar ta tsuguna tana hade hannayenta tana rizgar kuka ta ce" Ka wa Allah kar ka dada min, ni kam me na yi ne? A satin nan ko kayan kowa ban taba ba bale ace na tabo na matar soja , dan Allah in me muka yi a fada mana sai mu bada hakuri da a kashemu kai tsaye "

Hamza dake rike da kugunsa ya saki wani nishi yana fadin" Hasana suke son sannin inda take, wannan din Mijin Nuriyah ne, Nuriyah tawa y'ar gidan Hasana da kika ce ba y'ata bace mijinta ne shi"

Daga Matar tasa har Hamza sai da suka sha jinnin jikinsu a lokacin da sula kallo Kan GIWA, tabas sai yanzu Hamza ya gane dalilin da ya sa Kan giwan ke dan dakatawa da horon Hamzan, ashe uban matarsa ne, to aman ai shi ya shiga uku da ya dagargaje ya janyo kafar mutumen nan, duda ya san ba abu mai sauki bane sai sa Kan GIWA aikata haka, domin su shaida ne baban matarsa Djamilarth din nan babu iya shegen da baya shukawa dan yana uban matarsa, da kansa yake biya yana cewa ai ya isa a barshi kawai ya yi Allah shirye shi, tunda kuwa aka kawo kan wannan akoy matsala ne, kuma bayan wannan yaushe ya karra aure ne? A sanninsu matansa biyu sai budurwa daya Izabel

"Hasana kuma? Wace hasanar?" Ta fada tana zarro idannuwanta a haukace hankalinta na sake tashi

Lawali ya yarfe hannu yana kawar da kansa ya ce" Wace kika daka kafin ki mikata wa....."

" Lah ka yiwa Allah ka rufe bakinka na mikata wa wa? Na mikawa wa ita? Inace kai kace tunda ubanta ya gudu da kudin da ka so ka yi masa fashi ya tafi da komai sai gida ya bara mata kuma ka siyar da gidan ta haifi y'ar da sam bata kama da kai ba y'arka bace kai kam ka saketa ta je? Ni kuma nace idanfa ta samu danginta suka dawo aka rufeka fa? Shine ka kori mai mata aiki da kanka ka hade su da sale a daki daya yake haike mata daga baya kace ya aureta ya kaita inda zai kaita ko ba'a yi haka ba?"
Ta fada da ihun da ya saka shi zarro ido da baki da mamakin shari irin na mace yana kallonta ya ce" Yanzu ni zaki yiwa wannan karyar yau? Ni zaki saka a uku? Du irin abinda kika ringa turani ina aikatawa kuma da wannan zaki karra saka mini? Ashe haka kike? Da kike cewa ko me ya taso kina tare da ni ashe burga ce? Yau tsal a nan kawai har kin fara fadin haka? Dama karya kike yi? Dama soyayar ta karya ce? Cikinta karya ce?" Ya fada da murya mai raunin gaske irin wace zata nuna maka cewa abin ya fara dira masa har cen kasan zuciyarsa

Tana kallonsa ta ce" Ka ga Aban ihsan ka daina maganar soyaya a nan gaskiya, kai fa kace mijin y'arka ne du tsananin azabarka ba zata kai tawa ba, dan haka gaskiya ka daina hadani da wannan abin, shekara kusan goma sha tara a zo yanzun a hadani da wata fitinar da ba zan iya dauka ba? Aa ni bana ciki"

Hamza ya kalli Kan giwa ya ce" Sir me zai hanna a kirawo sauran ne mu zane su?"

"A zane mu kuma dan Allah kar a zanemu dan Allah ka hanna a zanemu harda mahaifin matarka fa?" Ta fada tana kallon Kan Giwa hankalinta na sake tashi domin a lokacin ta fahimci wanene , dan a dazun kwata kwata bata gane shi ba walahi

Kan GIWA ya maida dubansa kan mai gadin da tunda ya tsuguna kamar ya mace a haka bai dago ba, ya sake kallon sauran baki daya harda budurwar da ya kula a tsayen nan da take kamar fatar jikinta ta fi damunta da wulakancin da iyayenta ke ganni

Dan haka ya kalli Hamza a nutse ya ce" Hamza ka kamo wancen itama ka fara zanetan kafin ka kirawo sauran a hade su kawai , bara na je na dawo sai mu ga abinda zai samu, ko summa aka yi kar ka bari"

Ai kam Hamza da wata rawa raw aya karasa ya damko hannun ihsan da ta tsala wani uban ihu ta silale a kasa tana ja yana ja, gannin zata bata masa lokaci ya kinkimota ya watsota kusan iyayenta sannan ya aniya lafta mata belt din nan
Ya mata lafta biyu ya dakata jin abinda take fadi da bakinta tana rike da zannin mahaifiyarta tana ja itama tana ja Da kuka take fadin" wayo mama fuskata, kar ya dakar min fuskata, kar ya lalata min fuskata, wayo mama ni kuma ina ruwana da wannan rigimar ne?"

Belt din nasa ya ajiye ya gigibota daga jikin uwar ya aniya riketa da kyau domin wajen da bata so ya lalata din zai farauta, dan ya gane me yasa uban gidan nasa ya nemi da a taba yarinyar, dan kuwa cikin biyu ne a yi daya idan uwar bataa falasa ainahin abinda yake faruwa ba, to fa y'ar zata fada ne da kanta sanadiyar kukan y'ar

Daya tak ya fala mata ta saki fitsari a dogon wandon yan gayun nata ta nemi sumewa
Muryar kukanta a ciki take fadin" Walahi, walahi ko haihuwata ba'a yi ba da suka aikata wannan abin, ni dai nakan ji Mama na yawan magana da wani kanninta a cen anguwarsu takan ce masa kar ya bari ta ji dadin duniya ya gana mata azabar da zata kasheta, na sha ji Mama na cewa matarma yar wulakanci ce ta ki mutuwa, kuma akoy lokacin da na tsinci maganar Mama da kawarta cewa a sume suka fitar da ita suka shedawa anguwa ta mutu ne zasu kaita wajen danginta a rufeta, daga nan suka batar da ita , ka ga Allah banda ni a ciki sunne"

Lawali da zuciyarsa take masa daci sosai ya kalli matarsa ya ce"Ashe haka mata suke? Da kin san irin karyar da na sake harhadawa dan ki kubuta da baki fadi haka ba, imace kece kika sake zaunar da ni a kan maganar yarinyar nan ba tawa bace? Kuma ke kika shaketa har ta summa muka fitar da ita muka kaiwa kanninki dake taadanci muka bashi ita , ni dai daga nan ban kuma jin labarinta ba, "

Ya maida dubansa kan Hamza ana fadin" Yalabai, tabas nine mai baban laifi a cikin tafiyar, nine na sayi yan daban da ita ta hadani da kanninta ya kaini wajensu muka yi da su zasu dira su kashe kowanta sai ta ci gado, itama na kasheta na malaki komai, ban san wa ya fada masu ba, suka gudu suka bar gidan da suke ciki kawai da takardarsa da kayan ciki, da wannan bakin cikin ma hango da yawa an barni da kadan na ringa gana mata azaba, dama ba wani dadina take ji ba, ta gabatar da ni gidansu na zama tamkar bawa na masu biyaya kaina a kasa na nuna masu ni maraya ne gaba da baya bayan iyayena a raye sunna cen anguwarmu na gudu dan son abin duniya da takama da kyauna dake daga darajata a kan ta wasu samarin, na samu na malaki zuciyarta na aureta da yardar budurwata wannan, mahaifinta ya sakani a kampani ya bani matsayi daidai misali domin ba wani karatu na yi ba, shi kuma mutun ne mai akida baya take abinda ya yi niyya sai idan ka bi tsarin da ya kamata, wanna yake min ciwo gannin ina aurar y'arsa aman ya ki sakar min komai, duda babu abinda na rasa na rayuwa , ina hawa mota, ina saka suturu na alfarma, iyayena kuwa na watsar da su na zubar , idan na shiga anguwar nan dan na ganta ne na kai mata kudi, kulun muna tare da ita tun kafin mu yi aure, gatanan da cikin baban danmu ta shigo gidana, daga nan ta ci gaba da sake saka min tsanar Hasana, da bayanar min da komai, sai dai na san idanma da saka hannunta to fa nine mai baban kaso, a yanzun kam na gama fada maka gaskiya, walahi walahi daga lokacin nan ban kuma bi ta kanta ba, ban san inda ta kaita ba, dan haka maganar y'arta ta yiwu gaskiya ne" ya karashe yana sake sadda kansa dan ya sani ne a yau kam tashi ta karre, karyarsa ta kare, rana daya ta mai kaya ce ta same shi

KAN GIWA sai da ya ji kamar zai yi loosing din control, da kyar ya daidaita nutsuwarsa ya dawo gidan ya tsaya yana binsu da kallo daya bayan daya

Wannan karron da kansa ya damko wuyan matar Lawali ya mata wata jijigar da ya cirota da dandar kasa ya riketa a sama
Idonsa idonta ya ce" Ina take?"

Da muryar guguwar tashin hankali take fadin" Tana hannun kanina, ban san a ina ya ajiyeta ba aman a wajenshi take, jiyama mun yi waya da shi tana wajensa na rantse da girman Allah!"

Sakinta ya yi ya kalli Hamza yana fadin" Ka tabata ka fito da ita ta kaimu wajen kannin nata, su kuwa ka barsu, da ita da y'ar uwarta da y'arta zasu tsayar da magana kan su rufe su ko su barsu domin akoy y'a a tsakani"

Daga haka ya fice ya bar Hamza da su, wanda sai da ya sake wujijiga su tamkar zai kashe su da balaki sannan ya barsu yana fadin " Gwarama ku kai kanku da kanku, domin idan oga ya yafe gaskiya Maza fa sun ga gidanku, na tabata zasu biyo dare su karasa ku, domin barin irinku a doron kasa hatsari ne baba!"

Da ita ya fito da lafcecen hijab dinta kamar zai kayar da ita kamar ta Allah , ga wayarta a hannu tana tafe kamar zata kifa ta sake gwada kiran kannin nata



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
4?? 4??



Kira ta sake buga masa tana tafe da kyar, wuyanta wani irin zafi yake mata, mutanen anguwa kuwa sun cika makil kamar zasu manna mata ido da baki a jikinta, yau ita hajia itace aka tiso a gaba ? Sai da ta ce da Yusuf ya kashe matar nan yace aa a barta wahala zata kasheta, babu yadda bata yi da Yusuf ba aman firrr ya kiya, yau gashi an sameta bata shiryawa haka ba kai tsaye za'a kaita? Ta san ta zama kamar kashi komai nata ya bace batt ta zama abar tausayi, ta san idan aka ganta a cen za'a harbeta dan girman laifinta, ta san a yau tata ta kare, tun daga nan ta san idan har ta kubuta daga wannan abin to fa fa kafarta zata gudu a anguwar nan, dama jira ake a ga ta ci baya ta lalace, dama jira suke su ga ta komaa baya , yau gashinan tata ta sameta

Jiki ba karfi ta shiga bayan motar tana waya da shi, daga muryarta ta so ya gane akoy matsala, sai dai bata san rashin hankalin Yusuf ne ya kai haka ba sam bai fahimta ba, saima irin kwatancen gidan da Hasanar take da ya bada dala dala ba tare da ya yi kuskure ba, kwatancen da ya bata mamaki domin a da a sanninta a jiyama yace a kauye take kuma a buka irin marar gaba da bayan nan, a yanzu kuwa ya yi kwatancen cikin gari hankalinsa kwonce abinsa, har ta sake maimaita masa hasana fa take nufi ya nuna mata ya gane?

Shiru ta yi ta ja hijab din ta rufe ko'ina na jikinta tana fatan Allah ya fitar da ita lafiya suka daga suka dauki hanya

Basu yi wata tafiya mai nisan balaki ba suka karaso wajen da ya yi kwatancen

Basu kuma kiransa ba dan kar ya gane ya gudu , haka itama basu barta da wayar a hannunta ba ,

Da wajen da ya yi kwatancen Kan GIWA ya fara ganewa ya parker Babur dinsa ya sauka a nutse yana sake bin anguwar da kallo da mutane uku dake tsaitsaye cikin shiga sasauka sunna kallon motar da kuma Kan GIWA

A kausashe Hamza ya saukota ta hanyar kama hijab dinta kasa daga bakin motar yana fadin" Ina ne gidan ki bude idannuwanki da kyau mana"

Da sauri ta ja hijab dinta tana fadin" sai mun sake kiransa ai yalabai"

Wata murya mai karfi irin ta maza ce ta furta" Ba sai kun yi kirana ba ai gani daga nan aunty"

Kan giwa ya fara sauke dubansa a kan mutumen da ya yi maganar, cikin shigar jalabiya yake shima da hularsa da kuma carbinsa a hannunsa, kana ganninsa yana da baki sosai aman kuma yana da annurin da ba'a san ko na menene ba

Itama ido ta tsura masa tana furucin" Yusufa kaine? Yusufa ina matar nan take ne? Dan Allah kace da ranta ka ji Yusufa?"

Shiru ya yi yana kallonta bai furta komai ba, hakan ya hasala Hamza ya nufo shi yana fadin" Kai mu fa a nan ba maganar shekara mai laifi ta kansa muke bi kawai ka yi magana da sir fa muke tsaye"

"Kar ka taba shi " Kan giwa ya fada yana duban Hamza, kafin ya sake fuskantar Yusuf ya ce" Dukan da zaka masa, ko kashe shi zaka yi na zai saka ya fadi maganar dake ransa ba"

Ya sake duban Yusuf sosai ya ce" Inace da ka fito daga gidan yari da kanka ka fada min cewa ka ajiye komai zaka koma ka bautawa Allah, me ya sameka bayan nan?"

Sai a lokacin Yusuf ya saki wani Murmushi yana kallon Hamza yace" Oga wannan yaron naka irinsu ke mana Dukan mutuwa basa gane irin dabarunka su saka mu magana, har na sare dan ba zan manta dukan da na ci a kan maganar satar Laria ba"

Shima murmushi ya yi ya mika masa hannu suka yi musabaha yana furta" Ba san me yasa kuka zabi a taba lafiyarku da ku fadi gaskiya ba, "

Yusuf ya ce" Taurin kan ne ke hadasa haka"......

Kan GIWA ya fuskanceshi sosai ya ce" Wace aka baka horo abokiyar tagwaitakar matar mahaifina ce, ina fata baka ilatata ta yadda zamu sake fadawa a halin rashin dadi ni da kai ba"

Wajen da yayarsa take tsaye ya juya yana kallo kafin ya kama hannun Kaan GIWA suka nufo soron gidan nasa suka ja suka tsaya yana fuskantarsa ya ce" Kwarai na bata horo, Hasana da kake gani a lokacin da aka bani ita jeji na kaita na yi buka na sakata, na bar mata tukunya da gero da dan abinci, idan na je ta'adancina nan wajenta nake guduwa na buya idan na san ana nemanmu, sannu a hankali nake dan karra siya mata dan kayan abinci idan ta raya min, domin a zamana da ita na yi zagi na yi duka na yi fada sai dai ta sada kai ta yi kuka, kulun tana azumi, kulun tana ibada, sallar dare kuwa inaga ko liman ya ganta nan ya barta nan, bata taba min gardama ba, haka kuma bataa taba yarda mun kwana daki daya ba, watau hasana mace ce mai kamun kai......zan takaice maka oga a haka na karasata wani kauye muka samu dan gida na kama mana mai daki biyu, hasana sai ta shiga yar sana'a bayan na yarje mata da kyar take siyar da su awara ne da sauransu, bata hulda da kowa, aman akoyta da son yara da taimakawa tsofafi, babu wanda zai ce yau ya san cikinta domin bata bude shi wa kowa ba, haka kuma sau uku tana samun damar falasa ni aman bata aikata ba, ban san dalili ba, a haka har lamarin Laria ya samu aka kaimu gidan maza, Oga tunda na shige yan uwana da iyayena du sun ji babu wanda ya taba kokarin lekani ko taimaka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login