Showing 12001 words to 15000 words out of 124070 words

Chapter 5 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

324

mata wajen da zata kasance cikin kwonciyar hankali, aman sai kayi min alkawaririka da dama


Mubarack yayi murmushi yace" Aba , KO wani alkawari kake SO insha Allah zan yi maka kuma da yardar Allah zan kiyaye

Malan isyak ya ce" da farko dai ka kula da lamarin yarinyar nan, duda ni zan rakata da kaina sannan da sunana za'a rubuta ta ? wannan gida, aman ina SO yanda zaka kula da abinda kanwarka ke ciki itama haka,

Na biyu ina son du ranar da kake aiki ka bugo min waya mu gaisa da ita,

Mubarack na SO ace ka SO yarinyar nan na aura maka ita, sai dai kash yanzu duniya ta canza, ba kai nake ji ba, aa, ita yarinyar kar tauye hakin yayi yawa, aman insha Allah da safe zan dauketa mu tafi tare

Mubarack ya ce" Aban mu, nayi alkawarin zan kula da lamarin Nuriyah mudin raina na gangar jikina

Malan isyak yayi murmushi ya ce " Allah yayi maka albarka

Garin Allah na wayewa bayan ta gama sallah ta fito da niyar fara aikace aikacen ta, tana fitowa abin mamaki sai ta ga abansu zaune da farar jalabiyarsa har kasa ya dora dan mayafin nan da limamai ke dorawa a saman kansu,

har kasa ta duka tana gaishe shi, inda cikin sakin fuska yake amsa mata,

Nuriyah, karki fara aikin nan, ki je kiyi wanka ki canza kayanki ki fito mu tafi kinga sauko ake yi fa " cewar Malan isyak Yana kalonta

Ba tare da ta tambaye shi inda zasu ba, ta mike ta je tayi yanda ya ce, ta saka doguwar abayarta baka ta dora hijab dinta fari kar ta dauko nikaf dinta ta saka silifas dinta Ta fito zuciyarta cike da tunani kala kala, na inda zasu tafi, sannan da muguwar fargabar yanda zasu kwashe da Habiba

Tana fitowa ta tarar da Habiba ma ta farka tana zaune sai iya yi take yiwa mijinta,

Habiba ta dago tana kalonta cike da mamakin wanka ne tayi da safiyar nan, ina zata je,

Bata gama tunaninta ba taji Aba na cewa " yawa bismillah mu je

Habiba ta ce" Malan ban gane ba ku je, ina zaku tafin ?

? hankali malan isyak ya juyo ya c???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?e" zamu je na kaita *Neman na kanta* ne, kinsan gwara ta kara kaimi KO ta ringa kawo maki ? Nairori Kina rabawa Kina bawa Farida tana saka Kati dan ta ji labarin saurayinta na kasar waje

Yana gama fadar haka ya bi bayan Nuriyah da ta dade da fita ya bar Habiba tsaye cike da fargabar daman ya san abinda yake faruwa ?

Tafe suke ? cikin Adaidaita sahu, inda Mubarack ya zauna ? gidan gaba, malan isyak Yana gidan baya zaune da Nuriyah, a tsakaninsu za'a iya saka wani mutun din, cikin nutsuwa Aba ya ce" Nuriyah

ta dan juyo tana kalonsa

ya ce" shin kin yarda da ni ? Kin yarda bazan yarda wani abin ya cuce ki ba ?

Nuriyah ta gyada kai

ya ce " alhamdulilah, wato nuriyah na san du abinda kike ciki, ina sane da irin kangin rayuwar da kike ciki nan da sati guda na gani da idannuwana, ina mai baki hakuri, ina rokonki da ki yafe mana

da sauri Nuriyah ta ce" Aba ba komai, ni ban taba rike kowa ba Aba

malan isyak yayi murmushi ya ce" masha Allah, Nuriyah, zamu je ne na kaiki gidan da Mubarack yake aiki, nan da yan kwanaki da suka shige Mubarack ya Zo min da shawarar na.................... ......... Nan ya kwashe du yanda suka yi, da yanda ya ringa bin bayanta, da yanda su baba suke magana ? kanta, da komai da komai, har zuwa shawarar da ya yanke na hakan shine kwonciyar hankalinta

kwarai nuriyah tayi amana da hakan, duda bata san mai zata kuma tarar ba, aman ta sani bazata kuma fita yawon aiki ba, sannan ai shima wannan din *Neman na kanta* ne, hakan ya sa ta nunawa malan isyak amincewarta harma ta amsa da amin daidai lokacin da suka yi adu'ar Allah ya sa a dace su dauketa


tafiya ta fi ta awa abinka da go slow ga nisa,

wasu irin shukoki ne suka fara shigowa irin maina manya manyan nan sunyi runfa , wata iska mai dadin sanyi ne ta fara buso su, abin mainan nan ya dan lulube wajen sai ba'a gannin hasken ranar da ta kyanlare garin , daidai wata igiya da wani soja ? tsaye ya tsaya Yana cewa to daga nan bama iya tsanlaka gidan kan giwa

? nan suka sauka suka bashi dubu biyu da dari takwas wai dan ma na gida ne

tun daga bakin wannan igiyar Nuriyah ta saki baki tana mamakin irin wannan tsaro, duda Mubarack ma'aikacin gidan ne aman du inda ya Zo sai ya tsaya an caje su ya nuna takardar da Hajiya tayi sinye ta buga tambarin kan giwa sannan su samu hucewa, sannan ? tsakanin wata kofar zuwa wata akoy soja biyar kowane tsaye da bindigar sa a dane Yana jiran ta ware KO ta walare,

suna zuwa get na uku aka ce ai dole sai ta cire nikaf dinta da safarta na hanu da kafa,
ba yanda ta iya domin ita wani irin tsoron su take tunba idannuwansu ba, kowane yayi ja gashi hausar kirki ma basuda ita, hakan ya sa kafin ya rufe bakinsa har ta ja ta cicire ta mika masa, sannan suka shige

Wata bakar mota ce mai shegen kyau ta daukesu da alama idan ka ISO nan wannan motar ke dauka ta karasa da kai can cikin palas kan giwa,

A cikin motarnan ba mai gannin kofa, wato dai baka iya ganin abinda ake ? kofar sai mai tukin kadai shima dan ya saka gilas ne Wanda zai haskaka masa bakin madubin motar,

Wasa wasa gurugudu Yake aman sai da suka shafe minti ashirin sannan ya ja ya tsaya inda ya ce " Aboki, kafa caba hajiya Na Yinka

Mubarack yayi murmushi Yana cewa " sai na sako akoy magana, sannan ya rufe ya tardo abansa da Nuriyah da suka yi Shatata Da baki suna kalon wannan ikon Allah,

Mubarack na karasowa kafin yayi magana malan isyak ya ce" Mubarack yanzu wannan abin idan muka hau bazai fashe mu fada ciki ba ? , sannan ina kofar shiga ? Mubarack kaina juyawa yake yanzu da mutane ? ciki ? Mubarack wa'innan maduban basa tsoro su tarwatse su rufun musu ? Shin Mubarack sun san kuwa ana mutuwa ?

Da sauri Mubarack ya tare mahaifinsa ya ce" Abana daukakar kenan, da jama'a ? ciki, iya nan ne mai madubin mai yawa haka dan bangaren hajiya farar kasa ce mai kyan gaske sai shukoki, mu je Abana ba abinda zai samemu insha Allah

haka suka dunguma itama sai sauri take domin matukar tsorata to a tsorace take, idanuwanta sun kasa tsayuwa sai juya kwayar cikin take cikin firgici da tsoron fa anya har yanzu suna cikin duniya ???

Suna shigowa wajen daukan yan aikin suka tarar yan mata, mata, samari, da kuma manyan mazan, kowa ya ci kwaliya ya hakimce harda nasaru sun sha kananun kaya wai sun Zo neman aikin aikatau ? gidan kan giwa,

? hankali ya mika takardar aka mikawa wata mata dake hakimce, ita ce mai alhakin kulawa da daukan masu aiki, sai ? wannan lokacin Nuriyah ta hango wasu matan zazune daga can sama, da wani gilas fari ? tsakiya Wanda ya kare su,

Murmushi ne ya subuce mata lokacin da ta hango tsohuwa mai sadakar waina ta hanyar yan wankin hula, wani mamaki kuma ya dirar mata ? lokacin da wannan matar da aka mikawa takarda ta Dago ta ce" *Nuriyah malan isyak*

Nuriyah tayi saurin mikewa tana amsawa da na'am

? tare suka juyo suna kalonta, inda wannan matar ta ce" no, bazai yiwu ba, yarinyar nan ba karatun shukoki tayi ba, ba karatun girki tayi ba, ba wani digiri KO shaidar tayi karatu gareta ba, Hajiya kiyi Hakuri aman kan giwa yayi gargadin kar mu saki mu dauki irin hakan,

Daga saman nan sai muryar wannan mata tayi salama, ta ce" ke, inada tambaya, nace wai inada tambaya, da ban haiho Karibullah ba, da zai haifo kan giwa ? To dan ubansa ni nan ni nace ? daukan min yarinyar nan, ni na yarda da ita,

Wace take da hakin zabar ma'aikatan gidan ta dan juyo gaban computer ta, wace da alama mutun ne ke sauraronsu kuma yana ganin komai, ta ce" Oga kan giwa, yau ga abinda da Hajiya ta dora

Kasa kasa kake Jin kamar Yana waya, can yace" to dad, za'a daukar mata, ba shikenan rigimar ba? ,

Can ya ajiye ya ce" ki dauketa daga ita kar ? kuma daukan KO wacece indai ba shaidar takardu, ita kuwa Allah ya shiryeta


Daga saman ta ce" Allah ya shiryi ubanka dai, wato na ma zare KO ? Ba komai, yarinya kuma ? daukan min ita ban ce a rubuta mata takamaimai aikin da zata yi ba, ni nan zan bata aiki


Daga cikin computer ake cewa " idan idan ka kuma yiwa mamaana magana zan saba maka, haba ka barta mana

Yayi saurin kashe camera dan kar su ji abinda zai fada

Nuriyah aka ja zuwa dakin hoto,inda akayi mata na carte aka lika ? kusan sunanta wace zata Bata damar shiga KO'ina ? cikin gidan ? matsayinta na ma'aikaciyar gidan, nan da nan aka bata wasu suturu ? cikin wata jaka wace ake ja ? kasa da kuma ky na dakinta Wanda yake ? bangaren su Hajiya,

Tana ji tana gani tayiwa su Malan isyak salama harda hawayenta domin kwarai ta tsorata da irin wannan daula, KO Yaya zata rayu ? wannan gida ?



Shin waye kan giwa ????, ya rayuwar Nuriyah zata kasance ? gidan kan giwa ?????????? =?K? @&=ض? @&=ض? @&
*>?&? @&>?&? @&>?&? @& NEMAN NA KAINA>?&? @&>?&? @&>?&? @&*


Marubuciya: *SAJIDA*


*P+


*(12)*




A hankali take takawa tana biye da Mubarack Wanda yayi mata jagora dan ya nuna mata gefen Hajiya,

Wani get din suka kuma shiga, Wanda suna shiga wani sanyin dadi ya kuma ratsa su, ? hankali Nuriyah ta lumshe idanuwanta daidai lokacin da kafafuwanta suke nutsewa cikin farar kasar balbalin gidan, abubuwan kiwo suka fara daukar hankalinta domin daga gefe du tsuntsaye ne masu kyau sannan manya manya, harda su dawisu du sai dan zagaye suke a balbalin gidansu a wadace,

Tana ta waige daidai inda suka karaso wajen shukoki na fulawowi, sai wata uwar mangwaro wace tayi babar runfa, sai yar runfa irin ta gargajiya anyita ta dan zubo gwanin ban sha'awa, ni'imar wajen kadai ta Isa ta saka bawa cikin nutsuwa,

? wannan lokacin Hajiya tsohuwa da Elhaj tsoho suna saman mamakekiyar terass dinsu wace suke zama da safe har zuwa lokacin bacin su yayi su koma ciki, sai kuma fitowar yama

? hankali suka taka yar matatakalar da sai an hayeta ake hawa filin, suna hawa Mubarack yayi salama inda itama nuriyar tayi salamar

? tare suka juyo suna ansawa inda Elhaj tsoho ya ce" Dan gidan hajiya, kanwar taka ce ba ??

Mubarack ya dan duka alamar girmamawa ya ce" eh Aba ita ce

hannu hajiya tsohuwa ta mikawa Nuriyah tana cewa kinga Zo nan y'a ta, ki je kiyi wanka ga dakin ki can ki kwonta ki huta, za'a kawo maki abinci, zuwa gobe insha Allah sai na fada maki dan abinda zakina yi kin ji ?

Nuriyah ta gyada kanta tana farin cikin kasancewarta ? karkashin innuwar hajiya, domin Sam bata da kyankyanin talaka

Cikin nutsuwa ta nufi dakin da aka yi mata nuni, ta bude da ky din nan ta shiga da adu'a sannan da salama ? bakinta,

Sai da gabanta ya wani fadi dalilin tsaruwar dakin, gado ne ? jikin katangar sai sip, Da coiffeuse mai madubi ? hade wada kana iya gannin kanka ? ciki Gaba dayanka, gefe dama na gadon kur'anai ne da litatafan musulunci, gefen hagu kuwa bible ne sai kuma yar sarka irin ta christocin nan mai +,

? hankali ta taka ta karasa shiga, daman ba abinda ta dauko daga gida hakan ya sa bata da komai a nan, cikin nutsuwa ta dan zauna ? kasa tana kalon dakin tana tawasali ga Allah da ya bata wannan kyauta,

ta kusan shafe minti ashirin, Kiran sallar la'asar ta fargar da ita, masalacin tamkar ? kofar dakinta, cikin azama ta Mike ta fada bayin inda nan ma ta tsaya kalon tsaruwar sa, ? hankali ta ce" Gaskiyar Aba da ya ce, shin sun kuwa san ana mutuwa ? Nan wai dakin yan aiki to ina da nasu ? , ? hankali ta lumshe idanuwanta ta ce" ya Allah, ka sa wannan dukiyar halal ce, ya Allah kar ka bani ikon cin haram ? cikina,

Wanka ta tsala da sabulun dake bayin da sabon soso, sannan ta bude sabon brosh ta kama darzar hakoranta har sai da taji su fara zafi ta Bari, ta dauro alwallah ta mayar da abayarta ta fito ta tada sallah,

Tana gama salolinta ta kama karatun alkour'ani inda kwarai nayi mamakin daman haka take da karatu ? kanta ?

A ranar nan tayi ibada har ta more, rabonta da irin wannan ibadar har ta manta, sosai ta roki Allah subahanahu wata'ala kan lamuranta, haka innarta ,

Bayan sallar isha'i aka kawo mata abinci kaya guda inda ta tankwashe kafafuwanta ta kwashi abincinta hankali kwonce tayi hamdallah, tana faman tashi aka kuma bugawa, ta bada izini aka shigo

Wani farin fata ne, wato nasara ya tsaya ya ce" hi

Nuriyah ta dago ta danyi murmushi, ya matso cikin turanci ya ce" ni ke kula da ganin idan kowa ya ci abinci, sannan na fadawa kowa kayan da zai saka domin kowace rana da kayan da ake sakawa na masu aiki ? gidan nan

Nuriyah ta dan fahimci inda ya dosa, domin bokon nata ba har can bace, hakan ya sa ta bishi da kalo inda ya nufi sif din nan ya ja ya bude,

Idannuwa ta waro, tana mamaki, kenan na dazu da aka bata na ranar nan ne wato talata,

Jawo wasu bakar siket da jar Riga ya mika mata, ya ce" wa'innan sune na laraba, sai takalma kafa ciki, sai kuma wannan dan kwalin shi zaki Yana, ki kula banda kazanta, sannan gashin kanki ki tabatar da kin tsefe idan ? kitse yake ki wanke ki daure, ina fatan kin fahimta ?

Nuriyah ta gyada kanta tana mamakin irin tsare tsaren gidan nan, wannan KO dai gidan shugaban kasa aka kawota ???

Bata kwonce kan nata ba, tayi kwonciyarta nan saman abin sallarta, ta gyara tayi adu'a ta dukunkuna da hijabinta, carbin da ta tarar ? nan ? hannunta tana ja har baci yayi awon gaba da ita

kamar yanda ta saba farkawa tun karfe biyar, haka ta farka, yauma ta fada bayin tayi wanka iya yinta ta fito tayi sallah, ta ja carbinta, sannan ta Mike ta dauko kayan nan, ta daga sket din tayi tayi ta shigeta aman ina wajen duwaiwanta taki shiga ga shegen kwari,
Zama tayi ta dafe goshinta domin bata san ya zata yi ba, sket din irin na ramamun nan ne, shi kuwa bai gane yannayin jikinta ba dan ? lulube take sai kawai yayi aiki da ramar kafadunta ya ciro mata

Kuma mikewa tayi tana kokowa da sket din, sai ji Tayi An shigo Da salama

Idanuwanta ta zaro zata fada bayan gadon dan ta labe jikinta tana dan sakin kara na firgitar tarar da ita ? hakan da aka yi..............


Shin wanene ya shigo ????? >?&? @&
*>?&? @&>?&? @&>?&? @& NEMAN NA KAINA>?&? @&>?&? @&>?&? @&*


Marubuciya: *SAJIDA*


*P+


*(13)*



Hajiya Murjanatu ce, wato Hajiya tsohuwa ta shigo tare da wani saurayi fari kar tamkar dan larabawa,

Da sauri ya juya Yana kalon kofa inda Hajiyar tayi saurin nufarta tana cewa" Ya rab, Nuriyah kiyi ? hankali mana karki jiwa kanki ciwo plz

Kamota tayi kunya kamar zata nitse cikin kasa tana ta sine kai

Hajiya ta duba cikin sif din ta dauko wani sket din Wanda yafi wancen girma ta mika mata tana cewa saka wannan tabas zaiyi

Nuriyah ta karba ta saka ta gyara rigarta tana dan kara jan ta dan ta kara sauka kasa sai dai ina bakin tsayinta kenan

Hajiya ta ce " tashi mu tafi na nuna maki yanda zaki jera min waina ? cikin Baban roba dan na tafi kar rana tayi

Tana fadi ne tana tafiya gaba da wannan saurayi Wanda tayi Kira da Rislan

Falon hajiya suka shiga Wanda ya kawatu da irin adon mutanen da, wato dai harda su wata kwarya ta sha Zane abin sha'awa,

hajiya ta juyo ta ce" Nuriyah ki shiga ki ce su baki kayan aikin

Nuriyah ta juya ta shiga kofar da aka nuna mata, Inda Rislan ya rakata da kalo, ya juyo ya ce" waouh, Hajiya, ? ina kika hadu da Yar ethiopia ? Sannan ta iya hausa ?

hajiya tayi murmushi ta ce " ba yar ethiopia bace, inajin dai ta cakulu da filani baka ganin yanayin tsarin fuskarta, ni abinda yake bani sha'awa da ita nutsuwarta, shiru shirun nan Bata yankawa kowa ba bare ace tayi

Rislan har zaiyi magana sai gata ta kuma fitowa da katon tarmous ta shiga zuba wainar da aka toya take ta kanshi, ? haka har ta gama ta rurufe, Hajiya sai sannu take jero mata, can ta fito ta ce" Yawa Nuriyah, ki tabatar kin tsefe kanki kafin na dawo dan ? gyara maki gashin nan naga kitson har ya bace

da sauri Rislan ya ce" na rakata wajen momy saloon tayi mata irin na auta ta gyara mata kan da kyau

Hajiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login