Showing 51001 words to 54000 words out of 124070 words

Chapter 18 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

337

ringa hanna kawarkima sha domin yana hadasa rashin lafiya kin ji?" Ya fada da sanyayar hausarsa a lokacin da yake fuskantar NURIYAH

Da wani mahaukacin mamaki ta dago dara daran idannuwanta ta sauke a saman fuskarsa mai cike da kwarjini da girma irin ma daraja, lokaci daya kuma ta maida duban nata kasa sak jikinta ya nemi kwasar bari
Abin ne ya zo mata wani iri a kuma lokacin da bata taba hango shi zuwa ba
Dama yana magana a hankali haka?
Idan bata manta ba maganar da ta hadata da shi sau dadin da yan yatsunta suka yiwa yawa ne shima a kan karin ta bata masa ya daka mata tsawa na farko a gaban Kakarsa wace ta hanna ta shiga tsakani, sai na baya bayan nan da suka zo a haguncen da ba zata iya tantance girman bacin rai ko akasin hakan ba, shi yasa take jin tsoronsa take kuma shayinsa duda ko ma'aikatan da suka cika zuzuta tashin hankali irin nasa babu wanda zai ce yau ya tardo shi ya ci zarafinsa dan kawai yana aiki a karkashinsa, tabas ana zafin fitar da kai a aiki idan aka fuskanci baka san girma da darajar aikinka ba , wannan kuwa masu tantance ma'aikatan gidan ne keda hurumin haka ba shi ba, suma kuma a kan aikinsu suke na kar su bar abinda zai batawa uban gidansu rai
Lokaci daya ta ji kamar sai ta janye wata gingirmemiyyar rantsuwa ta gitta kan baa zasu kuma duban ice cream ba daga ita har kanwarsa tunda abu ne da baya so, sai ta ji kamar ta zube kasa warwas ta daga hannayenta ta ce da su da alewa mai zaki sun yi hannun riga, ko ba komai KAN GIWA ai KAN GIWA ne
Sai dai gaba daya ta kasa tabuka dayan biyu sakamakon rikicewar da ta sameta har ya bar wajen bata sani ba tana kamawa tana kuncewa har sai da Murjanatu ta tabata tana fadin" Hei???????" Ta yi firgigit kamar aan wanka mata mari tana kallon ko'ina dan neman inda yake aman bata ganshi ba

Tana nunawa bakinta na bari ta ce" Auta, yayayayayaya kin ji wai magana ya min a hankali ya ce nima da ke mu daina shan zaki dan zai ilatamu? Ya ce yana hadasa rashin lafiya, ya ce........................"

"NURIYAH?" AUTA ta fada da sauri dan ta dakatar da ita domin ta kula a rikice take

Dif ta yi tana kallon Auta ta kasa amsawa

Murjanatu ta ce" Menene?"

NURIYAH ta nuna mata saman table din sai kuma ta dubeta ta ce" A hankali ya min magana Auta.......... Dama yana magana a saukake haka?"

Murjanatu ta yi Murmushi tana komawa ta zauna ta nuna mata wajen zaman itama

Zaman ta yi dan ta daina yawo da kafafuwanta domin ta kasa tsayawa waje daya tana fuskantar Murjanatu

Murjanatu ta ce" Yana magana a hankali Nuriyah"

NURIYAH ta girgiza kanta da sauri ta ce" Auta, a hankalin nan? Auta ashe shi din ya san darajar dan Adam, idan ka bata masa ne ransa ke baci har ya nuna?"

Murjanatu ta sake yin yar dariya tana kallonta ta ce" Shi kuwa ya san darajar dan Adam, ina mamakin wani lokaci da na kama hirarsu a kicin sunna cewa baya magana, akoy wanda ya kai yayanmu surutu idan ya saka kansa kuwa? Shi baima cika son body language ba ai Nuriyah"

Nuriyah bata gane meye Body language din ba, aman matuka yau ta samu kanta a farin ciki da ta ga wai itama yar aiki ficik karshen karshe a gidan nan marar takarda ko ta sisin kwabo an mata magana da sanyi kuma an nuna mata kan lafiyarta ne harma aka hannesu, duda ta san darajar Murjanatu ta ci, sai ta ji dadin abin , domun a duniyarta masu sakata ko hannata basu da yawa, kalilan ne suke tsawatar mata dan lafiyarta ko ci gabanta a rayuwa
A hankali ta ce" Tashi mu je mu yi girkin da kika yi min alkawarin zamuna shiga kicin baba muna yi Auta"

Murjanatu ta tashin suka yi cen baban kicin din gidan, domin idan suka ci gaba da zaman babu dan abin tabawa baki mai dan galmi galmi yayansu ya kwashe gwara su karra gaba
Sun cika dare a cen wajen ma'aikatan, har aka kai abincin bangaren aka dawo cikin gagawa aka kuma hada wani hadin na musaman wadda yanzun babar kicin din ce da kanta ta dauka tana turawa bayan ta sake kula da tsaftar komai ta tafi bayan ta fada masu cewa su yi su koma inji Kan Giwa

Cikin gagawa suka gama suka dauki abubuwan da suka yi da kansu suka nufi bangaren Kan Giwa

A lokacin da suka shigo suka ga wani cenji, cenjin kuwa shine Matansa ne kadai zaune saman table kowace na alamun tana cin abinci aman yannayinsu zai nuna maka kamar a cikin yar damuwa suke, haka kuma babu mai yiwa yar uwarta magana, sai dayan gefen kuwa chef din kicin din ce tsaye a kofar dakin Kan Giwa ga dukkan alamu jira take yi

Itama NURIYAH da kallo ta bita kafin suke shigewa dakinsu, Murjanatu ko gaishe da matan na yayanta bata yi ba, itama da ta gaishe sun basu amsa mata ba dan haka ta bi Murjanatun suka shige ciki

Shafa'i da wuturi suka yi bayan sun gama wanka , Murjanatu ta dora waya da iyayenta , ita kuma ta kwonta tana jan carbi da tunanin rayuwa har barci barawo ya kwasheta bayan sun gaisa da Hajia

Kamar yadda ta saba yauma sai da ta tashi ta yi aikace aikacenta tsaf sannan ta koma ta kwonta dan mararta dake dan sukanta , tana jin fitar Murjanatu bayan ta tabata da tunanin ko barci take , a haka har barcin ya dauketa domin idan tana al'ada ita tamkar kasa sai barci


Cen cikin barcinta take ji Murjanatu na tayar da ita da yannayi na farin ciki a cikin muryarta

A hankali ta buda idannuwanta tana adu'ar tashi a barci a cikin zuciyarta tana kallon Murjanatu

Murjanatu ta ce" Idan na fada maki sai kin daka tsalen farin ciki, wayo Allahna farin ciki , tashi tashi albishirinki, albishirinki"

Kafafuwanta ta sauko da dogon wando mai santsi na barci a jikinta da rigarsa wace zata kai gwuiwarta aman itama mai santsin ce dan kuwa sai lafewa take a jikinta , sai hula wace ta yau mai roba ce a bakin bata saki kan nata ba , da abin barci barci tana fadin" Goro fari kal kal kal " ga mararta na dan mintsininta tana dan lumshe manyan idannuwanta dan ta rike zafin ciwon

Murjanatu ta ringa juyi tana kama hannunta ta ce" Mike mana wai, karatu ne, karatu yaya ya saka a ringa koya maki, na boko sannan na arabi yace mu ringa yi ni da ke da malamina na arabi"

Da farko wani iri maganar ta zo mata, sai kuma ta shige ta daki kirjinta, bata ankara ba maganar ta ratsa ilahirin jikinta, wani irin emotion ya sake damkarta, a hankali ta furta" KARATU? KARATU DAI KARATU IRIN NA BOKO AUTA?"

Murjanatu ta gyada mata kai tana ta farin cikin abin, domin yau ita da shi suka karya, sunna gamawa aka sheda masa bakon ya zo, baban malami ne da ake ji da shi wanda ya kware yake kuma da hakurin koyarwa ya shigo, a nan suka gaisa da mutunta junna da KAN GIWA , cikin nutsuwa ya dan kwatanta masa cewar yarinyar bata iya komai da ya shafi hakan ba, a bata dukkan kulawar da ya dace da ita......, A nan ne ta fahimci cewa malami ne aka daukarwa Nuriyar, ta ringa ihun murna yana kallonta yana Murmushi da mamakin shakuwarsu, shine yake fada mata na islamiyar sai su ringa yi tare da Ustazzzzzzzzzzzzzzzzz,

NURIYAH ta saki hannayen Murjanatu da sauri ta tare gaban goshinta da hannayenta bibiyu sai kuma ta saki ta mike itama ta daka tsale hadi da saka ihu irin na Murjanatun suka rukunkume junna lokaci daya ta fashe da wani irin kuka mai karfi domin ta kasa rike hakan ta kasa hanna kanta hakan, gashi kofar a bude suka barta hakan na nufin hayaniyar zata kai falo inda su KAN GIWA ke zaune

Da sauri ya mike da jalabiyar dake jikinsa mai gajeran hannu ya nufi dakin

Yana zuwa hannunsa ya saka ya shiga da niyar yin magana sai dai ya yi gummm da bakinsa ya ja ya tsaya kaan kafafuwansa yana kallonsu

Kuka take yo har fuskarta ta dauki ja da hannunta a jimke cikin na Murjanatu tana fadin" Karatu ni? Ilimi ni? Korar jahilci ni? Auta ni Nuriyah marar galihu? Ni da ake kyamata a wajen NEMAN NA KAINA? Ni da na rasa dan samun garin da zamu ahwa a bakinmu ni da kakata? Auta me zan ce da gidanku? Me zan ce da Hajia da ta yarda na shigo aiki a matsayin wace bata da takardar da ta dace sannan ta bani danar rayuwa ba a tsangwame ba? Me zan ce da ke da yah Rislan da kuke hira da ni sakewa da ni har kike kirana kawarki yah Rislan kuwa ya kireni kanwarsa?, Me Me zan ce da Mai gidan nan da zai bani damar korar jahilci? Da me zan iya saka maku a duniya ni kuwa? Ya Allah......"
Ta sake kokarin fashewa da wani kukan, hakan ya sa da Sauri Murjanatu ta ringa dago fuskarta tana fadin"



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
3?? 6??



Ta sake fashewa da wani kukan hakan ya sa da sauri Murjanatu ta ringa dago fuskarta tana fadin" Nuriyah ya isa haka mana, wannan kukan ai ya yi yawa Nuriyah, da kike ta zanen me zaki ce da wane ko wane ba mune wa'inda zaki godewa ba, ALLAH ne zaki godewa domin shine ya haliceki yake kuma tsara maki tsarin rayuwarki, ni da kaina na samu surprise mai girman gaske, sai dai sanin da na yi cewa shi din mai son yaki da jahilci ne, shi din mai taimako ne sai mamakina ya watse na ringa yi masa adu'ar gamawa da duniya lafiya........"

Da sauri Nuriyah ta cafe maganar da fadin" Allah ya sa ya gama da duniya Lafiya, Allah ya rufa masa asiri duniya da kiyama, Allah ya kare shi da sharin dukan abin ki, Allah ya bashi y'aya masu jin kan iyaye wa'inda zasu so shi su yi masa biyaya a lokacin da yake raye sannan su dore da yi masa adu'a a bayan mutuwarsa, Ku, Kuma Allah ya faranta maku daga nan duniya har kiyama, Auta kuma zan tata yi maku adu'a daga ku har wanda ya min sanadiyar kasancewa a gidan nan ......."

Idannuwansa ya dan kifta daga tsayen da yake a hankali ya jimke hannun nasa mai ciwo kafin ya idasa jimke shi gaba dayansa tamkar ba wani ciwo a jikin hannun ya juya ya nufi wajen Malamin ya masa alamu da sunna zuwa sannan ya shige cikin dakinsa da bai san cewa matansa duka biyu sunna ciki ba a lokacin da ya yi bakon

Mamaki ne da wasu kalamai biyu a saman harshensa na wannan yarinya, wai daga kirawo mata malami tsal shine duka wannan kuka da farin ciki har haka?, Shi ya yi mata haka ne dan kawai a jiyan ya yi mamakin cewa mutun mai shekaru kamarta har haka ba ilimi? Ilimin adini da na boko a rayuwar nan da ta ci gaba? Ilimi ai shine hasken rayuwa da bayan rayuwar gaba daya, shi ya yi haka ne dan ya daidaita lamarin zamanta da kanwarsa, ba zai so ko da wasa ba ace zaman da kanwarsa ke yi da ita ta karu da wani abu na rashin dadi a nan gidan duniya ba, kowa ya san aboki yana da baban karfi a rayuwar abokinsa, tana iya tambayarta shawararta a kan komai na rayuwa, ba zai so ta samu gurguwar shawara daga yarinyar ba, tunda Auta ta nace ita wannan din itace kawarta babu yadda zasu yi su hanna, domin ya kula yarinyar nada fada a ji a duniyar hajia kaka , shi yasa ya saka aka samo malamin da zai iya koyar da ita, ya fada cewa a samo mai hakuri sannan mai zafi, wanda zai jure ya kuma tankwasata da karfi da yaji kan ta yi biyaya ta koya, shima ya kudurta ne zai tsaya idan har ta nuna ba zata iya yin karatu ba ya bata abinda ta nema na tashin hankali, dan ya tabata irin sangartar nan ce ta gaban kakanni yaro ya nuna baya so a taimaka masa ya ki yin karatu!

Sai dai a yanzu irin kukan da ya ji ya kuna hango tana yi da dukkan gaskiyarta na farin cikin samun yin karatu a yau sai ya tsaye masa a kahon zuciyarsa, irin yadda ta yi furucin dake nuni cewa itama ashe tana da daraja ya tsaye masa a ransa, a gangaro kan adu'o'in da ta zuba masa harda maganar ya gama da duniya lafiya sannan ya samu y'aya masu yi masa sai ya samu mamaki mai tsananin gaske da tunani mai girman gaske

A hankali ya nemi zama saman kujera yana tunanin ashe akoy wanda zai iya yi masa irin adu'ar nan bayan kakarsa, mahaifinsa, matar mahaifinsa, kannensa a duniya ne?
A saman lebensa ya furta kalmar " *Y'AYA* " Da baban baki yana neman zama, murmushi na subucewa a saman fuskarsa wanda ya same shi ne sanadiyar hangen yan yara da irin tafiyarsu ta jinjiri mai shekara daya zuwa biyu Idan yana cikin koshin lafiya,
Bai taba irin wannan tunanin a kankin kansa ba sai yau

A hankali ya maida dubansa wajen da Nadia cike da yannayi na damuwa a saman fuskarta ta furta" Hubby" tana kallonsa

Kallo daya ya mata ya dauke dubansa ya maida kan Djamilarth, itama tana tsayen ne fuskarta na nuni da damuwa a kanta a kwonce

A hankali Nadiya ta karaso ta rungume shi ta baya ta dora kanta saman bayansa ta rike kirjinsa da hannayenta biyu tana rintse idannuwanta
Gjamilarma ta karaso da gagawa ta gefensa ta rungume shi a jikinta ya kasance sunna neman yi masa kawanya gaba da gefensa

A raunane Nadia ta ce" Me yake faruwa ne? Me yake damunka ne? Gaba daya tamkar ba kai ba, ashe baka da lafiya ban sani ba? Me ya samu hannunka ne?"

Djamilart ta amshe da fadin" Me yasa ka daina zama cin abinci tare da mu ne? Me yasa ka bada umarnin kar mu fita ko nan da nan ne? Me yasa ka daina nemanmu a saman shinfidarka ne?"

Nadia ta ce" ko Elizabeth ce ta dawo take neman daukeka gaba daya? Ko mun yi maka laifi ne? Ba haka ka saba yi mana ba KAN GIWA "

Idannuwansa dake lumshe yana jin tukukin abinda ke damun zuciyarsa game da zamantakewarsa da iyalin nasa ya samu a hankali ya sabuke hannayensu daga jikinsa ya karasa saman kujera ya zauna yana kallinsu

A hankali ya ce" Baku min laifi ba, gaba dayanku....asalima nine na fara bada hanyar baraka a gareku"

Ya furzar da iska mai zafi a bakinsa yana sake fuskantarsu a kausashe ya ci gaba da fadin" Mina rayuwa ce wace ita ba ta musulunci ba, ita ba ta nasarun ba, domin zan iya cewa ko ta nasaru ta fi tamu tsari"

Jajayen idannuwansa ya sake dorawa a saman kansu yana gannin yadda suke ta wara idannuwansu a kansa na son fahimtarsa da mamakinsa ne ko meye oho ya dora da fadin" Aurenku na yi ba zaman banza muke yi da ku ba, ba sai na koya maku menene zaman aure ba, na baku damar ku koyi zama da ni ko yayane......mu zauna mu fuskanci junna yadda ya dace,"

Ya shiga dan motsa kujerar da dan bacin ran dake hawa kan fuskarsa ya ce" Zamu zauna ne da irin halin da kuka zabarwa kanku, idan kun gane kun sauko mu gyara baki daya, idan kun kasa ganewa kunna sama mu je a haka.............. Abinda na sani shine dan samun ladan aure da rayuwa irin yadda na ga wasu na yi ina iya fitar da biyu na dauko hudu......."

Daga haka ya mike ya bar masu dakin ya tafiyarsa cen baya ya barsu kowace bakinta ya mutu kamar an dantsa mata ky a lebe ta kasa magana, maganarsa ta zo wata iri ta girmi tunaninsu baki daya

________________________________________


Sannu a hankali ake tafiyar da koyarwarta, kwonci tashi har an dauki sati uku tana daukan karatu na arabi da na boko, wanda ta matukar bayar da dukkan wata nutsuwa, hankali, dukkan abinda take ta zubar ta bada hankali a kai
Takan tashi da sasafe ta yi aikinta da ta dorawa kanta, ta gyara wajen daukan karatunsu ta zauna ta shiga bitar ABCD din da ta gama shanyewa da dukkan abinda yake ta fara fahimta, Malamin kan zo ne su dauki awa biyu sunna daukan darasi, da an gama ya tafi sai ta je su karya da Murjanatu, idan sun gama kuma su koma cen bayan gida inda suke zaman hutunsu, da karatu, da hira
Hakan ya rage yawan haduwarsu da mai gidan gaba daya, domin wani lokacin har sai malaminsu na islamiya ya zo ya basu nasa darasin ya tafi sannan suke komawa, shi kuwa mai gidan a yanzu ya zama wani irin hamshakin marar zama da yawa, domin damar da ya ce zai ba matansa ya basun, yana masu gashi ne ba da zagi, duka, ko hanna abinci ba, yana masu gashi ne cikin ruwan sanyi, gashi dai babu abinda suka nema suka rasa aman rashin samun sake irin na da na matukar damunsu, haka kuma abinda suke tunanin ko dan shi zai zauna da su ya dauka ya watsar tamkar bashi ba, wannan dalilin ya sa suka adabi zaman lafiyarsu da tunanin shin Elizabeth ta dawo rayuwar mijinsu ne dan ta raba su wannan karron ko me? Ko kuma wata ya samu wace ta dame Elyzabeth ta shanye? Aman kuwa idan haka ne da sun shiga uku, domin ko Elyzabeth din da wajewa suka yi da ita , wannan din wacece kuma? Yaya zasu sameta su dora magana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login