Showing 33001 words to 36000 words out of 124070 words

Chapter 12 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

342

su dukansu biyun fatansu ya amince cewar Nuriyah ta koma bangarenta , watau dakinta ta yi rayuwarta har wace ta daure mata ta dawo, domin su a kankin kansu daga ita Nadiar har Djamilar basu taba jin wani abu a kan mu'amalarsa da matan da yake yi jefi jefi irin Tsoron zaman yarinyar a bangarensu ba, haka kawai aiki irin na shedan ke son rikita su a kan maganarta bayan su din sun gama gane cewa mijinsu dole sai ya samu karri sama da su shi yasa suka watsar da mu'amalarsa da izabel a kwondon shara suka gwamace kishiyar waje fiye da ta gida dan ko ba komai sun fita daraja su kam kuma du iskancinta bata isa ta zama mata a wajen only one Kan giwarsu ba, su biyu ne suka ci zaben daga su kuma ba karri

Tun daga kasa har sama ya bi jikin nadiya da kallo , cikin shiga take na wando sakake sosai har kasa budade ne sosai wanda iya kugunta ya rike, sai rigarsa wace iya mamanta ta rufe hakan ya sa cibiyarta da shafafen cikinta ke waje harda dan kunnen dake cikin cibiyar nata a bayane wanda ya dan zirro kadan har kusan wandon dake jikinta

A hankali ya sake maida dubansa kan Djameelarth itama yana kallon shigarta, ita kuma tana sanye ne da sket da riga na atampa, wa'inda suka amshi jikinta ta nada wani katon dauri a saman kanta wanda baban mamakinsa da kuma abinda yake son ganewa zanni nawa ne ya mata daurin nan, sai ya maida kan Baby dake tsaye watau Murja karama auta ita kuma ta yane kanta da dan kwali tana rike da tsatsonta tana jira ta ji me zai ce, domin ita dai a gabanta ai kaka ta ce su zauna a nan kau? Idan kuwa ya kori Nuriyah saboda wadinnan ababen zata bita ne su zauna domin ita ba zata bar yar mutane ita daya a cen ba, sai kuma ya juyo wajen da Nuriyarr ke tsayen itama kanta a kasa har kamar ta dan karra matsawa ta rakube a dalilin shigowar tasa

Tun daga kasa har sama itama ya bita da kallo a lokacin da ya samu kansa da sake bin cinyoyinda dake cikin doguwar riga da kallo yana mamakin wannan yarinya ko me yasa take anfani da cikon nan irin na kanti da ake siyarwa? Mata kam wani sa'in yakan rasa me yake damun wasunsu, to wanann gabjejen abin ai sai ya hannaka zama da kyau, ita zata iya daukan wannan abin ne? Hmmm yarintahhh zalla
Sai kuma ya tabe bakinsa da ya sauke kan hijab din dake kanta madaidaici ya juya ya nufi dakinsa ba tare da yace ku ci kanku ba



A tare suka raka shi da ido daga su nadiar har Murjanatu baki da hanci bude, domin a tunaninsu su dukansu ai ihu ya dace ya dan masu ko yayane ya kuma fada masu su fita a idannuwansa ya rufe baya son shirme, sai kawai ya tafi ya barsu bayan fada ne ake shirin yi?

Djamilar ta taba hannunta tana kallonta ta ce






*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
2?? 8??




Djamilar ta taba hannunta tana kallon Murjanatu ta ce" u see, ke baki san komai ba, ke yarinya ce karama, baki iya komai ba, kin ga bamu da matsala da ke, ke kanwar wanda ya auremu ce, idan kyakyawar mu'amala ba zata shiga tsakaninmu da ke ba bama so ki zamto abokiyar hamayarmu domin komai na iya faruwa ciki.......mun gama shawara da ni da Nadia cewar mu biyun mun isa, bamu hanna masa kula wasu a waje ba dan yana da damar hakan, aman wannan yarinyar da ban san a ina aka samo bahaushiya mai hausa da kuma kamaninta ba ba zata zauna mana a bangare ba koda na second daya ne, ta tafi kawai, wai acema du fadin palace din nan sai a nan zaku zauna?"

Murjanatu ta hadiye jin haushin da ta kumsa na yayanta gannin bai yiwaa wadinnan mutanen magana ba da mamaki tana kallonta ta ce" Kina nufin, kun gama yankewa kanku hukunci ne a zamantakewarku da shi cewa yana iya bin wasu bayanku a matsayin da ma muharamansa ba?"

Kai ta gyada cike da bata tabacin hakan take

Murjanatu ta tafa hannu tana fadin" lalle yau na sake yarda cewa an tafka asara mai girman gaske ta lokaci da dukiya wajen ajiye abinda ba shi ba, ba zan ce da ku komai ba a kan d?cision dinku domin da hakoranku na ganku, abinda zan fada shine in sha Allah ba dai ya ci gaba da abinda kuka zabar masa ba , Allah kuma zai bashi mai sonsa mai kishinsa wace zata guji ya mutu ya fada wuta sanadiyar aikata alfasha bi izinillah, ku kuma zaku girba kuma daidai da shukarku, zama kuwa daram a bangaren nan sai na ga wace zata hanna!"

Juyawa ta yi ta damki hannun Nuriyah dake kallonta da mamaki tana tunanin da itama ta iya fada har haka

Ido Nuriyar ta zarro gannin ta jata ta nufi wajen dakunnan tana bankadawa tana lekawa sai ta janyo ta rufo ga dukkan alamu tana son bambance nasu da wa'inda ba mutun a ciki ne

Daga inda suke sai ya zamto kururuwarsu ce ke tashi, ita ibo dama ba zata yi fadan gigayar jiki ba ana zaman lafiya, bale a je kan ba indiya da bata tashi da wannan wasan ba sam, sai suke ta kyruruwa irin daidai wace suka fi kwarewa a kai sunna biye da su da kokarin dakatar da su bama kamar idan Nuriyah ta juya yadda ababen bayanta ke rawa kamar tana luluka masu ashar ne da su da gangan

Sake budewa ya yi ya fito da shiga irin ta riga da wando dogo, ita rigar mai dogon hannu ce a balla boturan cen jiki na hannayen ne yake dan kokarin balawa aman ya kasa

Wajen da Murjanatu ta nufa zasu shige dakin da ta gama yarda cewa nanne wanda suke iya zama ya nufa yana fadin" Auta bala min"

Da sauri Nuriyah ta koma gefen daya hakan ya sa mazaunen sosai suka juya a cikin doguwar rigar irin juyawa mai ma'anar nan wace ta saka idannuwansa suka kai wajen ba tare da ya aikesu ko ya san zasu iya kallon nan din ba

Dan kasakai ya yi cike da mamakin to dama abin cikon ana siyar da mai ruwa ruwa wanda zai ringa abu kamar na gaske? Kai yarinyar nan du inda taa fito ta yi rashin ji sosai

Murjanatu ta kama hannun rigar tasa ta bala masa boturan nan da kyau bayan ta juyar da shi yadda ake masa, sannan ya sake juyawa yana kallon yan matan matayensaa dake tsaye cirko cirko su dinma shi din suke kallo ya bata dayan hannun shima yana dan gyaran murya kadan dan sake sakin muryarsa sakamakon ruwa mai sanyi sosai da ya sha

Tana gama bala masa ta janye hannun Nuriyah suka shige cikin dakin ta maro kofar da karfi sannan ta saki hannun Nuriyah

Ido ya zubawa kofar dan harga Allah marowar kamar ta kwala masa dutse a kansa ya ji kafin ya dan rintse idannuwan nasa ya juya ya fice a falon gaba daya

Nan fa suka dora nasu meeting din na cewa lalle lalle wannan abu ba zai yiwu ba, su din matansa ne sunna da daraja fiye da wannan sangartaciyar kanwar tasa
Su mamakinsuma da ta mako masa kofa aman dan rashin adalci bai ce mata komai ba
Duda sun kula kamar yana da wajen zuwa mai mahinmancin da ya sa bai tsaya kula su gaba dayansu ba, aman kuma yana da wani hali irin na yankan tsagwaron wulakanci dake iya raya masa cewar ya yi watsi da shirmensu, shi yasa suka kasu suka rabu suka tsaya a kaan matsayar lalle lalle zasu yi jiran dawowarsa idan ya gama dukkan abinda zai yi su sake gabatar da muradinsu na a fitar masu da yaren nan a bangare, ko ba komai yana da dabi'ar dane mace a falo fa, shin yaya zai yi idan hakan ta raya masa ga su Murja a gefe? A yadda yakr kakau da tarbiyar yarinyar yadda yake hannata aikata komai sun tabata ba zai so ta ganshi a yannayi irin wannan ba....da wannan suka rufe suka tashi suka koma kowace ta shiga lamarin gabanta na abinda zai karrata, ba tare da sun kula da harkar girkin abincin da zai dawo ya tarar ba, sun dai san idan lokacin hawa table din ya yi za'a hau koda ba'a so ne, idan yana ra'ayi zai ci, inma baya yi zai bari, su din kansu basu riga sun daidaita zama irin na haka da shi ba,, sai yanzun dai koma meye za'a yi



A sanyaye Murjanatu ta karasa kusa da kujerar da Nuriyah ke zaune tana maida numfashi ta zauna itama ta sauke dubanta kasa zuciyarta cike da daci, tana jin daci har cen kasan ranta , tana tunanin shin da ace mahaifiyarsu na raye zata kyale kan giwa aikata irin haka kuwa? Zata bari matansa su saka shi a hali irin wannan kuwa? Shin yaya zata yi ta samo mafita wa yayanta? Yaya zata yi ta gyara lamarin yayanta?

"Na shiga ukunna, ta yiwu kafin Hajia ta dawo ya koreni, Innalilahi wa inna ilaihi raj'une me yasa matansa basa so na zauna ne? Ni kam Sis da kin barni na koma cen din sai na labe har Hajia ta dawo sai na fitowata hakan zai sa a manta da ni kwata kwata ba wanda zai kore ni, auta idan na fita daga nan ina kuma zan dosa......?"
Maganar take yi a harhade tana dan jimke cinyoyinta dake nuni da abin daga zuciyarta yake, subutar baki ne ta yi tana fada mata tsoronta firgicinta da kuma muradinta na kasancewa a nan din , watau a cikin gidan hakan na nuni da tana tsoron komawa nata iyayen
Wannan sai ya dan bata mamaki, ita dai ta san wanda ya kawota gidan nan ya ce ne ita din yar uwarsa ce watau Sabiu daya daga cikin ma'aikatan gidan wanda ya yi sanadiyar kasancewarta a gidan

A sanyaye ta ce" Nuriyah?"

A dan firgice ta dubeta, sai kuma ta ankara da abubuwan da ta fada din
Da sauri ta mike ta shiga yayumar abinda aka shinfida saman gadon tana fadin" Bara na tsaftace kayan nan dan ba zamu kwonta saman su ba ko?"

Murjanatu bata ce da ita komai ba tana dai kallonta har ta shige bayin ta karasa bangaren da washing machine take ta hada komai ta saka ta kunna sannan ta ci gaba da tsaftace bayin duda ba wani dati ta yi ba sai kura dake nuni na ba'a anfani da ita

Sai da ta gama tsaf sannan ta sake fitowa ta kuma tarar da Murjanatu zaune an kusa yin kiran sallar magariba

Murjanatu ta sake gyara zamanta ta ce" Zo ki zauna"

Nuriyah sai ta samu kanta da tsayawa tana kikifta ido tana kallon Murjanatu, ita dai ta dan girmi Murjanatun aman a yadda ta yi maganat a dan dake sai ta ji shayinta na neman kamata, jinnin dake yawo a jikin yarinyar irin na yayarta ke sakata rikicewa lokuta da dama ta dauko hali irin na riginar yayanta

A hankali ta zauna tana fuskantarta ta ce" Baki ga lokacin sallah na gabatowa ba gashi bamu kawo suturunmu nan din ba?"

Murjanatu ta ce" Kin manta na tashi da kwana daya da bako kika tashi da shi? Ko ke a kwana daya yake dauke maki?"

Yawu ta hadiye tana lumshe manyan idannuwanta tana tunanin yadda zasu kwashe

Murjanatu ta dan muzguta a hankali ta ce" Ki bani labarinku mana......?"

Gabanta sai da ya kwonci kwonci ya fadi, hankalinta ya nemi tashi
Labarin nata ta ringa maimaitawa a samab lebenta tamkar wace take son ta sake gane me yaren yake nufi ba

A hankali Murjanatu ta kama hannayenta tana kallonta ta ce" Tunda na zo gidan nan nake son fahimtar da wace takarda kika shigo a matsayin mai aiki? Sai da grandma ke fadan cewa lalalalaalalala baki karanci karatun girki ba, ita dai yaron nan Sabi'u ta yarda da tarbiyarsa ya nemi ya kawo yar aiki ta kuma amince, sai na ringa tunanin to yaya aka yi haka? Nuriyah tl me, ki dan bani labarinki mana idan ban takuraki ba?"

Nuriyah ta lumshe idannuwanta hawaye na neman kwace mata, a hankali ta ringa shanyewa, sai dai abin na neman fin karfinta, da sauri ta sake sada kanta tana ambaton sunnayen Allah a kasan zuciyarta kafin ta fuskanci Murjanatu cike da rauni ta ce" Da ace zan samu, da zan samu da kin bar maganar son sannin ko ni wacece, domin ina tsoron sannin hakanan ya haifar maki da tsanata fiye da kima dan ina mai tabatar maki cewa zaki kyamaceni fiye da tunaninki"

Da mamaki Murjanatu ke kallonta har bata san lokacin da ta furta cewa" Subahannalah, kisan kai kika yi ko shirka da har kike fadin irin haka?"

Da sauri Nuriyah ke girgiza kanta, sai kuma ta sada kanta saman cinyarta tana mai shashekar kukan da ya kwace mata

Jikin Murjanatu ne ya yi sanyi a hankali ta shiga shafa bayanta tana fadin" its ok Nuriyahrtahhhh, dainan kukan haka na bari na bar tambayarki labarinki kin ji?"

Da sauri Nuriyah ta dago tana sake yin shashekar kuka ta ce" Ba zan daina ba Murjanatu, zan fada maki domin kema kin kasance mai min adalci a rayuwa, bakya kyamatata kamar yadda hajiya ta amshe ni take kuma kamanta adalcin rayuwa a gareni bayan bata san takamaiman wacece ni ba, Kin ga ni ba jinnin Sabi'u bace, shima yana daya daga cikin mutanen da suka taimakeni suka yi min adalci a rayuea suka bani damar rayuwa tamkar kowa ta hanyar nuna min rashin karatuna ba zai zamto ila a rayuwata ba tunda har inada hardar alkur'ani daidai gwargwado kuma ina da hadisai zan ci gaba da neman ilimi a nutse aman tunda ina da zuciyar nema na nema dan na rayu......Auta a rayuwata ni ban rayu da kankara hakori a abin hannun kowa ba, ban rayu da jiran sai an bani ba, marikiyata uwata kuma kakata wace ta min adalci a rayuwa ta rikeni har ta koma ga ubangijinta wace ta fadan cewa Mahaifina shine mutumen dake korata tamkar kare baya so na rabe shin nan ta koyan nema, ta fada min cewa duniya tun kafin ya zo yanzu, watau tun a da idan kana son wulakanci to fa ka dogara da abin hannun mutun .....ta kare fada min cewa ko iyayen da suka haifeka suka kawoka duniya daidaikunne zasu ci gaba da yiwa yannayinka uzuri da zarar ka yi girman da kake iya cinye kwano daya, ta fadan cewa sana'a ba laifi bane, da sata gwara sana'a da zubar da mutunci gwara sana'a, ta ce min Nuriyah ki tashi ki *NEMI NA KANKI* dan duniya ta dawo ko zaman lafiya baka samu da mutane sai kana dan lasa masu, ba wai maganar rashin kauna bace ko wani abin, lamarin ne ya zo a haka koda ba'a sonka ba za'a kasheka ba, kuma ana iya mu'amala da kai, aman ko a gidanku mai shi shine baba koda kuwa shine auta....., Auta ina ta ce da ni riba komai kankantarta itace alkhairina, sannan na nema dan ciyar da cikina ba dan na tara na yi matashin kai ba...........bara ki ji labarina a iya abinda na sani gaskiyar wacece ni...........SUNANA *NURIYAH* mahaifina kam takamaiman wanene din ban fahimta ba tukunnan, na taso a hannun Inna Baraka............................" A nan Ta kwashe dukan labarinta ta sanarwa Murjanatu, wace ta yi wani irin kasakai take kallonta cike da mamaki da al'ajabi har ta dire aya

Kukan da ta fashe da shi ya saka Murjanatu mikewa da sauri ta rungumeta a jikinta tana rintse idannuwanta itama muryarta na rawa ta ce" Ki yi hakuri Nuriyah, kowani bawa na fuskantar jarabawar rayuwa, aman lamarin Lawali da inna tace shine mahaifinki na bani mamaki, shin da gaske haka ne? In haka ne ganganci ne ko rashin jin Tsoron Allah ya yi tasiri a duniyar Lawali har ya aikata haka? Subahannalah Astagfrullah wa atubu ilaikah , ya salam........."

Kanta ta dago tana kallon Murjanatu da mamaki ta ce" Baki ji ba? Marikiyata cutar HIV ce fa ta kasheta, Murjanatu wannan dalilin ya sa idan aka ji ake guduna"

Tausayinta ya sake cikata, a hankali ta sake rungumeta a jikinta kafin ta saketa ta zauna tana fuskantarta ta ce" Cutar HIV ko ke kike dauke da ita Nuriyah an samu ci gaban da za'a zauna da ke a rayu da ke cikin mu'amala tsaftataciya, ke bara na kare maki ki yi aure ki hayayafa har sia wa'adinki ya cika zaki bar duniya, wa'inda suka jahilci abim ne suke ci gaba da jahiltarsa, ba zasu taba daina jahiltarsa ba ........now stop crying, na matsa maki har na tuna maki rayuwarki ko? Allah ya jikan Mama idan kuma tana raye Allah ya bayana mana ita, Allah ya bayana mana ahalinta, idan kuwa babu rabon ganninsu Allah ya sada mu a aljanah, aman ba zan kuma barinki ki yi kukan kadaici ba ko na rashin gata, Allah ne gatanki....mune ahalinki, ko aure kika samu in sha Allahu mune danginki ba zaki yi maraici ba!"

Abin ya yi mata zuwan ba zata hakan ya sa take YIWA Murjanatu kallo mai girman gaske har zuwa lokacin da wayar dakin ta dauki kuka

Murjanatun ce ta mike tana fadin" Nadia da Djamilarth take ko wa sunna sak gayanan aman su ibo sun karkata shi walahi idan balaki suke nema zasu samu da ni suke maganar!"

Tana dagawa da niyar a kwasa ta daga sai dai muryar da ta ji da umarnin da ya bada ya kashe ya sakata hadiyar yawu ta cewa Nuriyaj tana zuwa

Ita dai da ido ta bita tana tunanin Allah ya sa kar a yi wata rigima a kanta a gidan, Allah ya sa su ganewa junna a samu sasanci ta koma cen ita ta fi sakewama

Tunda ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login